🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒
*******Bayan wata 8******Khairi na kwance a kan gadon umma kafafuwanta sun kumbura sosai, ba abun da mutum ke gani se rusheshen cikin ta da yayi rumfa. Ga ta fingi fingi se kwalelen ciki kamar na yan biyu, cikin yasa ta kara lalacewa da rama saboda laulayi be zo mata da sauki ba, Ga rashin umar da ya addabi zuciyar ta. Kusan kullum se tayi kuka dan tana missing dinshi a kullum.
Ga rashin cin abinci . Duk sati se Alh yasa an kawo duk wani nau'in abun dadi ko na marmari kala kala. Wasu abubuwan ma ba sanin su sukayi ba se de su umma su ci na ci su kyautar da na kyautar wa.
Kullum da safe se Alh ibrahim ya kira yaji ya jikin khairi da dare ma haka. Kowa lallabata yake kamar kwaiUmma ta shigo dakin tare da zama a gefen gado ganin har a lokacin khairi na kwance.
"Lafiya har yanzu baki fito parlor ba, karfe 11 fa yanzu"Khairi ta dan yamutsa fuska sannan tace
"Ji nayi bayana ya rike shiyasa na kasa tashi amma yana saki zaki ganni"Umma ta danyi dimm sannan tace "Allah ya sawake"sannan ta fito daga dakin, tana fitowa ta koma dakinta ta fara hada akwatin haihuwa, ta sa duk abun da ake bukata a jaka sannan ta rufe ta ajye, tasan a cikin yau ko gobe ko jibi khairi zata iya haihuwa depending on severity na labour da take jikinta yayi danye dan haka umma tasan lokaci yayi. Adduan umma shine Allah ubangiji ya kawo mata da sauki ya raba su lafiya.
Umma ta koma ta hado ma khairi tea, tana shiga dakin ta tarar da ita ta hada gumi tana ta bata rai saboda ciwo.
"Yaya de khairi? Ciwon ne?"
Umma ta tambaya"Umma ciwo, bayana, mara ta, cinyoyina duk sun rike"
Umma ta bata shayin saboda tasan dole zata bukaci karfi kafin abun ya galabaitar da ita. Da kyar khairi ta iya shan rabin cup din.
Haka ta cigaba da fama da pains, ya zo ya koma, yayi karfi yayi sauki har kusan karfe 5 na yamma. Da umma taga abun ya fara tsanani ta kira Abdullah ya kaisu asbiti a mota.Suna zuwa asbiti ko awa 2 basu cika ba khairi ta suntulo yarinyar ta mace. Bouncing pretty little cute princess. Abba da umma ne kawai suka san khairi na labour babu wanda aka fadawa se da ta sauka. Ko Alh ibrahim baa fadawa ba saboda sun san yanzu ze birkice ya daga hankalin sa. Tun da khairi tayi wata 7 yace khairi ta tafi America ta haihu a can amma taki yarda, tafi son ta haihu a gida kusa da iyaye da yan uwa.
Baby tabarkallah katuwa ce don se da ta kara khairi gurin haihuwa akayi mata stiches.
Umma ta shigo labor room cike da farin ciki ta rungume khairi tana cewa
"Allah yayi miki Albarka ummulkhair, Allah ya albarkaci zuriar ku"Khairi da ta fita daga hayyacin ta jike jagaf da gumi kamar wadda aka ciro daga cikin ruwa tace
"Ameen umma, kema Allah ya saka miki da mafificin Alkhairi irin wannan wahalar da kika sha muka zo duniya. Tabbas se mutum ya haihu yake kara sanin darajar uwa"
Umma ta danyi murmushi
"Ummulkhairi kenan, Amma kinyi kokari nayi tunanin zan dinga jiyo ihun ki daga waje""Umma dauriya kawai nayi amma ni kadai nasan me naji"
Daga haka se ga nurse ta fito da jaririyar an gama gyara ta, ta miko wa umma.
Umma ta karba yar ta tsura mata ido, bayan minti kadan se ga hawaye na zuba daga idon ta. Ko baa fada ba umar ta tuno.
Khairi na ganin umma ta fara kuka ita ma ta fara, ta kasa karbar jaririyar da umma ke miko mata."Karbe ta khairi, karbi kiga abun da kika haifa"
Khairi ta kasa karbar yarinyar, ta kasa motsi ma saboda a lokacin jin tayi wani irin yanayi. Ba abun da take tunawa se Umar dinta, mijinta abun son ta.
Se da ta shafe kusan munti biyar bata motsa ba, da umma taga haka se ta saka mata jaririyar a jikin ta.
YOU ARE READING
Sarkakiya
RomanceLabarin tsantsar soyayya me cike da sarkakiya ce ta kullu a tsakanin su. Ummulkhair ta zamo Allura cikin ruwa wanda me rabo ne ze dauka. Shin wa zata zaba a cikin su? Boyayyen masoyi Abdulkareem wanda yayi dakon soyayyar ta na tsahon lokaci ko kuma...