49

923 43 1
                                    

*SHI NE SILA!*
           😪😪😪

              Na Princess Amrah
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
                           (2018)


49~  "Ki yi ha'kuri ki gafarce ni Ikram 'yata. Na san cewa dole zaki neme ni wanda kuma na san ban cancanin hakan ba, saboda na watsar da ke a baya.
    Zan tafi inda ba zaki 'kara ganina ko jin labarina ba. Dama babban burina in had'u da jinina, to alhamdulillah! Na ganki kin ganni, kuma ko yanzu mutuwata ta zo ina maraba da ita. Ki gafarce ni a kan tafiyar da na yi ba tare da saninki ba. Na tabbatar idan na fad'a miki ba zaki tab'a barina tafiya ba, idan kuwa har na zauna to zan zame miki wani nauyi ne a rayuwa. Dan Allah kar ki yi kuka ko kuma ki saka damuwa a ranki, saboda kina tare da mutanen kirki wanda zasu d'ebe miki kewar iyayenki baki d'aya.
    Sai anjima, daga mahaifinki mai 'kaunarki Halliru."
    Baki d'aya jikinsu ya yi sanyi, momy kam sakin takardar ma ta yi baki da'ya tana kallon Ikram, tana jiran ganin abin da zata yi.
     Runtse ido Ikram ta yi tana matso k'walla zafafa, a hankali ta ke gya'da kai tana fa'din "Allah gani gare ka ya Allah! Idan wani laifi na maka ka yafe min na tuba. Wannan jarabta da ke ta bibiyata ..." bata gama fad'i ba momy ta toshe mata baki. "Kar ki yi sab'o mana Ikram. Ki dangana al'amurranki ga Allah, shi kad'ai ya san me ya ke nufi da ke da kuma rayuwarki."
    Rungumar momy ta yi bayan ta saki ledar kayan data siyawa Halle tana kuka sosai mai tsuma zuciya.
   Babu wanda bai tausayawa halin da ta ke ciki ba.
   Haidar ya ce "Kuma fa har da asubar nan sai da na zo na dubashi yana nan bai tafi ba. Ki daina kuka Ikram, addu'a zaki yi, Allah yasa ya fad'a hannu na gari, rayuwa mai kyau."
   "Haka ne." Khalid ya fad'a shi kanshi cikin wani yanayi wanda ba zai iya misaltashi ba.
    "Ku kwashi kayan mu tafi kawai Khalid." Momy ta fad'a jiki a sanyaye har yanzu bata saki Ikram da ke rungume da ita ba.
    A hankali ta kamata suka nufi mota, bata daina kukan ba sai dai yanzu a hankali ta ke yi, ruwan hawayen kawai ke fita.
     Ko da suka isa gida a parlor suka tsaya, sosai momy ke mata nasihu a kan yarda da k'addara mai kyau ko akasinta.
   Cikin kuka ta ce "Babu komai komy, na yarda na kuma d'auka a zuciyata cewa wannan *K'addarata ce* wadda dole sai ta hauni ko ina so ko bana so. Bana fatan ko mak'iyina ya ga jarabta irin tawa. Allah na gode maka, Allah ka canza min rayuwata ka had'ani da farin ciki mai d'aurewa har abada!"
    "Ameen 'yata. Goge hawayen kar na kuma ganinsu kin ji?" Momy ta fad'a tana share mata hawayen da hannu.
    K'irk'iro murmushi Ikram ta yi ta ce "Barin shiga d'aki momy. Ina jin bacci sosai."
    Momy ma murmushin ta yi ta ce "Ai kin isa ki jishi Ikram. Kin sha aiki sosai yau. Allah ya yi miki albarka ya baki zuri'a ta gari, wanda kema zasu miki ladabi da biyayya kamar yanda kike ma na gaba da ke."
   Kunya Ikram ta ji sosai, ko ameen d'in ma kasa fad'i ta yi sai hayewa sama da ta yi hannunta rik'e da wayarta.
     Haidar kuwa d'akinshi ya shiga ya zauna a bakin gado. Murza sumarshi ya yi da duka hannayenshi yana fad'in "Whats wrong with me? Me ke shirin faruwa da ni? Soyayya? Impossible!" (Ni ko na ce 'pyaar impossible ke nan.Sunan wani film🤣)
    Wata zuciyar ta bashi amsa da "You are in love guy.."
    Saurin gyad'a kanshi ya yi alamar k'arya zuciyar tasa ke masa.
    'To idan ba so ba menene?' Wani b'aren zuciyarshi ya sake tambayarshi.
    'Kai a'a! Ko soyayya zan yi ai ba zan yi da Ikram ba. Yarinyar da bata ko 'kaunar had'a ido dani. Yarinyar da ta d'auke ni wani *makashin* mahaifiyarta. Zan dai aure ta ne kawai dan umurnin mahaifiyata ba wai dan soyayyya ba. Me ma zan yi da wannan 'yar 'karamar yarinyar? Wadda bata wuce a ce a mata wanka ba?'
     Sake murzar gashin kanshi ya sake yi had'e da jawo laptop 'dinshi ya kunna film d'in Ankur Arora (the murder case) yana kallo. Sosai ya raja'a da kallon film 'din saboda ya matuk'ar tausayawa yaron. Kamanta kanshi ya yi da halinshi. Kusan abin da ya ma Mahaifiyar Ikram ke nan. Sai dai kuma shi d'in ai da banbanci. Kuma ko a lokacin akwai babban dalili ne, wanda shi kad'ai ya barwa kansa sanin ko wane dalili ne.
   
***
    *'Karfe biyu da minti arba'in da biyar na dare (2:45am)*

SHI NE SILAH!Where stories live. Discover now