47

975 55 4
                                    

*SHI NE SILA!*
           😪😪😪

              Na Princess Amrah
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
                           (2018)


47~  Da sauri suka yi kan Ikram momy ta rud'e sosai, Khalid da Haidar ma sai ka kasa tantance wanda ya fi wani damuwa a cikinsu.
     Momy kam da ha'bar gyalenta ta ringa fifita Ikram tuni hawaye ya fara wanke mata fuska.
    "Ku kamata ku kai mota Saifullah." Momy ta fad'a a rikice.
    Cikin k'arfin hali Halle ya fara yun'kurin mik'ewa, da sauri Mallam Maharazu ya komar dashi zaune yana fad'in "Ina zaka tafi kai da baka da lafiya?"
    Kuka ya ke sosai yana fa'din "Ina gudun kar gudan jinina ta tafi ta barni. Ina sonki Ikram! Na sani ni mai laifi ne a gare ki wanda bai cancanci ki yafe masa ba, amma ki sani cikin da nama Rumana yana da'ya daga cikin abubuwan da a koda yaushe na tunosu su ke damuna." Kuka sosai ya ke.
    Cike da tausayi Mallam Maharazu ya ce "Yanzu dai ka yi ha'kuri ka zauna. Insha Allahu Ikram ba zata tafi ta barka ba, zata dawo gare ka Halle. Yanzu ma firgici da tashin hankali ne."
   Kanshi ya had'a da guiwa yana kuka sosai cike da nadamar abin da ya kasance yana aikatawa tun kafin ya san ciwon kansa.
    Tuni Haidar ya wawuri Ikram da iya k'arfinsa ya kaita cikin mota. Momy ta zauna a bayan motar rungume da kan Ikram sai Haidar na tu'ki, Khalid kuma da wadda suka zo da ita shi da Haidar ya tafi, sai 'boyayyin sojojinsu biye da su.
    Kai tsaye gida suka nufa, a nan di'n ma Haidar ne ya 'dauki Ikram, d'akinshi ya nufa da ita saboda can ne ke da kayan aikinsa.
    Kan gado ya kwantar da ita a hankali yana binta da kallo. Kyakkyawan ka'ramin bakinta ya kalla wanda ba komai ya ke cike dashi ba face tsiwa, dogon hancinta kuwa kamar an zana haka ya ke. Sai eye lashes d'inta da suka yi zara zara ba'ki wulik. Jar fatar nan tata kuwa sai she'ki ta ke, ta yi jaa saboda kukan da ta yi.
   Lab'banshi ya d'an ciza a hankali ya d'auke kallonshi daga gare ta. Momy da ke tsaye bakin gado hankali tashe ta ce "Ka bata taimakon gaugawa mana ka tsaya sai tunani kake kai kad'ai."
     Abin auna numfashi ya fara amfani da shi sannan ya shiga toilet, ruwan heater mai 'dan zafi ya 'dibo a kofi sannan ya fito dashi ya zauna bakin gadon kusa da inda ta ke kwance.
    Ka'dan ya shafa a hannunshi sannan ya shafe mata fuskarta da hannun a hankali. Sai da ya yi hakan sau uku amma Ikram bata farka ba. Shi kanshi a wannan lokacin kam hankalinshi ya fara tashi.
     "Akwai allurar da zan rubuta a siyo yanzu a mata. Firgici da tashin hankali ne ya d'arsu a cikin zuciyarta. Matuk'ar tana yarda hakan na kasancewa da ita zuciyarta zata iya bugawa lokaci guda wata rana ta rasa rayuwarta."
     Sosai hankali momy ya ke a tashe "Ka je ka siyo allurar da sauri ka mata, bana son na rasa Ikram." Ta sake fashewa da wani kukan.
      Kafin ya fita sai ga Khalid ya shigo, takardar daya rubuta allurar ya bashi ya ce ya siyo da sauri ya dawo. Shi kuma ya d'aura mata drip sannan ya koma ya zauna yana sake bin kyakkyawar halittar Ikram da kallo. Bai tab'a sanin cewa Ikram ta had'u har haka ba sai yau.
     A haka su ke zaune har Khalid ya dawo hannunshi rik'e da allurar, da sauri kuwa Haidar ya had'a komai sannan ya jawo hannun Ikram, a jijiya ya mata allurar wadda yana cakawa sai da ta d'an zabura sannan ta ci gaba da baccinta.
     Yana gama zuba ruwan allurar ya ce "Momy ina ganin sai mu d'an bata wuri ta samu hutu ko? Saboda ba zata farka ba har sai natsuwarta ta daidaita."
    "To babu damuwa." Ta kamo hannun Ikram ta d'aura a nata "Allah ya tashi kafadu'nki Ikram. Allah ya sani ina k'aunarki har cikin zuciyata, dan Allah kar ki tafi ki barni." Sannan ta saki hannun nata ta bar d'akin.
    Khalid ma fita ya yi cike da tausayin Ikram, bai ta'ba ganinta a cikin irin wannan yanayin ba sai ko ranar da ya bata jini. Amma ko wancan bai kai tsananin na yau ba, tun da yau har maganar zuciya a ke, wancan kuwa kanta ne ta bige jini ya fita sosai.
     Haka ya bar d'akin yana yi yana waigen Ikram har ya fice.
   Haidar kuwa band'aki ya shiga ya d'an watsa ruwa sannan ya fito ya saka k'ananan kaya ya koma parlor.
   Cirko-cirko su duka suka yi kowa da abin da ya ke sa'kawa a zuciyarsa. Babu wanda ke iya furta komai a cikinsu
    "Ku kwantar da hankalinku, zata tashi insha Allahu, kuma da natsuwa da kwnaciyar hankali zata tashi d'in. Ku cire damuwa a ranku ai na mata allura." Haidar ne ya fa'di hakan duk da shima 'din zuciyarsa cike ta ke da tausayin Ikram.
    "Ta ya zamu iya samun natsuwa bayan kuma har yanzu Ikram bata farfad'o ba? Ehnn, ta yaya zamu iya kwantar da hankalinmu?" Momy ce ta yi wannan maganar cikin kuka sosai.
     Khalid ya ce "Ki daina kukan mana momy. Ai kukan babu abin da zai amfana miki sai ma ciwo da zai iya sakar miki. Ikram zata tashi da izinin Allah."
    "To ina fatan hakan Khalid." Ta fad'a had'e da share hawayenta.

SHI NE SILAH!Where stories live. Discover now