DSS

167 11 0
                                    

🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Abdulkareem da khairi sun kulla soyayya me zurfi da ban sha'awa tun bayan tafiyar sa paris. Kullum a cikin video call suke, duk abun da takeyi yana kallon ta a waya. Da weekend ma tare suka yini a waya duk da bambancin lokaci tsakanin paris da Nigeria, har girki tare sukayi, idan yaje restaurant haka zayi ta nuna mata abincin da ya ci, duk inda yaje tana biye da shi a screen din waya.

Work days ma haka sukeyin video call duk da be kai na weekend ba saboda aikin da sukayi amma suna samun faraga ake dauko waya a ci gaba daga inda aka tsaya, Basu da wani suran damuwa se farin ciki da annashuwa a kullum.

Umar kuwa tun rananr da yayi kicibus da Ak a gidan su khairi ya shiga cikin damuwa, yasan suna soyyayya amma zuciyar sa ta kasa aminta da hakan, ta kasa hakura da khairi, se wutar kishi da ke ruruwa a cikin zuciyar sa a kullum.

Da farko yayi murnar tura Abdulkareem paris amma murna ta koma ciki da yaji kusan ko da yaushe khairi na magana a waya, yana jiyo dariyar ta daga office dinshi kuma yasan ba da kowa takeyi ba se Ak. Wani lokacin ma barin office din yake gaba daya saboda baya son jin abun da ze daga masa hankali.

Wani lokacin se ta gama aikin da ya bata ta kai masa se ta neme shi ta rasa, se ta ajye itama ta tafi gida daman gaba ta kaita, gobarar titi a kasuwa.

Yau ma ta gama video call da Abdulkareem sannan ta fara aikin da umar ya sata. Ta gama ta shiga office dinsa don ta kai mishi bata same shi ba, ta dawo office ta ci gaba da danne danne a waya.

Kamar daga sama taji an hankado kofa mutane 3 sun shigo cikin office din dukkansu sun sha suit.
Cikin tashin hankali ta mike saboda tsoron da mutanen suka bata sannan tace

"Lafiya???"

"Lafiya zamu tafi da ke office zaki ji komai a can"
Daya daga cikin su ya bata answer

"Office kuma, ban gane me kame nufi ba"
Khairi ta tambaya saboda confusion

"Muje can zaki gane koma menene"
Ya kara bata amsa

Khairi tayi shiru na dan lokaci sannan tace
"To ina da tambaya, dan Allah ku su waye?"

Dayan mutumin ne yayi magana yanzu
"Kina bata mana lokaci madam tafiya muka zo yi da ke ba muhawara ba

Wanda ya fara magana ne ya katse shi
"No she has the right to know where we are taking her"

Ya juyo ya kalli khairi
"Mu jami'an SS ne, mun zo mu tafi da ke ne a bisa charges na fraud"

Bata san lokacin da tayi dariya ba, saboda taji abun kamar a film
"Aa yallabai ina ganin your are in the wrong office, maybe ba nan ya kamata ku shigo ba"
Khairi ta fada duk a rude saboda ta kasa gane me yake faruwa

"Ba ke bace ummulkhair ishaq?"
Wanda beyi magana ba tun farko ya bata answer

"Ehhh...... ehh nice"
Ta fada har tana i'ina

"To ke muka zo tafiya da"

"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun, Allahumma ajirni fi musibati wa aklifini khairan minha"
Abunda tayi ta maimaitawa kenan saboda tashin hankali

Haka jami'an Ss suka taso ta a gaba, tana tafe tana salati. Ko wayar da jaka bata dauka ba haka sukayi gaba da ita.

Suna fitowa bakin kofa taga jidda duk a rude ta hada gumi kamar wadda tayi ma me gari karya, itama se salati takeyi.
Khairi tana ganin jidda ta fara tambayar ta

"Aunty Jidda lafiya, me nayi ne za'a tafi da ni"
Jidda ta kasa cewa komai se hawaye da yake sauka daga idanun ta.

"Kiyi hakuri ummulkhair kiyi hakuri"
Kukan da jidda takeyi da hakurin da take bata ya kara tsoratar da khairi, ya kara tura ta cikin kogin confusion.

Haka suka tafi da ita kowa na company se da ya fito kallo amma babu wanda ya iya cewa komai, ko ya hanasu tafiya da ita.

Ko da suka isa office din SS idanun ta sunyi luhu luhu saboda kuka, ita da Ko police station bata taba zuwa ziyara ba yau gata a ofice din DSS. Akan lefin da bata da masaniya.

Suka ajye ta a wani office suka barta a wajen se bayna awa biyu sannan wani officer ya shigo. Ya ja kujera ya zauna a gabanta sannan ya fara da cewar

"Duk abun da zaki fada yanzu hujja ne a gare ki a kotu, sanna zaki iya kin amsa tambayar da zamuyi miki idan kina da bukatar se lawyer ki yazo"

Ahh yau ana wata ga wata, me ya kawo maganar court har da wani lawyer, to me tayi ne haka da tsananin, Kamar wadda tayi kisan kai?

"Dan Allah ka fada min lefin da nayi da kuka kawo ni nan"
Khairi ta fada hawaye na bin kuncin ta daya na bin daya

"An kawo ki ne saboda employer dinki wato Alh ibrahim yana tuhumar ki da hada kai, da yin zabba cikin aminci na yunkurin siyar da company shi ma turawan kasan America. Wannan international case ne shiyasa muke handling dinshi"

Khairi ta saki baki tana mamakin sharrin da akayi mata, me ya hada ta da company da har zaa ce zata hada kai da turawa, tsakanin ta da bature se de a film. Wacece ita a company haka? Ita da take matsayin coper

"Ina tunanin gaskiya kunyi kuskure ni fa coper ce a company, ban san abun da kuke nufi ba gaskiya"

Officer ya fito da wani flash a aljihun sa ya nuna mata
"Kin gane wannan flash din?"

Khairi ta karewa flash din kallo bata gane na waye ba
" Aa gaskiya ban gane shi ba"

"Amma a cikin drawer ki aka gani"
Office ya kara kara mata flash din a fuskar ta, se a lokacin ta tuno flash din wanene.

Flash din Umar wanda ya bata yace shine weapon din destroying company ta rike a hannun ta dan ya zama guarantee cewar baze aiwatar da plans dinshi ba. Ita kuma ta ajye shi a cikin drawer ta ta office ba tare da tasan meye a ciki ba, Ta manta da shi kwata kwata ma

"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun"
Ta dinga maimaitawa, lallai yau ta shiga cikin masifar da bata san yaya zata fita daga ciki ba

🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Bintu. A
09034346763

SarkakiyaWhere stories live. Discover now