shi ne silah page 3

1.4K 105 0
                                    

*SHI NE SILA!*
        😪😪😪

  Na Princess Amrah
          (NWA)
            2018

3~ A rikice Ikram ta koma gida, a lokacin har ciwon cikin ya ci karfin Ummah, daga kan gado ta gangaro kasa, har yanzu rike da cikinta. Ga wani irin numfashi da ta ke yi sama sama wanda ya tabbatar wa Ikram ce wa har da athma din Ummanta ce ta tashi.
       Kuka ta ke sosai ta ce "Ummah tashi mu tafi asibiti, duka chemists din a rufe su ke, wuri daya na samu kuma matarshi ta hanashi fitowa. Lallaba a hankali sai mu tafi."
     Kada kai kawai Umman ta yi alamar ba zata iya ba. Da kanta ta fara kokarin kamata amma ta kasa, kasantuwar Ikram karamin jiki ne da ita ba wani babba ba.
     Miyar da ita ta samu ta yi a hankali bisa gado kafin ta cije yatsarta ta na neman mafita.
    A hankali wata dabara ta fado mata "Allah ya sa baron Mallam na nan, sai na samu na sakata a ciki saboda ba zan iya ciccibarta ba." A zahiri ta yi wannan maganar kafin ta fita da gudu daga dakin.
      Babban gida ne wanda ya ke dauke da lunguna da dama, hakan ya sa Ikram ta hau zagayen gidan a hankali har ta ci karo da baro (kura) an jingineta a bango. Murmushin karfin hali ta yi kafin ta samu ta jawota har kofar dakin Ummah.
    Bayan ta shiga dakin ne ta kamota a hankali tana dan tatakawa da kafarta har suka fito kofar dakin. Wurin sakata cikin baron ma sun sha fama, da kyar da jibin goshi ta iya sakata.
       A hankali ta ke tura baron har suka isa primary health care din cikin garinsu. Saukin Ikram ma daya ba wani nisa sosai ba ne zuwa unguwarsu.
      Da isarsu ta hanzarta ta kira malaman asibiti, kasantuwarta karamar asibiti ba wani kula ke akwai ba ya sa aka yi biris da ita kafin daga baya Allah ya jefo wani likita wanda ya ke zuwa zagayen asibitin duk bayan sati daya, alhamis ke nan, tun safe ya ke zuwa sai sha biyun dare ya ke tafiya.
     "Ya Salaam! Me ya sameta?" Ya tambayi Ikram ganin ta yi tagumi ga ummanta kwance cikin baro har yanzu babu malamin asibitin da ya yi kokarin zuwa dimin ceton rayuwarta.
     "Ciwon ciki ne ta ke fama da shi likita, dama kuma tana da athma ina tunanin ko har da ita ta tasan mata, saboda yanda na ji numfashinta yana fita."
     "Allah sarki! Sannu mama." Ya fada yana kallon Ummah. Kai kawai ta iya jinjina masa.
     Ma'aikatan asibitin ya kira domin su dauketa. Babu bata lokaci kuwa aka kai ta accident and emergency.
      Abin awon numfashi ya fara amfani da shi, inda ya ci karo da numfashinta ba daidai ya ke ba.
    A iya binciken da zai yi kuwa ya gane ulcer ce ke addabarta matsananciya, wadda da gani ta yunwa ce, saboda kallo daya zaka yi wa Ummah ka san ce wa mabukaciya ce.
     Alluran athma ya mata sannan ya mata allurar omeprazole, babu jimawa bacci mai nauyi ya dauketa.
      Ikram ya kira ce wa ta biyoshi Office dinshi, bin shi kuwa ta yi cike da natsuwa har ya shiga sannan ita ma ta shiga.
      Bayani ya fara kamar haka "Ba wani abu ne ya saka wa mamanki ciwon ciki ba face Ulcer da ta kamata mai tsanani. Anya baiwar Allah'n nan kuwa ba ta zama da yunwa ?"
    Shiru Ikram ta yi na dan lokaci kafin ta ce "bata zama da yunwa likita." Cikin rashin gamsuwa da maganarta ya ce "Tou yau ta ci abinci?"
      Guntun tunani ta yi kafin ta ce "yau dai kam ban ga lokacin da ta ci ba, amma da ya ke bacci na yi sosai ina ganin ta ci sanda ina bacci. Tabbas ma ta ci." Ta jinjina kai.
      "Ki dai kara bincikawa, saboda wannan ulcer'n da ta kamata lokaci guda ta rashin cin abinci ce. Idan ta farka ki tabbatar da kin tambayeta idan ta ci abinci yau, kin ga idan ta ci sai mu san cewa ba rashin cin abinci ba ne, sai mu canja salon maganinmu."
     "Haka ne likita. Mun gode kwarai, Allah ya saka maka da alkhairi."
     "Amin, ki je inda ta ke, amma fa a nan zaku kwana, zan bar komai a hannun nurse saboda ni da sha biyu ta yi zan tashi, Allah ya bata lafiya kin ji?"
     Tashi ta yi ta tafi dakin da aka kai Ummah. Bisa kujera ta zauna ta yi tagumi sai hawaye ta ke. Yanzu inda da galihu wa ya kamata ya zauna da Ummanta? Ta tabbatar cewa duk shige da ficen da ta ke yi a cikin gida Goggo Indo na jinta, bata yi niyyar fitowa ba ne kawai. Wace irin rayuwa ce wannan? Wane irin bakin jini ne wannan? A ce har uwar Umma bata sonta? Lallai akwai dalili. Ta share hawayenta ta ke kuma ta yi kokarin cirewa kanta damuwa.
       Da bargon kan katifar ta lullube Ummah, ita kuwa dan kwalin kanta ta cire ta shimfida kasa sannan ta rufa da hijabinta saboda sanyi da ake yi.
      Da asubar fari ta farka saboda muryar Ummanta da ta ji tana son tashi ta yi fitsari, da hanzarinta ta mike tsaye, ganin ummanta ta ji sauki ba karamin farin ciki ya sakata ba.
    Fitsarin ta kaita daga nan ta yi alwala ta dawo da ita kan gado har lokacin sallah ya yi suka gabatar da ita kafin wani baccin ya sake daukarta saboda allurar da aka mata akwai mai saka bacci a ciki.
      Sai da safe ta farka, ta ji sauki sosai ko ta fuska idan ka kalleta. "Ikram! Ikram" ta kira sunanta. "Ikram tashi mana har gari ya waye sai bacci ki ke, ki tafi gida ki yi shirin makaranta kar ki makara, kin ga duk satin nan ba ki je ba, tun da kin ji sauki yau ai sai ki shirya ki je."
      Baki Ikram ta tunzuro ta ce "Umma ya za'a yi na tafi makaranta na barki a wannan halin? Ai kin san ba zan iya ba."
     "Kamar ya ba zaki iya ba? Na ji sauki fa Ikram, zan iya yi wa kaina komai, kuma ma malaman asibitin na ke jira su shigo su sallameni saboda ban ga zaman da zan ci gaba da yi a nan ba bamu da abin da zamu ci, gwara ko bin bashi na je na yi kafin a cinye kudaden."
       "Umma ya za'a yi ki ce a sallameki bayan kuma ba'a gama kula da ke ba?"
      "Ai na ji sauki sosai yanzu alhamdulillah! Kar ki ji komai 'yata." Ta mata murmushi.
       "Amma dai duk da haka Umma ba zan je makarantar nan ba, yau fa jumu'a ba wani abu sosai a ke yi ba."
     "Ai nasan tun da ba ki yi niyya ba ba zaki tafi ba, je ki kirasu su bamu sallama."
     Har Ikram ta tashi kuma ta zauna, a natse ta fuskanci Umma ta ce "Umma akwai maganar da zamu yi dama."
     "To ina saurarenki Ikram." Umma ta fada tare da miyar da hankalinta ga Ikram din.
      "Umma jiya kin ci abinci kuwa?"
      Shiru ta yi bata bata amsa ba kafin daga baya ta ce "amma me sa kika min wannan tambayar?"
     "Umma saboda likita ya tabbatar min da cewa yinwa ce ta kamaki sosai har ulcer ta shigeki, kuma ya ce min jiya baki ci abinci ba saisa ciwon cikin ya dameki sosai."
      Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce "na ga kin tashi da yunwa ba ki ci abinci ba Ikram, ba zan iya jurar ganinki da yunwa alhalin ni ina da abincin da zan ci. Saisa na yanke hukuncin na baki nawa ni na zauna da yunwa Ikram. Ke budurwa ce, ba zan so ki fada irin tarkon da na fada a baya ba, yanzu laifi ne dan uwa ta hana kanta ta mallakawa yaranta abu?"
      Cikin kuka sosai Ikram ta ce "laifi ne mana Umma, a kan me zaki yi haka? Ai da sai ki ce mu ci tare ko da ba zai ishemu ba dai ya fi babu."
      "Ko ke kadai ba zai kosar da ke ba barin mu biyu Ikram. Bani da wani zabin da ya wuce wannan saisa na yi haka." Ita ma kukan ta ke.
       "Ki yi shiru to ki daina kukan Umma, dan Allah kar ki sake zama da yunwa, likita ya ce in dai zaki ringa zama da yunwa to zaki ta fama da ciwon ciki, umma ni kuma ba zan ji dadi ba. Ko ban ci ba ni babu komai ke dai ki samu ki ci." (Allah sarki! Uwa da 'ya ke nan, kowa na burin farantawa kowa.)
     Suna cikin haka ne wata malamar asibiti ta shigo, Umma ta nemi sallama amma ta ce ai har yanzu ba ta gama warwarewa ba, saboda haka dole sai ta kara kwana a asibitin. Babu yanda Umma ta iya dole ta hakura. Ta cewa Ikram "ki je gida ki ma Goggo Indo bayanin duk abin da ya faru."
    "Umma ta sani fa." Ikram ta bata amsa.
     "Kin fada mata ne?" Ta tambayeta
     "A'a Umma, amma ai ta ji duk shige da ficena na jiya."
     "Wannan ba hujja ba ce, ki je ki fada mata, ko ma me zai biyo baya dai ai an fada mata din babu yanda za'a yi ko mallam ya dawo ta ce ba'a fada mata ba."
      Ikram bata da wani zabin da ya wuce ta bi maganar Ummanta, amma har ga Allah bata so ta fadawa Goggo Indo ba, dan ta san ko ta fada mata aikin banza ne sai ma masifa da zata jawo ma kanta.
Wattpad: PrincessAmrah.

SHI NE SILAH!Where stories live. Discover now