36

814 54 0
                                    

*SHI NE SILA!*
           😪😪😪

              Na Princess Amrah
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
                           (2018)

36~  Isar su Momy Station suka ma Inspector bayanin abin da ya ke tafe da su, Haidar ne ya iya yin bayanin saboda Momy da Ikram kuka kawai su ke, tun a cikin mota ya ke fama dasu su yi shiru amma sun 'ki. Shi d'in kanshi k'arfin hali ne kawai ya hanashi zubar da hawayen, sai zuciyarsa da ta ke ta faman tafarfasa.
    Inspector ya d'auki duk bayanan da Haidar ya yi sannan ya ce "Insha Allahu zamu yi bakin 'kok'arinmu dan ganin mun gano Khalid. Amma kafin nan, baku san wasu mak'iyanshi ba?"
    Momy cikin k'arfin hali ta ce "Yallab'ai Khalid baya da abokin fa'da a rayuwarshi. Ko ka yi mishi abu da niyyar ya yi fushi ba zai ta'ba sakashi yin fushin ba. Haka ya ke tun yarintarsa baya fad'a da kowa."
    Ajiyar zuciya ya sauke ya ce "To babu damuwa. Insha Allahu za'a sameshi ku kwantar da hankalinku."
    Gaisawa suka yi da Haidar tare da barin station d'in ba tare da kowa ya ce uffan ba.
    Sokoto tv suka nufa daga nan inda suka bayar da sanarwar b'atar Khalid tare da tura masu hotonshi a waya. Bayan sun biya kud'i aka kar'ba lambobin wayarsu sannan suka tafi. Daga nan d'in ma ba gida suka wuce ba, sai da suka fara nufar MTN Office.
    Lambar Khalid ya bayar ya ce a masa bincike a kanta, a kuma yi tracing layin ko za'a gano location d'in da ya ke.
    Iya bincike sunyi sai dai abin da kawai suka iya ganewa shi ne; wai near Mr. Bigs aka yanke amfanin layin, sannan kuma wayarshi ta k'arshe da Haidar d'in  ya yi tun daga nan babu wanda ya yi waya dashi.
    Gida suka zarce daga nan cike da takaicin faruwar wannan al'amarin.
     Kowa d'akinshi ya zarce bayan sun isa gida, hakan ya tabbatarwa Naanah mai aiki cewa babu nasara a tafiyarsu. Ita d'in ma tun da suka tafi suka barta ta ke ruzgar kuka.

***
    Bayan Ikram ta koma d'aki ne Barr. Kareema ta kirata. Gaisawa suka yi sannan ta ce "Saura kwana uku fa a fara zaman kotu, har ma an aika masu da sammaci."
    Tana fa'din haka sai da gaban Ikram ya fad'i, 'to ko dai hakan yana da nasaba da b'atar Khalid ne?' Ta ayyana a ranta. A zahiri kuma ta ce "Yaya Kareema Yaa Khalid ya b'ata tun jiya ba'a ganshi ba. Yanzu haka daga station mu ke har yanzu dai babu wani labari a kanshi."
    Salati Kareema ta da'uka cike da mamaki ta ce "Ya bata? To ina ya shiga? Ko kuna zargin saceshi aka yi?"
    "Allah masani Yaya Kareema." Ta fashe da kuka.
    "Ya isa haka to ki daina kuka. Bana zargin saceshi aka yi gaskiya. To waye zai saceshi? Na tabbatar cewa dangin mahaifinsa ba zasu tab'a saceshi ko kuma su saka a saceshi a halin yanzu ba. Saboda su kansu a tsorace su ke tun daga sanda aka tura masu da sammaci. Idan kuwa saceshin aka yi to tabbas wasu ma'kiyan ne gareshi na daban wanda babu wanda ya sansu."
    Ajiyar zuciya Ikram ta sauke ta ce "Haka ne Yaya Kareema. Amma ni a iya sanina Yaa Khalid bashi da wani mak'iyi, shi fa ko fad'a baya yi, ko mutum ya nemeshi da fad'a a k'arshe sai dai ya ji kunya, dan ba zai tab'a biyeshi su yi fad'an ba."
    "Ba a nan ta ke ba Ikram. Ki raba kanki da mutanen yanzu da kana bacci wani na maka nasari. Amma dai nima bari zan yi nawa k'o'karin, insha Allahu Khalid zai bayyana nan da gobe ko jibi. I promised!"
    "Na ji dad'i sosai Yaya Kareema. Allah ya taimaka ya bada iko." Ikram ta fad'a cikin nishad'i dan har ga Allah ta ji da'din kalaman Kareemah.
    Tsinke wayar suka yi sannan ta nufi ban d'aki ta yi wanka da alwala ta fito. Salla ta gabatar sannan Baabah Naanah ta kirata a kan ta zo ta ci abinci. Abincin ta tasa a gaba amma ta kasa ci, da zarar ta kai loma d'aya baki ta tuno da b'atar Khalid sai ta ji komai ya fice mata. B'atar mutum fa ba b'atar kaza ko zakara ba ce, wanda da zarar an nema ba'a samu ba za'a hak'ura. Hawaye ta ji yana zubo mata wanda bata san sanda suka fito ba.
   Momy kam dama ta ce kar a zubo mata abincin dan ta san ba iya cinshi zata yi ba. Kuka kawai ta ke tana k'ara tuno Khalid d'inta mai fara'a, barkwanci da kuma  annashuwa, mai san saka mutum farin ciki a duk sanda ya ganka cikin damuwa. Mai kula da damuwarka fiye da tashi damuwar.
    Saukowa ta yi daga dining d'in  ta zubo wani abincin a plate tare da nufar inda Momy ta ke ta zauna, hannunta ta d'ora akan cinyar momy bayan ta yi 'kok'arin tsayar da nata hawayen.
   "Dan Allah momy ki daina kukan nan, bana son wata cutar ta sameki. Insha Allahu za'a samu Yaa Khalid babu abin da zai sameshi."
   "Ikram ke nan, kamar da wasa fa haka b'atar Feenah ta kasance, sai da ta kwana ta yini sannan aka nemi kud'i muka kai. Amma kin ga shi har yamma ta yi ana neman yin magrib kud'in ma an k'i nema. Bana son wani abu ya samu Saifullah..."
   Saurin tsayar da ita Ikram ta yi ta ce "Babu abin da zai sameshi sai alkhairi. Insha Allahu zai bayyana."
    "Ina fatan hakan Ikram." Momy ta fad'a a bayyane.
    Duk abin nan da ke faruwa Haidar na tsaye yana saurarsu. A karon farko ke nan da ya ji Ikram ta burgeshi. 'Ko wane lokaci tana k'ok'arin saka mahaifiyata a farin ciki. Tana d'aukar damuwar family'na a matsayin tata damuwar. Ko shakka babu Ikram yarinyar kirki ce, halin 'kin nuna damuwar da na ke mata sam bai dace da ita ba.' Maganganun da ya ke yi ke nan a zuciyarshi kafin ya tako ya iso inda su ke.
    Zama ya yi ba tare da ya ce komai ba, sai dai kallon yanda Ikram ke bama Momy abinci a baki kawai ya ke.
   Tana bata abincin tana 'dan k'irk'iro murmushi wanda zan iya kiranshi da yak'e. Da zarar momy ta ce ta k'oshi sai Ikram ta ce dan Allah ta d'an k'ara kad'an. Da haka har ta ci sosai sannan ta je ta dama mata kunun alkama wanda ta san momy na sonshi sosai. Madara ta zuba a ciki sannan ta zuba zuma saboda momy ba wani san suga ta ke ba. A kofi ta zubo ta kawo mata ta bata. Sosai momy ta ji dad'in kunun, sai da ta shanyeshi tas sannan ta ajiye kofin. "Na gode sosai Ikram, Allah ya miki albarka."
   "Ameen momy. Amma fa kin san bana son godiyar nan da kike min, ashe dama idan 'ya ta ma uwarta abu sai ta mata godiya?"
    Murmushi kawai ta yi ba tare da ta ce komai ba.
    Wani irin yanayi Haidar ya jishi, tun da ya ke a rayuwarsa in banda Feenah da mahaifiyarsa ba'a tab'a wata 'ya mace da ya ji ta burgeshi ba kamar Ikram. Ashe dama haka ta ke? Saisa a ke so ka kyautata zato ga mutum, kallon wata marar kunya kuma tsagera ya ke mata, bai tab'a tunanin cewa haka ta ke ba, har ta damu da Momy haka? Tashi ya yi jiki babu k'wari ya nufi d'akinshi.

***
Bayan kwana biyu.
    Zaune ya ke ya buga uban tagumi, kukan ma ya gaji ya daina, sai mamakin wanda ya aikata masa haka kawai ya ke.
    Jin muryar bafulatanar nan ya yi tana fad'in "Baffa aradu yau ban kaima Kad'o abinshi ba. Ni kam na gaji da wannan ajiya, gashi Umari ya ce zai dawo amma har yanzu bai dawo ba, mu dama abincin da zamu shi da yaya mu ke samunshi barin kuma ga Kad'o?"
    Mijin ya ce "Ashe dai ba ni kad'ai ba ne abin nan ya ke damu. Gaskiya yau ko goben nan zamu sakeshi ya gudu in har Umari bai dawo ba."
    Duk firarrakin nan da su ke a kunnen Khalid ne. 'To waye Umari?' Ya tambayi kanshi.
    Kad'a kanshi ya yi ya ce "why? Why kuka satoni kuka kawo nan? Me na maku? What is happening?" A bayyane ya yi wannan maganar wanda ya yi daidai da isowar fulanin a bakin window'n da suka saba jefa masa abinci.
     Jin ya 'dan yi turanci yasa matar ta ce "Baffa aradu kad'o ya iya yaren yahudu. Ni kam ko dai yana da hankalinshi ne?"
     Cikin tsoro Baffan ya ce "Kuma fa ban ta'ba ji mahaukaci ya yi yaren yahudu ba. Aradu ko da hankalinshi, yanzu zamu sakeshi kuwa."
     Hamdala Khalid ya yi sanda ya ji haka, "Somebody help me." Ya fad'a dan su k'ara jin ya yi turancin.
    Matar ta d'an ja da baya mijin kuma ya bu'de bayan ya tallabo sandarshi wai a nufinshi ko da Khalid zai nasa wani abun.
     Saurin tasowa Khalid ya yi ya ce "Wallahi tallahi da hankalina ni ba mahaukaci ba ne, wasu mutane ne kawai suka shiga gabana sanda ina tuk'in mota, shi ne suka bigeni tun daga nan ban kuma sanin inda kaina ya ke ba."
     Jinjina kai Baffa ya yi had'e da ajiye sandarshi ya ce "Na yarda da kai Kad'o. Aradu ma kuwa na yarda da kai. Ban san kai d'in mai hankali ba ne da ba zan yarda a ajiyeka a nan har haka ba. Ka yafe mu Kad'o."
     Murmushi Khalid ya yi ya ce "Na gode da ka fahimci haka. Na yafe maku har ga Allah. Ku taimaka min da ruwan sha."
     Da sauri matar ta 'dibo masa ruwa had'e da shimfid'a masa tabarma, zama ya yi bayan ya gama shan ruwan ya ce "Na gode sosai, bara na yi sauri na tafi kafin su zo, Allah kad'ai ya san abin da zasu sake yi min."
    Baffa ya ce "Ehh gaskiya gwamma ka tafi. Ban tab'a sanin cewa Umari mugu ba ne sai yanzu, aradu ma kuwa mugu ne tun da har suka iya satoka suka kawo mana da nufin wai kai d'in ba mai hankali ba ne. Na maka al'kawari ba zan tonaka ba, zan san abin da na fad'a masu insha Allahu."
     Khalid ya ce "Na ji kuna maganar wani Umari, waye shi ne wai?"
    Shiru Baffa ya yi kafin ya ce "Mahaifinshi shi ke da gidan gonar nan. Amma ba zan fad'a maka ko waye mahaifin nasa ba."
     "Dan Allah Baffa ka fad'a min, wannan ita ce alfarma ta k'arshe ba zan sake neman wata ba."
    "Ka yi hak'uri Kad'o, na maka alk'awarin zan fad'a maka ko shi d'in waye amma ba yanzu ba. Ka bani adireshinka har gida wata rana zan kawo maka ziyara kuma zan fad'a maka ko waye mahaifin Umari."
     Cike da gamsuwa ya ce "Ina za'a samu takarda da abin rubutu?"
    D'an tunani ya yi kafin ya ce "Akwai wacce Alhaji ya ke rubutu wani lokacin idan ya zo. Bari na ga ko tana nan." Ya nufi 'dakinsu.
     Babu jimawa kuwa sai  gashi ya dawo, hannunshi rik'e da memo da bak'ar biro ya mik'a masa.
    Adirenshi kuwa ya rubuta masa sannan ya bashi ya ce "Ni sunana Khalid. Duk d'an mashin 'din da ka ba wannan takardar in dai ya iya karatu to zai kaika har k'ofar gidanmu. Na gode k'warai da taimako." Ya tashi ya tafi.
     Tafiya ya ke sosai da k'afarshi har sai da ya d'an fara hangen titi, wata ash 'din mota ya ga tana kunno kai a daidai kwanar da ya ke tafiya. Dam! Gabanshi ya fad'i, kar dai a ce wanda suka satoshi d'in ne suka dawo.


Nagode k'warai masoyana masu bibiyar labarin *SHI NE SILA!* Ku sani cewa kuna raina kuma ina masifar k'aunarku.

*team Ikramhaidar*
*team Ikraminnocentkhalid*

SHI NE SILAH!Where stories live. Discover now