Zumudi

163 10 1
                                    

🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒
"Wani labari naji yanzu a cikin gari, naji umma tace ranar friday za'a zo tambayar auren ki"

"Emm"
Answer da khairi ta bayar sannan ta kara gyara zaman da tayi a kan kujerar 1 seater

"Ban gane emm ba, you mean what I heard is true?
Umar ya fada fuskarsa da wani kwantaccen sadness a tattare da ita.

"Eh hakane"
Ta kara bada answer a takaice tana wani cin magani

Umar ya taso daga kan three seater da yake ya dawo 1 seater da ke kusa da ita

"Don't tell me Abdukareem ne?"
Shirun da khairi tayi ya bashi answer tambayar sa. Ji yayi idanun sa suna zafi, numfashin sa har sarkewa ya fara yi tsananin bakin ciki. Brain dinsa ya toshe har Baya iya tunani me kyau

Umar cikin daga murya yace
"How do you want me to prove how much i love you. my life revolves around you, duk wani jin dadin da zan ji a duniyar nan se de ya biyo bayan ki. Can't you see? cant you see how my heart bleeds for you"

Ita ma khairi cikin masifa tace
"My own heart beats for someone eles, kaima can't you see ne? Dan Allah dont make things difficult for me, dan Allah kayi hakuri ka bar wannan maganar"

duk da maganganun shi sun sa zuciyarta ta karaya, tausayin sa ta fara amma kuma bata son umar ya zame mata matsala tsakanin ta da Ak.

" na baka answer da kake son ji, zaka iya tafiya"
Khairi ta mike ta nufi hanyar kofa, yayi sauri ya mike cikin hanzari ya sha gaban ta wanda ya sa ta tsaya chak

Idanun sa suka ciko da hawaye ya sa hannun biyu ya riko nata

"Why do you hate me this much, meyasa baza ki bani chance ba. Wallahi my life is meaningless without you, saboda ke na samu passion for life, saboda ke nake son nayi living life to the fullest, i have become an entirely new person because of you, dan Allah ki janye maganar zuwa a tambayi auren ki. Bazan ce kar ki auri Abdulkareem ba amma ina so ki bani time din da zan nuna miki love dina, just few months and after that you can make your choice. Idan har a lokacin Abdulkareem kike so wallahi i promise to let you go"

Kwalla ce ta kubuce daga idon sa amma be damu ya share ba. he looked desperate, kallon khairi yake cikin ido da idon sa da yayi laushi, kallo me kashe jiki

A gaskiyan zahiri her heart skipped a beat da taga hawaye a idon sa, taji kalaman sa kuma. Ya bata tausayi matuka, amma tayi reassuring zuciyar ta cewar Yanzu ba lokacin nuna tausayi ko emotions bane saboda baza ta bashi false hope ba. Gwara tayi cutting duk wani lingering feelings da take ji game da shi ta tsaida energy da love dinta a kan Abdulkareem

Bata yi magana ba, illa zare hannun ta da tayi a hankali daga rukon ta da yayi, ta bi ta gefen sa ta fita daga parlour. Ta barshi tsaye lifeless kamar an daura masa dutse me nauyi a zuciya

Tana fitowa taci karo da Aminu wanda ya saki baki yana kallon ta saboda yaji duk abunda suka fada.
Aminu ya ja hannun ta zuuu se daki, ya zaunar sa ita a gefen gado sannan ya fara magana

"Me nake ji yanzu, umar son ki yake daman?

Khairi tayi rau rau da ido
"Dan Allah yaya kayi shiru da bakin ka, bana son kowa ya sani. Ka rufa min asiri yaya"

Aminu ya bi ta da kallon bazan kamar ze dake ta
"Baki da hankali ne? Menene aibun umar, daga jin kalaman sa ba karamin son ki yake ba. mata da yawa suna neman wanda ze so su haka basu samu ba se ke. Gashi kuma umar dan uwan ki ne , Ke wace irin shashasha ce wai, bari umma ta dawo taji zancen nan"

Khairi tayi sauri ta sulale a kasa tasa gwiwar ta a kasa a gaban Aminu tare da nade hannun ta buyu tana rokar sa

"Dan Allah yaya na roke ka da girman Allah kar ka fada wa kowa, wlh akwai wanda nake so. Muna tare da shi tun tuni, dan umar dan uwa na ne se na yaudari wanda nake so? na yaudari kaina kuma? Ina son umar a matsayin sa na dan uwa amma ba wai aure ba. Dan Allah mu bar maganar nan a nan yaya"

SarkakiyaWhere stories live. Discover now