*SHI NE SILA!*
😪😪😪Na Princess Amrah
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
(2018)59~ Da sauri cike da farin ciki Ummi ta iso inda momy ta ke ta rungume ta, sai kuka su ke wanda suka rasa tantance ko na menene.
Bayan Ummi ta share hawayenta, ta ringa yi wa Kaka bayani cikin yaren larabci, saboda ita bata jin hausa ko kaɗan, kaka kuwa duka da hausar da larabcin tana ji.
Har ta gama bayanin momy bata daina kuka ba, ajiyar zuciya Kaka ta sauke ta ce
"Ba wai iyayenki basu sonki ba ne Ummu Salmah. Bayan kin tafi yin fitsari a cikin Airport ɗin pneumonia ɗin Sarah ta tashi sanadiyyar iskar da ake yi sosai. Babu jimawa yarinya sai numfashi ta ke da ƙyar da ƙyar kamar zata mutu. Hakan yasa Ummanku rikicewa sosai ta shiga tashin hankali mara misaltuwa, ko kaɗan bata kawo a ranta cewa wani abu zai faru da ke ba, tun da ta ga ke da kanki kika tafi fitsarin. Da sauri ta kira Baban su Ummin Juwairiyya ta shaida masa halin da ake ciki, gashi kuma Abban naku har jirginsu ya tashi.
Shiru ta jishi bai zo ba, wanda shi kuma yana tahowa motarshi ta lalace ya tsaya neman mai gyara, ita kuma ta yi gajen haƙuri da kayanta da komai ta bari wai da nufin idan kin dawo daga fitsari ki ɗauko, sai bayan ta tafi ne ta kira baban nasu ta ce idan ya tashi kawai ya je daidai wurin masu gadin wurin, ta bar saƙo da kuma Ummu Salmah sai ya taho da ita, saboda ba zata iya jiranshi ba yarinya bata numfashin kirki.
Ko da ya iso ya samu securities ɗin, kayan kawai suka bashi amma suka ce su basu ga wata yarinya da ta ce ta je fitsari ba, kuma su har wuraren da ake fitsarin babu inda basu zagaya suna bincikata ba.
Nan fa hankalinshi ya tashi, shima ɗin ya sake kiran Umamnki ya sanar da ita halin da ake ciki, take abu ya haɗe mata goma da goma, ga rashinki, ga kuma ciwon ƴar uwarki. Tama rasa abin da zata yi, gashi ta kira lambar Abbanku wayar a kashe, da alama basu isa India ba har a lokacin.
Nan fa aka hau cigiya da sanarwar ɓatarki, yayin da Ummanki har a lokacin tana asibiti, likitoci na kan Sarah saboda bata farfaɗo ba sai oxygen ma aka saka mata.
Iya kiɗima Ummanku ta shiga, nan da nan ta kira Babansu ta ji ko akwai wani labari game da ke? Amma amsar ɗaya ce cewa shiru ne ana dai jiran tsammani.
A ranar da daddare Sarah ta amsa kiran mahaliccinta, gashi kema har an gaji da cigiya an fara cire rai da samunki.
Sosai ta yi kukan rashinku, wanda har suma ta yi sai washe gari aka samu ta farfaɗo, wayarta ta nema domin ta sanar da Abbanku halin da ake ciki.
Koda ta duba ashe ya kirata fin sau goma bata ɗauka ba, da sauri ta latsa kiranshi, ya kashe sannan ya sake kiranta.
Tana ɗauka ta fashe da kuka ba tare da ta furta komai ba.
A kiɗime Abbanku ya ce "Lafiya? Me ya faru kike kuka?"
Cikin kuka sosai ta ce "Shi ke nan na rasasu. Na rasasu su duka biyun!"
Cikin rashin fahimta ya ce "Ki ajiye hankalinki ki min bayani yanda zan gane. Su waye kika rasa?"
Kamar tana jiranshi ta ce "Ummu Salmah da Saratu."
A razane ya ce "Garin ya muka rasasu? Ina suke?"
Nan ta kwashe labarin komai ta faɗa masa tana kuka sosai. Shi kanshi tana gama faɗi ya fashe da kuka kamar ba namiji ba. Ɓatar mutum ba wasa ba, gwara ma wadda ta mutun an san mutuwa ce ta yi, wadda ta ɓacewa kuwa a airport babu wanda ya san inda ta ke.
Washe gari bai ko tsaya ganin likitan ba ya dawo Misrah. Nan fa ya tarar da tashin hankali, ya ƙara tabbatar da cewa lallai babu Ummu Salmah kuma babu Sarah.
Tun daga nan Ummanku ke jinya, bata sake samun lafiya ba saboda cutar hawan jini data kamata, Abbanku kuwa ya mata alƙawari cewa zai yi bakin ƙoƙarinshi dan ganin an gano ki.
Tun daga nan yake fafutukar bincike har kusan shekara biyu amma babu wani labari. A lokacin ne ya samu Ummanku cewa ta fawwala al'amirranta ga Allah. Insha Allahu duk inda kike in dai kina raye komai daran daɗewa zaki dawo gare su.
Tun daga sannan basu sake wahalar bincike game da ke ba, sun barwa Allah komai.
Shi da kanshi ya kan zauna yana tunani, a haka fa suka rasa Mahmoud! Kamar wasa lokaci ɗaya suka rasashi, wanda shi ne auta a ɗakinsu.
Kin ji yanda abun ya faru Ummu Salmah, iyayenki ba wai basu sonki ba ne, kuma har yanzu basu cire tsammanin sake ganawa da ke ba. Tun bayan ɓatarki da rasuwar Saratu kuwa duk wani saɓani da kika san suna samu basu sake ba, sai zaman lafiya kawai ne a tsakaninsu.
Na gode Allah da bai ɗauki rayuwar ko ɗaya daga cikinsu ba har sai da kika bayyana, kuma insha Allahu da kaina zan miyar da ke gare su." Kaka ta yi shiru daga nan ita kanta tana jin wani farin ciki mara misaltiwa, duk da bata haɗa komai da Momy ba amma ta yi zaman arziƙi da iyayenta, saboda momy ɗin ɗiyar wan mijinta ce.
Cikin turanci Ummi ta ci gaba da mata bayani cewa sanda suka rabu kusan tsarakin juna ne ita da momy, kuma suna so junansu sosai, a duk family ɗinsu jininsu ya fi haɗuwa su biyun, hakan yasa suka kasa mance junansu, duk da yake lokacin suna ƴan shekara goma sha biyu ne ba lallai bane su iya riƙe komai a tsawon shekarun nan kusan talatin da uku ko da huɗu.
Sake rungumar juna suka yi, har yanzu kuwa momy bata daina kuka ba, ta tausayawa iyayenta sosai tare da yin tir da abin da ta aikata, na ƙin waiwayar iyayenta duk da tana da damar yin hakan, ta kasance mai jin haushin iyayenta bayan kuma ta tabbatar suna ƙaunarta, fushi da son zuciyarta ya sata aikata babban kuskure. Godiya ta yi ga Allah da yasa iyayen nata basu mutu ba har yanzu. Insha Allahu suna da rabon ganawa.
YOU ARE READING
SHI NE SILAH!
Romanceshi ne silar rugujewar farin cikin rayuwarta. shine silar shigar ta cikin kunci da bakin ciki. shi ne silar rashin gata hadi da galihu a rayuwarta. shin waye silah? ku biyoni a cikin wannan labarin inda zan warware maku zare da abawa.