Matambayi

235 12 0
                                    

🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Abdulkareen yana zaune office dinsa yana danne danne a laptop, aiki yakeyi akan wani construction design. Can kuma ya tsaya da yin aikin, kansa ya kulle  basirar sa ta dauke gaba daya. Ya tabbatar da baze iya tabuka abun arzuki ba idan ya ci gaba da aikin.
Rufe laptop din yayi sannan ya janyo wayarsa a aljihu ya kira amininsa Ahmad.

Ahmad ya daga wayan suka gaisa sannan suka taba hira. Kafin suyi sallama ne AK ya fada masa makasudin kiran da yayi masa. Ya bashi labarin ya ga  yarinyar da yake nema  amma ta bace masa.
Ahmad ya nisa sanan yace

" ka kara komawa makarantar  da ka ganta ko zakayi dacen sake ganin ta"
Ahmad ya bashi shawara

"Ahmad bana so na kara wahala  kamar yadda na wahala a kano, da ina da ikon cire ta a zuciya ta da tuni na cire, naga alama zan wahala da yawa"
Ak ya fadi muryarsa cike da damuwa.

"Kar kace haka Ak, kar kayi saurin karaya mana. Ka cigaba da addua idan da alkhairi Allah ya hada ku, idan kuma babu Allah ya cire maka sonta a ranka"

Haka Ahmad yayi ta bashi shawara da karfin gwiwa sannan sukayi sallama.

Maganar da sukayi da Ahmad ya bashi kwarin gwiwa sosai da har yayi tunanin tafiya bwari a lokacin.

Ya isa bwari bayan azahar, kai tsaye makarantar da ya ganta ya nufa. Yana zuwa ya tarar da babban gate din makarantar a kulle da kwado, se karamar kofar ce a bude. Ya tarar da me gadi a gefe akan benchi yana jin radio.  Ya isa wajensa suka gaisa sannan ya tambaye shi ya yaga makarantar a rufe lafiya kuwa ? Me gadin ya sanar da shi ba makaranta ay, yau asabar ce.

Lallai aiki yayi masa yawa da har be gane ranakun sati. Idan suna da aiki da yawa har weekend  suna shiga office don karasa aikin.

Har ya juya ya fara tafiya yayi wani tunani ya dawo gurin me gadin.

"Don Allah tambaya nake"
Me gadin ya taso daga kan bencin ya matso kusa da shi don ya fi fahimtar abunda ze tambaye shi.

"Allah yasa na sani".

"Akwai wata baiwar Allah da nake nema a makaran tar nan ko Allah ze sa ka gane ta"

"Tohh alhaji kasan daliban suna da yawa ba lalle na gane kowa ba, amma de menene sunanta."

Dankari kenan, shima neman sunan yakeyi. ya tuna be ganta da uniform ba Kuma ita kadai ke tsaye, ko ma ba daga makarantar ta fito ba ne?
Har  ze hakura a ransa amma kuma ay matambayi baya bata.

"Bana tunanin daliba ce, jiya ma na ganta a bakin gate dinnan , fara ce sosai, siririya kuma bata da tsayi sosai"

Me gadin ya danyi jimm sannan yace

"Kode sabuwar malamar nan kake nufi? Wata fara sosai. amma ban san sunanta ba, kuma ina tunanin malamar bautar kasa ce"

Tabbas ita dince domin haskenta ba me buya bane. Ko a cikin farare ita din fara ce. Be san lokacin da yace " eh ita ce"
koma ba ita bace akalla an samu me yanayin ta. Ko ba komai ze yi fatan ita dince. Da wannan fatan ze samu kwarin gwiwar dawowa ranar monday. 
Ya tambayi yaushe ake tashi a makarantar me gadin ya ce masa 1:30 Yayi masa godiya sannan ya tafi
🍒🍒🍒🍒🍒🍒

Ranar monday da farin ciki ya tashi saboda daman yana ta Allah Allah monday tayi, Se rawar jiki yake yi. Tun kafin asuba ya tashi yayi wanka, yayi sallah sannan ya shirya. Yau da wurwuri ze je aiki don ya gama duk abinda zeyi kafin karfe 1 na rana, kai ko be gama aikin ba ma ze ajye idan ya dawo ya karasa.

Ya isa office da sassafe ya shiga aikin sa, bini bini se ya kalli agogo. ya dinga jin wani abu a cikinsa. Excitement da anxiety ya hana shi sakat. Ya kammala aikinsa karfe 12:50 ya tashi yayi alwala a toilet ya nufi hanyar fita domin yin sallah a massalaci daga nan ya wuce.

Ya murda handle din kofa ze fita a daidai nan ne jidda ta sanyo kai ita ma zata kwankwasa kofar sa Suka kusa yin karo.
Ba shiri ta tsorata ta saki kofin da ke hannun ta, tayi saurin kai hannu zata tare shi amma dayake kofin me nauyi ne Se da ya kai kasa.

Duk sabuwar shekara company na rarrabawa maaikatansu kofinan tangaran, (mugs) littafai da biro da sunan company a jiki. Ba aikin ta bane rabon kayan amma saboda tana son excuse din ganinshi yasa ta dauko nashi jiki na rawa ta taho

Ta danyi kara saboda zafin da hannunta yakeyi. Bata yanke ba amma ta bugu a hannu yayin da ta kai hannu zata tare.

"Subhanallah, sannu kinji, sannu"
ya fadi tare da nuna damuwar sa sannan yace
"Muga hannun"

Jidda ta dago da hannun tana nuna masa tana wash wash a hankali.

" sannu, da alama kofin ya bugeki sosai, shigo ciki mu gani"
Ya juya cikin office din itama ta bishi. Ya bude cikin drawer sa ya dauko man zafi, dama baya rabo da shi. Ya mika mata ta karba ta shafa. Yayi ta mata sannu don be ji dadi ba, tsoron da ya bata ne yasa ta saki kofin har ta ji ciwon.

Jidda da ke zaune tana shafa man zafin a hannunta farin ciki ne ya cika zuciyar ta, farin cikin ya hana ta jin zafin ciwon da ke hannun ta. Yau ita Ak ke lallabawa haka, ya yi mata sannu yakai cikin charbi.
Ya zaayi baza ta so shi ba, kyakyawan saurayi me cikar zati.
Ak ya kara bata hakuri sannan yayi mata bayanin yana sauri ze je wani waje. Ya fada mata idan ita gama ta ajye masa man zafin a kan table.

Ya fice da sauri se BWARI.

🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Bintu. A
09034346763

SarkakiyaWhere stories live. Discover now