*SHI NE SILA!*
😪😪😪Na Princess Amrah
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
(2018)21~ Ganin Maman Sulaim kwance bata motsi sam bai sa ko kad 'an d'in tausayinta ya ji ba, Kareema ce kawai ke ta d'an bubbugata da nufin ta tashi amma ko motsi bata yi, Auntyy d'in da ke wa su Sulaimi lesson ce ta taimaka mata wurin kaita mota, yaran kuwa sai kuka su ke suna biye da su har suka isa bakin motar.
"Aunty Keth ki tafi kawai, zamu je asibiti da yaran." Kareema ta fad'a.
Cike da tausayi Aunty Keth ta ce "Ok ma, Allah ya bata lafiya." Ta kama hanyar tafiya.
Sulaimi da Ummul-khair suka zauna gaba, Deedah da Momy kuma baya tare da mamansu sai kuka su ke, Deedah da Ummul-khair kam ba wani fahimtan komai su kayi ba, kawai dai suna kuka ne ganin mamansu ta k'i ko motsawa, su kuwa wanda suka d'an yi wayon suna kuka ne dalilin fad'an da iyayensu ke yi.
Hamdala clinic suka fara cin karo da ita, aikuwa nan d'in kawai ta shiga da ita.
Nan da nan ta biya kud'i nurses suka d'auko gado aka d'orata a kai, taimakon gaugawa suka hau yi mata kafin suka fad'awa likita.
Kareema ta masu bayani ce wa fad'uwar gaba da tashin hankali ne suka sakata suma, jin haka ya sa aka hau dudduba numfashinta, ganin baya tafiya daidai yasa aka saka mata oxygen.
Waje Kareema ta koma ta zauna inda yaran su ke, kiran mijinsu ne ya shigo mata a waya, tsaki ta yi had'e da latse kiran, duk da irin tashin hankalin da ya sakasu a ciki yanzu ba ta wannan ta ke ba, farfad'owar Maman Sulaimi shi ne kawai matsalarta sannan su yi tunanin mafita. Sake kira ya yi nan ma dai latsewa ta yi. Wayar maman Sulaimi da ke hannunta ta gano sunan mahaifiyarta ta latsa kiranta. Bugu biyu kuwa ta d'auka da sallama a bakinta. "Nana yanzu kuwa na ke k'ok'arin kiranki, sai Ikilima ta ke ce min na bari kawai zata je gidan, dama tambayarki zan yi, a aiko miki da man shanun ko zaki zo ki karb'a?"
Jin ta d'igawa zancen aya ya sa Kareema fad'in "Ba ita ba ce Mama, Kareema ce abokiyar zamanta. Ina yini?"
Da sakin fuska maman ta ce "Lafiya k'alau Kareematu, ya yaran?"
"Alhamdulillah." Ta yi shiru daga nan, tana tunanin ta inda zata fara fad'a mata rashin lafiyar Maman Sulaim.
"Ina Nana ta ke ne? Ko bata kusa?"
"Um..uhm, dama...gata can bata da lafiya." Ta fad'a a susuce.
"Me ya sameta, tana ina?" Ta tambayeta cikin tashin hankali.
"muna nan asibiti, Hamdala clinic ta Jan bulo."
"Subhanallahi! To gani nan zuwa." Ta tsinke wayar.
Bayan kamar mintuna talatin wata nurse ta fito tana neman kareema, "Sister ta tashi ne?" Ta yi saurin tambayarta tun kafin ta mata magana.
"Ehh ta tashi, an mata gwaje gwajen jini, kin san yanzu a ka'idar ko wace asibiti idan an kawo patient dole a masa wannan gwaje gwajen, har ma na kaiwa Dr. Results, ya ce a nemi wadda ta kawota, dama kiranki na zo yi."
Damm! Gaban Kareema ya fad'i, 'awon jini? To Allah ya jishemu alkhairi.' Ta fad'a a zuciyarta. A zahiri kuwa ce wa ta yi "Sulaimi ki kula da k'annenki kin ji? Zan je Dr. Yana nemana, Ummanku ta tashi ku mata addu'a, kun san Allah yana saurin karb'ar addu'ar k'ananan yara irinku." Ta masu murmushi sannan ta bi bayan nurse d'in.
Kai tsaye Office d'in Dr. Suka nufa, bayan sun shiga nurse d'in ta ce "Dr. Wannan ita ce ta kawo patient d'in nan, wadda na kawo maka result na gwaje gwajen jini da aka mata ka ce na nemo wadda ta kawota."
"Alright, You can go." Ya ce da nurse d'in. Fita kuwa ta yi ta barshi daga shi sai Kareema.
"Baiwar Allah ya kike da wannan mara lafiyar?" Ya tambayeta.
Har zata ce kishiyarta ce kuma ta fasa, saboda ta san in har ta fad'a masa gaskiya ba zai yarda ya bata amsa ba. Sai ta ce "Dr. Sisterna ce."
"Are You sure?"
"Am very sure Dr." Ta fad'a tana kallonshi.
Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ce "Tana da aure ne?"
"Ehh tana da aure." Ta bashi amsa.
"Ok, wato a rayuwar nan ko, idan har ka fahimci abu to ba zaka tab'a bashi wata mummunar fassara ba, kuma duk yanda ake d'aukar abun nan ba haka ya ke ba. Cuta ba mutuwa ba ce, in har mutum ya kiyayi shan magani yanda ya kamata to wani mai lafiyar ma zai mutu ya barshi. Ana yi wa cutar nan mummunar fahimta ne kawai, amma ko malaria ta fita saurin kashe mutane, ita babbar matsalarta shi ne mutum ya sakawa kansa damuwa, saboda mafi yawancin masu cutar da su ke mutuwa to hawan jini ya ke kashesu sai a ga kamar cutar ce. Amma da zarar ta kiyayi komai ta bishi yanda ya dace komai zai zo mata da sau'ki."
Sakin baki Kareema ta yi tana kallon Dr. Ba tare da ta fad'i komai ba.
"Cutar k'anjamau da wuya ta yi kisa, sai dai tana dauwama a jikin mutum har k'arshen rayuwarsa, wannan patient d'in tana d'auke da cutar nan ne kuma har ta zama AIDS, wato ta kai minzalin da ba ma k'ananan magunguna zata ringa sha ba, saboda ta d'an jima a jikinta, ki kira mijinta shi ma d'in a masa gwaji, idan yana d'auke da ita sai shi ma a d'orashi bisa shan magani, insha Allahu babu wata damuwa."
"Munafuki ne ya san komai, kuma shi ne ya jefamu a wannan halin." suka jiyo muryar Maman Sulaimi tana k'ok'arin shigowa, a bayanta kuma mahaifiyarta ce da k'anwarta, ashe suna tsaye duk sun ji maganganun da su ke yi.
Kuka sosai Kareema ke yi ta dafe kanta da ke barazanar fashewa.
"Dr. Ita ma wannan a aunata saboda akwai yiwuwar ta goga." Ta fad'a tare da nuna Kareema.
"Ta ce min ita k'anwarki ce ai." Ya fad'a.
"Ba k:anwata ba ce kishiyata ce, a yi gaugawar aunata Dr. In har bata da ita Kareema ya zama dole ki hak'ura da auren Abban Sulaimi, dole a raba auren."
"Gaskiya ne Nana, amma dai Lawal bai kyauta ba, ya zama azzalumi, ta ya ka kwasowa iyalinka abu kuma ka ki fad'a masu har ka ringa shan magani a b'oye? Wato su mutu su in mutuwa zasu yi."
Kuka sosai Kareema ke yi, ita ma awon aka mata aka tabbatar da tana d'auke da ita amma HIV ce bata kai da zama AIDS ba, za'a d'orata a kan magani k'arami kullum ta ringa sha sau uku.
"Har yaran naku ma ya kamata a masu awon, dan a san matakin d'auka idan suna da shi."
"Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun! Abban Sulaimi ka cucemu." Kuka su ke sosai.
Yaran aka fara aunawa, Sulaimi ce kawai bata da ita, amma Momy, Deedah da Ummul-khair suna d'auke da ita, ta Momy da Deedah ma har ta zama AIDS, ta Khairat ce har yanzu HIV kamar ta mamanta, alamun daga baya ta kama Kareema ke nan, Khairat kuma tun tana cikin ciki ta goga.
Kuka sosai wurin ya d'auka, babu mai iya fad'in komai sai Maman Husnah da har yanzu bata daina tsinewa M. Lawal ba, a kan wannan mugun halin da ya jefasu, baki d'aya ya gama ruguza rayuwarsu.
Kiransu likita ya sa aka yi ya masu bayani, "Kar ku ji komai dan Allah, cuta ba mutuwa ba ce, bana son ku saka damuwa ko kad'an a ranku dan ita ma d'in zata iya haifar maku da wata cutar, zamu d'auraku a kan magani, in har zaku bi k'a'idar shan maganin to ina mai tabbatar maku da cewa sai kun yi mamakin kanku, duk wata rama da masu cutar k'anjamau su ke yi ku ba zaku tab'a yinta ba, kawai dai abin da a ke so duk wata dokar maganin ku bita, insha Allahu babu abin da zai faru. Ga wannan takardar." Ya mik'awa Kareema saboda ita ce mai d'an k'wari k'wari, Husnah hankalinta a tashe ya ke. "Takardar karb'ar maganin ce, duk ranar talata a ke bayarwa a General Hospital. Ku ringa karb'owa, mutum d'aya ma zata iya wakiltar ku duka har da yaran. Allah ya sawak'e ya baku lafiya."
Tashi suka yi jiki babu k'wari, inda suka bar maman Husnah da Ikilima k'anwarta tare da yara suka nufa a sanyaye.
Baki d'aya suka bar asibitin, gidan Husnah suka nufa su duka har ita Kareema. Bayan sun shiga gidan suka samu M. Lawal zaune yana kallo abinshi, babu wacce ta tanka masa sai Maman Husnah da ta yi k'arfin halin fad'in "Sannu Lawal! Kai wato har ma kana da damar zama ka yi kallo bayan halin da ka jefa matanka a ciki, lallai d'an adam abin tsoro ne, wallahi ka cucemu ka ci amanarmu, kuma ko baka so dole a raba aurenka da Nana."
Cikin halin ko in kula ya tashi zaune, "Aikin banza aikin wofi! Ehh na san ina da cutar k'anjamau kuma ina shan magani a b'oye basu sani ba sai kuma me? Ko ana da yanda za'a yi da ni? Kuma da kike maganar a raba aure aikin gama ai ya riga ya gama, wa kike tunanin zai aureta idan mun rabu bayan cutar da ta ke tattare da ita? Babu wanda zai aureta wallahi, idan ma kuka b'oye baku fad'a ba to ni zan bi na tona asirinku. Dan haka ni a ganina gwarama kawai ki barta mu k'arisa rayuwarmu a haka, idan kin ce a'a kuma can ta matse maku..." Tun bai gama maganar ba ta sharara masa kyakkyawan mari wanda har sai da ya duk'e k'asa. "A tunaninka dan tana marainiya shi zai sa ina ji ina gani a cuceta? Ba'a yika ba kuma ba za'a tab'a yinka ba Lawal! Kuma dole ka sakar min 'ya ko baka so, zamanka da ita ya k'are yau, Allah ba zai tab'a k'yaleka ba kuma."
Wani irin yanayi ya tsinci kansa, tabbas ya san yana k'aunar Husnah, amma kuma me, k'aunar ta banza tun da har ya iya cin amanarta. Takarda ya d'auko kuwa ya rubuta mata takardar saki, saki uku ya mata tun da dama saura igiya d'aya ta rage masu.
Had'o kayanta ta yi kuwa suka tafi, Ikilima ta tayata kwasar wasu, Deedah kawai ta d'auka hakan ya sa ya dakatar da ita, "Ki kwashi yaranki ki tafi dasu, dan ba zan iya kula dasu ba, zan ringa aiko miki da kud'in kula dasu duk bayan sati d'aya."
Da sauri Kareema da ke duk'e tana kuka ta ce "Ni zan kula mata da yaran."
"Matuk'ar kina gidana ne ban amince ba, bana son yarana su tashi a hannun matar uba." Ya shige d'aki abinsa bayan ya fad'i haka.
Komawa suka yi suka kwashi kayan yaran wanda zasu iya d'auka, Ikilima ta ce su barsu haka ita zata dawo ta d'auki sauran.
Tare suka tafi da Kareema ta saukesu gida, nata gidan ta wuce cike da damuwa, ta rasa abin da ke mata dad'i, ji ta ke inama ace mafarkin wannan ranar ta ke, wannan rana ta zame mata bak'ar rana wacce ba zata tab'a mantawa da ita a rayuwarta ba.
Wanka kawai ta yi ta latsa kiran mamanta, bayan sun gaisa ta fashe da kuka, ta ma rasa ta ina zata fara fad'a mata?
"Kareema ya kin kirani kuma kina min kuka? Lafiya?" Ummanta ta tambayeta.
"Umma ba lafiya ba, wallahi ba lafiya ba." Ta kuma fashewa da wani kukan.
"Ya Salaam! Me ya faru? Ko Ummul-khair ba lafiya ne?"
"Umma bari na zo gidan na maku bayanin komai." Ta fad'a da shesshekar kuka.
"Kina a wannan halin ne zaki yi tuk'i? Bari na fad'a ma Abbanku yanzu gamu nan zuwa gidan." Ta katse kiran da sauri.
Minti arba'in ya sadasu da gidan Kareema, zaune ta ke bisa kafet ta had'a kai da guiwa, Khairat kuwa tuni ta yi bacci bayan ta gama sharar kukanta ganin Maminta na kuka. A daburce Ummanta ta yi gaba, Miemie da Abba a baya, "Kareema fad'a min abin da ya faru." Ta fad'a bayan ta dafa kafard'arta dan bama ta san da wanzuwarsu ba.
"Umma wallahi mugu ne, ya cucemu umma.." kuka ya kufce mata.
"Waye mugu me kuma ya maku?" Abba ya jefo mata wannan tambayar.
"Baban Khairat ne Abba, maciyi amana ne kuma mazinaci, Abba babu abin da gaugawa ta haifar min face dana sani! Na yi takaicin wannan hali da ya jefamu a ciki, dama tin kafin na aureshi sai da aka kira aka min wasu tambayoyi a kanshi amma na yi biris da maganar, soyayya ta rufe min ido, tsabar son ganin na yi aure ya sa babu binciken kirki aka d'aura mana aure."
"Ki mana bayani Kareema, yanzu me ya miki, ko ya sakeki ne?" Abban ya tambayeta.
"Bai sakeni ba Abba, amma zamana da shi ya k'are..." ta labarta masu kaf abin da ya faru.
Salati suka d'auka su duka, Miemie cike da tsana ta ce "Yaya Kareema dama na fad'a miki tun kafin aurenku, na ce miki sam hankalina bai kwanta dashi ba. Yanzu ga abin da ya faru."
"Mai faruwa ta riga ta faru. maganar a raba aurenku ma bata taso ba, kin riga kin goga fa, idan aka raba wa zai aureki? ko so kike ki dauwama babu aure bayan kuma da yarintarki?" Abba ya fad'a cike da damuwa.
"Abba na gwammaci zama babu aure a kan na ci gaba da zama gidan baban Khairat." Ta fad'a tana kuka sosai.
"Ba haka za'a yi ba Kareema, hak'uri zaki yi ki rungumi k'addara, domin kuwa duk d'an adam baya wuce k'addararsa, abin da duk Allah ya nufi ya sameka dole sai ya sameka, ki dage da addu'a a kan wannan halin da kike ciki, Allah zai fitar da ke. Ki barshi da Allah shi zai miki sakayya." Ummanta ta fad'a tare da goge hawayen daya fito mata.
Kuka ta kuma fashewa da shi ta rungumi k'anwarta suna kukan tare.
Wannan ke nan. Back to our story.
YOU ARE READING
SHI NE SILAH!
Romanceshi ne silar rugujewar farin cikin rayuwarta. shine silar shigar ta cikin kunci da bakin ciki. shi ne silar rashin gata hadi da galihu a rayuwarta. shin waye silah? ku biyoni a cikin wannan labarin inda zan warware maku zare da abawa.