57

847 52 1
                                    

*SHI NE SILA!*
           😪😪😪

              Na Princess Amrah
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
                           (2018)

57~  Su Momy ne suka sauko daga taxi yayin da masu taxi ɗin suka ringa jido masu kayansu da suka samu mai ɗauri ya ɗaure su tam!
      A layi aka jera kayan sannan suka jira har sanda aka gama komai suka shiga jirgi.
     Da misalin ƙarfe biyar na asuba jirginsu ya lula sai ƙasarmu ta Nigeria. Daga nan sai marubuciyar ma ta biyo su ta bisa iska dan ko kaɗan basu san cewa tana biye da su ba.
    
***
    Kafin su taho dama Momy ta kira Haidar da Khalid ta samar masu ko ƙarfe nawa zasu taso, da kuma ƙarfe nawa suke sa ran sauka, sannan ta ce masu kowa ya zo da mota daban saboda kwasar kaya.
    Ko da jirginsu ya sauka su Khalid na zaune cikin mota ƙarar isowarshi ce ta sasu hanzarta fita tare da nufar departure ɗin.
     Ɗaya bayan ɗaya suke fitowa ana masu screening har aka zo kan Ikram da momy.
    Ana gamawa suka fito, da gudu Khalid ya isa gare su, yayin da Haidar uban ƙasaita ke tafiya a hankali har ya iso inda su ke.
   Da fara'a momy ta ce "Saifullah a nemo masu dako su kwashi kayan dan suna da yawa. Shiisa ma na ce maku kowa ya zo da tashi motar."
    Khalid ya ce "To bara a nemo su momy." Da sauri ya tafi yana kiran ƴan dako.
   Haidar sai da ya iso daidai inda su ke sannan ya saki murmushin jin daɗi.
    "Sannunku da isowa." Ya faɗa tare da ɗan satar kallon Ikram.
    "Yauwa sannu fa. Ta ina ka ajiye motar taka?  sai ku tafi da Ikram da wannan kayan na hannunmu, ni kuma zan jira har sai na ga an gama kwashe kayan nan duka sannan mu taho da Khalid." Momy ta faɗa tare da miƙawa Haidar ɗin jakunkuna guda biyu data riƙo a hannu.
    "Ok momy, tana can parking lot ɗinsu." Haidar ya faɗa bayan ya karɓi kayan.
   "Ok to ku tafi Ikram, sai mun zo." Momy ta faɗa a daidai isowar Khalid tafe da mutum biyar wanda zasu kwashe kayan.
    Bin bayan Haidar ta yi jiki ba ƙwari, bata wani so momy ta yi hakan ba, sai dai ko ba komai dama ta ƙosa ta isa gida.
    Booth ya buɗe ya saka kayan hannunshi sannan itama ta saka na hannunta.
    Buɗe mata motar ya yi ta shiga sannan ya rufe shima ya koma nashi ɓangaren.
     AC ya kunna bayan ya tada motar sannan suka ɗauki hanya. A hankali ya ke ɗan janta da fira ta hanyar faɗin "Autar Momy ki bani labari."
   Ɗaure fuska ta yi ba tare da ta ce komai ba. Dama kuma bai yi mamakin hakan ba.
   "Ikram in ce dai kin zaɓowa amaryata kayan kirki? Dan na fi so komai nata ya banbanta da sauran amare." Duk da shi ɗin da gayya ya yi, ya san ta san zai aure ta, sai dai kuma ita a nata ɓangaren sam bata san Hadar ya sani ba. Dan haka sai ta ɗan nuna damuwarta a kan maganar.
     Shiru ta yi nan ma bata faɗi komai ba.
   Magana ya sake yi a karo na uku ya ce "Kin yi shiru ko dai azumin magana kike? Wai kin ga yanda kika yi kyau kuwa? Kamar wata amaryar da za'a yi bikinta nan da wata ɗaya."
   Sai a lokacin ta ɗago da kanta ta ce "Ni dama can haka nake. Sannan kuma ka daina alaƙantani da amarya, kai dai da kake ango sai ka ji da abinka." Ta taɓe baki.
    Dariya ya yi sosai wadda tun da Ikram ta ke bata taɓa ganin ya yi irinta ba, sosai har da sauti ke fita sannan ya juyo ya kalle ta.
    "Mallam ka miyar da hankalinka ga tuƙi kar ka kashe mu kwanakinmu basu ƙare ba." Ta faɗa cikin tsiwa.
    "To to to na ji autar momy. Ni na isa in kashe autar momy bayan kuma bata ga aurenta da saurayinta Bash Osca ba?"
     Sake kallonshi ta yi kafin ta sunkuyar da kanta, ta ma rasa abin da zata faɗa.
    "Ai na san yanda kike sonshi shima haka ya ke sonki. Kawai ki ce masa ya fito mu aura masa ke." Ya faɗa har yanzu yana dariya.
    Ita abin mamaki ma ya ke bata. Ashe Haidar na tsayawa ya yi doguwar magana har haka? Ita kam bata taɓa sani ba, kuma wai har da wasa da dariya, lallai a jiƙata a ruwa a sha.
      Ɗaure fuska ya yi kuma kamar ba shi ne ya gama dariya ba ya ce "Like seriously, dama akwai maganar da nake son yi da ke."
   Shiru ta yi tare da kasa kunnuwanta domin jin abin da zai faɗa.
   "Game da guy ɗin nan Bash Osca. Idan ma akwai wani abu da ya ke haɗaki da shi to ki tsayar da shi. Ni na san halinshi kuma na san ko waye shi, saboda ni ne likitanshi."
    Kallonshi ta yi ta ce "To sai kuma aka yi yaya?" Ta harare shi.
     "Calm down ƴan mata. Yaron nan fa yana da cutar ƙanjamau yanzu haka. Sanann kuma yana ɗauke da cutar syphilis (Wata cuta da ake ɗauka ta hanyar saduwa wadda bacterium ke kawowa), Allah kaɗai ya san adadin matan da ya gogawa jangwam. Dan haka ki rufawa kanki asiri da shi, saboda na taɓa gittawa ta wurin kotu na ganku tare."
     Sai a lokacin Ikram ta tuna ranar, ashe ma ranar da suka fara haɗuwa ce.
    Ɗaure fuska kawai ta yi ba tare da ta furta komai ba, sai dai kuma har ga Allah ta ji daɗin yanayin da Haidar ke mata magana yanzu, ta kuma tabbatar da cewa babu sauran wulaƙanci a tsakaninsu, tun da har ya iya kula da abin da zai cutar da ita, ta san koda dai baya sonta amma zai iya kare ta daga dukkan abin da ka iya cutar da ita.
     Har suka isa gida Haidar dai shi ke kiɗanshi kuma ya ke rawarshi. Duk halin da kuka sani da shi na miskilanci kamar an ɗauka an miyarwa Ikram ne, banza ta yi da shi har aka buɗe masu gate suka isa cikin gida.
    Suna isa ba da daɗewa ba su momy ma suka iso, sai da suka yi sallar azahar sannan Baabah Nana data dawo jiya ta fara jera masu abinciccika.
   Har da su Haidar aka zauna inda aka fara cin abinci cike da farin ciki. Kallo ɗaya zaka ma Haidar ka tabbatar da cike ya ke da jin daɗi.
    Bayan sun gama Ikram ta ce "Haba har na ji daɗi wallahi. Lallai babu abinci mafi daɗi sama da namu na nan. Amma ka haɗa da can da mutum sai ya daure ma cin abincinsu?"
    Momy ta ce "Ai ke ce baki saba da wannan ba Ikram. Ko Saudia fa kika je haka abincinsu ya ke. Sai mutum ya daure ma ci."
     Khalid ya ce "Ni kam na ma fi jin daɗinsu." Ya kalli Ikram haɗe da yi mata gatsine kamar wani mace.
    Harararshi ta yi ta ce "Yo dama ai kai ba mutum ba ne. Duk abin da mutane ke so kai ba shi kake so ba."
    "Ke yarinya ni kike cewa ba mutum ba? To aljan ne?" Ya faɗa yana dariya.
     "Oho maka. Amma dai kam kai ba mutum ba ne." Ta faɗa itama tana dariyar.
    Haidar dai shiru ya yi, dan ya san da zarar ya saka baki a maganar zata yi shiru, wata ƙila ma ta tashi ta tafiyarta.
    Kallon momy Khalid ya yi ya ce "Momy na gama komai na makaranta. Qatar zan tafi kawai, masters ɗinsu akwai sauƙi kuma bama a cika shekara ɗaya an gama, shiisa ma kawai na canza zaɓi. Next week zan tafi insha Allahu, har visa na yi."
    Shiri momy ta yi kafin ta ce "To Saifullah, Allah yasa hakan ne mafi alkhairi."
    "Amin" ya faɗa a hankali.
      Ikram ta ce "Ayyah har na tausayawa Aljan, dan na san zai yi kewarmu ba kaɗan ba."
     "Bakya jin magana wallahi Ikram. Amma kar ki damu, akwai ramuwa." Ya nuna cikinshi da hannu cikin zaulaya.
    Harararshi ta yi haɗe da tunzuro baki ta mai kallon uku saura kwata. "Ni Allah ya kyauta min." Ta furta ƙasa-ƙasa.
    "Ke cikin cin abincin ne kike cewa Allah ya kyauta miki? Kin yi dai-dai yarinya." Ya faɗa har yana siƙewa dan dariya.
    Momy ta ce "Kai ya fa ishe ka haka, ka tasa min yarinya gaba sai janta kake."
    Haidar ya ce "Momy barin tafi, an gayyace ni wani meeting a General Hospital, ƙarfe uku za'a fara."
    "To Allah ya taimaka. Kayan fa ko sai gobe zaka gani?" Momy ta tambaye shi.
    Sosa ƙeya ya yi ya ce "Ni ba sai na gani ba Momy, tun da dai ke da Ikram kuka zaɓo ai na san ba zaku ma amaryar taku zaɓin banza ba."
    Sai a sannan Khalid ya ɗan samu sassauci, a ranshi ya ce 'Ke nan har yanzu Yaya bai san wacce zai aura ba. To da alama ba soyayya su ke da Ikram ba, ranar da na gansu kawai dai co-incident ne.' A zahiri kuma ya ce "Ahh Big bro ai ya kamata a zauna a buɗe mana mu sha kallo kafin in tafi."
      Bai ce dashi komai ba ya fice abinshi.
    Momy ta ce "Mai hali baya barin halinsa. Miskilin mutum dai bai ji daɗi ba. Mutum da ba halinsa ba rana tsaka ya ɗaukarwa kansa."
    Khalid ya ce "Ai momy dama can haka ya ke kawai dai lokacin ba'a gane ba ne. Kuma yanzu abin sai ya haɗu da shi ɗin likita ne. Kin san likitoci basu cika son damuwa ba."
     Ajiyar zuciya momy ta sauke ta ce "Haka ne."
    Ikram a ranta ta ce 'Ya ji da baƙin halinsa.'
    (Ni kam Amrah nace Ikram bayan kuma kin ce kin yafe masa ai ya kamata ki fitar da wannan tsanar da kika masa. Sai kuma na tuna da ai tun da ta riga ta tsane shi ke nan.)

***
    Washe gari ita da su Miemie suka je kasuwa fitar da ashobe, kala biyu suka zabo na kamu da na dinner, sai kuma suka fitar wa momy nasu na mother's day.
      Bayan sun koma gida Momy ta sa Ikram ta gwada masu lefe, har ɗakin momy suka shiga nan suka fara duba kaya, akwati saiti biyu ne, sai kuma na ango saiti ɗaya. Amma Ikram ta masu wayo ta ce kayan Momy ne ba sai an buɗe su ba, dan kar ma Miemie ta fahimci wani abu.
   Wanda ya kamata a kai ɗinki suka fiffitar mata, Miemie ta ce "Ikram kin yi sa'ar dangin miji masu kirki wallahi. Ki ga wannan tulin kaya kamar dai ke kika zaba da kanki."
   Da ƙyar Ikram ta iya haɗiyar yawu jin maganar da Miemie ta yi.
    "Allah dai ya gwada min nima Yaa Haidar ɗina ya haɗo min nawa haka." Ta faɗa tana ƙara ɗaɗɗaga kayan musamman ma Materials ɗin da Ikram zata saka a events.

***
   Sai da yamma suka tafi, a lokacin har sun gama tsara duk wani event, za'a yi bridal shower, kamu, sai kuma dinner wadda sai ranar ɗaurin aure za'a yi.
      Miemie ta ce "Mu dai fa ya kamata a haɗamu da angon nan ko kuma abokan ango dan mu ringa yin magana, saboda mu san abubuwan da ake ciki."
     Ikram samu ta yi da ƙyar ta haɗiyi yawu ta ce "Ke shi fa babu ruwanshi, zan dai masa magana ya haɗani da abokinshi koda guda ɗaya ne sai in tura mashi lambobinku. Na san dai dinner kawai zasu yi attending."
    "To sai mun jiki. Tashi ki miyar damu gida yamma ta yi." Husnah ta faɗa, ita kam ta san komai.
     Tashi kuwa ta yi ta miyar da su gida, a ranta tana tunanin yanda miemie zata yi ranar da duk ta gane Haidar ne zata aura, wanda kuma ta tabbatar da dole sai wannan ranar ta zo.
     Bayan magrib ta isa gida zuciyarta fal da tunane tunane.

*Team Ikramhaidar*
*Team Ikramkhalid*

SHI NE SILAH!Where stories live. Discover now