*SHI NE SILA!*
😪😪😪Na Princess Amrah
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
(2018)17~ Ikram ce zaune d'akinta ta kalli mirror ta k'urawa kanta ido, a ranta ta ke fad'in "Oh ni Ikram, wai yau ni ce a cikin wannan gidan na zo da niyyar zama dindindin. Allah sarki Ummana, Allah ya ji k'anki da rahama, dama kafin ki rasu kin fad'a min kar na damu da inda zan zauna, domin Allah yana tare da ni, ga zahiri kuma na gani, lokaci guda Allah ya had'ani da mutanen kirki wanda basa k'yamar talaka, basu sanni ba basu san asalina ba, basu damu ba da ko gaskiya na fad'a masu labarina ko kuma k'arya na masu. Allah sarki Momy, Allah ya saka miki da alkhairi." Hawaye ya fito mata.
Jin k'arar tafiya alamar ana zuwa d'akinta yasa ta saurin goge hawayen tare da yin pretending na shafa powder da lip gloss.
Naana ce ta shigo ta ce "Ikram Hajiya na kiranki, ta ce wai ki shirya zaku tafi kasuwa da Khalid."
"To Baaba Naana gani nan zuwa, a shirye na ke kaya kawai zan saka." Ta fad'a tare da mik'ewa da nufin fiddo kaya.
Jallabiya ce bak'a ta fitar had'e da d'an kwalinta, bayan ta saka rigar ta d'an yafa d'an kwalin ba wai da nufin gayu ba, amma ta yi masifar kyau, kallo d'aya zaka mata ka san jinin masu kud'i ce, dan ko sanda Ikram tana kauye mai son gayu ce, Ummanta kuma tana kokari dan ganin ta sai mata duk wasu kayan gayu wanda basu fi karfinta ba, haka Mallam ma, in dai zai zo Kano to zai siya mata abubuwan kwalliya. Kallon kanta ta yi a madubi ta ce "Kai, kamar ba ni ba, wai Ikram ce da gaske? Ya Salaam, haka na ke da kyau dama?" Ita kad'ai ke ta surutunta.
Fita ta yi bayan ta d'auko wasu flat shoes daga kan shoe rack.
"Momy gani nan zuwa." Ta fad'a tana 'kok'arin saukowa daga bene saboda k'wala mata kira da Momy ta sake yi.
Bayan ta sauko k'asa ta ce "Je ki d'akin Khalid ki fad'a masa kin shirya, tun d'azu fa na fad'a masa zaku fita amma ya k'i zuwa."
"Ok Momy, na san baya wuce wannan shegen charting d'in nasa na ibada. Zan karb'e wayar ne da na je." Ta hanzarta domin isa b'angarensa.
Video call ta samu yana yi da yayanshi Haidar, bata ko tsaya kallon abin da ya ke yi ba ta fizge wayar tare da jefar da ita bisa kujera. "Momy ta saka abu amma kana nan kana shirme."
"Ke waya da Yayan ne shirme? Allah yarinyar nan kin masifar rainani, wuyanki ya isa yanka ko?"
"Ehh d'in naje na fizge, ko ma da wa ka ke waya ai kiran Momy ya fishi." Ta fad'a had'e da murgud'a baki. "Kuma ka taso mu tafi yanzu ba zan fita ba sai tare da kai."
"Ai kin dai bani wuri na canza kaya ko?" Ya tambayeta yana binta da kallon zaki gane kuranki.
"Zan fita amma wallahi ka yi sauri dan bana son jira." Ta baza da gudu dan ta san sai ya biyota sanadin wannan maganar da ta yi.
Wayarshi ya koma ya d'auka, ashe har yanzu Haidar bai kashe wayar ba yana sauraren komai, "Laah, Yaya ashe baka kashe ba, wannan yarinyar ce ke neman kawo min raini."
"Ina jinta ai, to ka fad'a mata idan tana cin k'asa ta kiyayi ta shuri, ni babu ruwana da ita, kaima d'in kuma kai ka ja, kuma zata mugun rainaka tun da abin da ka d'aukarwa kanka ke nan."
"Haba Yaya ya da fad'in wannan maganar? Allah kuwa Ikram yarinya ce mai hankali bata da matsala, na d'auketa tamkar Feenah da ta rasu duk da ya ke Feenah jinina ce Ikram kuma ba haka ba."
"Da Allah ka tubarwa Allah, yarinyar da baka san asalinta ba kake dangantata da 'yar uwarka uwa d'aya uba d'aya?"
"Yaya mun san asalinta mana, ai ta mana bayanin komai." Ya fad'a rai b'ace.
"Kun sani ko ta fad'a maku karya ne? Ka san ko ta 'kirk'ira ne kawai? Allah wannan halin naku kai da Momy sai kun canzashi, idan ba haka ba kuma wata rana zaku d'auko ajalinku."
"Yaya abeg a bar maganan nan, bari na shirya na tafi zamu fita da Ikram Momy ta aikemu, I'll call You idan mun dawo." Ya kashe kiran cike da jin haushin d'an uwansa.
Cikin hanzari ya shirya cikin k'ananan kaya ya fita, "Yanzu na ke k'ok'arin binka ai, Allah ya taimakeka da ka fito."
"Da me zaki yi yarinya?" Ya fad'a bayan ya d'auki makullin mota.
"A dai bar kaza cikin gashinta, kai dai ka godewa Allah tun da ka fito."
"Ungu wannan Khalid." Momy ta mik'awa Khalid ATM card. "Ku je duk inda ya dace, ta zab'i kaya ready made da kuma atamfofi da laces da komai, idan kun siyo sai ka kaita wurin telan Feenah, a biya a mata koma nawa ne." Ta juya ga Ikram ta ce "Ki zab'i duk abin da kike so Ikram, kar ki ji komai, duk tsadarsu ki d'auka, akwai wadatattun kud'i a ATM d'in, nima dan na jima ban je Dubai ba ne, ban yi saari ba."
Murmushi Ikram ta yi ta ce "Nagode k'warai Momy Allah ya saka da alkhairi, sai mun dawo." Suka fita.
Karaamah shoping mall suka fara dosa, wani babban shago ne wanda ya ke k'unshe da abubuwa da dama irin su atamfofi, laces, shadda, english wears, inners da sauransu. Ba a kayan mata kawai suka tsaya ba, suna da kayakin maza da takalma different designs, b'angaren jewelries ma dai akwaisu kala kala, abin dai ba'a cewa komai.
Tun da suka shiga Ikram ke rarraba ido, tama rasa ta inda zata fara, ganin Khalid ya nufi b'angaren k'ananan kaya yasa ita ma ta nufi b'angaren tana d'an duddubawa. Bata d'auki komai ba sai kalle kalle kawai da ta ke yi, ko da Khalid ya fahimci haka ya ce "Malama sai ruwan idon tsiya ta ma rasa abin da zata zab'a."
Jin dad'in maganarsa ta yi ta masa murmushi ta ce "Ehh na ji, ai sai ka zab'ar min mu ga taka iyawar."
Aikuwa kamar yana jira ya hau bibbincika kaya yana zab'o mata masu kyawun gaske kamar shi ne macen ma. K'ananan kaya kawai wanda ya zab'ar mata sun kai kala goma sha biyar, tun daga dogayen riguna, riga da skirt da kuma top gauns. Daga nan kuma suka koma b'angaren atamfofi, nan ma dai zab'ar mata ya yi masu kyau da laces da kuma shadda, a nan b'angaren kawai sai da ya zab'ar mata kala ashirin da biyar. Gyaluluwa ma haka ya ringa jidar mata har saida ta tsayar da shi. "Mallam ka bari ya isheni haka, sai kwasar kaya ka ke ba zaka tausayawa mai biyan ba?"
"Malama ki min shiru ai ita ce ta ce a yi hakan, idan ma bamu yi ba zata iya yi mana fad'a."
"Amma dai Yaya Khalid ido ba mugu ba ai ya san kima, ka bari haka."
"To na ji na bari haka, sai ki koma wancan b'angaren kuma ki yi zab'en da kanki." Ya fad'a yana mata dariya.
Ko da ta kalli b'angaren inners ne, kunya ta d'an ji kad'an sannan kuma ta basar ta ce "baka da dama wallahi." Ta nufi sashen.
Ta zab'a komai kala biyar sannan ta kai inda sauran kayan su ke. Ko da Khalid ya ga ta gama ATM ya mik'awa mai wurin, da POS ya yi amfani ya cire duka kud'in sannan aka saka a leda, mai d'aukar kaya ya d'aukar masu har bakin mota.
Daga nan kai tsaye wurin telan Feenah suka nufa, sun sameshi da bak'i hakan yasa suka zauna har saida ya sallami wancan mutanen.
"Barka da zuwa Khalid babban yaro." Telan ya fad'a tare da baiwa Khalid hannu suka gaisa.
"Tak'adarin bisa, wato har da wani kilbibi a dole ka ganni da budurwa ko? To aradu ba zan baka ba sai ka biya na rashawa."
Kai na gyad'a, a raina na ce 'wannan mutum, duk inda ya je sai an san dashi.'
"Khalid baka da dama, hali dai yana nan."
"Mallam Audu baka da dama, surutu dai yana nan." Ya fad'a cikin irin maganar telan.
"Bar ni a Audun na yarda, d'an rainin hankali. Ya gida ya su Momy?"
"Tana gida, wai a gaisheka, k'anwata na kawo da d'inkuna, amma dan Allah kar ka mata masu kyau, ka mata wanda ka san zata iya yin kuka ma idan ta gani." Ya k'yalkyale da dariya bayan ya gama maganar.
"Wallahi Yaya Khalid mugu kake, shi ai ba irinka bane." Ikram ta fad'a.
"Aikuwa dai fad'a masa k'anwata, kar ki damu, d'inkuna zan miki masu d'aukar hankali, wanda kowa sai yayi sha'awarsu, ki k'yale wannan garan yayan naki, dama ya saba yi wa Feenah haka." Ya mata murmushi.
"Wato dai na fahimceku, daga had'uwa har kun fara soyayya shine kuka had'e min kai ko? Zan rama nima."
"Idan muka biyeka ai ba zamu yi abin da ya kawomu ba, ga d'inkunan." Ta mik'a masa manyan ledoji guda uku. Dama akwai wata mace wadda suka aje musamman saboda auna mata d'inki, ita ya kira ta auna Ikram sannan ya tambayeta irin d'inkunan da ta ke so, kasantuwar ita ba wani sanin d'inkunan zamani ta yi ba yasa ta bar masa zab'i "Ni dai na bar maka wuk'a da nama, ayi min masu kyau, kuma Momy ta ce kar a yi wanda zasu kame jiki sosai."
"Ok to insha Allahu za'a yi." Ya fad'a tare da fara miyar da kayakin a cikin ledojinsu.
"Nawa ne kud'in duka?" Khalid ya tambayeshi.
A bada yanda na ke yi wa Feenah kawai, sai a cire kud'in kala uku matsayin discount."
"To madalla, amma kuma babu cash a hannuna sai ATM momy ta bayar, bari na je gobe zan kawo maka da yardar Allah."
"To ba damuwa ai ana tare, d'inkunan kuma idan na gama zan kiraka ka zo ka karb'a, ko kuma ma na zo da kaina na kawo."
Godiya Ikram ta masa sannan suka fita suka nufi motarsu.
Da murna suka isa gida, tana shiga ta samu Momy zaune tana kallon shirin gari ya waye na arewa 24, ado da kwalliya ake yi hakan yasa Ikram na shiga Momy ta ce mata "Yauwa gwara da kika dawo kuwa, ado da kwalliya ake yi ina son ki ringa bin shirin, zaki k'aru sosai."
Murmushi Ikram ta yi ta ce "Zan kalla kuwa Momy." Ta miyar da baki d'aya hankalinta a tv.
Fira aka yi da wata mai make up, ta yi bayani sosai sannan kuma a k'arshe ta fad'i cewa tana da shaguna a Kano, Abuja da kuma Katsina. A daidai nan kuma aka kammala firar, sosai Ikram ta ji dad'i, sai dai kuma duk a bayanan sunan abin kwalliya ko d'aya bata iya rik'ewa ba sai foundation, tunda dama ba saninsu ta yi ba.
"Aikuwa insha Allahu zan kai 'yata a koya mata, amma dai kafin nan a sakaki School ki fara zuwa sannan ki shiga, ko a weekends ne sai ki ringa zuwa, Ikram d'ita ma ta zama babbar mai make up." Momy ta mata murmushi.
Dad'i ta ji sosai, bata san sanda ta rungume Momy ba kaman yanda ta saba yi wa Ummanta. "Nagode k'warai Momyna, Allah ya saka miki da alkhairi ya bar zumunci."
"Ke wallahi kar ki koyi wannan abun mai miyar da mata masu fuskokin aljannu." Khalid ya fad'a a daidai shigowarsa.
"To shugaban masu shisshigi, yaushe ka san fuskar aljannu?"
"Allah ni dai na fad'a miki, abin da ya ke canzawa mata baki d'aya fasalin fuskokinsu su koma kamar wasu zararru." Ya fashe da dariya.
"Ehh na ji dai, a hakan kuma za'a kalleni idan na yi kuma har na burge mutane."
"Wa zaki burge, ba dai ni ba ko?" Ya tambayeta har yanzu bai daina dariya ba.
"Oho maka, ni bari na yi abin da ke gabana, na tsaya biye maka." Ta tashi da ledar ready made dresses d'inta ta haye sama da su cike da farin ciki.
Wani irin kuka ta fasa bayan ta zauna a bakin gado, "Ya Allah ka sakawa wannan baiwar Allah da alkhairi ka biya mata dukkanin buk'atunta, Allah ka kareta daga sharrin masu sharri. Na ji dad'in kasancewa tare da ke Momy, ina ji a jikina mutuwar Ummana ita ce k'arshen shiga damuwata." Ta share hawayenta. Ni kuwa Amrah na ce 'To Allah dai ya sa haka.'
Toilet ta shiga ta yi wanka sannan ta d'auro alwalar sallar magrib dan an kusa fara kira. Zuciyarta sayau ta ke jinta a halin yanzu, d'ari bisa d'ari hankalinta ya kwanta da Momy.**
Ku yi hak'uri rashin jina kwana biyu, banda lafiya ne yanzu ma da k'yar na samu na maku. Nagode k'warai wanda suka kirani domin jin ko lafiya nake, da ma wanda basu samu damar kirana ba duka ina godiya. Allah ya bar zumunci ya bar so da k'auna.
@wattpad: PrincessAmrah
![](https://img.wattpad.com/cover/145187938-288-k711487.jpg)
YOU ARE READING
SHI NE SILAH!
Romanceshi ne silar rugujewar farin cikin rayuwarta. shine silar shigar ta cikin kunci da bakin ciki. shi ne silar rashin gata hadi da galihu a rayuwarta. shin waye silah? ku biyoni a cikin wannan labarin inda zan warware maku zare da abawa.