Amana

156 10 0
                                    

🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒

"Yes wacece"
Ya fada hannun sa daya a kan stiring din mota dayar kuma ya kara wayar  a kunne

Cikin sheshekar kuka jidda take magana

"Sir jidda ce, an zo an tafi da ummulkhair yanzu"

"Ban gane ba ? wa ya tafi da ita"
Hankalin sa ya fara tashi jin yadda take kuka yasan ba karamin abu bane

"SS......su suka tafi da ita office dinsu"
Jidda na magana kukan na kara cinta

"Me ya faru, meyasa suka tafi da ita. Tana ina yanzu!!"
Ya fada da karfi dan hankalin shi ya gama tashi

"Tana head quater su, lefi na ne si......"
Kafin ta karasa magana umar ya kashe wayar, tare da juya motar yayi hanyar headquarter SS, yanzu ba lokacin da ze saurari wani abu bane, Burin sa ya ganshi tare da ita don yasan ba karamin tashin hankali take ciki ba.
Se da ya kai office din sannan ya fara tunanin to me tayi ne da har DSS zasu kama ta.

Da hayaniya ya shiga office din yana ta masifa se sun barshi ya ganta, babu yadda beyi da su akan ya ganta ba suka ki yarda.
Daga dan bayanin da wani officer yayi mishi ya gano bakin zaren, laifin  sa ne ya shafe ta.

Zuciyarsa tayi baki, idanun sa sukayi ja yar baya gani sosai. Motarsa ya koma ya ja a miliyan se company.
Yana isa ya wuce office din baban sa straight. Duk wanda ya ganshi a hanya yasan ba lafiya ba ko daga  yadda yake wulla kafa saboda sauri, ga fuskar nan babu alamar rahma.

Ko knocking beyi ba ya banka kofar da karfi wanda yasa Alh ibrahim yayi saurin kallon kofar don yaga wani mara hankalin ne ze shigo masa office haka

Umar ya gani rai a bace har yana huci, gadan gadan ya taho kan baban cikin ihu yayi magana

"Who gave you the right to do that to her!!!!!"

Alh ibrahim yayi murmushi sannan yace
"Well, zamu gani idan tana da gaskiya ko bata da shi"

"Gaskiya????"
Umar ya maimita tare da saka hannun sa biyu a kan desk din baban sannan ya rankwafo yadda ze kalli baban ido cikin ido, ya ci gaba da magaba

"Kasan wace ummulkhair kuwa, kasan me tayi domin ta cece ka. do you know what she did for you and your fucking dammn company"

Ya buga hannun sa da karfi a kan table din wanda ya sa Alh ibrahim fusata shima duk da yasan fadan rashin gaskiya yakeyi. Amma rashin kunyar tayi yawa ace dan da ka haifa shi zaizo yana buga maka table disrespectfuly

"Ta hada kai da kai dan ku cuce ni, kuna so kuci amana ta. do not think you would get away with this, kaima ka jira kaga yadda zanyi da kai"

Umar ya tuntsure da dariyar takaici yana mamakin wai wannan ne mahaifin sa. Mutumin da be san darajar kowa ba sai kudi. Se da yayi dariyar sosai wadda yafi kuka ciwo sannan ya daure fuska tare da cewa

"See who is talking, kai har zaka iya maganar cin amana. Ba amanar kaci ta kawo ki inda kake yanzun ba?"

"Umar!!!!!!!!"
ALH ibrahim ya daka masa tsawa.
Umar ko gizo beyi ba, daman ba tsoronsa yake ji ba.

"Get out, out of my office"
ALH ibrahim ya ci gaba da ihu yana nuna masa hanyar waje.

"I said out of my office!!!"
Ya kara nanataa da karfi.

"Just wait and see se naga bayan ka, se na kawo karshen zalincin nan"
Umar ya fada sannan ya fice daga office din a zuciye ya rufe kofar da karfi ya tafi neman jidda, domin yasan tana da masaniya akan abun da ya faru.

Yana shiga office din jidda ya tarar da ita ta sha kuka, idanuwanta duk a kumbure tana zaune tayi tagumi hannu biyu.

Ya karso inda take yana mamakin kukan da tayi kamar ita aka kama. Tana ganin shi ta mike da sauri

Cike da tashin hankali a fuskar sa yace
"Me ke faruwa ne jidda, ya akayi suka tafi da khair"

Jidda ta kara matse hawaye, da kyar take magana
"Lefi  na ne, dan Allah ya yafe ..... min"
Ta karasa maganar tana sheshekar kuka

"Me kikayi, don't tell me you are behind all this"
Umar ya fada cike da fushi yana nuna ta da yatsa

Kukan da ta ci gaba dayi ne ya bashi answer, ji yayi kansa ya kulle, a hankali ya sulale ya zauna a kujerar da ke kallon ta

"Why jidda, why!!???"

"Ka yafe min, kayi min gafara, kayi hakuri wlh ban san abun zeyi tsananin haka ba"

"What did you do!!"
Ya fada da tsawa wanda yasa ta rikice
Baki na rawa tace
"Na shiga office dinta ranar da bata nan na fara dube dube anan naci karo da wani flash a cikin drawer dinta, wlh kamar bazan dauka ba shedan ya raya min na dauka na duba abun da yake ciki"

Jidda tayi shiru tana kallon umar da idanu sunyi shabe shabe da hawaye, tana so taga reaction dinsa. Bacin rai ta gani a kwance a fuskarsa kamar zeyi exploding. Nan da nan taji maganar ta kafe a bakin ta

"Continue!!"
Ya kara daka mata tsawa

"Shine na duba se naga content din da ke ciki. Ina gani na san cewar idan na nunawa CEO to tabbas korar ta zeyi daga aiki. Ni kuma daman abun da nake so kenan. Ina so ta bar company nan gaba daya. Tun bayan maganar da mukayi da kai naga alamar baza kayi komai ba shiyasa nayi kokarin nemawa kaina mafita"

Umar ya kalle ta da ido na tsana da takaici.
"Yanzu ribar me kika ci da kikayi hakan"

"Wlh ban taba tunanin CEO ze dauki abun da zafi ba haka"

"Shut up!!!, dont try to give silly excuses. Kar ki taba tunanin i will let this slide. Idan bata bar company ba definitely ke zaki bari. Daga ke har Alh ibrahim kunsan who was behind it. Kunsan ni nayi komai amma knowingly kukayi framing innocent lady for it. I will never forgive you two"

Yana gama magana ya fita fuuuu, ya koma office dinta ya fara dube dube. Shi kansa be san me yake nema ba. Anan ya ci karo da jakar ta da waya, ya tattaro su sannan ko dauki mota se office din SS.

Da yaje akayi ta bala'i da shi dole se ya ganta. Bayan an kai ruwa rana suka barshi ya shiga inda take  , don sun  ga umar din ba hankali gare shi ba

🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Bintu. A
09034346763

SarkakiyaWhere stories live. Discover now