42

982 64 5
                                    

*SHI NE SILA!*
           😪😪😪

              Na Princess Amrah
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
                           (2018)

42~  Washe gari da sassafe ta yi shirin makaranta, d'akin momy ta same ta tana Adhkar, ganinta ya sa momy ta aje 40 Rabbana d'in hannunta da murmushi ta ce "Ikram har an shirya?"
    "Ehh momy, har ma na karya sai tafiya." Ikram ta fad'a had'e da duk'awa k'asa ta ce "Ina kwana momy?"
    "Kin tashi lafiya?" Ta tambayi Ikram.
    "Alhamdulillahi momy. Bara na tafi daga nan zan shiga d'akin Yaa Khalid na dubashi da jiki."
     "To shi ke nan Ikram babu damuwa Allah ya tsare. Idan kin dawo akwai maganar da na ke so mu yi da ke." Momy ta fad'a tare da mik'a mata kud'i.
   Karb'a ta yi da godiya ta fice daga d'akin ta nufi na Khalid.
     Da sallama ta shiga ta same shi zaune bakin gado ya rafka tagumi sai zancen zuci ya ke. Ganinta ya sashi sakin murmushin k'arfin hali. "Sannu patient. Da alama dai sau'ki ya samu." Ta fad'a bayan ta k'arisa shigowa d'akin.
    "Ahh alhamdulillahi kam. Na samu sauk'i sosai Ikram." Ya fad'a wanda sam ba hakan ba ne. A zuciyarshi wani irin rad'ad'i ya ke ji wanda ba zai ta'ba iya misaltashi ba, ya fi jin wannan rad'ad'in a duk lokacin da ya kalli Ikram ya tuno da cewa ba shi zai aureta ba, sai dai kuma yana samun sau'ki idan ya tuna cewa ai ba fita zata yi daga zuri'arsu ba.
    "Na gode k'warai da kulawa Ikram. Allah ya bar zumunci." Khalid ya fad'a bayan ya sunkuyar da kanshi k'asa.
    Harara ta maka masa had'e da fad'in "Ni ka ke wa godiya? Ka fa san ba son haka na ke ba ka daina."
    Jinjina mata hannu ya yi ya ce "To na bari ranki ya dad'e. A tafi makaranta kar a makara."
   Murmushi ta masa sannan ta fice ta nufi parking area.  A can ta samu Haidar yana ta faman tada motarsa ta k'i tashi. Ya fito ya d'an bud'e gabanta amma sam bata tashi ba, shi kuma ga sauri yana yi sai kiranshi a ke wai ga patient can unconcious.
    Ko kallonshi Ikram bata yi ba ta shige motar momy data saba hawa ta tayar had'e da fara yin reverse tana kallon bayanta dan kar ta kaiwa wani abu karo.
    Ganin haka yasa Haidar d'an d'aga mata hannu alamar ta tsaya amma ta 'ki tsayawar. "Ikram!" Ya fad'a da d'an k'arfi yanda zata jishi amma sai kunnen uwar shegu ta yi da shi.
    Mai gadinsu ne ya ringa tsayar da ita ganin kamar bata ji na Haidar ba. Da sauri kuwa ta tsaya had'e da sauke glass d'in saitinta tana fad'in "Lafiya Baba?"
    "Aliyu ne ke magana ranki ya dad'e." Ya gwada mata Haidar da ke tsaye sai shan k'amshi ya ke. (Ni ko na ce a banza tun da dai nema ka ke.)
    Kallon inda Haidar 'din ya ke ta yi sannan ta tada motar ta nufi daidai gabanshi. "Magana ce?" Ta tambayeshi cikin halin ko in kula.
     "Motata ce ta lalace, ki tafi dani ki saukeni Office." Ya fad'a ba tare da ya kalleta ba.
    Cikin ranta ta ce 'Shi ke nema amma sai ya saka izgilanci ciki.' Ta yi guntun tsaki had'e da bu'de masa gaban motar. Shiga ya yi kuwa sannan ya rufe suka kama hanyar asibitin.
      Ko da suka isa a bakin Office d'inshi ta paka motar, a nan ta hangi mutumin da aka kawo unconcious d'in mimmi'ke kamar matacce. Cike da tausayi ta ke salati, Haidar na fita itama d'in ta bi bayanshi suka nufi inda mutumin ya ke, wai a nufinta koda Haidar ya nemi ya wulak'anta mara lafiyar ita sai ta d'aukeshi ta nufi wata asibitin da shi.
     "Ku shigo dashi ciki." Haidar ya fad'a ga mutanen da suka kawo mutumin. Ciki kuwa suka shiga da shi, bud'e 'kofar ya yi ya shiga, suma d'in suka mara masa baya, Ikram ma ba'a barta a baya ba sai da ta shiga har ciki cike da tausayin marar lafiyan.
     "Me ya ke damunshi ne?" Ya tambayi dattijon mutumin da ke rungume da wancan mara lafiyar.
    "Wallahi ta'kamaimai bamu san abin da ya ke damunshi ba. Abin da muka sani dai shi d'in wahalalle ne a baya kafin ya samu sauyi a 'yan lokutan nan, kullum cikin aikin k'arfi ya ke daa, to a tunaninmu ko abin da ke tambayarsa ke nan, k'ila wahalar da ya sha a baya ce kawai ke damunsa."
    Jinjina kai Haidar ya yi sannan ya d'auko abin auna numfashi ya danna saitin zuciyarsa.
    "Numfashinsa daidai ya ke tafiya." Ya fad'a a hankali.
    Jotter'n asibitin ya jawo ya d'an yi rubutu sannan ya mi'kawa dattijon ya ce "A siyo wannan allurar yanzu, ita zan masa ko zai farfad'o sannan a yi duk abin da ya dace."
    Da sauri Ikram ta kar'bi takardar ta cewa mutumin "Zo mu je a siyo." Saboda ganinsu da alama ma babu ko sisi a tattare dasu.
     Godiya ya yi sannan ya bi bayan Ikram suka tafi pharmacy.
    Suna fita Haidar ya gyad'a kai, a cikin zuciyarsa ya ce 'Ikram sarkin tausayi.' Ya d'an yi murmushi had'e da sake tambayar d'aya mutumin cewa "Wane irin aikin k'arfi ne ya ke?"
   "Wane irin aiki ne ma mutumin nan baya yi? Shi ne sarar icce, shi ne dako, shi ne wanki da guga. Kai duk dai wata hanyar da mutum zai samu na sakawa a aljihunshi bawan Allah'n nan yana yi, cikin lokaci guda kuma Allah ya taimake shi ya samu sauyi. Amma dai na san duk waccan wahalar ce tattare dashi"
    Kad'a kai Haidar ya yi da tausayi ya ce "Neman halak ke nan."
    "Wallahi kuwa. Gashi fa shi ko iyali bashi da su, shi ka'dai ke rayuwarsa." Mutumin ya fad'a cikin yanayin tausayi.
    Suna cikin maganar ne su Ikram suka dawo rik'e da allurar. Mik'awa Haidar ta yi sannan ta d'an ja da baya.
    A bisa wani gado ya umurta a d'orashi wanda aka zagaye da makimancin labule. Allurar ya masa sannan ya fito ya ce "Ina ganin a barshi ya d'an huta kafin nan ya farka ko?"
      Da sauri mutumin ya ce "To yalla'bai. Mun gode k'warai."
    "Zaku iya fita waje sai ku jira. Duk yanda ake ciki zan sanar maku."
    Ikram ta fara fita cike da tausayin mutumin, ita dai haka ta ke dama, akwaita da tausayi sosai, ko bata ta'ba ganin mutum ba ta ganshi cikin wani hali sai ya bata tausayi.
    Bayan sun fita ta cewa bawan Allah'n "Dan Allah kana da waya kuwa?"
    Wata tsohuwar tecno ya zaro daga aljihunshi ya ce "Ehh ina da wannan, amma batirinta gocewa ya ke sai ta mutu da kanta."
    Karb'ar wayar ta yi ta bud'e, batirin ne bai cika wayar ba saisa ya ke gocewa. Takarda ta nema ta cika daidai inda bai kai di'n ba ta rufe ta mik'a masa. "Gashi nan ina jin yanzu insha Allahu ta gyaru."
    Karb'a ya yi ya ce "To Allah yasa." Ya yi murmushi.
    "Lambata zan baka dan Allah sai ka nemeni duk halin da ake ciki. Ko da magani aka rubuta sai ka kirani na siyo."
     "Allah ya miki albarka 'yar nan. Gaskiya ke yarinyar kirki ce, iyayenki sun yi sa'ar haihuwa da Allah ya basu ke. Allah ya baki miji na gari."
    Kar'ba ta sakeyi ta saka masa lambar ta yi dialing, fad'in ake babu ko sisi a wayar hakan yasa ta kashe sannan ta masa transfer'n d'ari biyar ta sake kira. Bayan ya shiga ta kashe ta ce "Idan ka tashi ga lambar nan na yi saving da Ikram. Ka yi k'ok'ari ka kirani please, nima 'din zan ringa kira a kai a kai, makaranta zan tafi ne."
    "To madalla. Ki tafi kar ki makara mun gode." Ta nufi motarta.
  
***
    Kai tsaye makaranta Ikram ta nufa, ko da ta je Aunt Juwairiyya ce cikin class d'in nasu, bayan ta gaisheta cikin yaren turanci ta amsa tare da bata izinin zama, zaman kuwa ta yi kusa da k'awarta Husnah.
     Baki d'aya ta miyar da hankalinta kan abin da balarabiyar malamar tasu ta ke koya masu. Kala kalar yafin mayafi ne a ke koyawa kuma sosai su ke fahimta.
    Bayan an gama duka suka tashi ita da Husnah suka nufi inda Aunt Juwairiyya.  Sake gaishe ta Ikram ta yi cike da fara'a ta mata bayanin yanda su ke fahimtar darasinta. Da fara'a itama balarabiyar ta ce Ikram na burge ta sosai, idan babu damuwa zasu ringa gaisawa, wai tana mata kama da wata 'yar uwarta. Musayar lambar waya suka yi sannan suka tafi ita da Husna bakin mota, har gida ta kai Husnah sannan ta wuce asibiti domin duba lafiyar mutumun d'azu.
     Ko da ta je kai tsaye ta isa Office d'in, hanata shiga Musa masinja ya yi hakan yasa ta ce ya je ya fad'a masa cewa Ikram ce, babu musu kuwa ya shiga ya fad'awa Haidar ga Ikram nan, umurtarshi ya yi cewa ta shigo.
      Shigowar kuwa ta yi ko glasses d'in fuskarta bata samu damar cirewa ba. "Sannu yaya." Kawai ta fad'a da k'yar.
    "Yauwa Ikram, ya School d'in?" Haidar ya fad'a yana 'yan rubuce rubucenshi.
     Kasa amsawa ta yi saboda mamakin Haidar, lallai da gaske dai ya fara yin sanyi. "Alhamdulillahi. Ya mai jikin nan kuwa?"
    Bai d'ago kanshi ba ya ce "Ba laifi. Yana male ward."
     Mik'ewa ta yi bata kuma fad'in komai ba, daidai k'ofa ta jiyo muryar Haidar ya ce "Kun yi magana da momy?"
   Juyowa ta yi ta d'an saci kallonshi ta ce "Magana? Wace kake nufi?"
    "Barshi kawai jeki." Ya fad'a cikin halin ko in kula.
    Bata ce dashi komai ba ta fice ta nufi motarta. Male ward ta nema aka kaita, a baki baki ta ga wancan mutumin tsaye da wani wanda da alama babban mutum ne amma shi ya juya baya.
        A hankali ta taka har ta isa inda su ke, mamaki ya kamata ganin M. Lawal ne tsaye da mutumin. Kawar da mamakin ta yi ta hanyar gaishe da wancan mutumin ta d'an du'kar da kanta.
     Washe baki M. Lawal ya yi ya ce "Ahh Ikram ce?"
    "Ehh" kawai ta fad'a a tak'aice.
    "Kina da mara lafiya ne?" Ya tambayeta da wani shu'umin murmushi.
     "Na zo dubiya ne. Baba ya mai jikin?" Ta tambayi d'ayan mutumin.
      "Mai jiki alhamdulillah, ai dama na fad'a miki ya farfad'o tun d'azu da kika kira."
     "Ehh haka ne.  Ko zaka rakani na dubashi? Dan ban san gadon nashi ba." Ta fad'a.
     "Ikram dama kuwa ina da magana da ke. Ko zaki zo mu d'an tattauna?" M. Lawal ya fad'a.
      Banza ta yi kamar bata jishi ba. Sake maimaitawa ya yi sannan ta ce "Ka yi ha'kuri dan Allah ka k'yaleni. Ni ba abin da ya kawoni ke nan ba."
    "Haba mana Ikram. Wai mesa kike son wulak'anta mutumin da ya ke sonki tsakani da Allah?" Ya matso inda ta ke. "Ina k'aunarki Ikram, dan Allah ki bani dama na dama." Ya sake yin wani murmushin.
     Tsaki kawai ta yi ta shige cikin d'akin, da sauri M. Lawal ya bi bayanta har suka isa ciki yana fad'in "Mallam Maharazu yi gaba ka gwada mana hanyar gadon." Ya ce da mutumin nan na d'azu.
      Can daga k'arshen d'akin ne gadon mara lafiyar, ganin Maharazu ya tsaya nan yasa Ikram da M. Lawal ma suka tsaya sai shan k'amshi ta ke cike da jin haushinshi.
      Kwance ya ke ya kalli d'aya gefen ya yi shiru, jin muryar Maharazu ya yi ya ce "Mallam Halle idan idonka biyu ga Alhaji M. Lawal ya zo dubaka, ga kuma Ikram dana baka labarinta wadda ta tausaya maka d'azu."
      Da sauri mara lafiyan da aka kira da Halle ya juyo, kallon Ikram ya yi tare da tashi zaune, kasa d'auke idonshi ya yi daga gareta sai wani irin kallo ya ke binta dashi. Cikin lokaci k'ank'ani Halle ya samu *SAUYIN YANAYI,* baki d'aya ya ma kasa had'iyar yawu, ya kasa tantance yanayin da ya ke ji game da ita.
     Saukar da idonta ta yi cikin ladabi ta gaishe shi ya amsa. "Na gode k'warai Allah ya miki albarka." Halle ya cema Ikram.
     "Yallab'ai sannu fa." Ya ce da M. Lawal bayan ya d'auke kallonshi daga Ikram.
     "Halle ya k'arfin jiki? Na jiraka tun jiya ai shiru, shi ne yau na bi sahunka har gida 'yan gidan suka shaida min wai baka da lafiya har ma an kawoka asibiti. Sannu, na yi kewarka sosai."
     Da sauri Ikram ta mik'e ta ce "Zan tafi Baba, Allah ya k'ara lafiya. Insha Allahu zamu zo ni da Momy'na mu dubaka anjima."
     Murmushi ya yi ya ce "To Allah ya kaimu. Na gode sosai."
      Dubu d'aya ta zaro daga jikarta ta mi'kawa Maharazu. "Gashi a sai masa lemu da kankana, ban samu na siyo masa ba a hanya saboda ina sauri."
    Dakatar da ita M. Lawal ya yi ya ce "Ki barshi zan bayar a  madadinki."
    D'aure fuska ta yi ta ce "Naka daban nawa daban, sannan kuma ba kai ka sakani ba ni na yi niyya." Ta d'ora a bakin gadon Halle tare da barin wurin.
      Ko da ta tafi zuciyarta sai tafarfasa ta ke "Wai mesa mazan yanzu basu da gaskiya? Mesa basu da adalci?" Ta fad'a a bayyane tare da tada motarta. Kafin ta bar asibitin aka kirata da wata number, kamar kar ta d'auka sai kuma ta dake ta d'auka. "Hello." Ta furta a hankali.
     "Ikram na san baki tafi ba ki dawo ki sameni Office." Ya tsinke wayar.
      Tsaki ta yi kamar kar ta koma d'in sai kuma ta daure dai ta juya akalar motar. Bata ma da lambarsa sai yanzu da ya kirata, ta yi mamakin ma yanda shi d'in ya ke da tata. Office d'inshi ta nufa, Musa bai hanata ba saboda Haidar ya ce idan ta zo kawai ya barta ta shigo.  Zuciyarta matse ta ke da jin dalilin da yasa ya kirata.
      Bayan ta shiga ta zauna yana aiki, jin zuwanta yasa ya d'ago kanshi fuskarshi babu alamar wasa ya ce "Ikram ki fita harkar mara lafiyar nan na 'dazu."
     Da mamaki ta ce "A kan me?"
     "Saboda ba mutumin kirki ba ne." Ya bata amsa.
     "To ai ni wannan bai shafeni ba. Mutum ne mai bu'katar taimako kuma na ke taimakonsa. Idan kai halinka wulak'anci ne to ni ba haka na ke ba, kuma ba halina ba ne." Ta fad'a cike da tsiwa.
     Gyad'a kai ya yi ya ce "Ni dai na fad'a miki ki fita harkarsa. Rashin lafiyarsa kuwa duk da wahala ce amma akwai wani 'boyayye da ni kad'ai na sani ko shi 'din ban fad'awa ba sai na ziyarce shi gobe zan sanar masa."
     Ajiyar zuciya ta sauke ta ce "Wane irin ciwo ne?"
     "Bayyanannen ciwon dai shi ne na wahala, wanda aikin k'arfi ya jawo haka har ya zube. B'oyayyen kuwa na gano cewa d'an homo ne, wanda har hakan ya fara illatashi, da alama dai ya dad'e yana yi..."
     Tun bai gama fad'i ba Ikram ta mik'e tsaye cike da mamaki tana kallon Haidar. "Kana nufin wannan gentleman d'in d'an homo ne?"
     Bai fad'i komai ba jinjina kai ya yi alamar ehh. Cike da mamaki ta fita daga Office d'in, zuciyarta sai rad'ad'i ta ke mata, jin mutumin ta ke tamkar nata ko kuma wani jininta, har ga Allah ta ji haushin kasancewarshi ba mutumin kirki ba. Ko da ya ke ai ba abin mamaki ba ne tun da har M. Lawal ya ziyarce shi. Da wannan tunanin har ta isa gida zuciyarta bata daina tunzurata a kan ta ci gaba da taimakonshi ba, ko ba komai wata 'kila taimakon da zata masa zai iya zama *sila* ko kuma ya karkatar da shi a kan hanya mai kyau.

_Masu karatu ina fatan dai baku manta da Halle wanda ya ma Umma Rumana ciki har ta haifi Ikram ba._

*team Ikramhaidar*
*team Ikramkhalid*

SHI NE SILAH!Where stories live. Discover now