46

864 67 0
                                    

*SHI NE SILA!*
           😪😪😪

              Na Princess Amrah
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
                           (2018)

_Godiya mara iyaka ga *maman Fareeda,* har ga Allah na ji dad'in yanda kika kula dani har kika sadaukar min da shafi guda sunkutukum na littafinki. Ban ma san hanyar da zan bin wajen gode miki ba. Ina kuke *RAZ?* Kuzo ku tayani nuna farin cikina ga wannan baiwar Allah. Na gode k'warai Allahu ya 'kara baseerah da 'daukaka. *Amrah* na miki irin soyayyar nan da ba kowa ta ke wa irinta ba._

46~  Murmushi Khalid ya yi had'e da mik'ewa ya ce "Kawu ni bara na wuce, akwai inda na ke son zuwa."
    A daburce Alhaji Kallah ya ce "To babu damuwa Saifullahi. Zaka ji komai cikin kwana uku." Ya yi murmushi tare da sake maimaita "Ehh, a cikin kwana uku zaka ji komai."
    D'an tauna lab'banshi ya yi had'e da fad'in "Bara na shiga mu gaisa da Mama, tana ciki ai ko?"
    "Ehh....ehh tana ciki fa, ehh ka je ku gaisa hakan ya yi." Alhaji Kallah ya fad'a.
     Ta 'daya k'ofar da zata shigar da mutum cikin gidan Khalid ya yi, Alhaji Kallah na biye dashi sai wani irin mugun kallo ya ke bin Khalid da shi har suka isa madaidaicin parlor'n gidan. Wata mata ce zaune ta hakimce bisa luntsumammun kujerun royal da suka ji ado, ta sha wani rantsattsen leshi kalar jaa, idonta sanye ya ke da medical glasses, wuyanta kuwa tafkekiyar sar'kar zinare ce a jiki.
   Ganin Khalid yasa matar sakin murmushi tana fad'in "Sannu da zuwa d'ana Khalid. Sannu sannu, iso ka zauna." Ta gwada masa kujera da hannu.
     Zaman kuwa ya yi kamar yanda ta bashi izini, da murmushi a fuskarsa ya gaishe ta ta amsa masa da sakin fuska. "An kawo mana ziyara ke nan yau." Matar mai suna Hajia Adama ta fad'a har yanzu bata daina smiling ba.
       "Wallahi kuwa, na zo wurin Kawu ne kan maganar 'yan kud'ad'en nan namu, da ya ke kin san an saka ranar auren Yaa Haidar, shi ne muka ga ya kamata mu raba saboda kowa ya san inda ya dosa."
    Da fara'a Hajia Adama ta ce "Gaskiya kun yi tunani mai kyau. Ko nima kaina na jima inama Alhaji maganar ya baku hak'kinku haka nan saboda ai duk kun girma, dama dan ana ganin kamar akwai k'uruciya a tattare daku ne. Oh! Ashe Haidar an tashi aure, gaskiya Hajia Salma bata da kirki yanzu, shi ne ko ta sanar mana?"
    "Ai da ya ke yau ne duka aka yanke maganar auren nashi. Na san zata sanar da kowa ai." Khalid ya fad'a.
    "To Allah yasa alkhairi, insha Allahu zan kirata. Aliyu Haidar dai Allah ya yi ba da Rabi'atu za'a yi ba, na san har kuka sai ta yi idan ta ji an saka ranar aurensa."
    Alhaji Kallah da tun d'azu ya cika fam da takaicin kalaman matarsa sai a sannan ya ce "Nima kaina na so a ce mun had'asu aure ko dan zumuncinmu ya sake k'arfafa amma Allah bai nufa ba."
     Hajia Adama ta ce "Hakane kam. Allah yasa hakan  shi ya fi zama alkhairi."
    Mik'ewa Khalid ya yi ya ce "Bara na tafi momy, wata 'kila idan kawu bai kirani zuwa gobe ko jibi ba ni zan dawo. Wai ya maganar Umari? Har yanzu yana Italy d'in kuwa?"
    "Umari ai ya jima da dawowa, ashe Alhaji bai fad'a maku ba? Gaskiya kuwa ya kamata ya zo ya gaishe da Hajia Salmah, saboda itama d'in uwa ta ke gare shi. Bari ya dawo, yau ko gobe insha Allahu zan turo shi, ai bai kamata a ce ya dawo har kusan watanni biyar amma bai zo maku ba."
    Murmushin gefen baki Khalid ya yi had'e da yi mata bankwana ya tafi. Alhaji Kallah kuwa wani irin kallo kawai ya ke masa, bayan ya tafi ya kwashe da dariya had'e da fad'in "Ka yi fatan rayuwarka ta kai gobe ko jibin." Ya koma d'akinshi sai tufk'a da warwara ya ke.

     ***
           Da yammacin ne kuma Ikram da momy suka shirya domin zuwa asibiti su duba Halle, su biyu kawai suka tafi Ikram ke jan motar suna yi suna 'dan tab'a fira, firar abin da Alhaji Kalla ya masu.
    Ko da suka isa asibitin Halle kuka kawai ya ke, cike da tashin hankali Ikram ta ce "Lafiya kake kuka? Ko jikin ne? Ba kuka zaka yi ba, addu'a zaka yi ita ce makamin mumini."
    Mallam Maharazu ya ce "Wannan kukan da kuka ganshi yana yi tun d'azu da likita ya dubashi ya ke yinsa, na yi na yi dashi ya fa'da min damuwarsa amma ya k'i, na tambaye shi ko ciwon ne ya ce a'a."
     Cike da tausayi momy ta ce "Ai ba kuka zaka yi ba bawan Allah! Addu'a ce kawai zata taimake ka. Kana dai shan magungunanka ko?"
     "Kin ga magungunan nan tun d'azu na siyo da kud'a'den da kuka bashi, ya sha ya 'ki sha sai aikin kuka, ni kuma na ga duk da Allah ya ke da waraka amma maganin ma yana da nashi tasirin, kusa baki ko zai daure ya sha."
     Da k'arfin hali Ikram kamar zata yi kuka ta ce "Dan Allah baba ka daure ka sha magani. Kaga baka da lafiya fa, maganin ne kawai zai maka amfani. Ko ka fi son allura na kira likitan ya canza maka magungunan zuwa allura?"
    Kai ya gyad'a alamar a'a. "Yanzu me ya ke maka ciwo?"
     "Babu.." ya fad'a wani hawayen na zirara daga idonshi.
    "To mesa kake kuka?" Ta sake tambayarshi.
     "Ina kuka ne saboda munanan halaye na, ban kasance mutumin kirki ba ni Halle! Alhakin mutanen dana zalunta ma kanshi ba zai k'yale ni ba, zai iya kasantuwa shi ne ya ke bibiyata har i wannan lokacin..." wani kukan ya ci k'arfinsa.
     Kallo kawai su ke binsa da shi, to wane irin mummunan aiki ne ya aikata wanda har ya ke ikirarin zai iya bibiyarsa?
    "Koma dai miye ka yi shiru dan Allah. Ka ga nan asibiti ce ba wurin tonon asiri ba. Ka dage da addu'ar samun sau'ki. Ka ga idan ka samu sau'ki hakan zai baka damar komawa ka nemi gafarar wa inda ka zalunta d'in." Momy ce ta yi wannan maganar cike da tausayin Halle.
     Kai ya gyad'a sosai ya ke kuka ya ce "Kayya! Kayya!! A ina zan same su na basu ha'kuri? Idan ma na same su ya za'a yi su gafarta min bayan irin zaluntarsun da na yi? Allah gani gare ka ya Allah!" Kuka sosai ya ke.
     Mallam Maharazu ya ce "Ka daina wannan maganganun Halle, ina tunanin ko duk zafin ciwon ne ya saka wannan maganar."
     "Ba zafin ciwo yasa ni yinsu ba, cikin hankalina na ke sarai. Yanzu na tabbatar idan na ga wasu ba zan ga wasu ba, wata k'ila wasu cikinsu ma sun mutu."
     Ikram sosai ya bata tausayi, da sauk'i ma tun da har ya san ya aikata kuskure a baya, ke nan ya nadama.
    "Yanzu dai ka cire wannan damuwar tukuna har sai Allah ya baka lafiya. Insha Allahu zaka same su kuma duk zasu yafe maka." Ikram ta fad'a ha'de da share guntun hawayen tausayi.
     "Ina fatan hakan Ikram. Sai dai na san ku kanku idan kuka ji labarina sai kunyi tir! Had'i da Allawadai da halina da kuma mutum irina."
      Sosai su ke mamakin wannan mutumi, sun rasa wane abu ne ya aikata wanda har ya ke ma kansa wannan maganganun kuma gabansu su 'din da bai tab'a sani ba sai cikin 'yan kwanaki k'alilan.
     "Ni d'in mutumin wani k'auye ne can gabacin Kano. Ban wani girma ba sosai iyayena suka rasu, na gaji dukiya mai tarin yawa a wurinsu, hakan yasa na ke fantamawa yanda na ke so, sam ban samu tarbiyya mai kyau ba. Bani da aiki sai yi wa mata ciki ana zubarwa, ga bin maza da na ke, kud'in da gare ni yasa kowa ya ke so na. A duk cikin matan da na tab'a yi wa ciki mutum d'aya ce wadda bata yarda an zubar ba, sunanta *Rumana,* ban sani ba shin tana raye ko bata raye? Ta haifi cikin da rai ko kuwa babu rai? Mace ta haifa ko namiji? A wane hali su ke ciki yanzu? Allah ka'dai ya barwa kansa sanin wannan. Matar mai garin garinmu na nema hakan yasa aka yi min korar kare daga garin tare da fad'in 'kar a sake ganin na waiwayin garin, idan ba haka ba sai an min hukunci mai tsanani.' Hakan yasa na dawo cikin garin Kano da zama a k'ark'ashin wani mutumi mai suna Alhaji Ahmad. Ni na zama mai gadin gidanshi saboda a lokacin bani da tsiyar komai. Sosai mutumin ya ke kyautata min, kwatsam wata rana ya tare ni da maganar wai an masa transfer'n wurin aiki,  zai tashi daga Kano, dama shi 'din d'an sanda ne, wai an miyar dashi Sokoto, idan zan iya binshi mu koma can to, idan ba zan iya ba kuma babu damuwa zai sallame ni. Amincewa na yi na bi Alhaji ahmad saboda mutum ne mai kyautatawa da sanin darajar d'an adam.
     Bayan mun dawo nan garin da kimanin shekara bakwai Allah ya d'auki rayuwar Alhaji Ahmad. Iya tashin hankali na shige shi, saboda bani da sauran gata.
    Wata rana matar Alhaji Ahmad ta same ni zaune na yi tagumi ta zauna kusa da ni ta fara min magana "Halle wata magana ce tafe da ni. Gani na yi tun da dai Alhaji ya rasu kawai ka yi hak'uri da aikin nan, tun da dai muma ba a ka'rkashin kowa muke ba yanzu. Ka yi hak'uri kawai ka nemi wani aikin."
     Hankalina ya tashi sosai, dubu goma ta bani wai in ja jaarii, duk da raina bai so rabuwa dasu ba haka na bar gidan rik'e da 'yar jakar kayana.
     A lokacin ne na fara kuka sosai, saboda duniya ta juya min baya, ni Halle kamar ba nine wanda ke taka mutane yanda na ke so ba, kamar ba ni ne wanda ke fantamawa da ku'di ba. Ina tafe ina kuka sosai har Allah ya had'ani da wannan bawan Allah'n, mallam Maharazu.
      Shi ya taimaka ya bani wurin zama a wani shago da ke jikin gidanshi, duk da shima d'in haya ya ke a gidan.
     Shima kanshi d'in ba wani karfi ne dashi ba, ba ko yaushe ake samun yin girki a gidansa ba, duk ranar da aka yi kuwa sai an aiko min, idan ba'a yi ba a cikin dubu gomar da Hajia ta bani na ke siyan abinci. Da haka har ku'din suka k'are.
      Daga nan ne na koma aikin k'arfi, tun da yarintata na ke aikin wahala har na girma sosai.
     A iya wannan shekarun kuwa kullum cikin sha'awar namiji na ke, wani lokacin idan na kasa daurewa haka zan je jikin bango in riga gurza abin fitsarina a jiki har sai na ji ciwo jini na zuba. Hakan zai sa na d'an samu sassauci. Haka dai na ci gaba da rayuwa cike da wahala da 'kask'anci.
     Kwatsam! Kimanin wata d'aya da ya wuce ne Allah ya had'ani da wani bawan Allah mai suna Alhaji M. Lawal, ganina wahalalle yasa ya taimake ni da ku'di sosai har ina mamaki. Washe gari ya sake dawowa da ledoji k'unshe da abubuwan dad'i, har da kayan abinci.
     A nan ne ya ke sanar dani bu'katarsa, abunku ga mutumin da ya saba, dad'i na ji sosai wanda ban iya b'oye shi ba har shima d'in ya gane, ganewar da ya yi ce ta tattabar masa da cewa dama can na saba yi.
      Sosai mu'amalata da M. Lawal ta yi nisa, inda ya ke biyan buk'atars da ni, nima kuma na ke biyan buk'atata da shi.
       Wanann gallababben ciwon cikin ne ya addabe ni tun bayan dana fara mu'amala da M. Lawal, kwatsam ranar na tashi da wani irin jiri sosai wanda ina mi'kewa tsaye na zube, ko da na farka na ganni a gadon asibiti..."
     Tun sanda ya fara masu bayani Ikram ta mik'e tsaye, ko da ta ji ya ambaci sak labarin da ummanta ta bata na yanda Halle ya mata ta fara jaa da baya tana gwadashi da yatsa. Bata iya furta komai ba sai ruwan hawaye da ta ke.
      Runtse idonta ta yi cikin kuka ta ce "Allah ya isa tsakanina da kai! Inda ace na san kai ne daa tun farko ban tsaya har na taimake ka ba. Allah ya isa Halle! Ba zan tab'a yafe maka ba!"
     Su duka mamaki su ke, har da Khalid da Haidar da tun d'azu suna tsaye suna sauraren Halle. Saboda sanda Khalid ya koma gida mai gadi ya shaida masa cewa su momy sun tafi asibiti, Haidar ya kira ya ce su tafi asibitin gudun kar Alhaji Kallah yasa a masu wani abu, already Haidar ya kira Marwan har ya had'ashi da b'oyayyun sojoji.
     Babu wanda bai yi mamakin kalaman Ikram ba,  momy kam ta d'an fara fahimtar wani abu, sai dai ta kasa gasgatawa.
      Da 'kyar Halle ya samu ya tashi yana kallon Ikram "Duk da ban sanki ba, ban san a ina kika sanni ba, amma ina mamakin abin da yasa kika fad'i wannan maganar."
      Tuni ta samu ta yi ya'ki da ruwan hawayen suka tsaya, ido cikin ido ta kalle shi ta ce "Halle..." sai kuma ta yi shiru.
      Murje idonta da ya yi jajur ta yi ta ce "Ni ce Ikram, d'iyar Umma Rumana wadda ka ma ciki a k'auyenku.."
        Ido ya zaro sosai ya 'kara kallon Ikram, ya kasa fa'din komai sai dai kuma ya kasa d'auke kallonshi daga gare ta.
     "Ni ce wadda baka so na fito duniya ba, wadda ka so ummana ta yi kisan kai dan kar na sha'ki iskan duniya. Ka cuce ni Halle! Ka ja min gori ga d'umbin al'umma, ka ja wa Ummana *ba'kin jini* ga mutane. Kowa ya tsane ta saboda mugun dashe daka mata. *kai ne silar* wanzuwar ba'kin ciki a cikin zuciyar Ummana! Tir da hali irin naka! Ummana ta mutu da fushinka, ta dad'e da barinka ga Allah ya mata sakayya."
       Tana gama fad'in haka ta fasa kuka da k'arfi had'e da zubewa k'asa a sumammiya.


_Na gode sosai da yanda kuke bibiyar wannan labarin. Na gode da k'ara min 'kwarin guiwar da kuke yi a kowane lokaci._

*team Ikramhaidae*
*team Ikramkhalid*

SHI NE SILAH!Tahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon