*SHI NE SILA!*
😪😪😪Na Princess Amrah
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
(2018)44~ Bakin gadon Halle suka nufa, ya yi zaune had'e da rafka uban tagumi ko tunanin me ya ke oho? Ko da ganinsu Ikram ya saki murmushi had'e da fad'in "Sannunku da zuwa."
Gaishe shi suka yi sannan suka masa ya jiki. "Jiki ya yi sau'ki sosai." Ya fad'a.
Momy ta ce "Ai Ikram d'azu tana komawa ta ke labarta min abin da ya faru, shi ne na ce ta zo mu dubaka. Allah ya kyauta gaba ya 'kara lafiya."
"Ameen hajia, na gode sosai. Ina jinjina miki sosai saboda sa'ar 'ya da kika yi, gaskiya kin mata tarbiyya sosai irinsu ko wane iyaye su ke fatan samu. Allah ya miki albarka Ikram." Ya saki murmushi had'e da kallonta.
Bata ce komai ba sai murmushin da ta yi itama, har ga Allah tana tausayin mutumin, musamman da Haidar ya fad'a mata halinsa, tana jin mutumin har cikin ranta, ko ba komai ya dattijanta, ya kamata a ce duk irin wa innan abubuwan ya girma da yinsu.
Sun d'an jima kafin momy ta mik'e ta ce "Sai mu tafi ai ko? Yamma na yi." Ta ciro dubu biyu ta mik'awa Halle, "Ga wannan sai ka siyi maltina. Allah ya 'kara lafiya."
Karb'a ya yi da godiya sannan suka kama hanyar mota.
A bakin motarsu suka tayar da Haidar ya yi tsaye yana jiran futowarsu, momy da ke gaba ita ta fara ganinshi. Murmushi ta saki a daidai lokacin da suka ka'riso kusa da shi.
"Manya! Ya aka yi ka gane mun zo?" Ta tambaye shi.
Murmushin shima ya k'irk'iro ya ce "Yanzun nan muka gama theatre da Dr. Rafiq, kin san ba da mota na zo ba yau, shi ne na hau motarsa zai rage min hanya muka biyo ta nan kuma sai na hangi motar Ikram, shisa na tsaya har ku fito sai mu wuce."
"Aikuwa dai an yi a daidai. Sai mu tafi to." Khalid ya fad'a da fara'a a fuskarsa.
Ikram da tun ganinshi ta shige cikin mota gabanta sai fad'uwa ya ke, tun da momy ta mata maganar aurensa yanzu ko son ganinsa bata yi, ko had'a ido dashi ma ta kasa.
Cikin motar suka shiga su duka, Khalid ne a gaba sai momy da Haidar baya. Wa'karta 'yar kullum ta saka tana bi a hankali kamar ko yaushe, gudunta ta ke zurawa hankalinta a kwance.
A hankali ta ringa jiyo Haidar shima yana bin wak'ar, tabbatarwar da ta yi shi ne yasata canja wa'kar tare da fa'din "Na tsani wak'ar nan." Ta saci kallonshi ta mirror.
Murmushi ya yi wanda har hak'oranshi suka bayyana. "Ni kam ina k'aunarta. Please ki miyar min da ita, kin san duk wak'ar da kika ga ina binta har na iyata to tabbas 'kaunarta na ke." Ya sakar mata murmushi had'e da kallonta ta mirror.
Sarai ta san magana ce ya fad'a mata, banza ta yi dashi had'e da kashe wak'ar baki d'aya tana fad'in "Momy anya kuwa kin tab'a shiga tuk'ina?"
Sosai dramar tasu ta ba momy dariya sai dai bata bari ta yi ba, gyad'a kai ta yi ta ce "Yau ai na shiga Ikram."
Khalid da zuciyarsa ke neman fashewa tsabar kishi ya yi k'ok'arin taushe shi, a kullum k'ok'ari ya ke ya ga ya fitar da soyayyar Ikram daga zuciyarsa amma abu yana neman ta'azzara ko kuma fin 'karfinsa.
Kimanin minti talatin ya isar dasu gida, suna shiga gida ba da jimawa ba ana kiran sallar magrib.
Koda Ikram ta koma d'akinta sai ga kiran Kareema ya shigo mata, d'auka ta yi suka gaisa Kareema ta ce mata "Na samu wata idea ne, gobe idan Allah ya kaimu zan je asibiti Khairat zata ga likita. Mu had'u da ke bayan gari hanyar Shagari, ina ganin kawai abu ma fi sauk'i mu je wurin masu gadin gidan gonar nan, Khalid ya ce wai fulani ne, zasu yi sau'kin fa'dar gaskiya. (Ku yi hak'uri fulani, ba duka bane ke da sokanci...lol) kafin nan kema kin tashi daga school."
Jinjina kai Ikram ta yi cike da gamsuwa, sai yanzu ma fasahar hakan ta zo mata. "Hakan za'a yi yaya Kareema. Sai mu had'u around 12pm, idan ma Bash Osca d'in ne dai sai mu tabbatar."
"To babu damuwa Ikram. Allah ya kaimu goben." Kareema ta fa'da.
Sallama suka yi sannan Ikram ta nufi yin sallar magrib.
Adhkar ta yi sosai har sallar isha, bayan ta gama shafa'i da wutri ta mik'e, wanka ta yi sannan ta saka kayan bacci ta sauka parlor domin cin abincin dare kamar yanda suka saba ko yaushe.
Ta same su su duka har da Haidar suna zaman jiranta ta zo. Tana zama kuwa Naanah ta kawo masu abinciccikansu nan suka hau yin dinner, Khalid sai satar kallon Ikram ya ke, yanda ta ke cin abincinta cikin yanga da aji.

ESTÁS LEYENDO
SHI NE SILAH!
Romanceshi ne silar rugujewar farin cikin rayuwarta. shine silar shigar ta cikin kunci da bakin ciki. shi ne silar rashin gata hadi da galihu a rayuwarta. shin waye silah? ku biyoni a cikin wannan labarin inda zan warware maku zare da abawa.