68

903 52 0
                                    

*SHI NE SILA!*
           😪😪😪

              Na Princess Amrah
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
                           (2018)

_🖤Sometimes the best way to stay close to someone you love is being just a friend, nothing more nothing less.🖤 Happy married life my dear friend 💕💕(Xarah~b~b)💕💕_

68~  Ɗakin Haidar ɗin suka nufa kuwa. Ikram suka samu zaune har yanzu jikinta a sanyaye ya ke, tunanin Miemie ya gama mamaye duk illahirin zuciyarta.
   Ganin ƙawayen nata sun cika ɗakin yasa ta sakin murmushi wanda har haƙoranta suka bayyana.
   "Sannunku da zuwa." Ta faɗa tare da miƙewa daga bisa gadon ta basu wurin zama.
    "Ƴar rainin hankali ashe gudowarki kika yi ko?" Haneefah ta faɗa bayan ta zauna.
    "Wallahi ba haka ba ne. A asibiti fa muka kwana Miemie bata da lafiya." Ikram ta faɗa a hankali.
    Salati suka ɗauka su duka da ke ɗakin. Smart ta ce "Allah sarki! Ashe shiisa muka jiku shiru. Amma kuma laifin Husnah ne da bata faɗa mana ba ai da mun je mun duba ku."
    Ikram ta yi saurin cewa "Husnah ma fa bata sani ba. Babu wanda ya sani har Mama. Da yake gidan Yaya kareema ne ciwon ya same ta."
     Candy ta ce "Wayyo! Aiko ya kamata mu je mu duba ta ko?"
     "Ai an sallame ta tana gidan Yaya Kareema. Ina jin ma tare zasu zo nan ɗin. Ba sai kun je ba." Ikram ta yi saurin faɗi tana ɗan kallon Husnah da itama ita ta ke kallo.
      Ganin ɗakin ya masu kaɗan yasa Husnah ta je ta shaidawa momy. Ɗakin Khalid aka basu nan suka rabu, wasu suka tsaya ɗakin Haidar tare da amarya, wasu kuma suka nufi ɗakin Khalid.
    Ƙarfe sha ɗaya na safe aka shishhigo da abincin ƙawaye kala kala, tun daga kan fried rice, dambun shinkafa, masa, pepper soup na kayan ciki, pepper chicken, coleslaw, alkubus, funkaso, abinciccika dai gasu nan sai wanda mutum ya zaɓa. Ga kuma tray biyu na soyayyun kaji daban.
    Husnah zata fara serving wasu daga cikin ƙawayen suka ce a bari har a jima, tun da dai babu mai jin yunwa sosai a cikinsu.
    Tun da Ikram ta kalli agogo ta ga sha biyu saura kwata gabanta ke faɗuwa. Saura minti goma sha biyar ta zama matar aure, matar mutumin da bata taɓa tsammanin kasancewa matarshi ba.
    Momy ce ta zo da sauri cikin ɗakin da Ikram ta ke ta ce "Ikram zo." Sannan ta fice sai sauri ta ke.
   Ganin haka yasa bata jira komai ba ta bi bayan momy itama tana saurin.
       Fita suka yi har tsakar gida tare, ɗakin mai gadi ta ga momy ta shiga itama kuwa ta shiga ɗin.
     Tana shiga ta yi tozali da bayanshi, sanye ya ke da wata dakakkiyar shadda kalar siminti. Ga hula itama kalar siminti a bisa kanshi wadda ta zauna sosai.
   Bata gane ko waye ba tun da can ya kalla, sai dai jikinta ya bata wani ne mai muhimmanci a gare ta.
     Jiki sanyaye ta ƙarisa shiga da sallama. Amsawa ya yi haɗe da juyowa ya kalle ta da murmushi.
   Wa zata gani? Halle ne mahaifinta ya yi fes da shi kamar ba shi ba. Ya yi ɓul-ɓul abinshi kamar ba shi ne marar lafiyar nan ba.
    Tsabar mamaki sakin baki ta yi kawai ta kasa furta komai tun bayan sallamar da ta yi.
    "Ikram ƴata ga Babanki ya dawo gare ki. Dawowa kuma ta har abada!" Ya sakar mata murmushi.
    Ajiyar zuciya ta sauke ta ce "Na ji daɗin dawowarka a wannan lokacin babana. Ko wace ƴa tana burin ace an ɗaura aurenta a gaban mahaifinta ko da kuwa a ce ba shi ne waliyyinta ba, na jima ina tunanin ranar da wannan ranar zata zo ko dan wanda zai zama waliyyina. Sai momy ta bani tabbacin akwai abokin Abba wanda zai zama waliyin amarya da ango. Sai gaka Allah ya dawo min da kai a wannan lokaci. Allah na gode maka!" Ta faɗa jikinshi tana kuka.
      Ɗan janye ta ya yi daga jikinshi yana murmushi ya ce "To kuma miye abin kukan? Ba gani Allah ya dawo da ni ba?"
    Ikram ta ce "Baba ina ka tafi ka barni cikin damuwa? Wai ka ƙi faɗa min zaka tafi sai dai ka bar takarda a bani."
    Halle ya ce "Ba ta wannan a ke ba yanzu. Kawai dai abin da zan faɗa miki *SHI NE SILAH!* shi ya kaini ƙasar India ya ɗauki nauyin komai har Allah yasa na samu lafiya. Sannan kuma da saninshi, tun da shi ya ƙirƙiri tafiyar ma baki ɗaya tun asali.
      Bai fi saura minti goma a ɗaura aure ba. Ki koma wurin mutane zan baki labarin yanda komai ya kasance daga baya."
     Wata ajiyar zuciyar ta kuma saukewa sannan ta ce "To shi ke nan Baba. Allah ya ƙara bada lafiya."
    "Ameen." Momy ta faɗa haɗe da sakin murmushi ta ce "Ni sai kiran yayan naku ma na ke bai ɗauka ba. Na rasa dalili, ko yana cikin mutane ne oho."
     Halle ya ce "In dai Haidar ne fa baya nan. Na ji tun ɗazu ana ta jajenshi a wurin wai ba'a ganshi ba. Ga abokanshi ma sai nemanshi su ke wai a waya ya ce masu gashi nan zuwa."
    "To shi ke nan. Sai a fita ai ko Baban Ikram? Ko akwai wata matsala?" Momy ta faɗa.
    "Babu matsalar komai Maman Ikram. Bari in fita saboda mutane." Ya nufi hanyar fita.
   Ikram da momy ma suka fita kowa ta nufi inda zata je.
     Har ƙarfe sha biyu da rabi babu ango babu alamunshi. Har maɗauran auren sun ce kawai bari su ɗaura saboda mutane akwai wanda su ke da uzururruka.
    Wakilin ango ne ya fiddo sadaki naira dubu ɗari aka isar da ita ga Halle.
    Nan aka fara bayani cewa "Za'a ɗaura auren Aliyu Haidar da Ikram..." Kafin mai bayanin ya ƙarisa ya ji murya an ce "A dakata!" Da ƙarfi yanda kowa zai ji.
    Kallon kowa ya koma ga Haidar da ya iso yanzu, biye da shi Salim ne abokin Khalid, sai kuma Marwan abokinshi.
     "Takawarka lafiya angon Ikram. Barka da isowa." Mai bayanin ya ringa faɗin haka.
    Ɗaure fuska Haidar ya yi ya ce "Kawu Ɗahiru da Baba Halle Bismillah dan Allah."
    Mamaki kowa ya ke, tabbas akwai wata matsala ɓoyayya.
    Gaba ya yi Kawu Ɗahiru da Halle suka mara masa baya. Sai da suka isa bakin motar Marwan sannan suka dakata.
    Bayanin kusan minti sha biyar ya masu sannan ya miƙawa Kawu Ɗahiru kuɗi, suka jinjina kai suka yi gaba shima ya bi bayansu.
    Bayan sun isa ne suka ma mai bayanin jawabi, sannan Kawu Ɗahiru ya zaro rafar dubu ɗari daga alijuhunshi wadda Haidar ya bashi yanzu.
    "To masha Allahu! Ɗaurin auren ya koma biyu ke nan. Za'a ɗaura auren Aliyu Haidar Muhammadu da Aminatu Abdurrahman a kan sadaki naira dubu ɗari. Sannan kuma Khalid Muhammadu da Ikram Halliru Mahmoud itama a kan sadaki dubu ɗari. Gasu nan aje lakadan ba ajadan ba."
    Bayan an yi duk abin da ya dace sanann aka ɗaura aurukan guda biyu. Wanda Halle ya zama waliyyin Ikram da miemie, Kawu Ɗahiru kuma ya zama wakilin Haidar da Khalid.
     Nan aka hau rabon goro, bayan an gama aka fiffito da manya-manyan kulolin abinciccika aka fara ci.
     Mutane sai ƴan gulmace-gulmace a ke ta yanda ɗaurin auren ya canza akala lokaci guda. Sannan kuma an ɗaura auren Ikram da Khalid wanda baya ma ƙasar.
     Fuskar ango marubuciyar ta kalla, a zatonta ko zata ganshi cikin damuwa, sai dai mamaki abin ya bata, saboda ya saki jikinshi sosai abokanshi sai zaulayarshi su ke yana dariya.
     Kafin kace kobo magana ta fara yaɗuwa a cikn gida har ta isa ga momy wadda ta ɗauki abin kamar wasa. Sai dai kuma a wani ɓangaren na zuciyarta tana jin kamar ta yarda da maganar, amma mamaki ta ke sosai ta yanda hakan zata kasance.
    Abu wasa ba wasa ba kowa ya sani, sannan kuma duk inda momy ta gitta sai ta ga ana binta da kallo. Hakan ne ya fara bata tsoro da sauri ta matsa can bayan gida inda babu mutane ta kira lambar Haidar.
     Ta jima tana bugawa sannan ya ɗauka.
    "Me kunnuwana su ke jiye min ne wai?" Ta tambaye shi ido buɗe tana mamaki sosai.
    "Momy me fa?" Ya tambaye ta a hankali.
    "Da alama akwai wani abu the way (ta yanda) kake magana. Mu haɗu ɗakin mai gadi yanzu yanzun nan." Ta faɗa haɗe da tsinke kiran.
    Ɗakin da su Ikram su ke ta fara nufa. Ƙoƙarin kawar da damuwa ta yi sannan ta ce "Ƴan mata sannunku fa. Abincin dai ya ishe ku ko?"
    Ƴan *RAZ NOVELLA* da suka iso yanzu Ayeesher ta ce "Ahh alhamdulillahi momy. Gashi nan ma har an barshi da yawa."
    Murmushi ta yi ta ce "Haka na ke so to. Idan dai akwai wata matsala sai ku faɗawa Husnah ta neme ni. Ikram zo." Ta fita da sauri.
    Ikram kam ko a jikinta. A tunaninta ko maganar Halle ne, tun da su sam wannan maganar bata iso inda su ke ba. Tun da babu wata babbar mace da ke gicci ta wurin in ba momy ba.
     Suna isa ɗakin mai gadi suka samu Haidar da Salim a ciki.
     "Faɗa min gaskiyar abin da ya ke faruwa." Momy ta faɗa babu wasa ko kaɗan a fuskarta.
    Shiru Haidar ya yi kafin ya ce "Tun jiya Miemie bata da lafiya an kwantar da ita asibiti saboda...." Ya bata labari kamar yanda Ikram ta faɗa masu shi da Marwan. Sannan ya ci gaba da "Ɗazu da safe bayan mun kawo Ikram nan daga asibiti. Shi ne aka kirani da wata lamba ban ɗauka ba a zatona ko marasa lafiya ne. Gudun kar a shiga time na ɗaurin aure. Ganin an dage da kira yasa Marwan ya ce in daure dai in ɗauka in ji ko menene. Ina ɗauka na ji muryar Salim ya gaishe ni na amsa sannan na ce "Ka yi haƙuri fa. Wallahi ban san kai ba ne."
    Salim ya ce "Babu komai babban yaya. Dama wata magana ce babba tasa na kiraka. Amma in da hali ko zamu haɗu mu yita baki da baki?"
    Cikin mamaki na ce "Ikon Allah! Gashi kuma yanzu am too busy. Ko zaka bari zuwa anjima bayan an ɗaura aure?"
    Salim ya ce "Da dai zaka daure mu haɗu ɗin yanzu dan Allah."
   Ganin ya nace a kan mu haɗu yasa muka yi mahaɗa da shi a gidan Marwan tun da dama daga can zan yi shirin ɗaurin aure.
   Yana isowa na fuskanci yana cikin damuwa.
    Na tambaye shi  abin da ya faru ya ce "Game da aurenka da Ikram ne."
   Da mamaki na ce "Wani abu ya faru ne?"
      Salim ya ce "Ko ka san cewa Khalid ya daɗe yana dakon son Ikram kuwa? Ka san tun wane tsawon lokaci ya ke sonta ya kasa faɗa mata? Shin ko kana da labarin cewa abin da yasa Khalid ya tafi Qatar ƙarin karatu da ba zai iya jurar ganin bikinka da Ikram ba ne? Na tabbata duk baka san wainnan abubuwan ba shiisa hankalinka a kwance zaka auri rabin ran ɗan uwanka. Yanzu haka maganar nan da nake maka Khalid na can yana jinya. Nima kaina sai yau ɗin nan da sassafe aka kirani da wata lamba, cewa wai Khalid ya bada lambar, sun matsa a kan ya dawo ƙasarshi ko kuma wani nashi ya je gudun kar ya mace masu a can wani nashi bai da labari. Bayan sun min bayani na nemi su ba Khalid wayar mu yi magana, da ƙyar ya ke yin magana yana shaida min wai ciwon zuciya ne ya kamashi. Na masa faɗa a kan wace irin damuwa ce zai ɗaurawa kanshi da har zai kamu da ciwon zuciya at his age? Nan ya ke bani labarin wai Ikram ce zata yi aure, kuma wai kai zata aura, dalilin da yasa ma ke nan ya bar ƙasar. Na yi mamaki sosai kuma na ce tun da abin haka ne ni zan faɗa maka gaskiya, amma Khalid ya hanani, wai in barku ku yi aurenku, dan da alama Ikram na sonka, baya so ya aure ta alhali ba shi ta ke so ba. Kuma wai na masa alƙawarin ba zan faɗawa kowa ba, hatta da ciwon da ya ke baya son kowa ya sani, zai turo min da kuɗi in je Qatar ɗin kamar yanda malaman asibitin suka nema.
    Ko kaɗan ban gamsu da hakan ba, kawai dai na ce masa to amma na ji ba zan iya haƙura ba. Kar a je Khalid ya mutu da soyayya. Kuma ko da Ikram bata sonshi na san akwai shaƙuwa mai ƙarfi a tsakaninsu, wadda ita kanta zata iya zama soyayya. Wannan dalilin ne yasa na yanke shawara kawai in tinkare ka da maganar. Idan da yanda za'a yi sai a yi."
    Tun da Salim ya fara maganar na ke kallonshi. Sosai na ke son gasgata maganarshi saboda tunowa da na ke da abubuwa da dama wanda suka gabata. Abin da na fara tunowa shi ne; ranar da muka yi karo da Ikram har na faɗi, na ɗaga hannuna zai mare ta amma Khalid ya riƙe min hannun. Sannan kuma na tuna reaction ɗinshi a lokacin da na ga Momy na faɗa masa hukuncin da ta yanke a kan aurena da Ikram. Gashi kuma bai taɓa maganar zuwa masters wata ƙasa ba sai daga lokacin da aka fara maganar auren.
   Na jima inana tunane tunane kafin na sadda kaina ƙasa hawaye na zirara daga idona.
    Cike da mamaki Marwan ya ce "Namiji  ba dai kuka ka ke akan wannan ƙaramin abin ba ko?"
    Gyaɗa kai kawai na yi na kasa furta komai ban kuma daina hawaye ba.
   Salim ya ce "Gashi kuma ni ya bar ma maganar karatunta. Last week mun je da ita School clinic ɗin saboda gwaje-gwaje. Result ɗinta yana hannuna yanzu haka. Kuma Genotype ɗinta AS ne, sannan kuma na daɗe da sanin kaima naka AS ne tun a BUK Khalid ya taɓa faɗa min, wai momy'nku ke da AS Abbanku kuma AA, shiisa aka samu haka. Ban taɓa sanin kai ne zaka auri Ikram ba shiisa ban damu da sai na sanar da ku ba. Haka kuma ban kai mata result ɗin ba saboda ina jira a gama komai sannan in damƙa mata takardunta ta yi submitting ɗinsu. Gasu nan ka gani." Ya miƙa ma Haidar results ɗin.
   Bayan na karɓa na duba takardun sannan na aje su.
    "Ko da ace AA ne genotype ɗin Ikram sam bai kamata in aure ta ba. Khalid shi ne mafi cancantar ya aure ta. Ko ba komai Khalid *SHI NE SILAR* dawowar farin cikin Ikram. Shi ya kula da ita a lokacin da ta ke buƙatar taimako. Ya zama *SILAR* dawowarta cikin farin ciki. Sannan ni kuma yanzu haka ga wata can kwance tana jinya saboda ni. Saboda soyayyar da ta ke min. Na gode ƙwarai Salim da abin da ka min."
   Salim ya ce "Na ji daɗin hakan sosai Yaya, amma ya kamata mu san yanda za'a yi Khalid ya dawo yau zuwa gobe."
      Tun daga nan muka fita daga gidan, a lokacin har sha ɗaya na safe ta wuce. Lambar malaman asibitin da suka kira Salim na karɓa na kirasu. Nan na basu tabbacin Khalid ƙanina ne. Kuma ina so duk yanda zasu yi su yi su sama masa visa yau ɗin nan ya dawo Nigeria. Duk yanda zai yi da su kar su ƙyale shi. Allah ne kaɗai ya san ladar da zasu samu.
    Kuɗi na tura masu wadatattu sannan muka koma gidan Marwan. Lokacin har sha biyun rana ta wuce.
   Da hanzari muka shirya dan na san ana can ana jira, fatana dai Allah yasa kar a ɗaura auren sai mun isa. 
      Sai da muka fara biyawa gidan su Miemie babu kowa sai mamansu. A taƙaice na bata labarin duk abin da ya faru, da kuma auren Miemie da na ke so a ɗaura yau-yau ɗin nan da ni. Duk da ta yi mamaki amma bata hana ba. Sosai ta nuna jin-daɗinta kuma ta aminta da hakan. Ta ce kawai mu je duk wanda zai zama waliyyin Ikram itama miemie ya zama nata. Saboda mahaifinta baya nan ya yi tafiya. Daga nan muka kama hanyar gida.
   Muka yi sa'a kuwa, muna isowa dai-dai za'a ɗaura. Abin da ya faru ke nan. Yanzu haka Khalid na bisa hanya insha Allahu. Dan mun yi waya da su sun ce jirginsu ya taso."
      Haidar ya yi shiru daga nan cike da damuwa.
    Sosai momy ke kuka, da ƙyar ta samu ta iya faɗin "Allah sarki Khalid! Mesa zaka cuci kanka? Ka san Ikram kake so shi ne zaka yi zurfin ciki? Bakai min adalci ba. Da ace an riga da an ɗaura auren nan da ba zan taɓa yafewa kaina ba." Kuka ta ke sosai cike da tausayin ɗanta. "Tabbas Salim kai aboki ne na gari. Hakan da ka yi ka kyauta kuma haka ake son ko wane aboki zama ya kasance. Na ji daɗi ƙwarai da baka ɓoye mana wannan gagarumin abu ba. Tabbas Khalid shi ne mafi cancanta Ikram ta aura. Haka kuma Miemie ita ce mafi cancanta Aliyu ya aura."
    Ba Ikram kaɗai ba har Haidar sai da ya yi mamakin jin momy ta faɗi sunanshi. Tun da su ke har yarintarshi bai taɓa jin sunanshi a bakin momy ba sai yau. Lallai an yi abu mafi girma tun da har hakan ta kasance.
    Ikram da ta kasa komai sai aikin kuka ta ce "Yaa Khalid shi ne mafi soyuwar mutum a gare ni. Ban taɓa son kowane namiji ba sai a kanshi. Na yi zurfin ciki kamar yanda shima ya yi. Ban taɓa tsammanin yana sona ba hakan yasa na dinga ƙoƙarin ɓoye soyayyar da na ke masa. Ko ba komai ƴar hausawa ba'a santa da nuna tana son namiji kafin shi ya nuna mata ba. Na bi umurnin Momy zan auri Yaa Haidar ne kawai ba wai dan ina masa son aure ba, sai dai ina masa na ƴan uwantaka kamar yanda na zata Yaa Khalid yana min. Na ɓoyewa Miemie wanda zan aura gudun aukuwar wani abu. Sai gashi hakan sai da ta faru." Ta duƙe ƙasa tana kuka sosai. Kukan abubuwa kala-kala.

_(Genotype AA, AS and SS. Zan yi bayaninsu insha Allahu a littafina mai zuwa bayan sallah. Wanda abin da zai ƙunsa ke nan da izinin Allah.)_

_Masu ƙorafi duk zan saurari ƙorafinku bayan na gama novel ɗin da izinin Allah._

*Team Ikramhaidar*
*Team Ikramkhalid.*

SHI NE SILAH!Where stories live. Discover now