*SHI NE SILA!*
😪😪😪Na Princess Amrah
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
(2018)_Wannan shafin kyauta ce sunkutukum ga k'awayen albarka *RAZ,* you mean a lot to me. Allah ya bar zumunci (Rerbee'art sk nd my dear Zarah)_
20~ Zaune ta ke kamar ko yaushe, fuskarta d'auke da alamar damuwa, ita ba kuka ta ke ba amma kuma sam babu walwala a tattare da ita. Wata yarinya ce 'yar kimanin shekara uku ta zo ta sameta, bubbugata ta d'an yi tare da fad'in "Mami yunwa na ke ji."
Saurin kawar da damuwarta ta yi ta hanyar yin d'an guntun murmushi ta ce "Khairat ke nan, ke dai bakya tab'a buk'atar wani abu sai kin zo kin sanar da ni, ki je wurin Jamila ta zuba miki mana."
"A'a Mami, ni dai ke na ke so ki zuba min, Mama Jamila bacci ta ke." Yarinyar ta fad'a tana kallon uwarta.
"To tashi mu tafi, dama bamu sha maganinmu na rana ba." Ta mik'e tare da nufar kitchen, Khairat na biye da ita.
Bayan ta zuba mata abincin suka fito, a kan dining suka zauna tana bata abincin ita ma tana d'an ci kad'an kad'an, amma fa har yanzu aka kalleta sai an gane akwai damuwa a tattare da ita.
Khairat ta ci abincin sosai kafin daga baya ta ce ta k'oshi, bedroom mamin tata ta nufa, ta bud'e side drower sai ga wani magani ta d'auko ta nufi dining da shi. Fridge ta bud'e ta fiddo da faro water, ta b'allarwa Khairat ta dama mata sannan ta bata ta sha, itama shan nata ta yi ba tare da ta damashi ba.
Cikin yanayin damuwa Khairat ta ce "Wai mami yaushe zamu daina shan wannan maganin?"
Siraran hawayen da mamin ke b'oyo ne suka bayyana, saurin gogesu ta yi ta ce "Har abada Ummul-khair, ba zamu tab'a daina shanshi ba har sai ranar da muka mutu."
"To menene mutuwa Mami?" Ta tambayeta.
"Ki bar maganar kawai Khairat, ki bari idan kin girma sosai zan miki bayanin komai. Amma fa maganar daina shan magani ba yanzu ba, ki yi hak'uri kin ji 'yata? Bayan wuya sai dad'i." Ta mata murmushi. Ita ma Khairat murmushin ta miyar mata da shi.
"To tashi mu tafi na kaiki shopping, sweets da chocolates d'inki na ga sun kusa k'arewa." Tsalle ta daka da k'arfi tana jin dad'in kalaman maminta.
Shiryata ta yi cikin 'yar kanti baby pink mai farar falmara, ita kuma ta saka wata farar atamfa mai manyan flowers pink, pink mayafi ta yafa sannan ta d'auko 'yar k'aramar jakarta ita ma pink, makullin mota ta d'auko suka nufi parking area. Motoci ne manya manya a wurin masu tsadar gaske. Wurin wata elantra suka nufa, golden ce kalarta, Khairat ta zaunar a kujerar zaman banza sannan ta d'aura mata belt, ita ma ta koma nata side d'in ta tayar da mota suka kama tafiya.
Sun jima wurin shopping d'in kafin suka dawo gida, siyayya ta yi sosai har da kayan abinci sannan suka nufi gida, Kahirat cike da walwala, dama akwaita da shan kayan zak'i, ko kuka ta ke da zarar aka bata kayan zak'i sai ta daina.*****
Waiwaye adon tafiya.
Asalin sunanta shi ne Kareema, kyakkyawar mace ce mai ji da gayu, ta taso cikin gata a wurin iyayenta, Alhaji Aminu Zango shine mahaifinta, asalinshi d'an asalin jihar Katsina ne, haifaffen garin Zango. Mahaifiyarta ma 'yar Katsina ce, aikin gwamnati shi ne dalilin dawowarsu garin Sokoto har mahaifinta ya yi retire bai bar garin ba, dan yana tsananin jindad'in zama da 'yan Sokoto saboda sun san darajar d'an adam kuma basu da wariya ko kuma nuna banbanci. Babban d'an kasuwa ya zama bayan yin retire d'insa. Kareema ita ce d'iyarsa ta hud'u amma ita ce matsayin babba yanzu, saboda duk haihuwar da zasu yi sai yaron ya zama sickle cell ya mutu. Kareema ce kawai suka haifa babu sickler sai k'anwarta mai suna Aminatu suna kiranta da Miemie kasantuwar sunan kakarta ne aka saka mata. Su ne kad'ai kuma suka rayu. Sun taso cikin gata sosai, duk wani abu da su ke so shi su ke samu, basu tab'a neman wani abu a gunsu sun rasa ba. Tarbiyya kam ba laifi sun samu mai kyau, duk da kuwa irin gatan da iyayen su ke ma 'ya'yan nasu.
Ta yi makarantar Primary a wata private school mai tsada, sannan a cikin makarantar ta yi secondary, daga nan ta wuce ABU Zaria inda ta karanci LAW, a lokacin kuma k'anwarta Miemie ta ke Primary 3, dan akwai nisa sosai tsakaninsu.
Bayan ta zama cikakkiyar Lawyer ta karb'i kwalinta ne ta koma gida, nan fa ta fara aiki ba kama hannun yaro.
Tana aikin ne mahaifinta ya fara nunar mata da yana so ta fitar da miji domin ta yi aure, amma sam babu mai nemanta, kasantuwarta d'iyar masu kud'i sosai ba kowane namiji ba ne zai iya tinkararta da sunan yana sonta duk da cewa ita bata iya wulakanci ba.
Duk yanda iyayenta suka so ta yi aure dole suka hak'ura suka k'yaleta, saboda babu manemi su kuma basa so su tirsasata har ta fitar da wanda bai dace ba.
Hakan ce kuwa ta kasance, wani mutum mai suna Alhaji M. Lawal ya fara nunar da yana sonta. Mutum ne mai dukiya sosai wai a cewarsa shi d'an kasuwa ne, ta hanyar daraja ya bi saboda sai da ya fara neman izini a wurin mahaifinta sannan ya nemi soyayya a wurin Kareema. Daga farko bata amince ba, sai daga baya ganin yanda ta sha wahala kafin ta sameshi gashi kuma iyayenta sun matsu su ga sun aurar da ita, amince masa kuwa ta yi, ya fad'a mata cewa yana da mata har da 'ya'ya uku.
Bayan wata d'aya da had'uwarsu aka saka ranar aure wata d'aya mai zuwa. (Gaggawa aikin shaid'an).
Shirye shiryen aure ne suka kankama, sosai iyayenta su ke mata siyayyar kaya masu tsada, duk da Alhaji M. Lawal ya ce ba sai an siya mata kayan d'aki ba, amma iyayenta suka ki amanna da maganars@ saboda suna son siyawa d'iyarsu daraja da mutunci.
K'anwarta Aminatu kuwa ko kad'an hankalinta bai kwanta da auren ba, a cewarta wai an yi gaugawa, ba haka ya kamata a ce an yi wa aure ba.
Ana saura sati d'aya bikin uwar gidan M. Lawal ta nemi lambar wayar wayar Kareema ta kirata, a karon farko bata d'auka ba saboda tana shagon d'inki tana ta fama ba'a gama d'inka mata wedding gowns d'inta ba. Sai da ta dawo gida sannan ta ga missed call, zata kira kenan aka sake kiranta da lambar, d'auka ta yi da sallama, ba'a ko amsa ba ta ji an ce "Ina magana da Kareema ne? Ina mufin wacce Alhaji M. Lawal zai aura."
"Ehh, ita ce." Kareema ta bata amsa.
"To ban kiraki dan yin doguwar magana ba ne, zan tambayeki a kan wasu abubuwa ne. Shin kun tab'a bincikar wace irin sana'a ya ke yi kuwa? Kun binciki wane irin hali *ZAMANTAKEWARSA* da iyalinsa ta ke? Kun binciki ko d'an asalin ina ne? Kareema kar soyayya ta rufe miki ido ki kasa wannan binciken,) daga baya nadama da dana sani su shigo, kin san halin mazan yanzu, burinsu kawai su yaudari mata, wannan shawara ce na baki, idan kin d'auka ruwanki, idan baki d'auka ba kuwa ke a ke ji." Ta tsinke wayar.
Ta dad'e shiru bata ce komai ba, sai dai a zuciyarta akwai wasiwasi sosai akan wannan maganganun, ita dai ta san ta yarda da angonta, ta kuma san cewa gaskiya ne duk abin da ya ke fad'a mata. Tana cikin wannan halin ne Aminatu ta shigo, hijabin jikinta ta cire tare da fad'in "Yaya Kareema na gaji wallahi, wannan telan ya cika shiririta."
Jin shiru Kareema bata fad'i komai ba ya sata d'an bubbugata ta ce "Aunty amarya lafiya dai? Ko wani abu ya faru ne?"
Saurin kawar da tunaninta ta yi tare da yin guntun mirmushi ta ce "Ke babu komai fa, na gaji ne, ashe kema naki telan bai gama miki ba."
"Ina fa zai yi wannan abin arzik'in? Wai sai gobe na koma."
"To Allah ya kaimu." Kareema ta fad'a tare da goge lambar wayar da aka kirata d'in.
Saura kwana uku biki aka fara events, wa'azi aka fara sannan washe gari aka yi kamu, sosai amarya ta sha kyau, da yake banda anguna aka yi kamun, na mata zalla ne. Washe gari ta kama Friday, photo shoot aka yi, sosai 'yan uwa da abokan arzik'i suka ziyarci event d'in, ankon farar gown suka yi da farin head, amarya kuma maroon zalla ta yi, sun sha hotuna sosai, tun da dama dalilin k'irk'irar wannan event d'in ke nan dan su sha hoto kawai.
Ranar asabar aka d'aura auren Kareema Aminu Zango da Alhaji Muhammad Lawal a kan sadaki naira dubu d'ari. Ana d'aura aure aka fara haramar d'aukar amarya, sosai ta sha kuka, unguwar GRA aka nufa da ita a tafkeken gidanta ita kad'ai, tun da dama ya ce ba had'esu zai yi ba.
Da dare kuma suka hau shirin tafiya dinner, amarya ta yi kyau sosai, sai k'arfe goma aka tafi dinner d'in.
Sosai bikin ya had'u, mutane sun ci sun sha sannan kowa ya watse aka bar amarya da angonta.
Washe gari ya d'auko uwar gidansa ya kawo ta gidan Kareema, ya masu nasiha sosai uwar gidan ta ce "Insha Allahu ba zaka samemu masu maka tashin hankali ba." Tana magana Kareema ta ji kamar ta tab'a jin wannan muryar, basarwa kawai ta yi ita ma ta ce "Zamu yi zaman lafiya da yardar Allah, zan mata biyayya a matsayinta ta yayata."
"To na ji dad'i sosai, Allah ya yarda ya baku ikon zama lafita, ni kuma Allah ya bani ikon yin adalci."
"Ameen" Suka fad'a su duka, sosai hankalin Kareema ya kwanta da kishiyarta mai suna Husna, ita ma kuma Husna ta aminta da abokiyar zamanta, sai dai a zuciyarta tana matuk'ar tausayin Kareema, dan bata san halin da zata tsinta a cikin gidan ba.
Kwanci tashi babu wuya wurin Allah, Kareema ta samu ciki har ta haihu, sai dai abubuwa da dama sun faru a wannan lokacin, ta fahimci cewa Alhaji M. Lawal manemin mata ne sosai, sannan kuma ana yawan kawo masu zantuka kan cewa wai tare ya ke da manyan masu kudi suna aikata luwadi, wai a nan ya ke samun kudi, tun da dai babu wanda ya san asalin dukiyarsa. Duk da matan nashi basu rageshi da komai ba amma bai hanashi zama mazinaci ba. Kullum cikin kuka Kareema ta ke, ashe saisa kishiyarta bata damu da kishi da ita ba.
Wata rana Kareema na binciken wasu takardu saboda akwai wani case da zata yi a kotu washe gari, ta bincika takardun sosai bata gansu ba, hakan ya sa ta koma d'akin mai gidanta a tunaninta ko ta kai can ta manta ne.
Ko da ta shiga ta hau duddubawa bata gani ba, kamar an ce ta bud'e safe d'inshi sai ga wasu takardu ta gani. Ta farkon wasik'a ce ta hausa, tana dubawa ta ga rubutun hausa ne ta ninke, wata ta kuma bud'ewa head line kawai ta ga an rubuta 'TEST OF HIV/AIDS' Ci gaba da karantawa ta yi, sunan M. Lawal ta gani rubuce ce wa yana d'auke da cutar k'anjamau shekara biyar ke nan, kuma yana shan magani shi ne ya sake yin wani awon a tunaninshi ko maganin da wani malami ya bashi ya mishi amfani.
Ganin abin ta ke tamkar a mafarki. Ido zare ta sake maimaita karanta takardar, a rikice ta mik'e tsaye ta bar takardun yanda su ke, goya Ummul-Khair ta yi ta d'auki makullun motarta, kai tsaye gidan kishiyarta ta nufa saboda yau a can ya ke.
Gudu ta ke na fitar hankali, cikin mintuna kad'an ta isa gidan, ta sameshi zaune, ita kuma kishiyar daga gefe ana yi wa yara lesson.
A halin da suka ganta ya tsoratasu, bata ce masu komai ba sai wani irin mugun kallo da ta ke binshi da shi.
"Kareema lafiya?" Ya tambayeta.
"Ya akayi Maman Khairat?"
"Wannan mutumin munafuki ne Maman Sulaim, munafuki ne na k'arshe kuma macuci ne, ashe neman matan nasa abin da zai ja mana ke nan?" Ta fashe da kuka.
"Me ya faru? Ki daina kuka dan Allah."
Da k'yar ta iya saita kanta ta ce "yana d'auke da cutar k'anjamau shekara biyar ke nan, kuma yana shan magani a b'oye bamu sani ba, macuci azzalumi."
Salati maman Sulaim ta d'auka da k'arfi tare da zubewa k'asa ko motsi bata yi.*****
Kar ku damu da jin salon labarin ya canza, akwai dalili.
Love you all my fans.*****

أنت تقرأ
SHI NE SILAH!
عاطفيةshi ne silar rugujewar farin cikin rayuwarta. shine silar shigar ta cikin kunci da bakin ciki. shi ne silar rashin gata hadi da galihu a rayuwarta. shin waye silah? ku biyoni a cikin wannan labarin inda zan warware maku zare da abawa.