*SHI NE SILA!*
😪😪😪Na Princess Amrah
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
(2018)70~ Da sauri Salim ya ƙarisa ta inda ya ga ana fitowa idan an sauko daga jirgi.
Tun daga nesa ya hango irin gadajen nan na cikin jirgi wanda ake ajiye su musamman saboda ɗaukar marasa lafiya.
Departure aka nufa da shi Salim na hangensu hakan yasa ya ƙarisa shigewa ciki.
Da sauri ya isa inda Khalid ya ke kwance yana faɗin "Khalid!"
Khalid kuwa dama idonshi biyu yana dafe da zuciyarshi da har yanzu bata daina yi masa ciwo ba. A hankali ya ce "Salim.." Haɗe da ƙoƙarin ɗago kanshi.
"Khalid haka ka koma? Kuma a hakan ne ka so kar na faɗa wa kowa matsalarka?" Ya faɗa cikin muryar tausayi ganin yanda Khalid ɗin ya rame sosai kamar ba shi ba. Daga ido sai hanci kawai ke da auki a fuskar, duk ya canza kamanni kamar wanda ya shekara biyu yana jinya.
"Dan Allah ku kamo shi ga motar can wurin fakin." Salim ya faɗa da raunanniyar murya.
Ma'aikatan jirgin suka ɗauko shi suka bi bayan Salim da shi. Parking lot suka ƙarisa inda motar Salim ɗin ta ke ya buɗe gidan gaba tare da kwantar da kujerar suka ɗora Khalid a kai. Wasu kuma suka biyo su da kayayyakinshi.
Godiya ya masu sannan ya zagaye ya buɗe nashi ɓangaren ya rufe ya tayar da motar.
A hankali ya ke tuƙin yana faɗin "Baka kyautawa kanka ba ko kaɗan Khalid! Ka ga abin da zurfin ciki ya haifar maka ko?"
Shiru Khalid ya yi ba tare da ya furta komai ba.
"Yanzu inda basu tirsasaka a kan ka bada lambar wani ba ke nan da a haka zaka yita zama babu wani naka a kusa da kai ko?"
Sai a lokacin cikin ƙarfin hali Khalid ya ce "Salim ina son ka san cewa soyayya wata aba ce wadda sam mutum ba zai iya fasaltata ba. Matuƙar baka shiga tarkon so ba ba zaka taɓa fahimtar wani abin ba. Soyayyar da na ke wa Ikram ita ce ta zautar da ni har haka, tasa na ji bana sha'awar kowa daga ɓangare na, na yi sha'awar kaɗaicewa a inda babu wani makusancina. Ko kaɗan kar ka ga laifina a kan abin da na aikata, komai na duniya yana da *sila,* ni kam Ikram ita ce *silar* rayuwata. Gashi kuma na rasata rashi na har abada! Ta tafi inda bana tsammanin zata dawo gare ni. Duk yanda na so na cire ƙaunar Ikram daga zuciyata abin ya faskara, saboda soyayyar da na ke mata ta samo asali ne tun daga ranar da na fara ganinta har na bada jinina aka ƙara mata. Salim ta ya kake tunanin ba zan shiga damuwar da har zan kamu da ciwon zuciya ba? Tell me Salim..." Kuka sosai ya ci ƙarfinsa.
Dariya Salim ke yi iya ƙarfinshi ya kasa furta komai sai ci gaba da tuƙinshi da ya ke yana ɗan bubbuga sitiyari.
Binshi Khalid ya yi da kallo cike da mamakin dariyar da ya ke yi. Shi yana faɗa masa ne dan ya tausaya masa ko kuma ya bashi shawara amma ya zage sai dariya ya ke.
"Mtsw!" Ya yi tsaki haɗe da ɗauke kanshi daga fuskantar Salim ɗin da ya yi ya miyar ɓangaren da ƙofa ta ke.
Da ƙyar ya iya tsayar da dariyar ya ce "Na baka haushi ko?"
Banza da shi Khalid ya yi, iya ƙuluwa ya ƙulu da dariyar da Salim ke masa.
Samu ya yi ya yi shiru kafin ya ce "Amma Khalid ka tuna ranar da muka ɗauko Ikram daga makaranta sun gama jarabawa, har kake faɗa min irin son da kake mata? Tun a lokacin na baka shawarar ka faɗa mata ta cikinka amma ka ƙi...to ka ga abin da zurfin cikinka ya haifar maka..."
"Enough Salim! (Ya isa) Duk mai faruwa ta faru. Yanzu haka na tabbatar da an ɗaura auren Yaa Aliyu da Ikram. Dan haka duk wannan maganar a barta."
Wuri Salim ya nema ya faka motar sanann ya ce "Albishirinka."
Shiru Khalid ya yi yana mai tsananin jin haushin Salim.
"Idan baka ce goro ba ba zan faɗa maka wannan daddaɗan zancen ba." Salim ya faɗa bayan ya fuskanci Khalid.
"Ka faɗi abin da zaka faɗa Salim. Bana iya doguwar magana." Khalid ya faɗa a ƙule.
"Duk doguwar maganar da ka yi ɗazu waye ya maka? Look maza, ban sanka da fushi ba. Tun da na ke ban taɓa ganin mutum irinka ba Khalid, mutumin da bai san wani abu wai shi fushi ba, bai san miye ɓacin rai ba. Duk yanda mutum zai maka abu dan ya baƙanta maka rai ba zaka taɓa nuna masa hakan ba. Kuma a ko da wane lokaci ina alfahari da hakan.
Khalid abin da na ke son faɗa maka shi ne an ɗaura aurenka da Ikram yau ɗin nan. Sannan kuma Yaa Haidar da Miemie ƙawar Ikram."
Cikin ƙarfin hali Khalid ya fara ƙoƙarin tashi amma ya kasa, kasantuwar ya daɗe a kwance, ko cikin jirgi a kwance ya ke har suka iso.
"Koma ka zauna Khalid. Bayan mun gama waya da kai....." Salim ya kwashe komai ya faɗawa Khalid tun daga farko har ƙarshe.
Take farin cikin Khalid ya kasa ɓoyuwa. Jin ya ke kamar a mafarki ne, mafarkin da ya ke yawan yi wai ya auri Ikram shi ne yau ya kasance da gaske.
A hankali cikin fara'a ya furta "Dama Ikram ta daɗe tana sona? Me ya hana ki faɗa min Ikram? Ko alama ai sai ki nuna min idan ba zaki iya faɗa min ba."
Salim ya yi murmushi ya ce "Kai da kake namiji baka iya faɗa mata ba sai ita mace ce zata iya faɗa maka? Khalid akwaika da abin dariya." Ya dai-daita zamansa tare da tada motar suka ci gaba da tafiya.
Sai da suka fara biyawa ta asibitin Dr. Rafeeq, Salim ya bada refer letter ɗin Khalid aka karɓa.
Sun nemi su kwantar da shi amma ya ƙi yarda, ya ce wai zai ringa zuwa kullum domin duba lafiyar tasa.
Fara'a kwance a fuskarsa Salim ya kamashi suka isa mota, da ƙyar da ƙyar ya ke tafiya saboda jimawar da ya yi bai yi tafiyar ba.
Ƙarfe shida da rabi suka isa gidan Momy, har a lokacin gidan cike ya ke da mutane kamar ba yamma ba.
Bayan Salim ya kashe motar ya ce "Ka daure ka tattaka ƙafar sosai yanda kowa ba zai gane baka da lafiya ba."
Khalid ya yi murmushi ya ce "Ai dole a gane bani da lafiya, ko ba'a faɗa min ba na san na rame sosai Salim. *Dafin so* ya nemi illatani."
"Uhm." Kawai Salim ya faɗa haɗe da fita ya zagaya ya buɗewa Khalid ƙofar suka fita tare.
Kafin su ƙarisa gidan sai ga Haidar ya fito riƙe da keys a hannunshi.
Da sauri ya rungumi Khalid yana murmushi sosai cike da murna. "Ɗan uwana barka da isowa. Ya ƙarfin jikin?"
"Jiki alhamdulillahi big bro! Ya muka same ku?"
Bayan ya janye Khalid daga jikinshi ya ce "Lafiya ƙalau angon Ikram. Kai ko?" Ya ɗaure fuska cikin wasa. "Zurfin cikinka ya nemi ya ja mana matsala. Ka kyauta ai. Ka ƙara samun sauki akwai zama na musamman yaro, gwara ma tun wuri ka nemi kalmomin defending (kare) kanka."
Dariya suka yi su duka. Salim ya ce "Gidan babu mutane da yawa ne mu shiga?"
Haidar ya ce "Akwai mutane sosai kam. Gwara ma ku haƙura kawai ku koma mota, sai in kira maka Momy'n a waya ta fito ta dubashi."
Khalid ya ce "Yauwa har na ji daɗi, kuma..." Tun bai ƙarisa ba Haidar ya ce "Har Ikram ɗin ma dan na san ita kake son faɗi."
Duƙar da kanshi ya yi cikin kunyar ɗan uwanshi. Salim na dariya suka koma mota, Haidar kuma ya latsa kiran momy a waya ya shaida mata ta zo waje ga Khalid ya iso.
Da murnarta ta iso tana sauri ta ƙarisa bakin motar, a buɗe ta ke yana kwance sai Haidar tsaye riƙe da murfin mota suna magana.
"Oyoyo ga ɗana." Ta faɗa da fara'a sosai ƙunshe a fuskarta.
Murmushi ya yi haɗe da faɗin "Barka da hidima momy."
"Sannu ɗana. Ya ƙarfin jikin naka?" Ta tambaye shi cikin so da ƙaunar uwa da ɗa.
"Jiki ya yi sauƙi sosai momy. Ya taro?" Ya tambaye ta.
"Taro gashi fa munata sha. Ai ya kusa zuwa ƙarshe ma. Ƙarfe takwas na daren yau za'a kai maka amaryarka insha Allah."
Rufe fuskarshi ya yi cike da kunya, sai dai kuma a zahirin gaskiya ya matuƙar jin daɗi, ji ya ke a rayuwarshi bai taɓa yin farin ciki irin na yau ba.
"Salim an kaishi asibiti dai ko?" Ta tambayi Salim.
"Ehh Momy. Sun so su kwantar da shi ma ya ƙi, wai ya ji sauƙi kullum zai ringa zuwa ana dubashi tun da akwai magunguna a hannunshi."
Caraf Haidar ya yi ya ce "Haba wane magunguna kuma bayan ya samu babban maganinshi? Ai Ikram ita ce cutarshi kuma ita ce warakarshi. Ku bashi nan da kwana biyu zuwa uku ku gani, duk ramar nan sai kun ga babu ita. Babu abin da ya fi daɗi a rayuwa sama da mutum ya auri wanda ya ke so. Na tayaka murna ƙwarai da gaske ɗan uwana. Allah ya ƙara maka lafiya ya baka zaman lafiya da Ikram. Allah ya bata ikon yi maka biyayya da yin koyi da halayen Nana Aishatu (R.A) kai kuma Allah ya baka ikon yin haƙuri da juriya da ita. Salim ka kaishi gidanku ya samu ya yi wanka ko ya ɗan ji daɗin jikin nashi."
Momy ta ce "Haka ya kamata kam. Ni barin koma ciki in ma Ikram albishir. Kafin ƙarfe takwas ɗin sai ku zo Salim."
Ta koma cikin gida, Haidar kuma ya nufi can nesa da gida inda Marwan ke jiransa dan yana can tsaye da Khaleesat suna fira bai ma kula da su Khalid ɗin ba.
YOU ARE READING
SHI NE SILAH!
Romanceshi ne silar rugujewar farin cikin rayuwarta. shine silar shigar ta cikin kunci da bakin ciki. shi ne silar rashin gata hadi da galihu a rayuwarta. shin waye silah? ku biyoni a cikin wannan labarin inda zan warware maku zare da abawa.