15

1.2K 84 0
                                    

*SHI NE SILA!*
           😪😪😪

     Na Princess Amrah
              (NWA)
               2018

_Wannan shafin sadaukar ne ga *QUEEN MIEMIE* thanks for your care and support, Amrah loves Youh._

15~ Sakin Ikram Momy ta yi ta yi saurin karb'ar kayan hannun Naana mai aikinta.
    "Ina yininku?" Naana ta gaishesu. "Lafiya k'alau." Momy ta fad'a.
    "Ya mai jiki kuma?"
    "Alhamdulillah, jiki yayi sauk'i, gata nan sunanta Ikram, na yi sabuwar d'iya, autata ta tafi wata autar ta dawo." Ta yi murmushi tare da kallon Ikram cikin soyayya.
    Murmushi Ikram ta k'irk'iro ta ma Momy, kafin daga baya kuma ta d'aure fuskarta, saboda a ko wane dak'ik'a ta kan tuno da Ummanta, tunowa da Umman nata kuma ya kan gusar da duk wani farin cikinta. Wani hawayen ta ji yana k'ok'arin fito mata, da sauri Momy ta fara share mata shi da mayafinta tana fad'in "haba Ikram, dan Allah ki yi shiru haka nan ki daina mata kuka, wata k'ila ma yanzu haka Ummanki tana can tana jin dad'inta ke kuwa kina nan kina aikin zubar da hawaye, ki manta kin ji 'yata."
   Tana share mata hawayen wani sabo na fitowa, cikin kuka ta ce "ba zan tab'a iya mantawa da Ummana ba, saboda a dalilina ta rabu da gida, ta rasa magaifiyarta tun tana jinjira ko sunanta ba'a yi ba, ta girma tare da mahaifinta wanda ya zame mana garkuwa ni da ita, lokaci d'aya shima Allah ya d'auki tashi rayuwar, ya zame mata ni kad'ai na rage a rayuwarta, yau gashi ta tafi ta barni ba tare da ta hadu da danginta ba.." kuka sosai ya kufce mata.
    Khalid da ke tsaye cike da tausayi ya tsuguno inda ta ke, a daidai kunnenta ya kara ya ce "ke ja can da Allah raguwa da ke, ke wannan da ganinki ko dambe zan yi da ke sai na kayarki, idan kuma kina musu ne tashi mu gwada aga wanda zai kayar da wani." Bata san sanda ta yi dariya ba, "ai wallahi ba zaka iya kayar da ni ba, saboda akwai ni da k'arfi." Ta gwada masa damtsenta.
    "Akwaiki da k'arfi shi ne kuma ki ke ta yi wa 'yar Aljannah kuka? Insha Allahu Ummanki tana Aljannah yanzu haka tana ta sukuwa cikin tafkin madara da milo, ta yi katifa da bank'ararren rago sannan kuma ta yi filo da gasasshiyar kaza." Ya k'yafta mata ido d'aya.
    Wata dariyar ta kuma yi a karo na biyu. "Baka ji wallahi." Ta fad'a tana kuma yi masa dariya.
    Sosai wannan dramar tasu ta burge Momy, ko ba komai ta ga fara'ar Ikram, hakan ba k'aramin dad'i ya yi mata ba.
    "Nana zuba mata abincin ta ci, na san tana jin yunwa." Momy ta fad'a murmushi d'auke a fuskarta.
    "Allah na k'oshi bana jin yunwa, k'ila dai zuwa anjima zan buk'ata." Ikram ta fad'a.
    "Ji ko bakinta dan Allah, Allah na koci bana jin yunwa, kila dai juwa anjima jan bukata. Har da magana ma bata iya ba. Wallahi sai kin cishi ko kuma na miki d'ure, Momy kin tab'a ganin inda ake d'urawa mutum abinci?" Ya juya ya kalli mahaifiyarsa.
    Kai ta gyad'a ta ce "ban tab'a gani ba kuma ba zan fara gani a wurin 'yata ba, na san abincinta zata ci yanzu, ko Ikram d'ita?"
    "Ahh kar ma ta ci Momy, ku dai kawai ku zuba ido ku sha kallo, Baabah Naana zuba mata abincin, kuma kafin na k'irga goma idan baki fara ci ba ko, hmm... ni kad'ai na san abin da zan yi."
    Dariya duka suka d'auka, Momy ta ce "kai dai Khalid baka gajiya da barkwanci." Shima dariyar ya yi tare da zama a bisa kafet d'in da Naana ta shimfid'a masu.
     Farar shinkafa ce da vegetable soup, sai pepper chicken daban, zuba mata ta yi sannan ta zuba lemo a kofi ta mik'a mata, "ungo ki ci abinci kin ji?"
   "Hanzarta ki cinye a k'ara miki, kar wannan Khalid d'in ya kuma saka miki ido." Momy ta fad'a, "ko na baki a baki ne?"
    "Da na ji dad'i kuwa momy, Ummana ma idan ta ga ban ci abinci ba sai ta bani a baki, kin ga kin zama madadinta ke nan." Idonta ya cika taf da hawaye. Ganin haka ya sa Khalid saurin mik'ewa ya ce "kin gani ko Momy, ai dama na fad'a maku Ikram raguwa ce, ita magana ma kuka ta ke sakata, shi ne kuma zaki ce wai zaki iya kayar da ni, Allah ki zo mu gwada idan kin musa." Murmushi ta masa bata ce komai ba.
    A baki Momy ta ringa bata abincin tana ci, sosai ta ke ci saboda tsananin yunwar da ta ke ji, amma a haka wai da ta ce ta k'oshi ba yanzu zata ci ba.
    Sai da ta cinye tas sannan Momy ta hau bata naman tana ci, ta gama kuma ta bata lemo ta ajiye plate d'in a k'asa.
    "Dama irin abin nan ne wai ta k'oshi, gashi nan ta kwashe abinci tsaf kuma na san bata k'i an k'ara mata ba, su Ikram manyan k'asa." Pillow ta d'auka ta jefa masa tana fad'in "Allah yaron nan baka jin magana." Ta tunzuro baki.
    "Ke waye yaron? Amma yarinyar nan kin rainani wallahi, ki tambayi Momy ki ji na isa haihuwarki fa." Har da d'aure fuska ya yi irin da gaske ya ke d'in nan.
    "A tambayeni ta ina? Au shedar zur ka ke so na bayar ke nan, kar ki damu Ikram haka Khalid ya ke, idan yana zaune a wuri ba'a shiru, akwaishi da shegen surutu, haka kuma baya barin mutum cikin damuwa sai ya yi yanda ya yi ya sakaka farin ciki."
    "Ki k'yaleshi Momy zan yi maganinsa ai, dan yana ganina da drip ne, Allah zan rama ka bari na rabu dashi ka ga ikon Allah."
    Haka d'akin ya zama cikin raha da farin ciki, banda surutu babu abin da ke fita da barkwancin Khalid, sai da suka ga an kawo wata patient a d'akin sannan suka yi shiru dan kar su yi disturbing d'inta.
      Ko da dare ya yi Naana ta ce Momy ta koma gida ita zata kwana da Ikram amma sam Momy ta ce bata amince da hakan ba, ita zata kwana tare da ita saboda 'yarta ce.
    Hakan ce kuwa ta kasance, Khalid kafin ya tafi sai da ya tab'a barkwanci sannan suka tattara kayakin suka masu bankwana ya cewa Ikram "Yarinya Allah yau a ruwa ki ke, ina baki shawara da ki nemi air piece ki jona wak'a a waya kafin bacci ya d'aukeki, saboda nasarin Momy hana bacci ya ke yi, idan kuma baki nema ba ruwanki, ni dai kar na dawo ki ce min ta hanaki bacci, na fita hak'k'inki."
    "Khalid kai ko, yaro ya miyar da ni kakarsa? Allah ya shiryeka kai kam."
    "Ki barni da shi Momy, ni zan miki maganinsa, Allah dai ya bani lafiya na murmure ka gani." Ikram ta fad'a tana murmushi.
    Gwalo ya mata sannan ya fice Naana na binshi a baya.
    Bayan sun fita Momy ta ce "Khalid manyan k'asa, ba dai ya bar wuri bai saka mutanen wirin dariya ba." Saboda hatta da matar da ke jinyar mara lafiyar da aka kawo dariya ta ke, sosai Khalid ya bata dariya saboda yanda ta ga shi har uwar tasa ma ba k'yaleta ya yi ba.
     "Rayuwarku ta burgeni Momy, raha da farin ciki kawai ku ke yi" Ikram ta fad'a ta yi pillow da cinyar Momy tana mata susar kai sai bubbud'e yalwataccen gashin kanta ta ke.
    "Haka mu ke kam, banda yayanshi wanda ya ke bi ma, shi kam baya sakin fuska sosai, shima kuma asali ba haka ya ke, shekara daya da ta wuce ne ya koma haka."
    "Ayyah! Ya yi ciwo ne?"
    "Bai yi ciwo ba Ikram, tun da k'anwarsu autata wadda ke bi ma Khalid ta rasu ya koma haka, ta rasu ne sanadiyyar fyad'e da aka mata, wanda har yanzu kuma aka rasa gano wanda suka mata wannan ta'asar, ya d'auki alk'awarin ba zai tab'a daina bincike ba sai ranar da Allah ya d'auki rayuwarsa, tsananin shak'uwar da ke tsakaninsa da k'anwar tasa ya sa ya zama haka, babu ruwanshi da kowa sai ko Khalid da ke damunsa ko baya son magana sai ya sakashi, komai bak'in ranshi sai ya sakashi farin ciki, hatta da ni mahaifiyarshi baya fira da ni sai ko wani babban abu, tun yana da shekara goma sha biyar yana SS2 mahaifinsa ya masa jumping na shekara d'aya saboda yanda ya fahimci yana son zama likita, da shekara goma sha biyar d'in aka nema masa University of Madina, a can ya fara karatunshi lafiya lau, yanda kika ga Khalid da son fira da barkwanci to shi ma yayan nashi haka ya ke a lokacin, d'an son ban dariya ne k'warai. Shekara shida ya yi ya kammala medicine d'insa, yana da shekara ashirin da d'aya ke nan. Bayan ya gama ya dawo nan Nigeria ya yi house job d'insa, shekara d'aya ya yi ya kammala kuma ya tafi service. Da shekara ashirin da uku ya gama komai nashi sannan kuma ya koma Madina don ci gaba da karatunshi. A can ya karanci b'angaren neurology, karatun da ba kowa ke iya yinsa ba saboda yana da wahala sosai, ko kafin ya fara likitoci da dama sun bashi shawara akan kar ya karanci wannan b'angaren amma ya nace nan d'in ya ke so, da ya ke shi ya sa kansa kuwa ya ringa karatu sosai, shekara shida cif ya gama ya dawo nan. Tun da fa ya dawo ko wace asibiti suke buk'atarsa, saboda a duk garin Sokoto shi kad'ai ne wanda ya karanci b'angaren, kuma yanzu da dama mutane suna fama da matsalar data shafi nervous system. Yanzu haka yana aiki a asibiti da dama, dan kusan duk asibitin da ke cikin garin nan yana ziyartarta. Yanzu haka yau d'in nan ya tafi UK zai yi wani course na shekara d'aya.
    Ya dawo Nigeria bai fi da wata d'aya ba Nafeesa ta tafi makaranta aka saceta, sai da ta kwana biyu sannan b'arayin suka bugo waya wai Nafeesa tana hannunsu kuma sai an basu Miliyan tamanin sannan zasu saketa.
     Da dukiyarsu ta gado saboda dama mahaifinsu ya rasu tun sanda yayansu yana shekarar k'arshe na medicine ba consultant ba. Ko da aka kai masu kud'in suka ce a jirasu awa d'aya zasu kawota. Awa d'ayan na cika kuwa sai ga Feenah an jefo mana ita jini male male a jikinta, bata ko magana sai gwada mana gabanta da ta ke yi. A razane muka tafi da ita, kai tsaye asibiti muka nufa inda yayanta ya hau duddubata har ya gano mummunan fyaden da aka mata, taimakon gaggawa ya hau bata  amma ina, tuni rai ya yi halinsa. Tun daga wannan lokacin ya k'uduri aniyar d'aukar fansa ga duk wanda ya aikata wannan ta'asar, sai dai kuma babu wani labari, duk da hukuma da ta shiga maganar kuwa.
     Tsabar soyayyar da ke tsakaninsa da Feenah ya sa ya shiga wani hali bayan rasuwarta, babu ruwanshi da kowa, kullum daga kuka sai tunani, ya kai kusan wata d'aya a cikin wannan halin  ko wurin aiki ya daina zuwa kafin daga baya ya d'an samu sasaauci ya koma wurin aikinsa, amma fa babu wanda ke ganin fara'arsa sai Khalid ko kuma ni idan ya ga dama.
    Shekarunsa talatin ke nan yanzu, Khalid kuma yana da ashirin da biyar, k'anwarsu kuma kafin ta rasu daidai sa'arki ce, sha takwas gareta lokacin."
     "Allah sarki! Ashe dai kuma kun ga taskon rayuwa, case d'in fyad'e bashi da dad'i, nima kusan abin da ya faru da mahaifiyata ke nan ta haifeni."
    Cikin mamaki Momy ta ce "Da gaske? Me ya faru da ita?"
     "Labari ne mai tsawo, abin da ya faru shi ne..." Tun daga farko har k'arshe Ikram ta labartawa Momy, har da labarin asalin zuwan kakanninta Nigeria.
      Sosai Momy ta tausayawa rayuwar Ikram, har da kuka sai da ta yi, daga k'arshe ta ce mata "ni kuma na miki alk'awari zan samar miki da duk wani farin ciki da ya kamata uwa ta bawa 'yarta, zan zama wata fitila a rayuwarki, zan kula da ke tamkar yanda zan kula da 'yata Feenah idan tana raye, karatu kuma zaki yishi har sai kin ce kin gaji dan kanki. Kawo hannunki" Ikram ta mik'a mata tafin hannunfa. D'ora nata hannun ta yi ta ce "Daga yau kin yi sabuwar uwa, sunana Hajiya Safina, na yi alk'awarin rik'onki a matsayin 'ya har k'arshen rayuwata."
      Ikram ma ta ce "Na yi alk'awarin d'aukarki a matsayin uwa har k'arshen rayuwata." Suka rungumi juna cike da so da k'auna. Ni ma Amrah ba k'aramin dad'i na ji ba.

_gaisuwarku ta daban ce *RAZ NOVELLA*, Allah ya bar so da k'auna._

@wattpad: PrincessAmrah
Gmail: Amratuauwal20@gmail.com
Facebook: Amrah Auwal
Instagram: miss_amrahmashi
Watsapp me on 07037603276. For any comment.

SHI NE SILAH!Donde viven las historias. Descúbrelo ahora