48

1K 51 3
                                    

*SHI NE SILA!*
           😪😪😪

              Na Princess Amrah
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
                           (2018)

_I dedicated this page to a huge fan of mine *Lainat* from Candy's group chart, d'aya daga cikin manya manyan team Ikramhaidar. I heart you Lainat❤ Allah ya bar zumunci amin....ana tare 'kawar albarka😊 kin ce kina jiran page 48, to gashi nan na bakishi kyauta domin jin da'dinki_


48~  Siyayya suka yi sosai banda Ikram da ta kasa d'aukar komai dan a ganinta in ma Haidar ya yi hakan don gwaninta ne to sam bai yi ba. Khalid ne ya ringa d'aukar mata duk abubuwan da ta ke so sannan suka kai wurin biyan ku'di. Haidar ya mik'a ATM card d'inshi aka cira ta POS sannan aka sassaka a leda. Ledoji biyu aka cika da karikitai sannan suka kama hanyar motarsu.
    Ko da suka koma gida a gajiye su ke, Ikram bata jira komai ba ta haye sama dan ta matsu ta watsa ruwa, ji ta ke baki d'aya jikinta ya mata tsami saboda sumar da ta yi.
    Tana fitowa wanka ta saka kayan baccinta saboda magrib har ta kusa, wayarta ta ji tana ringing hakan yasa ta yi saurin dubawa.
   Sai da gabanta ya fa'di sanda ta ga sunan mai kiranta, a kasalance ta d'auka had'e da fa'din "Hello 'kawata..."
    "Ba wata k'awarki. Wallahi Ikram baki da kirki, ke wato indai mutum bai neme ki ba ke ba zaki ta'ba nemansa ba ko?"
     Shiru ta yi dan ta san bata da gaskiya, ko kad'an bata damu da Miemie ba, ita di'n dai ce kawai ta damu da ita, kuma da alama fushi ta yi da ita shisa bata sake waiwayarta ba sai yanzu, tun da last ita ta kirata har sau biyu bata d'auka ba.
    "Ki yi ha'kuri 'kawata na d'auki laifina." Ikram ta fa'da cikin sigar rarrashi.
    "Hmm! To naji, na yi. Ya gidan ya su momy?" Ta tambaye ta.
    "Lafiya 'kalau miemie, kwanaki ai muna tare da Yaya Kareema, sanda ta kai Khairat asibiti bata da lafiya."
    "Wallahi kuwa, nima yau a can gidan na yini sai yanzu na dawo gida." Miemie ta fad'a.
    "To ya yi kyau, ya jikin nata?"
    "Ahh ta ji sau'ki sosai har tana ta wasanta ma. Ina kyakkyawan saurayina na gidanku? Cikin kwanakin nan kullum sai na yi mafarkinsa Ikram, ji na ke inama mafarkin nan ya zama gaske, da ko sai na fi kowa farin ciki, na zama mai sa'ar rayuwa."
    Sosai gaban Ikram ya fad'i, bata san ta hanyar da zata fara fad'awa k'awarta cewa an saka mata rana da Haidar ba.
    "Kika yi shiru k'awata, ko da ya ke na tab'o miki wanda kika fi tsana a rayuwa dole ki min shiru. Gaskiya Ikram ya kamata a ce kin cire wannan mummunan abin daga zuciyarki, ki rungumi k'addara, abin da ya faru ga umma kuwa ko da Yaa Haidar ya kula da ita dole sai ta rasu, lokacinta ne ya yi. Dan Allah forgive and forget."
    Murmushin takaici Ikram ta yi ta ce "Ke dai ake ji. Ni ba wannan ne a gabana ba. Ya batun makaranta?"
    "Duka shi ne mak'asudin kiran naki ai, in fad'a miki idan matrics zaki yi to an fara maganarsa, ki bincika ki yi duk abin da ya dace." Miemie ta fad'a.
    "Abin da yasa kika kirani ke nan kuma kika tsaya yi min maganar da bata shafe ni ba? Ke kuma shawarar da zan baki ita ce; ki daina dakon son wanda bai san kina yi ba."
    "Hmm! Yaa Haidar ya dad'e da sanin ina sonshi tun da har wulak'antani ya sha yi a gaban mutane, sai dai kuma ina mai tabbatar miki da cewa babu macen da Yaa Haidar zai aura idan ba ni ba, in kuwa har ya auri wata bayan ni ku shirya siyan likkafani, saboda 'karshen rayuwata ya zo."
     Tsananta fad'uwa gaban Ikram ya yi, cike da mamaki ta ce "Lallai a gaishe ki miemie, wannan wane irin so ne kike ma Yaa Haidar? Kamar dai tare aka haife ku? Yo ko tare aka haife ku ai ba zaki fad'i haka ba. Allah ni dai shawara na ke baki, kima cire wannan daga ranki tun wuri, saboda wahala zaki sha."
    Guntun murmushi Miemie ta yi mai sauti had'e da fa'din "Wallahi Ikram duk abin da kika ji na fad'a direct ya ke daga zuciyana. Ina son Yaa Haidar fiye da tsammaninki. Ina masa son da ban tab'a yi wa wani daa namiji irinsa ba. Bana ji zan iya rayuwa ba tare da shi ba."
     "To yanzu idan kika ji labari kwatsam an saka ranar aurensa ya zaki yi?" Ikram ta jefo mata wannan tambayar.
    "Ai kin ji yanda kika fad'a, saka ranar aure ai ba 'daura aure ba ne."
    "Amma kuma dai duk alamunshi ne. Yaa Haidar fa ba yaro ba ne, ya kai minzalin a ce ya ajiye tashi zuri'ar, kin ga kuwa a kowane lokaci labarin hakan zai iya riskarki. Tun da a kowane lokaci momy cikin yi masa fad'an ya fitar da matar aure ta ke."
     "Zan bashi lokaci, nan da wata biyu, idan har bai ce yana sona ba ni da kaina zan cire kunya na tinkari momy da maganar. Na san insha Allahu zata amince dani na zama surukarta."
    Gyad'a kai kawai Ikram ta yi kamar miemie na kallonta, sosai ta ke tausayin k'awarta, wannan wane irin so ne? Ita duk irin wulak'ancin da ya ke mata amma a haka ta ji tana sonshi? Allah sarki miemie.
     "Ga sallah can ana kira, sai anjima ki gaishe da momy." Bata ko jira abin da Ikram zata fad'a ba ta tsinke wayar.
    Ikram dafe kanta ta yi tana jin wasu zafafan hawaye na fito mata, 'yanzu miye abin yi?' Ta tambayi kanta.
    'Ya zan yi da miemie aminiyata? Ya zan yi na fad'a mata an saka ranar aure na da mutumin da ta fi k'auna a rayuwarta? Allah gani gare ka, Allah ka bani mafita yaa Allah.' Ta mik'e domin gabatar da sallar magrib.

SHI NE SILAH!Donde viven las historias. Descúbrelo ahora