33

900 56 0
                                    

*SHI NE SILA!*
           😪😪😪

              Na Princess Amrah
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
                           (2018)

33~  "Zainabu akwai matsala! Ke kika ba wata Barr. lambata wai?" Sameerah ta fad'a a rikice.
    Itama Zainabu a rikicen ta ce "Nima ta kirani Sameerah. Amma ban bata lambarki ba. Hankalina ya tashi da jin maganganunta."
    "Sosai ma kuwa. Anya kuwa asirinmu bai tonu ba?" Sameerah ta fad'a.
    "Wannan zargin da na ke yasa na kiraki. To amma kuma waye ya san wannan sirrin 'boyen?" In ji Zainabu.
    "Babu wanda ya sani kam. Tabbas akwai matsala. Amma idan ba haka ba ina Khalid ina yiwa wata fyad'e? Kuma duk mutanen duniyar nan sai mu ne kawai zata kira wai mu bata shawara? A ina ma ta samu lambobinmu?"
     Ajiyar zuciya ta sauke ta ce "Ni kam blocking 'din lambarta zan yi."
     "Blocking kuma Zainabu? Kina so asirinmu ya tonu ne? Tun da har ta samo lambar wayarmu kin san gano inda muke ba wahala zai mata ba. Kuma idan ma wani abu ta ke son tabbatarwa da zarar kin yi blocking d'inta to zata tabbatar da abin. Mu k'yaleta kawai, idan ta sake kira kuma mu d'auka mu yi magana lafiya lau."
   Bankwana suka yi tare da tsinke wayar.

***
     Yau ce ranar da su Ikram zasu yi submitting asaignment d'in da Barr. Kareemah ta basu.
   Bayan ta tashi daga makaranta ta nufi kotu, a daidai inda zata yi parking ta ga motar Khalid, a ranta ta ce 'Ashe har ya zo.' Ta saki murmushi.
     Bayan ta kashe motarta ta fito rik'e da jaka da makullin motarta, ganinshi ta yi ya sha gabanta yana mata murmushi.
    "Ka bani tsoro Yaya." Ta fad'a had'e da tunzuro baki.
    "Matsoraciya." Ya fad'a cikin zaulaya.
    Murmushi k'unshe a fuskokinsu suka nufi Office 'din Barr. Kareema.
   Bash Osca da ke tsaye tun tsayuwar motar Ikram ya yi murmushi had'e da fa'din "Ke nan wancan guy 'din ne ya kar'bi wayar ranar har ya ke ikirarin zai wulak'antani ko?"
   Jibo ya ce "Wai kai Bash sai yaushe zaka rabu da wannan yarinyar? Ba zaka fita harkarta ka kama gabanka ba?"
     Dariya Bash ya yi sosai kafin ya ce "Ai wallahi sai ya san ya wulak'antani. Zan yi bincike a kansa nan da kwana biyu kuma zan yi maganinshi." Ya tayar da motarshi zuciyarshi fal da farin ciki.

***
    Dariya su ke sosai bayan sun bama junansu labarin abubuwan da suka faru. Ikram ta kunna recording 'din da Abbas ya mata, Khalid ma ya kunna wanda ya yi lokacin da Abbas na waya da Ikram.
    Kareema ta ce "Now, the game is getting to over. Kun gama naku saura nawa, ina k'ok'arin sakasu a damuwa ne sosai su wancan matan. Zuwa next week kawai sai mu shigar da k'ara, a lokacin kuma mun gama had'a kaf hujjojinmu."
    Khalid ya ce "To masha Allahu Barr. Allah ya taimaka ya saka miki da alkhairi."
    "Yaya Kareema to yanzu su wancan matan ya zaki yi da su?" Ikram ta tambayeta.
    Murmushi ta yi ta ce "Fad'a na ke son had'asu, har su fara tonawa junansu asiri. Kin ga nan ma zan sake samun wata hujjar. Dama na fad'a miki wannan k'aramin case ne ba wani babba ba. Zama d'aya ma za'a yi a kotu a gamashi. Kun ga idan su aka kamosu ai zasu tona asirin mutanen da suka saka d'in."
    "Hakane, Allah ya taimaka." Ikram ta fad'a.
    "Amin. Zan kiraku kome ke nan." Suka mik'e tare da yi mata bankwana suka nufi motocinsu.

***
    Yana zaune shi da momy abin da bai saba ba, sai dai kuma fuskar kamar ko yaushe babu annuri a cikinta. Kira ya shigo a wayarsa ganin new number ya sa ya yi tsaki had'e da rejecting.
   Sake kiranshi aka yi nan ma ya k'i d'auka har ta tsinke. A na uku ne momy ta ce "Wai waye ke kiranka haka ka ke 'kin d'auka?"
     Guntun tsaki ya yi ya ce "Ban san lambar ba ne."
    "Dan baka san lamba ba kuma sai ka k'i d'auka? Kai fa likita ne ka sani ko wasu ke neman taimako?" Momy ta fad'a cikin fad'a.
     Tun bai fad'i komai ba aka sake kira, daurewa ya yi ya 'dauka ya kara a kunne ba tare da ya fad'i komai ba.
      Ajiyar zuciya ta sauke jin ya d'auki kiran. "Dan Allah ina magana da Dr. Aliyu Haidar ne?" Ta tambayeshi.
    "Eh." Kawai ya fa'da a tak'aice.
    "I need your help please." Ta sake fa'di.
   "How may I help you?" Ya tamabayeta cikin k'osawa da wayar.
   "I've a sister that loves you so much, she can't even eat, she's always crying, please I want you to..."
   Tsinketa ya yi ta hanyar fa'din "please leave me.." ya yi tsaki had'e da kashe wayar.
    Momy da jin haka ta san dalilin kashewar. Kai kawai ta gya'da kafin ta ce "Wai kai yanzu haka rayuwarka zata ci gaba da tafiya? Kai ke nan baka ma tunanin soyayya barin aure?"
   Mik'ewa ya yi ya ce "Bari na tafi momy, bacci na ke ji kuma kaina yana ciwo."
   "Ungo naka nan." Ta masa dak'uwa. "Maganar tawa ce ta saka maka ciwon kai? Dama na jima ina son magana da kai. Dawo ka zauna."
    Babu musu kuwa ya zauna zuciyarsa na masa zafi, shi dai a rayuwarsa ya tsani a masa maganar aure dan bai ga macen da ya ke so ba ko kuma wacce zai iya so, a ganinshi ma wai soyayya b'ata lokaci ne.
     "Ka canza tunani. Ya kamata a ce kaima fa ka tara naka iyalin a halin yanzu. Me ka rasa a rayuwarka? Kud'i samunsu ka ke har ma ka rasa ina zaka sakasu, Ya kamata ka san cewa darajar mutum shi ne iyalinshi, duk yanda kake ganin kana da martaba a idanun mutane in har baka da iyali to aikin banza ne. Ka yi wa kanka karatun ta natsu, ko Khalid k'aninka ya isa ace ya aje zuri'arsa yanzu barin kai da kake da 32 yanzu."
    Kanshi sunkuye ya ke a k'asa bai fad'i komai ba, fuskar nan a d'aure.
    "Ko budurwa ce baka da ita?" Ta tambayeshi.
    Nan ma dai ba fad'i komai ba bai kuma d'ago kanshi ba.
    "Idan baka da ita ni zan nemo maka, dama Khalid ya sameni da magana cewa ya samu matar aure, jira kawai na ke kaima ka fiddo sai na had'aku ku biyu na aurar, tun da dama abokin mahaifinku ya masa al'kawarin upper da zarar ya gama bautar k'asarshi."
      Sai a sannan ya 'dago kanshi ya kalli momy. 'Ta zab'ar min mata?' Ya fad'a a zuciyarshi.
    "Lokaci ke k'ure maka wallahi. Idan har baka yi aure yanzu ba yaushe zaka yishi?"
     "Momy shi fa auren nan ba wai dole bane, sunnah ce dai mai 'karfi." Ya fad'a da murya 'kasa 'kasa.
    "Kar ka kawo min maganar banza! Tun da abin haka ne ma na baka sati biyu ka fiddo min da matar aure. Idan har baka fiddo ba to ni zan baka tawa za'bin. Tashi ka bani wuri.."
    Ya mi'ke ke nan su Ikram suka shigo, yau ma ranta fari ya ke tas sai Khalid a bayanta. Ganin yanayin Haidar bai sa sun ji mamaki ba, saboda dama shi haka ya ke, ko babu damuwa ma ba wata walwalar kirki gareshi ba.
     "Sannu babban yaya." Khalid ya fad'a yana masa dariya.
     "Yauwa ango. Ashe aure zaka yi?" Ya fa'da.
     "Au, ashe fa ban fad'a maka ba. Ai har ma na fiddo mata kai kawai momy ta ce na jira." Khalid ya fad'a.
     Kafa'da ya d'aga ha'de da barin 'dakin yana tunanin sati biyun da momy ta ce ta bashi.
     Ita kuwa Ikram wani kallo ta bi Khalid da shi 'Aure?' Ta nanata a ranta. Jin ta ta yi cikin wani sabon yanayi wanda ita kanta ta yi mamakin kanta. A zahirin gaskiya ita dai ba son Khalid ta ke ba, amma kuma ta rasa dalilin da ya sa ta ji gabanta ya fa'di a lokacin da Khalid ya ambaci aure, wai har ma ya fitar da wacce zai aura, to wacece ita? Dan ita a tunaninta ma ko har ya fad'awa momy wacce zai aura d'in."
    Jiki babu k'wari ta gaishe da momy sannan ta haye sama, momy na kiranta amma ta yi kamar bata jita ba kawai ta shige d'akinta. Kuka ta fasa wanda ita kanta bata san dalilin yinshi ba.

_Ayi hakuri da wannan, wallahi banda lafiya ne. Need your prayers._

*Team Ikramhaidar*
*Team Ikramkhalid*

SHI NE SILAH!Opowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz