61

872 52 4
                                    

*SHI NE SILA!*
           😪😪😪

              Na Princess Amrah
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
                           (2018)

_This page is Yours Basma erlele❤. Ina matuƙar jin daɗin yanda kike comments tare da bayyana naki ra'ayin game da *SHI NE SILA!* You mean alot to me. I heart you my dear😘_

61~  Washe gari da safe masu decoration suka zo suka fara aikinsu, saboda yau ne za'a yi wa'azi.
   Misalin ƙarfe goma su Ikram suka fita, sai da ta biya ta ɗauko su Miemie sannan suka wuce central market, soveniers suka kwasa kala kala har da na momy wanda zata raba mother's day da wa'azin yau. Da kuma nasu na kamu da dinner.
   Daga nan suka wuce one heart, inda zasu siyo karikitan bridal shower. Crowns suka siya guda hamsin na ƴan mata, sannan aka siya irin abun nan wanda ake rubuta _bride to be,_ wanda amarya ke ratayawa tun daga kafaɗa ya sauko har bisa cikinta, sai kuma wasu ƴan katika ƙananan masu ɗan tsinke wanda aka rubuta _Miss to Mrs,_ wanda su kuma ƴan mata ake samu wanda zasu riƙe su a hannu, guda goma suka siya wannan ɗin saboda ba kowa ne ke riƙe shi ba. Sai kuma wasu flowers guda huɗu wanda su kuma daga Miemie, Husnah, Smart sai Khaleesat ne zasu riƙe su. Haka dai suka kwashi tarkace abubuwan ban sha'awa irin wanda sai dai mutum ya gani a hoto.
    Kafin azahar har momy ta fara kiranta, ɗauka ta yi ta saka a handsfree sannan ta ajiye bisa cinyarta tana tuƙi ta ce "Hello momy."
   A ɗaya ɓangaren momy ta ce "Ikram wai ya na jiku shiru har yanzu? Lokaci fa na tafiya, kin san ni bana son saɓa lokaci. Ƴarfe huɗu na ce za'a yi kuma hakan nake so a fara. Malama Basma mai wa'azin ma yanzu na kirata ta tabbatar min da ba zata saɓa al-ƙawari ba."
    Murmushi Ikram ta yi ta ce "Gani nan zuwa Momy. Mun kusa gida ma da izinin Allah."
    "To Allah ya yarda." Ta kashe wayar daga nan.

***
    Basu wani jima a hanya ba suka isa gida. A lokacin an gama ƙawata gidan ya masifar yin kyau, kai ka ce yau ne ma ɗaurin auren.
   Ƙarfe biyu dai-dai suka ƙarisa cikin falo, mata ne gasu nan zazzaune, wasu na firarsu ta tsakani da Allah, wasu kuwa gulmammaki ne kawai su ke, saboda dama gidan biki ya gaji wannan.
    A hankali su ke kukkutsawa hannunsu maƙale da juna har suka isa ɗakin Ikram. Dama sun gama yanke hukunci cewa gidan su Miemie kawai zasu koma da zama, saboda nan ɗin ya cika, kuma basu son a ringa kalle ma amarya kwalliya, tun da ba wani shago za'a a yi ba  Husnah ce zata mata.
    Baki ɗaya kayan da Ikram zata buƙata suka ɗauka. Dama ita da su Juwairiyya sun gama fitar da na lefe, irin su inner wears haka da kayan shafa da duk dai wani abun buƙata.
    A ɗakin Khalid ta same ta yau ma. Tana zaune suna lissafin kuɗi ita da wata mata. Ganin haka yasa Ikram ta tsaya har sai da suka gama maganar sannan ta ce "Momy mun dawo."
   Cikin ujila momy ta ce "To sannunku. Sai a hau shiri tun yanzu ai."
   Baki Ikram ta turo ta ce "Momy shiri fa kika ce, tun yanzu? rana fa tsakiya ta ke, ai sai zufa ta lalata kwalliyar idan an yi."
   Murmushi momy ta yi ta ce "Har wata kwalliya zaki yi bayan kuma ranar wa'azi ce?"
    "Momy ana kwalliya ai. Ni yanzu ma gidan su Miemie kawai zamu koma da zama. Sai mu ringa shiryawa daga can tun da mutane sun cika nan ɗin. Kuma zasu ringa kalle min kwalliya."
    "Yo Ikram ita kwalliyar dama ba dan a kalle ta ake yi ba?" Momy ta tambaye ta.
    "Ni dai momy ki bari mu tafi can ɗin kawai. Har ma mun kwaso kayan fa ina ji suna bakin mota su miemie'n, har da Aunt Juwairiyya." Ikram ta faɗa a shagwaɓance.
    "To a tafi. Amma dan Allah ku taho da wuri. Ko da yake zan kira maman Kareema in ce ta yi saurin tunkuɗo ku. Na san itama ai zata zo."
   Da murna Ikram ta ce "Ehh na yarda ki kirata ɗin."
   Kai kawai momy ta gyaɗa tana dariya, ita kuma Ikram ta fice da sauri dan ta san su Miemie har sun isa bakin mota.
     Booth ta bule aka saka karikitanta, sannan suka shige tare da tayar da motar.
   Suna fita suka ci karo da motar Haidar ta kunno kai ƙofar gidan, saurin ɗauke kallonta ta yi daga gare shi haɗe da ci gaba da kallon gabanta.
    "Wayyo Allah Ikkey ga rabin raina. Har na ji sanyi-sanyi wallahi. Inama a ce wannan hidimar bikin tamu ce ni da Yaa Haidar, da na fi kowa sa'ar rayuwa kuwa."
   Kai kawai Ikram ta gyaɗa haɗe da faɗin "Ke dai kika sani."
     Signal Haidar ya masu haɗe da sakawar Ikram wani murmushi wanda shi kaɗai ya san manufar murmushin. Abokinshi Marwan da ke gaban motar ya ce "Abokina gata fa."
    Kallonshi Haidar ya yi ya ce "Kai matsalata da kai son wasa kamar Khalid. Sai kace kai ɗin ba soja ba."
    "To sai me? Dan ina soja kuma sai aka ce kar in saki raina? So kake in zama mai ƙuntatawa rayuwata kamar wani kai? Allah ya kyauta min wallahi." Marwan ya faɗa fuskarsa da fara'a.
     Bai daina kallon Ikram ba har sai da suka wuce suka barshi sannan ya faka motar a ƙofar gida ya ce "Barin shiga in ɗauko. Ba zan daɗe ba insha Allah." Ya fice ya shiga gidan.
   Babu jimawa kuwa sai gashi ya dawo fuskar nan ɗaure kamar wanda akama bushara da mutuwa.
   Yana shiga ya zauna Marwan ya ce "Guy ya dai?" Ya dafa kafaɗarsa.
     Guntun tsaki ya yi ya ce "Sun wani zo sun tara mutane cikin gida kamar kansu farau aure. Ko ɗakin nawa ma ban samu na ahiga ba saboda duk inda ka shiga gidan mutane ne. Ga wani jere da kwalliya da aka yi dan bidi'a kamar ba wa'azi za'a yi ba. Allah ya kyauta, wani abu sai mata." Ya tada motar suka tafi.

SHI NE SILAH!Où les histoires vivent. Découvrez maintenant