Soft spot

157 10 0
                                    

"Ummulkhair"
Ya kira sunann ta a hankali bayan ya shiga dakin da aka ajye ta.

Ta dago kanta da ta kifa a cikin gwiwarta Idanun sun kumbura, hawayen sun kafe saboda tsananin kuka da ta sha, ga matsanaicin ciwon kai da ke damun ta kamar ana sara mata kai, Dara daran idanun ta sun koma fici fici saboda kumburar da idon yayi.

Ganin ta da yayi a wannan yanayi ya karyar masa da zuciya tsananin tausayin ta ya kama shi, lefin da ya kamata ace shi zaa hukunta ya koma kanta.

Ya tako a hankali har ya isa inda take sannan ya tsugunna a gabanta

Da kyar ta ita bude baki tayi magana jiki babu kwari tace
"Kaga abun da ya faru da ni ko"
Hawaye ne ya kara ziraro mata, tasa hannu ta share a hankali

"Ban san da wani baki zan baki hakuri ba ummulkhair, bansan wani kalma zan fada miki da sanyayya zuciyar ki ba.

Khairi ta ja ajiyar zuciya sannan yace
"Na bar wayana a office dan Allah idan ka koma ka kira Aunty na ka fada mata abun da ya faru, nasan hankalinta ze tashi amma dole a fada mata"

Umar ya sa hannu a aljihu ya dauko wayar ta ya dauko a office ya mika mata
"Ga wayar ki amma Bazan bari ki kwana a nan ba, bazan bar wannan zalincin ba"

Khairi tayi murmushin takaici
"Ya zanyi, bani da wani gata a garin nan. Iyaye na ba masu hali bane da zamu iya ja da Alh ibrahim"
Ta fada tare da yar da sauke kai a kasa tana wasa da yatsun ta. Duk wanda ya ganta a lokacin se ya tausaya mata

"Abun ma bazai kai nan ba dan Nine me lefin, ni ya kamata a hukunta"
Umar yana ta kokarin danne bacin rai da ke cinsa a zuciya saboda yanzu ba lokacin baccin rai bane, se yanzu da ya ga khairi ya gane ba lokacin nuna zafin rai bane dole ya koma gurin babansa suyi magana ta fahimta saboda a samu a sako ta ta kwana a gida.

Umar ya janyo ledar takeaway da yayo mata, abinci kala kala ne a ciki saboda be san me zata so ci ba

"Ki ci abinci yanzu zan je na dawo"
Ya fada tare da mikewa daga gabanta. Khairi tayi sauri ta riko hannun sa wanda yasa yayi saurin juyowa suka hada ido, idanun ta sun ciciko da hawaye

"Tsoro nake ji"
Ta fada a hankali.

Umar ya kara durkusowa ya tsugunna a gabanta.
"Na sani, kiyi hakuri yanzu zanje na dawo Babu abun da ze same ki Insha Allah, you are not alone"
Haka umar yayi ta lallashin ta har ta yarda ta barshi ya tafi.

Ya koma company ya nufi office din Alhaji ibrahim, wannan karon be shiga a gadarar ce ba saboda ba fada yazo suyi ba.

ALH ibrahim yana zaune yana dube dube a cikin file ya ji shigowar umar amma be dago ya kalle shi ba har umar ya zauna a kujerar da ke gaban sa

"Ya akayi?"
Alh ibrahim ya tambaya still be kalli umar ba

"Kasan bata da lefin komai amma ka tozarta ta haka, do you call yourself human?"

ALH ibrahim yayi dariya sosai har yana kwarewa, be dena dariyar ba se da ya ga alamun hawaye sun cicciko a idon umar sannan yayi gyaran murya ya ajye biro da ke hannun sa ya fuskanci umar da serious face sannan yace

"Wacece ummulkhair a wajen ka"
ALH Ibrahim ya watsa masa tambayar tare da kalon cikin idon sa

"Ba hurimin ka bane wannan"
Ya amsa a takaice

"Haka ne, ba hurimi na bane kamar yadda ka fada nima ba hurimi na bane na shiga binciken Da Dss sukeyi"
Alh ibrahim ya sake daukar biron sa ya ci gaba da rubutun da yakeyi kamar ma ba'a hallici umar a gurin ba.

Abun ya bata ma umar rai makuka duk yadda yaso yayi calming kansa ya kasa. da masifa yace
"Are you serious?? kana tunanin Allah ze barka zaluncin da kayi. Nine culprit dinka ni ya kamata ka hukunta i dont understand why you're punishing someone eles"

Ko motsi Alh ibrahim beyi ba, ya ci gaba da abun da yakeyi

"Magana nakeyi"
Umar ya fada da karfi. Da ya ji ba answer ya ci gaba

"Ta cece ka daga kaskanci da jin kunya a gaban mutane, she saved your company amma abun da zaka saka mata da shi kenan?. Have you ever wondered why that flash was in her drawer??.
Ranar Aniversary nayi niyan karban company nan daga hannun ka, i had all my evidence stacked, lawyer din sarah suna nan a Nigeria, i have already filled a case of fraud with the American High court, nayi niyan disgracing dinka a gaban bakin da ka tara. Amma banyi hakan ba"

Umar ya zagayo ya tsaya daf da baban shi sannan ya ci gaba

"Do you know why??? Saboda ummulkhair. Ummulkhair ce tayi duk yadda zatayi ta hana ni aikata abun da nayi niya. She literally closed the door with key and blocked my way out duk saboda kar na fita. Na bata wannan flash dinne saboda ya zama guarantee bazan yi wani abun ba"

Alh ibrahim ya ci gaba da abun da yakeyi amma a cikin ransa zuciyar sa ta riga ta gama karaya. Nadama ya shiga yi sosai da yaji abunda umar ya fada, ya tausaya ma yarinyar sosai amma baze yarda ya nuna ma umar ba domin kada duk abun da yayi planning ya ruguje. A ko da yaushe yana fada ma kansa
'you have to be cruel sometimes to achieve something great'
Da wannan principle din ya gina rayuwar sa shiyasa har yake iya yin abubuwa na rashin imani.

Umar ya ci gaba da ihu yana reeking amma Alh ibrahim be kula shi, har ya gaji ya bar office din a fusace, ya koma office dinsa ya sha kuka sanan Ya sha alwashin se ya ruguza Alh ibrahim tunda rashin imanin sa ya kai haka.
🍒🍒🍒🍒🍒🍒
ALH ibrahim ya kira jidda bayan fitar umar daga office din wadda ta shigo a dar dar, fuska duk a kumbure

"Alh dan Allah kayi hakuri kayi ma ummulkhair gafara, wlh ban fada maka ba don ka sa a kama ta. Alh guiltiness baze barni nayi sukuni ba"

Alh ibrahim yayi ajiyar zuciya sannan yace
"Kar ki damu jidda zata fita barazana nakeyi musu su biyun amma za'a sake ta, yanzu na tabbatar da maganar ki da kika ce umar yana son ummulkhair, ban yarda ba da farko amma na gani yanzu. Ban taba tunanin umar had a soft spot left a heart dinsa ba se yanzu"

Alh ibrahim yayi shiru ya tsurawa bango ido yana tunani, bayan mituna kadan yace da jidda
"Kar ki sa abun a ranki sosai, zata fito zuwa gobe Insha Allah. Kya iya tafiya"

Jidda ta tashi sum sum ta bar office din.

ALH ibrahim ya ci gaba da tunanin da yakeyi.
Khairi ta zama weapon dinsa wanda ze iya defeating umar, duk da abun farin ciki ne a wajen sa amma a kasan zuciyar sa yana jin wani irin uneasiness. Ya kasa gane meyasa relationship din umar da ummulkhair ya tsaya masa a rai, Zuciyar sa ta kasa aminta da hadin nasu.

🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Bintu. A
09034346763

SarkakiyaWhere stories live. Discover now