shi ne silah page 6

1.1K 90 0
                                    

*SHI NE SILA!*
           😪😪😪

     Na Princess Amrah
              (NWA)
               2018

6~ A nan Rumana ta ci gaba da zama, ni kuwa masallaci na ringa kwana ina yi ina juya sauran kudadena ta hanyar siyo kayan shayi da buta ina yin irin na larabawa din nan, ina kuma ciniki sosai.
     Sai da na tara kudi ba laifi sannan na ke ma Rumana maganar aurenmu, itama nata kudin ta bayar saboda Mama mai abincin da take yiwa aiki tana biyanta kudi duk bayan sati daya.
     Ranar wata jumu'a ne aka daura mana aure ni da Rumana, inda mahaifin Indo (wata kawar Rumana ce tare suke aiki a wurin mai abinci) ya zama waliyyinta, ni kuma wani abokin kasuwancina shi ya zama wakilina. Dubban mutanen da suka halarcin sallar jumu'a a masallacin Aminu Kano Airport suka shaida daurin aurenmu akan sadaki mafi karanci naira dubu tara da dari biyar.
    Duk wasu gyare gyare da ake yiwa amarya Mama mai abinci ba'a barta a baya ba wurin yi wa Rumana, har da taro akayi na bikin, an sha hidima ba laifi, da dare ya yi aka kai amarya a dan karamin gidan hayar da na kama mana.
     A nan muka ci gaba da rayuwa har Allah ya ba Rumana juna biyu, mun yi murna sosai kuma hakan bai sa ko kadan mun ji ra'ayin komawa kasarmu ba.
     Shekaru da dama suka shude, amintakar da ke tsakanin Rumana da Indo kuwa kara karfi kawai ta ke. Mun haifi yara uku a lokacin amma duk suna mutuwa ta dalilin lamoniya (pneumonia) wadda ta ke zaman masu athma. Ta biyun da muka haifa ma ita har sai da ta girma ta shiga makaranta sannan ta rasu. Sauran kuma duk suna yara Allah ya ke daukar rayuwarsu.
      Wata rana Rumana ta tashi da zazzabi da kasala wanda suka tabbatar mana da zarginmu na cewa tana dauke da juna biyu.
    Asibiti ta je bayan sun shaida mata karamin cikin da ta ke dauke da shi ta nemi shawara a kan yanda zata kula da cikinta saboda athma din da ta ke dauke da ita kuma tana kashe mata yara.
    Nan aka bata shawarwari sosai a kan cewa "kar ta kara shan ruwan sanyi har sai ta haihu ta yaye jinjirin sannan. Ta kuma daina yin wanka da ruwan sanyi ko kadan. Idan ta ji iska ya yawaita kar ta ringa fita waje, komai zata yi ta yishi cikin daki. Idan so samu ne ma kar ta sake yin girki bisa icce saboda athma dinta mai tsanani ce, wai har sai ta haihu sannan. An kuma shaida mata cewa idan ta haihu kar ta ringa yi wa jinjirin wanka a waje, da ruwa mai zafi zata ringa yi masa wanka. Idan sanyi ya zo kuwa ta tabbatar da ta lullubeshi sosai yanda sanyi ba zai shigeshi ba, idan so samu ne ma har hanci da bakinshi ta nemi irin abin lullubewar nan ta ringa rufeshi da shi. Wannan hanyoyin ne zata bi dan ganin abin da ta haifa ya tsira da yardar Allah"
    Ta yi na'am da wannan shawarwarin, abin da bata kula da su ba kenan sanda tana da wancan cikin na baya.
     Da kula sosai har Rumana ta haifeki." Ya nuna Rumana mahaifyar Ikram da hannunshi. Sannan ya ci gaba da "Ranar da ta haifeki ta je wanka wata irin k'ura mai karfi ta taso, kasantuwar ban dakin da ba iri daya bane da na yanzu, da bude suke kuma ba'a yin na daki sai dai a tsakar gida.
    Wannan k'urar *ita ce silar* tashin asumarta. Ko da na shigo na samu bata fito daga band'aki ba sai Indo da ke rungume da jinjira tana rirrigarta sai kuka ta ke.
    Na tambayeta ina Rumana ta shaida min da ta shiga wanka tun dazu kuma bata fito ba har yanzu, ita tsoro ma ta ke yi ga iska ana yi kar asumarta ta tashi.
    "K'ura kam ake yi sosai, ko ni sai da na nemi wuri na fake har ta lafa sannan na iso gida, amma barin bincika ko lafiya ta ke." Na isa ban dakin da kaina.
     Abin da na tayar ba karamin tayar min da hankali ya yi ba. Ganin Rumana na yi kwance k'asa sai numfarfashi ta ke sama sama idanuwanta kafe wuri daya.
   Mantawa ma na yi a bandaki muke na ambaci sunan Allah sannan na daura mata zaninta na sunkuceta na kaita daki.
     A rikice Indo take tamabyata ko lafiya, na shaida mata a halin da na iske Rumana cikinshi.
    Kayanta na hau bincika har na gano inhaler dinta, da kyar na ringa shaka mata sai dai kuma ta kare saura 'yar kadan ta rage. 'Yar kadan din ita ce ta dan farfado da ita amma har yanzu dai ba daidai ta ke jinta ba. Cikin karfin hali ta fara magana "athma na tasar min amma tun da na ke ban taba jin mai tsanani kamar wannan ba. Bana tunanin zan tashi."
     Cikin kuka na ce mata "haba Rumana ki daina wannan maganar, ita cuta ai ba mutuwa ba ce, insha Allahu Allah zai tashi kafadunki kar ki ji komai."
    Kai kawai da gyada min sannan ta ce "ka yiwa 'yata huduba da sunana, ka kula da ita kar ka ringa bari ta shiga sanyi, sannan dan Allah ka auri kawata Indo, ka ga tun da tayi wancan auren mijin ya saketa a kan rashin haihuwa, na san ita ce kadai zata iya rike min amana da alkawari, zata kula da abin da na haifa kuma zata kular min da kai."
     Ita kanta Indo din kuka ta ke tana fadin "wane irin maganganu ne kike yi haka Rumana? Insha Allahu zaki tashi ki ci gaba da rayuwarki, ke zaki kula da 'yarki da kanki."
     "Indo ke nan, ni kadai na san abin da na ke ji, ke dai kawai ki yi min alkawarin zaki kula min da Ummu Rumana, sannan kuma kar ku bari ta taba sanin cewa ba Indo ta haifeta ba. Ku tashi daga nan unguwar dan ma kar ta girma wanda suka santa su fada mata. Mutuwa zan yi Hubbii Mahmoud! Kirjina kamar zai tsage, wani irin abu na ke ji tun daga kafata yana yawo har bisa kaina."
     Wannan kalaman nata su suka dad'a tayar mana da hankali, nan na hau bata salati tana amsa har rai ya yi halinshi.
    Iya tashin hankali na yishi, na k'aunaci Rumana na so ta amma mahaliccinmu da ya yita ya fini sonta. A dalilin kaunarta na rabu da zuri'ata baki d'aya, a dalilin k'aunata ita ma ta rabu da tata zuri'ar, yau gashi mutuwa mai *yankar k'auna* (Ummu Abdoul) ta rabamu.
     Nayi kuka sosai kamar ba gobe, Indo ma sosai ta koka, saboda sun shak'u sosai da Rumana, ita ta ringa koya mata hausa har ta iya. Yau k'arshen zamantakewarsu ta zo.
       Sosai Rumana ta samu mutane, aka sallaceta aka kaita tabbataccen gidanta.
    Jinjira kuwa na mata huduba da Ummu Rumana kamar yanda Rumana ta nema. Saisa kika ga ina kiranki da Rumana kamar yanda na ke kiran Mahaifiyarki da shi.
      Barin unguwar muka yi ga baki daya muka koma kauyen su Indo da zama, nan aka daura mana aure Indo ta ci gaba da kula da rayuwarki, madara mai tsada na ke siyo miki ana baki, har na saba da masu siyarwar ko banda kudi na je suna bani bashi.
    Kin ga kuwa Indo ta rike alkawari tun da baki taba sanin ba ita ce ta haifeki ha, ta baki kulawa irin wacce ya kamata uwa ta bawa 'yarta." Mallam ya k'arisa maganar yana kuka sosai, kukan tunowa da matarshi da ya yi.
     Cikin kuka Umman Ikram ta ce "tabbas Goggo Indo ta rik'e alkawari na rashin sanar da ni ba ita ce ta haifeni ba. Amma kuma me? Sam bata rike amana ba, tabbas malllam na san baka san abubuwa da dama ba. Duk da ya ke Goggo Indo tana gwada min kauna iya kauna a gabanka amma a bayan idonka sabanin haka ne wanda ni kaina a zuciyata kokonto na ke akan ta ya uwa ta haifi 'yarta amma kuma ta ringa nuna mata wannan halayen?
    Ka dade kana tambayata na fada maka dalilin yin cikin Ikram amma na ki fada maka sai dai kuka a duk sanda ka min tambayar, na ki fada maka ne dan kar na had'aka da Goggo Indo.
    Yau kam zan sanar da kai wannan sirrin wanda babu wanda ya taba saninshi, ko Ikram ban taba fadawa shi ba sai yanzu da zata ji." Ta share kwallarta sannan ta ci gaba da bayani...
@wattpad: PrincessAmrah

SHI NE SILAH!Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang