*SHI NE SILA!*
😪😪😪Na Princess Amrah
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
(2018)58~ Washe gari da safe Ikram ta sauko ta samu momy tana abin data saba na ƴan rubuce rubuce.
Da fara'a momy ta kalle ta haɗe da faɗin "Yanzun nan nake son kiranki dama."
"Sai ga ni Allah ya jeho." Ikram ta faɗa a dai-dai sanda ta isa cikin falon.
"To zo ki zauna nan." Ta nuna mata kusa da ita, da yake three seater ce ta ke zaune.
Sai da ta duƙa ta gaishe da momy sannan ta zauna.
"Momy anya kina baccin kirki kuwa?" Ta tambaye ta tana dariya.
"Ta ya zan yi baccin kirki bayan kuma an kusa yin bikin ƴata?" Momy ta faɗa itama tana dariyar. "Wane kalar ɗaki kike so? Na yi magana za'a turo da kayan ɗakinki ta jirgin ruwa, tun daga Turkey, kin san furniture ɗinsu akwai kyau."
Shiru Ikram ta yi cike fa kunya ta kasa faɗin komai.
"Kin yi shiru Ikram. Ki faɗa min kin ga ma sai in san kalar fentin da za'a miki."
Can ƙasa-ƙasa ta ce "Blue." A taƙaice.
"Zallar blue?" Ta sake tambayarta.
"Dark blue and light blue." Ikram ta faɗa kanta ƙasa tana jin kunya sosai.
"Je ɗakin yayanku ki kira min shi." Ta faɗa haɗe da duƙewa ta ci gaba da rubutunta.
Miƙewa ta yi ta nufi ɗakin Haidar ɗin jiki babu ƙwari. Tun bata isa ba ta ci karo dashi sanye da suit baƙa da green ɗin riga a ƙasa sai baƙin wando, green neck tie ya saka hannunshi riƙe da briefcase.
Kasantuwar kanta na duƙe ƙasa yasa suka yi karo da juna saboda shi ya taho a hanzarce ita kuma duƙe.
Suna yin karo da ƙarfi Ikram ta fara tangal tangal zata faɗi, da sauri Haidar a rikice ya tallabo ta ya dirar a ƙasa.
Ɗago kanta ta yi ta kalle shi a hankali ta furta "Thanks."
"Laifina ne ai. Ni ne na taho ina sauri. Am sorry Ikram." Ya faɗa da wata murya kakkaura.
"Momy na kiranka." Kawai ta faɗa haɗe da juyawa ta nufi falo.
Tana isowa shima ya iso kusan a tare suka zauna.
Gaishe da momy ya yi ta amsa ta ce "Aiki zaka tafi ne?"
"Ehh momy. Sauri ma na ke akwai important abu da zan yi a wata Private hospital."
"To shi ke nan. Dama maganar gyaran gida ne da muka fara jiya, ko da yake ai fenti ne kawai za'a yi ai ko?" Ta tambaye shi.
"Ehh momy. Sai kuma kitchen cabinates." Ya bata amsa.
"To shi ke nan. Sai a samu wanda zasu yi cabinates ɗin masu kyau komai tsadar su kar ka ji komai. Fentin kuma sai a yi light blue sama, dark blue ƙasa, walpaper kuma a gefen da za'a saka electronics kawai za'a liƙa, kuma a nemi mai blue a saka."
"To momy. Za'a yi." Ya miƙe zai tafi.
"Ko karyawa ba zaka tsaya ka yi ba?"
"Momy sauri na ke, kira biyu akai min ana jirana." Ya faɗa a hanzarce.
"To Allah ya taimaka ya bada sa'a." Momy ta faɗa.
Tashi ya yi ya tafi. Yana fita sai ga wata mata ta shigo sanye da hijabi sai kuma wata budurwa da alama ɗiyarta ce.
Gaishe su Haidar ya yi sannan ya fice ya nufi motarshi.
Matar na shigowa momy ta saki baki tana dariya. "Hajia Nana barka da zuwa."
Matar data kira da Hajia Nana ta ce "Hajia Salmah manyan mata. Uwar amarya da ango."
Momy ta ɗan harare ta cikin wasa ta ce "Uwar amaryar dai, na bar miki angon."
Ikram murmushi ta yi ta gaida matar, sannan ta kalli budurwar ta ce "Amrah, sannu ya gida?"
Budurwar mai matsakaicin jiki da tsawo ta murmusa ta ce "Lafiya ƙalau Ikram. Kwana biyu, ke dai na kula idan ba da Momy ba bakya zuwa gidanmu ko?"
Ikram ta ce "Ba haka bane Amrah. Dama gobe nake cewa zan zo in kawo anko, sai ki gwadawa *RAZ"*
Amrah ta ce "To ai tun da na zo sai ki bani."
"Tashi mu tafi ɗaki to." Ikram ta faɗa haɗe da miƙewa suka nufi up stairs.
Murmushi Hajia Nana ta yi ta ce "Kayan kitchen ɗin fa sun iso, yanzu haka suna Kano ina jin ma sun kamo hanyar Sokoto."
"To yayi kyau. Maganar mai gyaran jikin fa? Kin fara nema?" Momy ta faɗa tana kallon Hajia Nana.
Hajia Nana ta ce "Akwai wata mata ƴar Borno, ta iya gyaran amare sosai, har lalle ma tana da yaran da ke yi. Allah yasa ba'a yi booking ba, dan na kula date ɗin bikin za'a yi bukukuwa ba laifi."
"To Allah yasa ba'a yi ba, ni wallahi ko nawa ne bana ji zan bayar a dai gyara min autata." Momy ta faɗa tana murmushi.
"Bara in kirata in ji." Hajia Nana ta latsa kiran mai gyaran jiki. Bugu biyu kuwa ta ɗauka. Bayan sun gaisa ta ce "Dama wata amarya ce gare ni, saura sati uku da ƴan kwanaki bikin nata. Nan da sati biyu idan ba'a rigamu ba sai a fara gyare gyaren."
A ɗaya ɓangaren matar ta ce "Ai kuwa an yi sa'a babu wanda ya rigaku. Babu damuwa to, insha Allahu za'a mata duk abin da ya dace."
"To nawa za'a bada?" Ta tambaye ta.
"Hajia Nana ai da sani da sabo za'a yi. A bada dubu ashirin Allah ya mata albarka. Har da lalle."
Godiya ta mata sannan ta kashe wayar tare da cewa ta turo mata account number za'a mata transfer ɗin kuɗin.
Yanda suka yi ta shaida mata, momy ta ce babu damuwa, idan ta turo sai a tura mata kuɗin yanzu.
***
A ɗaki kuma Ikram da Amrah suka dage fira, duk da ba wani sabawa suka yi ba, kawai dai dan suna sa'annin juna ne, kuma Hajia Nana ƙawar Momy ce, Ikram na yawan raka Momy gidan, itama kuma Amrah suna zuwa ita da mamanta.
Uku daga cikin materials ɗin bridal shower Ikram ta ɗauko wa Amrah. "Na san fa ku ba'a rabaku ke da *aminnan junanki RAZ,* guda uku ne sai ku ɗauka ku ukun. Ga kuma na kamu da na dinner, a central shagon Raheem Jega zaku same shi."
"Ahh lallai abu da gindinshi. Har da ashobe aka mana kyauta? Zakuwa mu zo ni da *RAZ* har ma da fans ɗinmu."
Ikram ta murmusa ta ce "Haba babu komai ai ana tare."
Fira sosai suka ci gaba da yi, sai bayan azahar Hajia Nana ta ce da Amrah ta fito su tafi.
Sai da Ikram ta mata make up na ji da gani sannan ta ɗaura mata ɗankwali suka fito tare.
Momy da Hajia Nana mamaki ma abin ya basu, cikin lokaci kaɗan Amrah ta canja kamanni kamar ba ita ba, saboda irin make over ɗin nan ne Ikram ta mata.
"Hajia sai kallona ta ke ta ga na yi kyau."
Hajia ta ce "Haba ina kyan ya ke a nan? To da sauƙi dai tun da Ikram ce ta miki. Ba laifi."
Momy ta ce "Ahh ni ƴata Amrah ta yi kyau. Ki ga yarinya kamar irin cele ɗin nan amma ki ce bata yi kyau ba?" Tana dariya.
Da fara'a sosai suka rabu. Har bakin mota suka rakasu sannan suka dawo cikin gida.
Suna zama kiran Aunt Juwairiyya na shigowa a wayar Ikram, da sauri ta ɗauka tana fara'a ta gaishe ta.
Nan ta shaida mata cewa ta dawo Nigeria, har da Mamanta ma, saboda sama a hannun kakarta ta ke nan Nigeria, kakar tata ita ce ƴar asalin jihar Borno, shuwa ce asalinta har Allah ya haɗata da mijinta wanda suka haɗu a aikin Umarah har suka yi aure aka kaita Misrah, a can ta haifi mahaifiyar Juwairiyya da kuma ƴan uwanta maza biyu mata biyu. Lokacin da mijinta ya rasu ne ta ga babu amfanin zamanta a Misrah tun da ba kowa gare ta ba, ta bari yayanta wurin dangin mahaifinsu, ita kuma ta dawo Nigeria, inda ta auri wani basakkwace ya kawo ta Sokoto. Tun kusan shekara ɗaya data wuce Juwairiyya ta kawo mata ziyara, shine fa ta maƙale wai ita lallai Nigeria ta mata, zata zauna a nan, shi ne ta hanyar wata maƙwafciyarsu ta samu aiki a make up school ɗin da Ikram ta gama. Wannan ke nan.
Da murna Ikram ta ce mata "Am very happy for that. I'll visit you to greet her insha Allah. (Na ji daɗin hakan sosai. Insha Allahu zan ziyarce ki in gaishe ta.)"
Sosai Juwairiyya ta ji daɗi, ta kuma shaida mata cewa har da ƙannenta biyu mace da namiji duk sun zo, amma su musamman saboda bikin Ikram ɗin suka zo.
Sosai Ikram ta yi farin ciki. A ƙarshe suka kashe wayar da nufin zata turo mata address ɗinta har gida zata zo ta same ta.
Bayan sun yi sallama Ikram ta labartawa Momy abin da ya faru, ita kanta ta ji daɗi. Ta ce dama anjima zasu je ganin gida, daga can sai su wuce tare.
Bayan la'asar suka shirya suka nufi unguwar GRA, inda gidan Ikram ya ke.
Babu wani nisa daga nan gidan su momy, ko da ƙafa ma za'a iya zuwa idan ta lungu za'a bi, amma idan titi za'a bi ne ya ke da ɗan nisa.
A motar Ikram ɗin suka tafi, tun daga bakin gate momy ta ba Ikram makullin ta ce ta buɗe gate su shiga da motar ciki.
Buɗe gate ɗin tayi sannan ta dawo mota suka shiga ciki.
Wani irin babban gida ne, parking space ɗin kanshi abin kallo ne.
Bayan ta paka motar ta koma ta rufe gate ta dawo ta buɗe ƙofar da zata sadasu da cikin gidan.
Babban falo ne suka fara cin karo da shi, daga gefe guda kitchen ne da dining area. Jikin kitchen ɗin ke da wata ƙofa wadda idan ka bita zata sadaka da wani makimancin falo. Shi kanshi wannan falon abin kallo ne, an tsarashi tsari iya tsari, sai ƙofofi guda biyu masu kallon juna, wanda duka bedrooms ne akwai toilet a cikinsu.
Idan aka dawo wannan babban falon kuma sai wata kyakkyawar ƙofa itama opposite ɗin kitchen, nan ma wani falon ne da two bedrooms a ciki, sai dai kuma shi nashi ginin ya banbanta, da ka gani ka san na mai gida ne.
Bayan sun gama zagaye gidan suka rufe suka koma bayan gida, nan kuma lambu ne babba na ji da gani, ga wurin hutawa daga gefe guda irin kujerun nan na ƙasa har da teburi.
Sosai wurin ya ke ni'imtacce wanda cikin yanayin zafi dole ma mutum ya ji daɗinshi.
Bayan sun gama dudduba nan suka taho, gate ta buɗe sannan ta shiga mita ta fitar, tare da mony suka fito daga gidan suka rufe sannan suka kama hanyar address ɗin da Juwairiyya ta turo mata.
A mota momy ta ce "Ba laifi ai gidan ya yi kyau ko?"
Ikram ta ce "Ehh ya yi momy. Haka nan kika ce sai an yi fenti ma, ai akwai fenti lafiya lau."
Momy ta ce "A'a ai kuma ba kalar da kike so ba ne. Kalarki za'a miki irin na zamani." Ta yi murmushi.
Ikram bata ce komai ba har suka ƙariso daga dai-dai inda Juwairiyya ta ce ta kirata idan ta iso.
Tana ɗauka ta shaida mata, da murna ta ce ta jirata gata nan fitowa.
Ba'a wani daɗe ba sai ga Juwairiyya ta iso sanye da doguwar hijabi har ƙasa tana daga nata hannu. Tada motar Ikram ta yi ta ƙarisa inda Juwairiyya ta ke, shiga ta yi da hannu ta ke gwada mata gidan.
A ƙofar gida Ikram ta faka motar sannan suka shiga cikin gidan tare har da momy.
Suna shiga wata budurwa mai bala'in kama da Juwairiyya ta rungume Ikram da fara'a tana kallonta. Ita kanta ta san sun ɗan yi yanayi da Ikram, kamar ƴan uwan juna.
"You are highly welcome my Ikkey, I have been hearing about You. (Ina miki barka da zuwa Ikkiey, na daɗe ina jin labarinki.)" Ta mata murmushi.
Juwairiyya ta ce "Here's her Mother." Ta gwada mata momy.
Har ƙasa ta gaishe da momy sannan suka ƙarisa cikin gidan.
Bayan sun shiga wani falo Juwairiyya ta ce su zauna zata kira Kakarta da mahaifiyarta.
Ruwa ƙanwar Juwairiyya mai suna *Khaleesat* ta kawo masu sannan ta zauna tana ɗan jan Ikram da fira cikin yaren turanci.
Suna cikin firar ne Kaka da Ummi suka fito, sosai kakar ta dattijanta, sai dai akwai fara'a sosai kunshe a fuskarta.
Momy na haɗa ido da Ummi ta miƙe tsaye tana zare ido, ita kanta Ummin kallonta ta ke cikin mamaki tana gwadata da yatsa.
Su duka sun kasa furta komai, sai su Juwairiyya da ke binsu da kallon mamaki.
Da ƙyar Ummi ta iya furta "Ummu Salmah.." Daga nan ta yi shiru tana tuno wasu abubuwa wanda ita kaɗai ta barwa kanta sani.
A hankali itama momy ke faɗin "Am not very sure ke ce ko ba ke ba ce. Kaina ya ɗaure baki ɗaya, I don't even know what to do." Ta koma ta zauna dafe da kanta.
Shiru ya biyo baya kafin Kaka ta ce "Me ke faruwa ne?" Cikin yaren larabci.
Ummi ce ta ce "Wannan ita ce Ummu Salmah, wadda ta ɓata tun tana ƴar shekara goma sha biyu, ɗiyar wan babana. I can recognise her wallahi" Cikin larabcin itama ta yi maganar tare da sirka turanci.
Har yanzu Momy bata ce komai ba, sai dai idonta ya sauya kala izuwa jaa, ji ta ke kanta yana sara mata kamar zai fashe, zuciyarta na tafarfasa.
Ikram da mamaki ya gama kashewa, saboda tana ɗan jin larabci kaɗan-kaɗan, bata dai iya miyar da mai tsawo ne, amma in dai yi a ke a gabanta tsaf zata iya gane abin da ake faɗi.
Ƙasa ta duko gaban momy ta ɗago ta, "Momy me ke faruwa ne? Kin santa ne?"
Kai kawai momy ta gyaɗa tana kuka sosai wanda bama ta san abin da zata yi ba.
Cikin natsuwa Kaka ta ce "Ummu Salma."
Ɗago kanta ta yi ta kalle ta ba tare da ta furta komai ba.
"Kin san ko wacece wannan?" Ta gwada mata Ummi da hannu.
Kai ta ɗaga mata alamar ehh, sannan ta ci gaba da "Zamu so jin kaɗan daga tarihin rayuwarki, don mu tabbatar da zarginmu a kanki."
Shiru momy ta yi na wani lokaci kafin ta ce "Yau dai zan fitar da wani sirri wanda ban taɓa faɗawa kowa shi ba sai marigayi mai gidana. Ko yarana babu wanda ya taɓa jin asalina, amma yau gashi dalili zai sa ni faɗi." Ta share hawayenta kafin ta ce "Tun ranar da na fara saka Juwairiyya a idona na ke jin wani abu game da ita, nake ji a jikina tabbas akwai jini a tsakaninmu. Sai dai na bar maganar a cikina ne saboda bana son tada wani tsohon tabo daya daɗe da warkewa a zuciyata.
Sunana Ummu-Salmah Annoor, na taso a hannun iyaye na cikin farin ciki da ƙaunar juna, sun kyautata min amma hakan bai hanasu bani kyakkyawar tarbiyya ba. Ba laifi iyayena sun bani kyakkyawar tarbiyya duk da ba wani girma na yi a gabansu ba.
Babban abin da ya ke damuna a lokacin shi ne yanda babana da mamana suke yawan samun saɓani, wanda a gabanmu su ke faɗa sosai wani lokacin har da jefe-jefe.
Tun ina ƴar shekara huɗu ban wani san komai ba suke yi a gabana, har na fara sanin abin da su ke aikatawa.
Har akai min ƙanwa basu daina wannan halin ba, kullum cikin damuwa na ke, amma babu yanda na iya.
Wata rana Abbana zai tafi ƙasar India domin ganin likita a kan cutar ciwon suga da ta ke damunshi, muka tafi airport ni da Ummana sai kuma ƙanwata guda ɗaya mai suna Saratu. A lokacin ina da shekara goma sha biyu a duniya.
Bayan mun je airport ɗin ne bamu tafi ba har sai da muka ga jirgin su Abbana ya tashi. Ƙaddara da tsautsayi da kuma yarinta suka sa na tafi na bar su Ummana, saboda fitsari da ya matse ni, wurin yin fitsarin na nufa, sai dai kuma bayan na gama na nemi inda su Umma suke amma ban gansu ba.
Kuka na ke sosai sai ga wasu mutane sun zo mata da miji, wanda su kuma ƴan Nigeria ne, ganin ina kuka yasa su tambayata ina iyaye na? Amma ban san abin da suke faɗi ba, saboda ni larabci kawai na ke ji, sai ko turanci kaɗan kaɗan.
Kama hannuna matar ta yi da turanci ta ke tambayana idan iyayena su ke, amma tsabar rikicewa tasa na kasa faɗin komai sai nuna masu wani jirgi na ke. Jirgin kuma wanda zai tafi Nigeria ne na ke gwada masu, hakan yasa suka yi tunanin ko iyayena suna cikin jirgin ne, dama kuma suma jirgin ne zasu hau.
Shiru na yi ina kallonsu har muka ƙarisa ciki, nan suka hau bin layi-layi da ni wai ko a tunaninsu zan gano iyayena amma shiru. Tunani suka yi ko jirgin da ya tashi na Nigeria ne suke ciki, hakan yasa suka hanzarta zuwa wurin biyan kuɗi, a lokacin duk ba'a kawo wannan tsare tsaren yin abubuwa ba. Kuɗin kujerata kawai suka biya, hakan yasa suka yi missing flight sai washe gari muka tafi tare. Babban abin mamaki shi ne yanda har muka baro ƙasar bamu ji wata sanarwa game da ɓatana ba." Momy ta yi shiru daga nan sanadiyyar kukan da ya ƙwace mata.
Bayan ta yi shiru ta ce "Daga nan muka iso ƙasar nan, nan garin muka zo, kasantuwar mutanen ƴan garin Sokoto ne. Har gidajen television dana radio ta bada sanarwata, har da hotunana aka ɗauka ina kuka har BBC, amma shiru babu wani labari. Gidansu suka barni na ci gaba da zama, ban fi wata ɗaya a gidan ba Hajia Shafa ta ringa muzguna min, duk wani aikin gidanta ta miyar dashi a kaina. Daga ƙarshe dai mijinta ya tausaya min da abin da ta ke, bata ko san lokacin da ya ɗauke ni ya kaini gidan marayu ba.
A nan na ci gaba da rayuwa har na girma, na yi makaranta har matakin diploma, har a lokacin ban taɓa tunanin komawa ƙasata ba, saboda sam bana son halin da iyaye na su ke yi, kuma a ganina kamar ummana bata sona, tun da har bata nemeni ba. Ana cikin wannan lokacin ne Alhaji Muhammadu ya fara neman aure na, inda aka sha gwagwarmaya sosai kafin ya aure ni, saboda sam danginshi basa ƙaunata, sun so ya auri wata ƴar uwarshi ne amma shi ya nace lallai sai ni zai aura.
A lokacin da na fara haɗuwa da Ikram kanta sai da na ji wani abu, musamman data ambaci dangin mamanta ƴan Misrah ne, abin da yasa ban miyar da hankalina a kan abin ba, saboda sam bana sha'awar wani abu daya shafi Misrah, dan a ganina iyayena basu ƙaunata ko kaɗan." Ta yi shiru daga nan tana share hawaye.*Team Ikramhaidar*
*Team Ikramkhalid*

KAMU SEDANG MEMBACA
SHI NE SILAH!
Romansashi ne silar rugujewar farin cikin rayuwarta. shine silar shigar ta cikin kunci da bakin ciki. shi ne silar rashin gata hadi da galihu a rayuwarta. shin waye silah? ku biyoni a cikin wannan labarin inda zan warware maku zare da abawa.