*SHI NE SILA!*
😪😪😪Na Princess Amrah
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
(2018)_Wannan shafin naku ne baki ɗaya *Team Ikramkhalid* a bisa tausayinshi da ku ke. Na baku shi toshi dan ku sakar min mara haka nan. Irin su Khadija Candy, Queen miemie, Munay, Hindat, Asmau Umar, Sis Rabi'atu Sk da saura da yawa wanda baki ba zai iya furtasu ba. Amrah na masifar ƙaunarku kuma ana tare._
55~ Yau ta kasance ranar litinin kuma yau ne za'a yaye su Ikram daga make up School. Sosai aka gayyaci mutane kamar yanda aka saba yi ko wane send-up idan za'a yi.
Su Momy duk an zo da sauran iyayen ɗaliban har da wasu manya manya daga gwamnati.
Ɗalibai kuwa sun jera sun sha ankon wani haɗaɗɗen material pink and blue, ko wace ta yafa mayafi pink, ga uban make up da suka sha, kallo ɗaya za'a masu a gane cewa su ɗin make up students ne.
Ɓangaren da iyaye su ke daban, sai kuma ɓangaren da malamai suke ma daban, ɗaliban kuma kan wasu ƙawatattun kujeru suka zauna wanda kallo ɗaya zaka masu ka ji kamar ka sace ɗaya daga cikinsu ka gudu.
Nan fa aka fara kiran sunaye ana basu certificates. Bayan an gama MC (Mai gabatar da bayani) ɗin ya yi bayanin cewa "Akwai best ten, wato masu ƙwazo kuma jajurtattu guda goma wanda aka fitar, za'a basu kyaututtuka da abin da ya kamata." Nan fa ya fara kiran sunaye, su kansu best ten ɗin hawan hawa ne. Ikram ita ce ta zo ta biyu wanda maki ɗaya ne kawai ya banbantata da wadda ta zo ta farkon, ita ma ɗin dan saboda dama can tana make up, ƙarin ilimi kawai ta zo yi.
Wani irin make up kit ne aka ba Ikram mai girman trolly na biyu a cikin saiti. Babu abin da babu a cikin kit ɗin.
Fitowar Ikram lokacin da za'a bata kyautar kanshi abin burgewa ne, saboda cikin wani salon takunta mai jan hankali da ɗaukar ido ta iso, fara'a ƙunshe a fuskarta ta sha ɗaurin ɗankwali mai matuƙar kyau, wanda duk ƙoƙarin da ta yi na ganin ta ɓoye gashin kanta dole sai da kyakkyawar sumar da ke kwance bisa goshinta ta bayyana.
Nan fa aka hau yin tafi da ƙarfi, masu ɗaukar hotuna suna ɗauka, masu yin videos ma suna yi, abin dai gwanin ban sha'awa sai wanda ya gani.
Bayan an gama basu duka kyautukan best ten ɗin ne Aunt Juwairiyya ta karɓa micro phone inda ta fara nata bayanin cikin yaren turanci; "As you all know that we have different classes, each class has his own teacher, am the one who teaches; how to make a different types of veiling/rolling, and I have best three in my Class, I have; (Kamar yanda kuka sani cewa muna da azuzuwa daban-daban, ko wane aji yana da malaminshi, to ni ce wadda ke koyar dasu yafin mayafi kala kala. Kuma ina da gwaraza guda uku a nawa ajin, ina da) ; Husnah Muhammad Inuwa, Maryama Abdul, and we also have Ikram Mahmoud who came first. (Wadda ta zo ta ɗaya)"
Nan fa gwarzayen uku suka fito a tare cikin takun ƙasaita, da ka gansu ka ga *ƙasaitattun mata* inda suka shassha hotuna da Aunt Juwairiyya da kuma sauran malamansu.
Haka wadda ta koya masu salon ma ta zo ta kira nata gwarazan, a nan kam ta uku Ikram ta yi.
Momy sai farin ciki ta ke, ashe dai ƴar tata ba daga baya ba. Shi kanshi Khalid sai da ya yi mamaki, Haidar kam bai samu zuwa ba saboda yana da aikin da zai yi ƙarfe goman safe.
Sai misalin ɗaya na rana aka gama, inda aka ci gaba da cashewa, su Momy kam gida suka tafi suka bar Ikram data shige cikin ƙawaye ana ta hotuna wasunsu kuma suna rawa, saboda ita dama ba ma'abociyar rawa ba ce dan bama ta iya ba.
Kit ɗinta da sauran kyaututtukan data samu duk su momy suka tafi mata da su, saboda dama ba tare suka zo ba, itama ɗin da tata motar ta zo.
Samarin da suka ce suna son Ikram a wajen basu da iyaka, saboda Ikram dai kyakkyawa ce kuma mai tarin ƙwarjini da baiwa, ga uwa uba fara'a da gare ta wadda ke ƙara haskaka kyawun fuskarta a ko wane lokaci.
Sai kusan ƙarfe uku na rana Ikram ta koma gida a gajiye, fuskarta fal da farin ciki wanda ta kasa ɓoyewa.
Ko da ta shiga gida su momy ma hakan ne. Haidar ya dawo sai labari Momy ke bashi tare da gwaggwada masa kyaututtukan da Ikram ɗin ta samu.
Da ta shigo da murna ta rungume momy, take kuma sai hawaye wanda ta rasa tantance ko na menene, na farin ciki ne ko na baƙin ciki? Abin da ta kasa ganewa ke nan.
Da sauri momy ta ɗago ta ta ce "Me zan gani haka ƴata? Kukan kuma na menene? Yau ai ranar farin cikinki ce ko?"
Murmushi ta yi hale da kuka ta sake rungumar momy ta ce "Thank You very much momy. I'm very glad for what you did and always do to me, abin da kikai min, ko in ce kike kan yi min ko ƴar da kika haifa iyakacin abin da zaki mata ke nan. Allah ya saka miki da alkhairi.." Ta kuma fashewa da wani kukan.
Da ƙyar momy ta samu ta rarrashe ta ta yi shiru, ta ce "Bana son jin hakan daga bakinki Ikram, ke ɗin ai ƴata ce, bana jin zan iya banbantaki ko kaɗan da ƴar dana haifa da cikina."
Ƙirƙiro murmushi ta yi ta ce "Oya, je ki dining ga abinci can ki ci. Gobe muma zamu tafi ai."
Tashin kuwa ta yi, sai dai kuma ɗakinta ta nufa ta yi wanka ta saka ƙananan kaya sannan ta yi wanka ta sauko. Abincin ma kasa cin na kirki ta yi tsabar murna da ta ke yi.
![](https://img.wattpad.com/cover/145187938-288-k711487.jpg)
ESTÁS LEYENDO
SHI NE SILAH!
Romanceshi ne silar rugujewar farin cikin rayuwarta. shine silar shigar ta cikin kunci da bakin ciki. shi ne silar rashin gata hadi da galihu a rayuwarta. shin waye silah? ku biyoni a cikin wannan labarin inda zan warware maku zare da abawa.