63

889 50 0
                                    

*SHI NE SILA!*
           😪😪😪

              Na Princess Amrah
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
                           (2018)

_Bai zama dole a ce sai Miemie ta san wanda Ikram zata aura ba. Saboda idan muka yi la'akari da yanda bikin ya zo masu zuwan kwatsam, Duka cikin wata biyu aka yi komai da komai. Sannan kuma Miemie na ta son sanin wanda ƙawar tata zata aura amma ita Ikram ɗin tana ɓoye mata da dabaru kala-kala. Ke nan dai babu dole ga sanin, inda ace gidansu ɗaya ko kuma maƙwafta ne, shi ne za'a ce ya zama dole sai ta sani, amma fa ƙawarta ce kawai, kuma ba abun mamaki bane dan ƙawa bata san wanda ƙawarta zata aura ba har sai cikn hidimar biki, kuma yanzu ne ake kan yin hidimomin. Ina fatan masu karatu sun fahimce ni, sannan kuma zasu min uzuri. Da sannu za'a zo wurin in da rai da lafiya. Na gode._


63~  Yana shiga gidan ya buɗe ƙofa da makullin da ke jikin na motarsa. Ganin takalma ya yi birjik na ƴan mata daga bakin ƙofar shiga.
   Murmushi ya saki haɗe da ɗan lasar leɓonshi ya ce "Ke nan tun da suka gama abun basu tafi ba?" Ya sake sakin wani murmushin.
     Ƙarisawa ciki ya yi ciki a hankali ya ke taku har ya isa bakin ɗakin Khairat inda ya ke sa ran nan ƴan matan su ke.
    Tura ƙofar ya yi a hankali amma sai ya jita a rufe, ƙara dannawa ya yi ko zata buɗu amma still bata buɗun ba, da alama dai an saka sakata ne ta ciki.
   Guntun tsaki ya yi, take kuma murna ta koma ciki.
   Ɗaya ɗakin wanda shi ne na Kareema ya fara ƙoƙarin buɗewa dan ya tabbatar da ko cikin wane ɗaki su Ikram su ke. Sai dai kuma yana buɗewa ya ga Khairat da Miemie sai Juwairiyya da Munay ƙanwar Smart.
    Tsaki ya yi cikin rashin nasara ya wuce side ɗinshi sai faman shan ƙamshi ya ke.
   Yana shiga parlor ya ga Kareema  Zaune tana rubutu. Ƙara tsuke fuska ya yi bai ko tanka mata ba zai wuce uwar ɗaka.
    Murmushi ta yi ta ce "Me ya biyo da kai wannan hanyar bayan kuma ga wadda ta fi sauƙin shigowa daga parking space?"
    Tsaki ya yi bai faɗi komai ba bai kuma kalle ta ba.
    "Wai, ashe ba wannan ya dace in yi ba. Sannu da zuwa Oga, yau ka dawo da wuri fa, bari mu ga ƙarfe nawa?" Ta duba agogon bango. Wani murmushin ta saki ta ce "Ƙarfe biyu da kwata. Lallai kam ka dawo da wuri. Duk abokanan kasuwancin suka zo da wuri ne?"
     "Ke bana son shirme fa. Ki kawo min ruwan zafi da lipton yanzu." Ya shige cikin ɗakinshi .
   Tattara takardunta ta yi wuri ɗaya sannan ta shiga kitchen ta ɗebo masa ruwan zafi da lipton, sai sugar a wata roba.
    Bayan ta kai masa ta koma ɗaya bedroom ɗin nashi ta kwanta tare da kashe wutar ɗakin.

***
    A ɓangaren Haidar kuwa tun sanda suka gama waya da Ikram ya ke neman lambar Khalid amma ta ƙi shiga, duk layukanshi sai da ya nema bai samu ba hakan yasa ya ce wa Marwan "Ni fa na rasa abin da yake faruwa da Khalid. Tun sanda ya tafi Qatar sau biyu kawai muka yi waya. Daga ranar da ya isa, sai kuma sanda ya turo min text in tayashi da addua bashi da lafiya. Ita kanta momy'n basa waya, ina jin bai fi sau biyun ba suka gaisa."
   Marwan ya ce "Kai haba babu komai insha Allahu. Wata ƙila karatu ne ya masa yawa. Ka san masters yana buƙatar research sosai."
   Gyaɗa kai kawai Haidar ya yi ya ce "To Allah yasa hakan." Daga nan suka kwanta.

***
   Washe gari da asubah su Miemie suka tashi sallah, basu tashi Ikram ba saboda roƙonsun da ta yi, kuma suna tausayinta sun san ba zata sake samun baccin kirki ba daga yau har sai bayan bikin.
    Sai ƙarfe takwas Ikram ta tashi, a lokacin ƙawayen nata duk suna falo sai Juwairiyya da ba son hayaniya ta ke sosai ba kawai kwance wayarta na jikin chaji tana latsarta.
  Bayan ta miƙe zaune tama Juwairiyya murmushi ta ce "Weldone Aunt. (Sannu Anti.)" Ta sakar mata murmushi.
    Murmushin itama Juwairiyya ta miyar mata da shi tare da miƙa mata hannu suka gaisa.
    Toilet ta shiga ta wanke bakinta da toothpaste kawai tun da basu zo da brush ba dan basu yi tunanin nan ɗin zasu kwana ba. Har da fuskarta ta wanke da ƙafa ta canja pad sannan ta fito tana gpge jiƙar hannunta a kayanta.
    Bakin mirror ta isa ta ɗan shafa mai sama-sama sannan ta shafa powder da ɗan lip gloss. Kayanta na atamfa ta miyar sannan ta fesa turare ta fita, kai ka ce wanka ta yi.
    Tana fita falo M. Lawal na fitowa. Kallon juna suka yi a lokaci guda Ikram ta saddar da kanta ƙasa haɗe da ɗaure fuska.
    Shi kuwa ya saki fuska yana watse haƙora ya ƙarisa shigowa ɗakin.
    Gaishe dashi ƴan matan suka yi, da gudu Khairat ta je ta rungume shi tana dariya.
    "Ummul-khair ba'a je school ba yau?" Ya tambayi Khairat yana ɗan satar kallon Ikram data zauna bisa kujera.
    "Muna hutune Dady." Khairat ta faɗa.
    Maimakon ya bar ɗakin tun da ya ga cike ya ke, amma sai ma neman wurin zama ya yi sai famar wangale baki ya ke.
   Kallon-kallo suka ringa bin junansu da shi. Cike da takaici miemie ta miƙe ta nufi side ɗinshi inda Kareema ta kwana.
   Baki tunzure Miemie ta isa wurin Kareema, ta same ta tana gyaran gado.
   Tun daga nesa ta ke faɗin "Yaya Kareema..."
    "Na'am." Kareema ta amsa.
    "Ni dai ki fito kima mijin can naki magana. Ya ga ɗaki cike da mata amma ya je ya mana zaune, ya ja kowa ya yi shiru saboda nauyinshi da ake ji. Idan kuwa ba zai tashi ba gaskiya ba zamu wani jira kalaci ba gida zamu wuce."
     Cike da takaici Kareema ta ce "Wannan mutumi. Allah ya kyauta. Yo ke baki sani ba ai dan ya ga ƴan matan ne ma ya nufi can. Yana fin wata ɗaya fa bai ma je can ɓangaren ba. Ko shigowa zai yi ta nan yake bi, da yake ma waccan ƙofar saboda ku na buɗe ta, ina jimawa ban bi ta can ba."
    Miemie ta ce "To dai mu sai ki san yanda zaki mana da shi. Dan wallahi duk sun yi shiru shi kuma sai wani washe baki ya ke."
     Kareema ta yi gaba miemie na biye da ita har suka isa falon.
    Murmushi ta yi tare da kallon M. Lawal ta ce "Ban maka bayaninsu ba fa Oga, kawai dai na kiraka a waya ne cewa zasu zo ko? To Wannan ita ce Ikram, na san ma ba zaka rasa saninta a wurina ba. Wa'innan kuma duk ƙawayenta ne sun zo bikin. Jiya dare suka yi shi ne na ce kawai su tsaya su kwana. Yanzu da sun karya zasu wuce, kalacin ma ina jin ta gama haɗa masu ai, ka ɗan basu wuri sai su karya."
   Duk da bai so ba amma dole ya tashi saboda kunyar da ya ji,  haɗe da sakin murmushin yaƙe yana kallon Ikram ya fice daga ɗakin.

SHI NE SILAH!Donde viven las historias. Descúbrelo ahora