[10/04 12:28 AM] Princess Amrah✍🏻: *SHI NE SILA!*
😪😪😪Na Princess Amrah
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
(2018)*ƘARSHE*
72~ Hidima sosai aka sha gidan momy kamar ba kwana shida da suka wuce aka gama wata hidimar ba.
Da azahar kuma Ikram ta koma gidan su Miemie. Ƙawaye sai shegantaka su ke mata wai amarya ta yi ɗas da ita ta ƙara kyau. Kallonsu kawai ta ke tana dariya, dan basu san har yanzu yanda su ke itama haka ta ke ba.
Ƙarfe biyar aka ɗauki amarya. Ikram, Husnah da Khaleesat duka a motar Ikram ɗin su ke.
Har dare su Ikram basu tafi ba, an tsaya sai gyara amarya a ke, gida kuwa an baɗaɗe shi da ƙamshi haka amarya ma.
Dan zakwaɗi tun ƙarfe tara sai ga ango da Marwan riƙe da ledoji.
Bayan an yi addu'o'i aka masu nasihu sannan aka fara barkwanci. Marwan na faɗin "Ikram nima fa an zama ɗaya. Saboda nan da kwanaki kaɗan zaki ji an yi baiko."
Da mamaki Ikram ta ce "Baikon wa?"
"Nawa da Khaleesat mana." Ya kalli Khaleesat yana murmushi.
Fatan alkhairi aka masu duka ɗakin sannan kowa ya kwashi ya nashi ya nashi ya tafi. Marubuciyar ma ta tattaro ƴan komatsanta ta bi motar Ikram da Husnah.
Bayan ta sauke Husnah ta wuce gidanta cike da gajiya. Saboda sun sha aiki sosai a gidan amaryar, komai sai da suka gyara mata yanda gobe ba sai sun koma ba.
Bayan ta faka motarta dai-dai zata fita Khalid ya fito fuskarsa ɗauke da murmushi.
Zuwa ya yi gare ta ya riƙo hannunta yana faɗin "Barka da isowa ƙawar amarya."
"Yauwa sannu da gida. Ashe ka dawo." Ta faɗa bayan sun ƙarisa cikin gidan.
"Na dawo tun kafin magrib. Ke kawai na ke ma shiri."
Shiru ta yi har ga Allah tana shakkun wannan rana, gabanta sai faɗuwa ya ke musamman yanda ta ga sai wani zazzaƙe mata Khalid ya ke.
Ɗakinta ta fara nufa ta cire kayan jikinta ta saka na bacci sannan ta fesa turaruka kala-kala haɗe da miskin da matar nan mai gyaran jiki ta bata.
Tana gamawa Khalid na shigo shima sanye da pyjamas ya naɗe hannyenshi biyu a bisa ƙirjinshi.
Kallonshi ta yi cikin so da ƙauna ta ce "Ka biyo ni ke nan."
"Shiru na jiki ne wifey. Har toilet heater na kunna ke kawai na ke jira." Ya faɗa cikin murya ƙasa-ƙasa.
Kama hannunta ya yi suka nufi ɗakinshi. Sai da ya kama kanta ya mata addu'a sannan lamarin ya fara canzawa. A guje marubuciyar ta baro su har tana cin tuntuɓe. Dan bata son ganin sirrin amarya da ango, ko kuma mata da miji ma baki ɗaya. Bayyana wannan abin kuwa zunubi ne mai girma, saboda manzon Allah (SAW) ya umurci mutane da su sirrinta wannan al'amarin.
Fatan zaman lafiya tare da zuri'a mai albarka kawai ta masu sannan ta tafi.***
Washe gari fa sai ruwan shagwaɓa kawai Ikram ke sakar ma Khalid, wata irin soyayyar junansu ta ƙara shigarsu.
A ɓangaren Haidar da Miemie ma haka ne. Ji su ke tamkar babu wanda ya kaisu sa'ar samun junansu. Dan haka sai yalwataccen annuri ke tsakanin ma'auratan.
Bayan Ikram ta yi wanka ta shirya ne kiran Momy ya shigo mata. Cike da kunya ta ɗauki wayar dan ji ta ke kamar zata gane abin da ya faru.
Sallama ta yi suka gaisa cikin farin ciki Momy ta ce "Yanzu Babanki ya shigo muka gaisa. Ya ke shaida min hukuncin da kika yanke a kan zuwa ƙauye ko? To hakan ya yi kyau sosai, kuma yau ya kamata mu tafi tun kafin wani abin ya sha kanmu. Ke ga makaranta ma da zaki fara zuwa sati mai zuwa."
Ikram ta ce "Yanda duk kika ce haka za'a yi momy." Ta yi murmushi.
Khalid da fitowarshi ke nan daga wanka ya rungume Ikram tana kallonshi ta mirror har suka gama waya da momy.
Juyowa ta yi ta sakar mashi murmushi haɗe da faɗin "Wallahi Yaa Khalid kai ko..." Ta shagwaɓe fuska.
"Me kuma na yi?" Ya tambaye ta yana murmushi.
"Ka fi kowa sani ai. Mugu kawai." Ta murguɗa masa baki cikin soyayya.
"Zaki kirani da mugu ne yanzun nan ma.." Ya fara ƙoƙarin ***
Da sauri ta ce "Yi haƙuri dan Allah na tuba. Dama ƙauye na ke so mu tafi da Baba da momy. Shi ne Momy ta ce yau ya kamata."
Khalid ya ce "Babu komai wifey, insha Allahu ma tare zamu tafi."
Daɗi ta ji sosai ta masa godiya sannan ta saka doguwar rigar atamfa. Hijabi ta saka sanann ta ɗauki hand bag ta fito.
Tare suka fita gwanin burgewa, wannan haɗi naau ba ƙaramin abin burgewa ba ne. Sun yi matching sosai da junansu.
YOU ARE READING
SHI NE SILAH!
Romanceshi ne silar rugujewar farin cikin rayuwarta. shine silar shigar ta cikin kunci da bakin ciki. shi ne silar rashin gata hadi da galihu a rayuwarta. shin waye silah? ku biyoni a cikin wannan labarin inda zan warware maku zare da abawa.