Shi ne silah page 1

4.3K 195 5
                                    

SHI NE SILA!
    😪😪😪

Na Princess Amrah
          ®NWA
              2018

1~Kwance ta ke ta hada kai da guiwa ta yi zurfi a tunane tunane wanda ita kadai ta barma kanta sanin ko tunanin me ta ke.
    Jin murya kaman daga sama ya sa ta firgigit ta dawo hayyacinta.
    "Ikram zaman me kike da baki tafi makaranta ba. Ko har yanzu zazzabin ne?"
     "Ehh Umma, zazzabin yayi sauki yanzu kaina ke ciwo kamar zai fashe." Ikram ta bata amsa.
    "Kin sha maganin ko yau ma kin yar?"
    "Ban yar ba Umma Allah na sha. Ai jiya na dandana kud'ata. Ban yi baccin kirki ba."
     "To Allah ya baki lafiya. Tashi ki karya, taliya..." Umman bata karisa maganar da ta ke ba wata mata ta fito daga wani madaidaicin daki. Tafa hannuwa ta hau yi kafin ta ce "ba dai abincin dana girka shegiya zata ci ba. Wannan alkawari ne na daukarwa kaina cewa ba zan kuma bari Ikram ta ci  duk wani abu da ya fito daga hannuna ba. Sai dai idan yunwa zata kashe ki ki mutu daga ke har uwar taki." Ta ja dogon tsaki tare da neman wurin zama dan ma kar Ikram ta zagaye ta ci 'yar taliyar data dafa.
     Kuka Ummanta ta hau yi tuni Ikram ta ja hannunta ta kaita dakinta. Rarrashinta ta ringa yi tana fadin "Umma ke fa ba bakuwa ba ce a halayen Goggo Indo, ke ce ya kamata ki fadawa wani halinta. In da sabo ai ya ci a ce kin saba da hakan, sannan kuma idan kuka ne ai ni ce zan yi shi saboda ni take kira da shegiya duk da nasan ni shegiyar ce. Amma kuma me? Tun ina kukan ai gashi na gaji na daina, tun da dai babu abin da kuka zai min. Ki yi hakuri dan Allah Ummah. Ke kadai ce gatana, bana son ganinki cikin damuwa. Ki daina kukan kin ji?"
    Ajiyar zuciya Umma ta sauke tare da kokarin share hawayenta, Ikram ce ta ci gaba da share mata hawayen sosai ta ke kokarin sakata farin ciki ta hanyar kawo mata labaran barkwanci.
      Tuni ta manta da duk wata damuwarta. Habar zaninta ta kwance ta fiddo wata tsohuwar naira ashirin. Mikawa Ikram tayi, bayan ta karba ta ce "Ummah na menene wannan?"
    "Ki je ki siyi kokon goma da sugan goma ki sha sannan ki sha sassaken bagaruwa saboda wannan zazzabin naki da baya jin maganin turawa."
    Da saurinta ta fita, a inda suka bar Goggo Indo ta sameta zaune tana karkada kafa. Cike da izza da gadara ta ce "da dai ya fi miki, saboda har mallam na fadawa ba zan sake barinki cin wani abu dana girka ba. Uwarki ce dolenmu kuma ita ce kadai zan ciyar, ke kuwa sai ki san yanda zaki yi. Idan ma gangar jikinki zaki siyar sai ki siyar kamar yanda uwarki ta yi ta same ki."
    Kallon kofin kokon hannunta ta yi, tana kokarin yin kuka kuma ta fasa tare da nuna halin ko in kula ga Goggo Indo. Tafiyarya ta yi tana yi tana rera wakar rariya da ta kalla a gidan kawar Ummanta sanda ta aiketa gidan.
     Tun daga kofar gida yaran makota suke jan Ikram, "Ikram shegiya marar uba. Ai dai mun san komai, duk wani tinkahon yarinya na banza ne tun da dai mun san sirrinta."
    Ko a jikinta ta bar inda yaran su ke, ta riga da ta saba da halayen yaran unguwar da kuma irin wulakanci da gorin rashin uba da suke mata.
     Kai tsaye gidan Tambai mai koko ta nufa, bayan ta shiga ta gaishe da Tambai sannan ta mika mata kofin kokon ta ce "gashi Babaa Tambai, kokon goma za'a bani sai a zuba sukarin naira goma." Tambai ta ce "aikuwa Ikram sai dai ki dan jira a dama wani, kin ga wa innan duk shi suke jira, na dama ne ya kare."
     Wurin zama ta nema ta zauna bayan ta daura kofinta a bisa layi.
      Caraf cikin kunnuwanta ta ji wasu yan mata suna fadin "wai Lanti ba wannan shegiyar ba ce ta miki kwacen saurayi?"
    Wadda aka kira da Lanti din ta ce "ita ce fa, wai saboda ita Ilu ya guje ni, yayi mursisi ya fasa aure na, wacce ko asali batta da shi barib tushe mai kyau amma ya gujeni a kanta."
      Dayar mai suna Talatu ta ce "ke ba fa  a  kanki aka fara ba, kin san  Saratu ma haka aka yi, sai da aka je dandali ana wake da samari kawai Sade ya zabi Ikram a maimakonta. Na rasa ko wace irin mayya ce mai kwacen maza, kuma alhali ba kyau ta fi mu ba."
     Tana kaiwa nan Ikram ta mike tsaye, kusa da su ta matso cikin natsuwa ta mikawa Lanti hannu suka gaisa sannan ta mikawa Talatu ita ma suka gaisa.
     A natse ta fara magana "amma dai kun ji kunya, ku yanzu da girmanku ku ke gulma, sam! Hakan bai kamace ku ba kuma kun bani kunya. Sannan kuma maganar kwacen samari da kuka yi, kun san shi farin jini halitta ne daga Allah ko ince baiwa ce ba wai sai mai kyawun fuska ko na halitta ya ke da farin jini ba, wanda Allah  ya so ya ke ba. Idan kun kula da wani abu ni samarin naku ma basa gabana, makaranta da na ke ita ta dame ni ba wai kula samari ba. Su samarin dai ke haukansu a kaina. Shi kanshi Ilu da ya fara cewa yana sona ai korarshi na yi na ce ya komawa budurwarsa Lanti, da ya ke dama ba shi ya ke sonki ba ke ce ki ke sonshi ai kinga bai dawo wurinkin ba. Dan haka dan Allah ku kyale ni haka nan in sarara. Ku daina cin danyen naman jikina haka nan ko kun ragewa kanku daukar zunubi. Haka zalika shegantaka ba kaina farau ba, ba kuma kai karau ba, kafin ni an yi fin dubu, akan me za'a dame ni? Kullum magana daya babu hutu? Ku kanku ba zaku gaji ba haka nan?" Tana kaiwa nan ta yi shiru tana kokarin boye hawayenta, duk da tarin damuwar da ke cikin zuciyarta bata yarda ta bayyanata ba.
      Wurin zamanta ta koma cike da farin cikin mayar masu martani da ta yi, musamman ma yanda ta ga sun yi shiru alamar maganganunta sun ratsa zukatansu. Sallamarta aka yi ta bar gidan farin ciki fal a zuciyarta.
     A hanya ne ta samu ta fiddo hawayen da tun dazu take boyonsu, tun sanda tana rarrashin ummanta hawayen ke son fitowa amma dan bata sin ummanta taga damuwa a fuskarta ya sa ta ki bari su fito.
    Wurin zama ta nema sai da ta yi mai isarta sannan ta tashi ta nufi gida a lokacin har kokon ya fara hucewa.
     Da shigarta sallama ta yi amma Goggo Indo ta ki amsa sallamar, hakan yasa kai tsaye ta shiga dakin ummanta inda ta same ta ta yi tagumi hawaye sai zarya su ke mata a kumatu.
     Aje kofin kokon ta yi tare da risinawa gaban mahaifiyarta. Tuni ita ma hawayen ya ci gaba da ambaliya a kumcinta, haka suka rungumi juna sai sharar kuka su ke babu mai rarrasar wani a cikinsu. Kokon da Ikram ba ta sha ba kenan ta zauna da yunwarta har bacci ya dauke ta a haka.

****
Nasan da dama masoyana sun jima suna jiran posting dina, duba da dadewar da nayi bana watsapp. Kuyi hakuri rashin samun ci gaban labarin *DAFIN SO* Hakan ya faru ne bisa rashin samun farkon labarin da na yi, saisa na fara wannan, amma da yardar Allah idan na samu farkonshi zan kawo maku ci gabanshi. A gafarce ni. Ku kasance tare da wannan labarin, nasan insha Allahu zaku ji dadinshi. Labari ne wanda ya shafi tausayi, taba zuciya, soyayya da kuma tsantsar jin kai ga mahaifiya. Ina fatan yanda na farashi lafiya in kammala shi lafiya.

    Jinjina ga kawayen albarka, masoya na gari, aminnan juna ko kuma ince yan uwana abin alfaharina wato *RAZ.* Har gobe ba zan gaji da nuna soyayyata a gareku ba. Amrah ta ku ce ku nata ne. Ina fatan Allah ya bar mana zumuncinmu har karshen rayuwarmu.

     Dole na yabi kungiyar *NAGARTA WRITERS.* Har kullum kuna raina, Allah ya bar zaman tare ya kara bunkasa wannan kungiya tamu.

    *RAZ NOVELLA 1&2* Duk ina tare da ku. Allah ya kara hadin kai amin. Sauran groups da nake duk ina gaishe ku. Amrah na gaishe ku lodi lodi.

Ina ma kowa barka da shiga sabuwar shekara. Duk alkhairan da ke cikinta Allah ya sadamu da su. Sharrance sharrancenta kuma Allah ya nisantamu da su.

SHI NE SILAH!Where stories live. Discover now