shi ne silah page 8

1.1K 77 0
                                    

*SHI NE SILA!*
           😪😪😪

     Na Princess Amrah
              (NWA)
               2018

8~ A wannan daren ban yi barcin kirki ba, banda kuka babu abin da na ke yi, Goggo kuwa tana dakinta bacci har da nasari, wato ita sam bata damu da halin da ta jefani a ciki ba.
    B'arawo bacci ne ya sace ni wuraren sallar asuba hakan ya sa na makara salla har sai da gari ya fara haske sannan na yi zumbur na tashi tare da nufar band'aki.
    Wankan tsarki na fara yi ina yi ina kuka sannan na fito na yi sallar asubah.
     Da safe kuwa kasa fitowa ko tsakar gida na yi, idanuwana sun kumbura har da k'yar na ke iya bud'esu tsabar kukan da na sha.
      Goggo ce ta shigo dakina cikin fad'a ta ce "wato ba zaki taso ki gyara min wake ba har sai na makara kin ja min asarar rashin ciniki ko? To wallah in har na rasa ciniki sai irin abin da ya faru jiya ya kuma faruwa." Ta fice daga dakin. Jin ta fad'i haka ya sa jiki babu k'wari na fita, a daddafe na ke tafiyar saboda raunuka da Halle ya yi min basu da adadi.
     Haka na gama gyaran waken nan na d'ora ruwan zafi sannan na hau gyaran shinkafar da yake 'yar hausa ce sai an gyarata.
     Bayan na gama dafawa duka na koma d'akina, ina jin Goggo tana kirana wai na je na zuba tawa amma ko waiwayenta ban yi ba, saboda a halin da nake bana jin ko alamar yunwa, sai tarin bakin ciki da takaici kawai, ina mai tsananin jin haushin rayuwata a wannan lokacin, ji nake ina ma ace mutuwa ta zo ta daukeni da na fi kowa farin ciki. Sai dai kuma kash! Mutuwa ba ta zuwa a lokacin da ake sonta, ta fi zuwa daidai lokacin da mutum ya shagala da duniya ya ke tsantsar jin dadinta.
     Ko da Halle ya zo ya turo Goggo ta kirani wai yana son ganina, shigowa ta yi kuwa ta fada min sakonshi, wani sabon hawayen na ji da k'yar na iya saita kaina na ce mata "me kuma ya ke bukata a wurina? Goggo ki fada masa dan Allah ya rabu dani, wallahi na tsaneshi bana son ganinshi, ya rabu dani haka nan idan ba so ya ke takaicinshi ya kasheni ba." Na karisa maganar da kuka sosai.
     "Wai ke Umma wace irin shashashar yarinya ce? Yarinya ta girma amma ta kasa wayewa? Kullum ina kokarin wayar da ke da d'auraki bisa hanya amma kin kasa hawa? Idan kin kula fa Umma Halle yana kaunarki kuma yana da kudi, 'yan mata da yawa nema su ke ya so su amma ya k'i, ya nace sai ke, haba mana 'yata dan Allah kar ki bani kunya, ba wani abu bane kin ji Ummana?"
     Sosai kalamanta suka kara min haushi, ji na yi kamar na tashi na mammaketa ko zan samu sassauci, sanin haramcin hakan ya sa kawai na mata shiru tare da ci gaba da kukana.
     Ganin bani da niyyar saukowa ya sata fadin "ke kam kin shiga uku da bakin taurin kai, zuciya kamar ta fir'auna wadda babu wanda ya isa ya saukota? Ke ja can bak'auyiyar banza da wofi!" Ta yi k'wallo da tabarmar da ke aje tare da ficewa daga dakin.
      Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya kullum bani da aiki sai kuka har aka kwana shida da faruwar al'amarin. A na bakwai ne Goggo ta shigo d'akina ta sameni rungume da Qur'ani na gama karantawa na zurfafa a kogon tunani wanda dama aikina ke nan, in dai ba kuka ba to tunani mai zurfi.
     Sai da ta kira sunana har sau uku sannan na jita, share guntuwar kwallar da ta fito min na yi sannan na gaisheta. Bata ko amsa min ba ta ce "yau Mallam zai cika sati guda da tafiya, kuma yau na ke tsammanin dawowarsa saboda dama baya wuce sati dayan. Dan haka ina gargadarki da wannan kukan naki ki dainashi, sannan kuma kar ki sake na ji ko b'urb'ushen maganar nan a bakinsa, idan kuwa kika bari ya ji to sai ranki ya b'aci, kin kuma san yanda b'acin raina ya ke ba sai na fada miki ba, dan haka idan kunne ya ji gangar jiki ta tsira.." ta tashi ta fice. Saurin tsayar da hawaye na yi tare da tashi na ajiye Qur'anina a mazauninsa sannan na hau gyaran dakin na je na yi wanka domin tarar mahaifina.
     Ko kafin ya iso na dayaye sosai kamar ba ni ba, na koma kamar yanda na ke a baya.
     Goshin magrib ya dawo, da sauri na tarbeshi cike da farin cikin ganinshi, sai dai kuma ta ciki na ciki, saboda duk yanda na ke farin ciki da zarar na tuno da abin da ya sameni sai na ji farin cikin ya kau. Saurin gusar da damuwar na yi ta hanyar karbar kayakin hannunsa ina masa sannu da zuwa.
     "Sannu 'yar Mallam, na sameku lafiya?" Ya tambayeni fuskarsa dauke da annuri.
     "Lafiya kalau Mallam, ya kasuwa abu yana kyau dai ko?"
      "Ahh Alhamdulillahi Rumana, sai godiyar Allah. Ina Goggon taki ne?"  Ya tambayeni.
     "Tana dakinta, ina tunanin ta kabbara sallah, barin duba." Na nufi dakinta, kafin na shiga muka yi kicib'us  zata fito, na ce mata "Goggo mallam ne ya dawo, ya ce na kiraki." Murmushi ta min ta ce "ehh wallahi ina sallah ne, na ji shigowarsa ai." Muka karisa inda ya ke.
     Bayan na yi sallah shima ya yi ya fiffitar mana da tsarabarmu kamar yanda ya saba fuskar nan kullum cikin fara'a. Ban san lokacin da hawaye ya cika idona ba, tausayin mahaifina na ke, ta yanda ya yarda dari bisa dari cewa Goggo tana kula da tarbiyyata amma kuma sam ba hakan ba ne. Bai san cewa niyyarta baki daya na ta lalata rayuwata ba ne.
    Saurin goge hawayen na yi amma hakan bai hana Mallam gane abin da na ke ba.
      "Rumana lafiya dai ko? Ya na ga kamar kina kuka?"
     Murmushi na kirkiro na ce "ba kuka na ke ba mallam, wani abu ne ya fada min a ido tun dazu na ke kokarin fitar dashi ya ki fita, shi ne ya ke saka min hawaye."
     "Oh to sannu Allah ya kyauta, kin san dama hausawa sun ce wai ido baya son bako, kuma haka ne."
     "Ehh fa mallam, gashi nan ai ina ta fama."
    "Ai ke ce da karfin hali Rumana, duk yanda na hanaki wani abun ba kya bari, yanzu kin ga fa ruwan da kika jawo min ne ya sa wani abu ya fada miki kuma sai da na ce ki barshi amma kika nace sai kin d'ibo."
     Shiru na yi ina sauraron karyar da Goggo ta dage tana shararowa kafin na iya fadin "ai dole ne na yi aiki Goggo, ya za'a yi gani kuma ke ki yi? Bai kamata ba ai."
     "Maganar Rumana gaskiya ne, dole ne ta yi miki aiki, kuma ko ba komai ita mace ce, gidan wani zata je."
     "haka ne Mallam, Allah ya mata albarka ya baylta masu yi mata."
     "Ameen" mallam ya fada tare da mikewa domin nufar masallaci saboda an kira sallar isha'i.
       Bayan wata d'aya.
Har a wannan lokacin ban ga al'adata ba wanda kuma ya kamata ace na yi tun kusan sati biyu da suka gabata.
     Shiru shiru tun hankalina bai tashi ba har na fara tsorata. Ga wani irin haske da na ke yi had'e da k'iba wadda na rasa dalilin haka. Yalwataccen gashin kaina ya k'ara santsi da kyau gami da tsawo sosai fiye da yanda ya ke a baya. Ni kaina na fahimci wannan sauyin da na samu.
      Bayan Mallam ya yi wani zuwan har ya koma na samu Goggo na ke mata bayani "ni dai Goggo har yanzu fa ban ga al'adata ba, kuma ya kamata ace na yi amma shiru."
      Ido ta zaro cikin mamaki ta ce "kamar yaya baki ga al'adarki ba? Tun yaushe ya kamata a ce kin yi?"
     "Mako biyu da ya wuce." Na bata amsa.
     "Innaa lillahi! Kuma babu abin da ya sameki? Ba kya jin zazzab'i ko yawan tashin zuciya?"
      "Bana jin komai Goggo, sai dai wani lokaci idan na ci abinci mai manja sai na ji zuciyata tana tashi, amma da ya ke dama can manja yana min haka, yawaita dai kawai abin ya yi."
     Sai a sannan Goggo ta fahimci sauyin da na yi cikin kwanakin nan. Nan fa ta hau sallallami  tana fadin "shike nan mai faruwa ta faru an yi wa mai dame daya sata. *Abin da ake gudu* dai ya faru, Umma juna biyu kike dauke da shi.." bata ko karisa magabar ba na mike tsaye ina zaro idanuwa. Jin zancen na ke tamkar a mafarki, wai nice dauke da juna biyu, kuma na shege. Kuka na fasa da karfi tare da faduwa kasa, tun daga nan ban kuma sanin abin da ya ke faruwa ba sai farkawa na yi na ganni kwance bisa lasassiyar katifata.
     Koda na kara tuno abin da ya faru wani kukan na fasa wanda yayi dalilin shigowar Goggo dakin.
       "Rumana magana na shigo mu yi." Goggo ta fada, sannan ta ci gaba da  "Ina so ki sani yanda ban goya d'an shege ba haka ke ma ba zaki tab'a goyashi a cikin gidan nan ba, ya zama dole duk yanda zamu yi a yi domin zubar da cikin nan, saboda matukar aka bari kika haifeshi to tabbas kin siyar mana surutu ga mutane, mutuncinmu ni da mahaifinki kuwa ya riga da ya gama zubewa a idon al'umma in har ba'a zubarshi ba. Saboda haka tun kafin ya girma ki tashi mu tafi yanzu a zubar da shi. Kuma ko da wasa kar ki bar wannan maganar ta fita ko da kuwa ga Mallam ne."
    A tsorace na ce "goggo a zubar fa kika ce? Ni dai wallahi mutuwa zan yi na tabbata idan aka zubarshi. Sannan kuma me kike so na fadawa mahaliccina? Kisan kai fa ke nan Goggo."
      "In ji uban waye ya fada miki kisan kai ne? Abin da ba'a riga da an busawa numfashi ba ai bai zama mutum ba barin dan an zubar ace an yi kisa."
      "Abin da mutane suka kasa ganewa ke nan Goggo, ko sanda ya ke d'igon maniyyi ya zama halitta kuma kasheshi tamkar mutum ya kashe dan shekara talatin ne ko fin haka. Saboda haka ni kam Goggo ba zan yarda ba, zan zauna da shi kuma zan haifeshi, in dan Mallam ki ke ma tsoro kar ya gane ni ki bar duka laifin a hannuna, na miki alkawari ba zai taba sanin komai ba in dai zaki bar min cikin nan." Kuka ya kufece min.
      Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce "to shike nan ai tun da kin fi son jin kunya fiye da rufin asirinki, kuma wallahi duk wanda ya zageni gareki zan dora laifin, mallam kuwa sai dai ki toshe kunnuwanki duk abin da zaki ji na fada masa."
     Cikin rawar murya na ce "ehh na yarda Goggo, wallahi ki fada masa  koma miye, ni kam gwara na ji kunyar duniya akan na ji ta lahira."
     Tashi kuwa ta yi ta bar dakin, ni kuwa banda kuka da ya zame min abinci babu abin da na ke yi har dare ya yi.
@wattpad: PrincessAmrah

SHI NE SILAH!Where stories live. Discover now