🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Washe gari da sassafe aka sallame su daga umar har khairi ba tare da wani kwakwaran bayani ba. Shi daman umar yasan barazana babanshi yake musu domin ba huuja gare shi ba.Umar ya ce ma khairi ta shiga motar sa su tafi gida babu musu khairi ta bishi. Ya tada mota suka bar office din dss.
Suna tafe yana tunanin da wani baki ze bawa khairi hakuri saboda sanadiyar sa ce ta shiga cikin halin nan. Yana tuno yadda a daren jiya take bacci tana ajiyar zuciya, wani lokaci har razana takeyi a cikin bacci.Da kyar ya iya hado words ya fara magana
"Kiyi hakuri ummulkhair sanadiya ta ne yasa kika shiga cikin irin wannan matsalar. Ban san da wani baki zan baki hakuri ba kuma, i am ashamed of myself "Khairi ta yi murmushi me ciwo sannan tace
" ba komai sir, Allah yayi zan wahala ta wannan fannin. Kai ma baka san abun ze iya kaiwa haka ba, ni ma kuma bansan magnitude din abun da ke cikin flash dinba shiyasa na ajye a cikin drawer. Nice ya kamata na baka hakuri ma"
Haka suka ci gaba da tafiya kamar kurame kowa da abun da yake sakawa a zuciya har suka isa gida. Tare suka jero, kana kallon fuskar su zaka san akwai matsala.
Khairi tayi masa sallama da ta isa kofar apartment dinsu, shima ya shiga cikin nashi don ya huta.
Aunty maimuna tana ganin ta ta rugume ta saboda murna. Duk abun nan da akeyi bata san lefin da khairi tayi ba har aka tafi da ita tunda ba wanda yayi mata bayani. Se da ta bari khairi tayi wanka tayi breakfast sannan ta samu guri khairin tayi mata bayanin duk abun da ya faru.Ta bata labarin komai, alakar ta da Abdulkareem da kuma nacin da umar yakeyi a kanta. Ta bata labarin komai da komai da ya faru tun daga zuwan ta company hara kawo yanzu. Aunty m ta jajantawa
khairi matuka.Bayan sun gama labarin ne khairi ce
"Aunty yau zan koma kano Insha Allah""Kano kuma? Me zakiyi a kano"
Ant m ta fada da mamaki a fuskar ta"Aunty i am fed up na gaji da company nan, tun da na shige shi ban huta ba. matsalar yau daban na gobe da badan, kuma daman na kusa gama service saura clearance biyu. Zan dinga zuwa ending of month nayi clearance din"
Aunty M tayi ajiyar zuciya sannan tace
"Na gane khairi, bazan hana ki idan kina tunanin wannan ne mafita. Amma ki bari se zuwa next week se ki koma, yanzu idan kika je zaki tada musu da hankali ne"
"Aa bazan fada musu komai ba, kawai ina son na ji ni a gida ne. Komai ya hau kaina wallhi aunty"
Ta gama magana ido cike da kwalla suna jiran kiris su sauka"To yanzu idan ba'a gama case din naku ba yaya kenan"
Aunty m ta fada da damuwa a fuskar taRan khairi ya baci da ta tuno Alh ibrahim da jidda
"Sede ya biyo ni kano yasa a kara kama ni. Wlh aunty na tsani duk abun da ze hada ni da company. Ko clearance nazo sede na ce ma oga Ak ya taimaka ya fito min da paper"Khairi ta fada zuciya na zafi.
"Bari na barki ki huta, idan kin shira ina parlour, baba driver ze kaiki tasha"Khairi ta gama shirin ta tsaf tare da hada kayanta kaf dan ko ribbon bata bari ba. ta fito da niki nikin akwati da jakunkuna.
Aunty m bata so tafiyar ta ba amma ba yadda zatayai. Tayi sallama da aunty m da yaran gaba daya, baba driver ya ja mota se tasha.A hanya ne sukayi video call da Abdulkareem take fada masa decision din da ta yanke. Be ji dadin barin ta Abuja ba amma da ya tuno shine maslahar ta da shi gaba daya se yayi musu murna. Ko ba komai zata rabu da umar for good.
Ya kudiri aniyar yana dawowa daga paris ze je gidan su ya tambayi izni a wajen babanta. Idan komai ya tafi yadda ya kamata yana so a sa ranar su kar ya wuce wata uku, Gwara ayi auren kowa ya huta. wannan tunanin ya sa yayi matukar farin ciki, da yardar Allah khairi ta kusa zama mallakin sa.
Se yamma likis khairi ta isa kano. Se da ta isa sannan ta tuna mamanta tayi mata fadan dawowa ba tare da ta sanar da kowa ba, ta zaro waya ta kira umma.
Umma ta daga suka gaisa cikin raha sannan tace mata
"Umma yau zan dawo fa""Baki da hankali ne, yanzu fa 6 ta wuce, ko de gobe kike nufi"
Khairi tayi dariya sannan tace
"Nan da minti 20 zaki ganni""Auuu yauma abun kika kara kwatawa"
Cewar umma da lafazin fadaKhairi na dariya tace mata "se kin ganni kawai"
Ta kashe wayar.🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒
A abuja kuma umar ya gama bacci a apartment dinsa, tunda ya shiga apartment dinsa be fito ba yana ta sharar bacci saboda daren jiya be runtsa ba kwata kwata yana aikin gadin khairi.Se bayan laasar ya tashi yayi wanka yayi sallah sannan ya dauko waya ya kira khairi bata daga ba. Ya kirata ya kai sau 10 bata daga ba daga karshe ya yanke hukuncin knocking a gidansu ya tambaya ko lafiya.
Ya fita yayi knocking me aikin aunty m ta bude sanna ta sanar da aunty m sunan wanda yazo, aunty m ta bada iznin a shigo da shi.
Umar se kalle kalle yake yana son yaga khairi amma be ga wurgawar kowa ba in banda me Aiki da ta kawo masa refreshmentsAunty m ta fito suka gaisa sanna ta sanar masa da khairi bata nan ta wuce kano. A maganar da take masa ma tasan sun isa ko sun kusan isa.
Gumi yaji yana kyarto masa duk da sanyi Ac da ke parlour. Be ji dadin tafiyar khairi ba, ya so ya kara bata hakuri da lallamin ta
Ya roki Aunty m Alfarmar ta bashi address din gidan su khairi a kano. Da farko kamar baza ta bashi ba amma da tayi wani tunani se ta bashi.
Umar yayi mata godiya sannan yayi mata sallama ya koma apartment dinsa. Ranar ma be koma gida ba a nan estate din su khairi ya kwana.Washe gari da safe ya buga mota se kano
🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Bintu. A
09034346763
YOU ARE READING
Sarkakiya
RomanceLabarin tsantsar soyayya me cike da sarkakiya ce ta kullu a tsakanin su. Ummulkhair ta zamo Allura cikin ruwa wanda me rabo ne ze dauka. Shin wa zata zaba a cikin su? Boyayyen masoyi Abdulkareem wanda yayi dakon soyayyar ta na tsahon lokaci ko kuma...