52

962 51 0
                                    

*SHI NE SILA!*
           😪😪😪

              Na Princess Amrah
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
                           (2018)


52~  Washe gari da sassafe Hajia ta shiga ɗakin mai gidanta Alhaji Kallah domin ta gaishe shi. Wayam ta gani babu kowa a ɗakin hakan yasa ta zauna a bisa sofa dan a tunaninta ko ya shiga banɗaki ne. Shiru shiru har kusan minti sha biyar bai fito ba. Miƙewa ta yi ta ce "Alhaji idan ka fito ni dai mu haɗu dining, na haɗa maka kalacinka." Ta fice daga ɗakin ba tare da tunanim komai ba.
   A falo suka zauna su duka har da Umari da ke ta latsar wayarshi hankali kwance. Jin Alhaji Kallah shiru yasa Hajia ta ce "Nikam wai Alhaji lafiya? Ko baya gidan ne?"
   Sai a lokacin Umari ya ɗago kai ya ce "Ni na bashi shawarar ya gudu. A kan me zai tsaya mutanen da basu kai sun kawo ba su nemi takurashi? Ai wata ƙila ma Abba jirginsu har ya tashi."
     Da mamaki Hajia ta ɗago kai ta kalli Umari. "Ya gudu?" Ta faɗa tana kallonshi.
   "Ƙwarai ma kuwa ya gudu Hajia. So kike ya tsaya a kashe shi ko kuma a masa wani mugun abun wanda zai illata?" Umari ya faɗa cikin halin ko in kula.
    "Baka da hankali Farouk da alama har yanzu akwai yarinta a tattare da kai. Shi kuma Alhaji babu ko kunya sai ya biyewa maganarka? Wato mu ko oho ke nan, idan sun zo tafiya dashi sai su tafi damu madadinsa."
   Umari ya ce "Hajia ai wannan maganar a hannun sojoji ta ke ba ƴan sanda ba. Idan ƴan sanda ne su ne zasu tafi damu a maimakonsa har sai ranar da ya dawo. Su kuma sojoji ana ma iya rage masu muƙamansu saboda sakacin da suka yi har ya gudu basu kamashi ba."
    Rabi'atu kam kuka ne kawai aikinta, tana mai tir haɗe da allawadai da hali irin na Abbanta.
    Momy ma kukan ne ya ƙwace mata ta ce "Ai da ya sani sai ya damƙa min dukiyar yara ni da kaina in basu idan shi kunya ba zata barshi ya basu ba. A ƙarshe ma sai ya gudu ya barmu da abin kunya, nan na san ko biki ko suna na fita sai an ringa zunɗe na." Ta sake saka wani kukan.
     Miƙewa Umari ya yi zai fita suka ji sallamar Khalid. Biye da shi Barr. Kareema ce sai wani Barr. Umar mijin Sultana (Na cikin labarin wata shari'a).
    Ido buɗe Umari ke kallonsu ya ma kasa amsa sallamar dan bai tsammani zasu zo a daidai lokacin ba da tuni ya gudu shima daga gidan.
   Murmushi Khalid ya yi tare da miƙawa Umari hannu domin su gaisa ya ce "Assalamu alaikum Umari." Amma sam bai bashi hannun ba bai kuma daina kallonshi ba.
   Wani murmushin Khalid ya saki ya ce "Au! Ashe fa na manta kai ɗin ba Umari ba ne Farouk ne fa. Ashe wanda ya sace ni ne Umari.." Ya sake tullewa da wata dariyar.
    Iya ƙuluwa Umari ya ƙulu, ji ya ke kamar ya shaƙe Khalid ko zai huce.
   Khalid ya ci gaba da faɗin "Dan Allah idan ka san wancan Umarin ka ce dashi ya dawo min da motata, ko kuma in je gidan gonar da kaina in ɗauko dan tsaf zan gane hanyar tun da dama ni na fiddo kaina." Dariya ta ɗan ci ƙarfinshi kuma ya ci gaba "Afuwan fa Umari...dariyar ce na kasa tsayar da ita. Wani labari na ji an ce wai an nuno Kawu a gidan..." Bai gama maganar ba Umari ya ɗaga hannu ya wanka masa mari tare da ƙoƙarin kamashi da kokowa.
    Da sauri Barr. Umar ya kamashi iya ƙarfinsa yana faɗin "Kai! Baka da hankali ne?" Amma ina, Umari ya kamashi da ƙarfi dan dama Umari ba dai girman jiki ba. Ya samu ya yi nasarar kayar da Khalid ƙasa wanda tuni jini ya fara ambaliya daga goshinshi sanadiyyar POP ɗin da ya buga masa kai kafin ya isar dashi ɗin ƙasa.
     Da sauri Hajia ta iso bakin ƙarfinta ta ke dukan Umari tana janye shi amma kamar bai ma san tana yi ba, ya zama mahaukacin ƙarfi da yaji.
    "Ka sake shi nace ko baka jina? Wallahi idan ka ƙara mishi wani abu sai na tsine maka ka bi duniya." Hajia ta faɗa cikin kuka.
    Yana jin haka kuwa ya yi saurin sakin Khalid da ya kasa taɓuka komai sai huci ya ke. (Ni ko Amrah na ce my dear Asmau Umar ashe Khalid ɗin naku raggo ne..lol)
     Gyara kwalar rigarshi ya yi sai sauke ajiyar zuciya ya ke, cike ya ke da haushin Hajia data tsayar da shi amma da sai ya illata Khalid yanda ba zai taɓa mantawa da shi ba a duniya, amma ko yanzu da sauƙi tun da dai ya fasa masa goshi kuma har yanzu jini bai daina fita ba.
     Bayan ya gama gyaran rigar tasa ne ƴan sabda guda biyu suka shigo, "You are under arrest!" Wani ɗan sanda ya faɗa. Ashe tun shigowarsu Barr. Umar da ya ga take taken Umari yama wani ɗan sanda text ya ce su hanzarta zuwa, ya basu addresa ɗin gidan.
    Ido jajur Umari ya ce "A kan me zaku kamani? Me na maku? Ko dan na taɓa wannan wawan yaron? To wallahi inma dan shi ne yanzu na fara, kuma kamar yanda na yi *alwashi* sai na raunatashi."  Ya bi bayan ƴan sandan sai huttai ya ke.
    Khalid da ke kwance Barr. Umar ya taimaka masa ya miƙe dafe da goshinshi, nan fa ya ga uban jinin da ya zuba a hannunshi. Sake dangwalo jinin ya yi ya kalla, laɓɓanshi duka biyun ya tauna kafin ya gyaɗa kai wanda shi kadai ya san abin da ya ke nufi da hakan.
    "Ka yi haƙuri Saifullahi. Ka san Umari ya samu taɓin ƙwalwa, shiisa ma aka sallamo shi daga Italy tun bai gama karatun ba. Abbansu ne ya ce kar mu bari kowa ya sani saboda ba ko yaushe ne abin ya ke zo masa ba."
    Barr. Kareema ta ce "Kuma dole a masa hukunci a kan ya yi attempting kisa. Sai ko idan kuna da wani medical record ɗinsa ingantacce wanda zai iya gamsar da kotu, idan akwai ɗin su da kansu zasu turashi psychiatry (asibitin mahaukata.) Idan babu kuma zasu yanke masa hukunci daidai da laifinsa."
     Shiru Hajia ta yi saboda babu wata takarda data gamsar da hakan, itama dai Alhaji Kallah ne ya faɗa mata haka ba wai dan ta gamsu ba, saboda ita bata taɓa ganinshi ya yi wani abu na marasa hankali ba. Allah kaɗai ya san abin da ya aikata a Italy ɗin da har suka yarda aka ɗaura masa hauka.
     Cikin kuka ta ce "Ga wurin zama nan Khalid. Sannu. Rabi'atu jeki ɗauko first aid box ɗakin Abbanku, sai a masa dabara ko jinin ne ya tsaya kafin ya je asibiti."
    Bai musa mata ba suka zauna bisa kujera, Rabi'atu kuma ta yi kamar yanda Hajia ta umurce ta.
    Jinin suka samu aka tsayar sannan Khalid ya ce "Hajia Kawu baya..." Bai gama maganar ba Shehu Soja ya kirashi. Da sauri ya ɗauka cikin ƙarfin hali ya kara a kunne.  "Hello yallaɓai."Khalid ya faɗa a hankali.
    "Khalid idan kana kusa da tv ka kunna. Suprise." Ya kashe daga nan.
    Babu musu Khalid ya ce ma Rabi'atu "Ɗan kunna min kallo dan Allah."
    Kunnawar ta yi kamar yanda ya umurce ta, dama kuma a Sokoto tv ne ta ke har yanzu, saboda tun jiya da suka ga mummunan abu suka kashe kallon basu sake kunnawa ba.
    Hoton Alhaji Kallah aka nuno sanye da kayan  mata har da gyale ya yafa. Daga ɗayan gefen kuma an cire masa gyalen ne daga shi sai singlet da gajeren wando an ɗauke shi har fuskar ta kumbure.
    Zarah bb ce ta fara kawo bayanai kamar haka;
   "Kamar yanda rahoto ya zo maku jiya litinin cewa an kama ƴan fashin nan wanda suka toni asirin Alhaji Kallah cewa shi ya aike su. To yau kamar wasa aka kamashi a filin jirgi ya yi shigar mata ya hau bisa layi yana shirin barin ƙasar. Bai san cewa sojojin na kule da duk wani motsinshi ba, ashe dai tun daga gidanshi su ke bibiyarshi har airport suna son ganin iyakarshi. Sai da layi ya kawo kanshi ne suka samu nasarar cafke shi inda wani soja ya dake shi sosai a bisa raina masu hankalin da ya yi. Ga shi dai zaku ga komai yanda ya kasance."
   Nan fa aka nuno video'n Alhaji Kallah tun daga sabda ya baro gida ashe suna ɗaukarsa a waya har ya ɗauki drop na taxi ya nufi airport. Da kuma inda aka cire masa kaya ana yi ana dukanshi sai ihu ya ke yana faɗin "Na tuba." Amma ina, soja wuta! Sai da da kanshi ya gaji ya ƙyale shi. Daga nan kawai aka nuno sun jashi sun saka a wata buɗaɗɗiyar mota mai ɗauke da tambarin sojoji. Daga nan aka sake nuno Zarah bb ta ce "Wakilan namu dai biye su ke da su inda zasu kawo maku komai dalla dallah insha Allahu. Sai mu haɗu da ku da ƙarfe takwas na dare domin ganin yanda komai ya ke."
   Ƙit! Khalid ya kashe kallon haɗe da yin wani shu'umin murmushi wanda iyakarsa bisa leɓo.
   Kuka sosai Hajia ke yi tana faɗin "Baka kyauta ba Alhaji baka ma kanka adalci ba. Ka cuce ni ka ci amanata. Yanzu da wane ido zan kalli mutane?"
    Khalid ya ce "Ki daina faɗin haka Hajia. Ai ba ke kika yi ba barin a zage ki."
    "Na sani Saifullahi, amma dai ai ni matarshi ce, kuma ba'a canzawa tuwo suna." Hajia ta faɗa.
   Tashi Khalid ya yi ya ce "To hajia bari mu tafi kawai." Su Barr. Kareema ma suka mara masa baya.
   Da sauri Hajia ta dakatar dashi ta ce "A haka zaka fita jinin bai gama tsayawa ba?"
    Juyowa ya yi da fara'a ya ce "Kar ki damu Hajia. Zan je asibiti." Ya juya ya tafi.

SHI NE SILAH!Où les histoires vivent. Découvrez maintenant