*SHI NE SILA!*
😪😪😪Na Princess Amrah
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
(2018)56~ Ƙarfe biyar da rabi jirgin su Ikram ya sauka a babban birnin Dubai.
Tun da suka fara saukowa daga bisa jirgin Ikram ke bin ko ina da kallo, saboda zubin gurin baki ɗaya abin a kalla ne.
Sai da suka sake bin wani layin aka bincike kayansu sannan aka ringa kiransu domin basu masauki, saboda dama a visa ɗinsu har da kuɗin accomodation na mutum ɗaya suka biya.
Wata haɗaɗɗiyar hotel ce aka kaisu, hawa na huɗu su ke hakan yasa suka jima basu isa ba. Ko da suka isa Momy ta sa key ɗin da aka basu ta buɗe ɗakin, saboda hannun Ikram riƙe ya ke da ƴan kayakinsu.
Babban ɗaki ne mai ƙunshe da gado da saitin kujeru, daga wani ɓangare kuma ga fridge can ga kuma water dispenser, sai dining table daga gefen kujeru.
Bisa ƙaramar kujerar Ikram ta ajiye kayansu tare da furta "Alhamdulillah!"
Murmushi momy ta yi ta ce "Kin gaji ko?"
Itama Ikram murmushin ta saki ba tare da ta furta komai ba. Banɗaki momy ta shiga inda ta ɗauro alwala domin gabatar da sallolin da ake binsu.
Bayan ta fito Ikram ma ta shiga ta yi tata alawalar, nan suka hau yin sallah azahar da la'asar, kafin su gama ma har magrib ta yi, dan haka suka haɗa har da ita suka yi.
Daidai sun gama magrib kafin isha'i ne aka yi knocking ɗin ɗakin, Ikram ce ta miƙe jiki saɓule ta ce "Who is that? (Wanene)"
"Sorry ma, here is your food. (Yi haƙuri Hajiya, abincinku ne)"
Buɗe ƙofar ta yi ta kalli matashin saurayin mai jini a jika, kyakkyawa ne mai ƙwarjini sosai, amma hakan bai hanashi neman halaliyarsa ta hanyar aiki a hotel ba, saɓanin mutanenmu na nan da tsabar girman kai ba zai taɓa barinsu neman na kansu ba, komai sai girman kai da raina sana'a.
A wani makimancin keke ne ya jero abinciccikan nasu, shiga ya yi cikin ɗakin bayan itama ta shiga, bisa dining table ya hau jejjere abincin sanann ya masu bankwana ya tafi.
Bayan sallar ishai suka fara cin abinci, duk da abincin na larabawa ba wani jin daɗinshi su ke ba, momy ce ma ta ɗan ci farar shinkafa da aka ma haɗe-haɗen spices sai rabin kaza a kai. Ikram kuwa gurasa da miyar kaza ta ci duk da ba wani daɗin kirki kawai dai daurewa su ke, gwara ma kazar ita ce kawai mai ɗan daɗi.
Bayan sun gama duka suka ɗan taɓa fira kaɗan sannan Ikram ta jawo wayarta, nan fa ta buɗe data aka ci gaba daga inda aka tsaya.
Ganin Ikram ta yi shiru yasa ta ɗauko tata wayar ta latso kiran Haidar, so biyu tana kira bai ɗauka ba hakan yasa ta ce wata ƙila yana masallaci ne, tun da yanayin lokacin namu da can ba ɗaya ba ne, ba zai wuce a ce su Haidar lokacin su ke sallar magrib ba.
Khalid ta kira bugu ɗaya ya ɗauka. Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ce "Wai Allah ya yi! Tun ɗazu na ke kira bata shiga har na gaji na aje wayar."
"Wallahi ko muna bisa sararin samaniya." Momy ta bashi amsa tana dariya.
"To masha Allah! Kun sauka lafiya dai ko?" Ya tambaye ta.
Momy ta amsa da "Lafiya ƙalau saifullahi, ina yayan naku? Na kirashi bai ɗauka ba."
Khalid ya ce "Ehh ya je masallaci ne bai dawo ba."
"To kai kuma fa? Ko baka je ba?" Ta jefo masa tambaya.
Ya ɗan shafi sumarahi sannan ya ce "Momy bana dan jin daɗi ne shiisa ban je ba. A gida kawai na yi."
"Subhanallahi! Me ya same ka? Ko ciwon kewarmu ne har ka fara daga tafiya?" Ta faɗa cikin zaulaya.
Murmushi ya yi mai sauti ya ce "Ciwon kai ne na ke momy."
"To Allah ya baka lafiya. Idan ya dawo ka ce masa ya kirani." Momy ta faɗa haɗe da kashe wayar.
Bayan ya ajiye wayar a bayyane ya ce "Allah sarki Ikram! Na yi kewarki sosai." Ya koma ya zauna bisa kafet ɗin sallarshi dan dama lazimi ya ke.
Momy kuwa kwanciya ta yi bayan ta canza kaya, tana kwanciya kiran Haidar na shigo mata, ɗauka ta yi ya yi sallama ta amsa masa, "Ina yini momy?" Ya faɗa a hankali.
"Lafiya ƙalau. Ya gidan?" Ta tambaye shi.
"Gida alhamdulillahi momy. Ɗazu bayan mun dawo Baabah Naana ta fito wai itama kin ce ta je gida kafin ku dawo ko?"
"Ehh." Momy ta bashi amsa. "Ka turo min ATM pin ɗin wanann ATM ɗin daka bani. Kuma current account ne ko saving?"
"Savings ne momy. Zan turo miki pin ɗin insha Allahu." Ya faɗa, yana so ya tambaye ta ina Ikram amma ya kasa, saboda ya san ko ya kira Ikram ɗin ba wani abin kirki ne zasu yi ba.
"Ga Ikram ku gaisa ka mata ya hanya." Momy ta faɗa tare da miƙawa Ikram da ke kwance kan three seater wayar.
Karɓa ta yi tana ɗan yamutsa fuska ta yi sallama.
Wata irin nannauyar ajiyar zuciya ya sauke haɗe da amsa sallamar ya ce "Autar momy an yini lafiya?"
Baki ta tunzuro dan ita jin abin ma ta yi bambaraƙwai, wai namiji da suna Hajara.
"Alhamdulillah. Ina yini?"
"Lafiya lau, ya gajiyar tafiya?"
"Lafiya ƙalau." Ta yi shiru daga nan dan bata san kuma abin da zata ci gaba da faɗi ba.
A nashi ɓangaren ma hakan ne, bai san abin da zai ce mata ba hakan yasa kawai ya ce "To sai Allah ya kaimu." Ya kashe wayar daga nan.
Miƙawa momy ta yi ta ce "Bara dai in kwanta momy, na masifar gajiya wallahi."
Momy ta ce "Nima ai kwanciyar zan yi. Taso ki dawo nan kusa dani ki kwanta."
Samun kanta ta yi da jin kunyar momy. Ta ya zata kwanta ƙugu da ƙugu da surukarta? Duk da dai ita momy ba wannan ɗaukar ta mata ba, ɗaukarta ta yi tamkar ƴarta ta cikinta.
Runtse idonta ta yi ta buɗe sannan ta ce "Momy zan kwanta a nan."
Zaune momy ta tashi ta ce "Ya za'a yi ki kwanta bisa kujera? Taso maza ki dawo nan."
"Allah momy babu komai. Ki kwanta kawai, kin san kwanciyar kujera daɗi ke gare ta." Ikram ta faɗa tana murmushi.
Momy ta ce "To shi ke nan tun da ke kika zaɓi hakan. Allah ya tashe mu lafiya." Ta jawo abin rufa ta rufe ta ce "Idan kin gama sai ki kashe wutar."
Tashi ta yi kuwa ta kashe wutar sannan ta koma ta kwanta, inda ta ci gaba da charting a group ɗin *ENTERTAINMENT* da Miemie ta buɗe masu su huɗu, ita da Ikram, sai Husnah da Smart, wai ta buɗe shi ne musamman saboda maganar hidindimun biki da yanda abubuwan zasu kasance.
Miemie ta ce "Sai yaushe zaku dawo ne?"
"Sati biyu zamu yi insha Allahu." Ikram ta miyar da amsa.
Husnah ta ce "Ke nan saura sati huɗu biki zaku dawo? Amma gaskiya an makara har yanzu ba'a fiddo ashobe ba. Dan na san ba kowa ne ya ke da halin yin komai cikin ƙanƙanin lokaci ba."
Ikram ta ce "Wanda za'a saka ranar bridal shower dai Momy ta ce idan mun shiga kasuwa zan zaɓo mana duk abin da muke so aƙalla na mutum hamsin."
"Ahh lallai fa ana bikin ƴar gidan momy. Kar dai a yi zaɓen kayan ɗakin banza." Miemie ta sake rubutowa haɗe da alamar dariya.
Murmushi Ikram ta yi ita kaɗai, saboda tuno ƙaryar data ma Miemie cewa siyayyar kayan ɗakinta ne zasu yi a Dubai ɗin.
"Na tafi in kwanta ƴan mata. Ku ci gaba da tattaunawarku idan na tashi gobe zan ga komai. Allah ya tashe mu lafiya." Tana tabbatar da saƙon ya isa ta kashe data'n haɗe da jona chaji ta kwanta bacci.
Da asuba momy ta tashe ta suka yi sallah sannan suka koma bacci. Misalin ƙarfe takwas na safe har a lokacin baccin su ke suka ji knocking, cikin bacci Ikram ta miƙe haɗe da faɗin "Who is there?"
"Waiter." Ya faɗa.
Jiki sanyaye ta buɗe ƙofar ta ga kuma wani saurayin ne daban, alamun dai duty su ke yi ke nan.
Shigowa ya yi ya jera masu kayan kalaci bayan ya gaishe su sannan ya fita ya rufe masu ƙofar.
"Ni fa ban saba irin wannan kalacin na sassafe ba." Ikram ta faɗa tare da komawa ta kwanta.
Momy ta ce "Lafiya ce ta miki yawa shiisa, ni da ke da ulcer in ce zan biye ki mana." Ta miƙe tare da nufar banɗaki ta goge baki.
Bayan ta fito ta samu har Ikram ta haɗa mata komai, shayi ne irin mai kayan ƙamshi ɗin nan, sai madara mai yawa nufinsu wai ko da mutum yana son sha da madara. Sai kuma jam a cikin wasu ledoji guda biyu. Ga gurasa ga kuma cake. Kaya dai tarkace sai wanda mutum ya zaɓa.
Nan fa momy ta hau kalacinta hankali kwance tana shan shayi da gurasa tana shafa jam a jiki.
Ikram kam sai ƙarfe goma sannan ta karya, cake da lemo kawai ta sha, lemon ma tun sauran na jiya saboda ita sam ba ma'abociyar shan tea ba ce.
Tana gamawa ta shiga wanka dan momy har ta riga da ta shirya.
Ikram na fitowa ta shafa mai da ƴar powder sannan ta fiddo wata jallabiya baƙa mai adon stones light purple. Mayafi ta fiddo light purple sannan ta saka kayan ta ɗan yafa mayafin ta saka takalma.
"Na shirya momy." Ta faɗa.
Kallonta momy ta yi ta ce "You are always looking preety my Ikkey. Sai mu tafi kasuwar ko?"
Cikin kunya Ikram ta ce "Na gode momy. Mutafi?"
"Yeah." Ta ɗaga mata kai.
Fita suka yi a tare sannan Ikram ta rufe ƙofar ta saka makullin a cikin jakarta.
Drop suka ɗauka na taxi, saboda dama can momy ta saba zuwa ƴan sare sarenta yasa ta san kasuwar da zasu nufa ɗin, faɗawa mai taxi ɗin ta yi inda sai kaisu, babu ɓata lokaci kuwa sai gasu a bakin wata tafkekiyar kasuwa da aka zagaye da katanga mai tsawo kuma mai kyan gaske, kai ka ce ba kasuwa ba ce.
Da ƴan sauran dalolinta ta sallami mai taxi ɗin sannan suka shiga daga ciki.
Sai da aka bincike masu hand bags kafin aka barsu suka shiga, nan ma dai Ikram sai da ta yi mamaki, a ce wai kasuwar ma sai an yi wa mutum bincike kafin a barshi ya shiga.
Murmushi momy ta ma Ikram ta ce "Kin ga sauyi ko? Su nan komai nasu daban ya ke dana ƙasarmu."
Ikram ta jinjina kai ta ce "Na gani ai." Suka ci gaba da shigewa ciki.
Da shagon gwala-gwalai suka fara, sarƙa mai kyau ƙirar dubai momy ta bayar data Ikram da ta zo da ita, aka canza mata da wadda ta fita girma sosai da tsari.
Ta sai mata ƴan kunne daban da abin hannu babba guda ɗaya, sannan ta bada ATM ɗin Haidar aka ciri kuɗin.
Daga nan suka wuce shagon materials inda Ikram da kanta ta ringa zaɓar wa'inda ta ke so, sai da ta zaɓi guda goma ta barshi, momy ta ƙara mata da guda biyar, sannan suka fita, a bakin shagon ke akwai wanda ke ɗinka dogayen riguna masu masifar kyau.
Guda goma aka bayar ɗinki, take momy ta bashi kuɗin da niyyar nan da kwana biyu zasu dawo su karɓa ɗinkunan.
Daga nan kuma sai suka nufi shagon dogayen riguna da ƙananan kaya masu fitinannen kyau, nan fa Ikram ta fi auki, ƙananan kaya ta ringa judo kamar yanda momy ta bata umurni, har idan ma ta ga kamar Ikram ɗin tana ɗan jin kunya sai ita ta ɗaukar mata.
Tsakanin ƙananan kaya da dogayen riguna sai da Ikram ta haɗa kaya kala ashirin da biyar sannan suka tafi.
Shagon da momy ta saba sarar jaka da takalma suka nufa, an kawo sabbin yayi wanda ko ɗisonsu basu iso ƙasarmu ba. Sosai Ikram ta ruɗe, dan ita kam gwana ce a hand bags, tana masifar son kwalliya da jaka.
Guda goma ta zaɓa momy ta ƙara yi mata nata zaɓin guda uku.
Kai tsaye bayan sun bar nan, suka nufi wani tafkeken shago wanda ke ƙunshe da manyan laces da materials masu kyau, da alama dai wanann shagob basa siyar da ƙananan abubuwa, komai nasu mai tsada ne.
Ciki suka shiga, mai shagon ya gaishe da momy cikin yaren turanci, da sakin fuska momy ta amsa, hakan ya tabbatarwa Ikram da cewa sun saba shi da Momy.
Momy ta ce tana so ya fiddo mata da sabbin fitowa laces da materials ɗin, kala-kala kuwa ya ringa zaro mata, tace da Ikram ta zaɓi wanda ta ke so, sannan itama ta zaɓar mata aƙalla guda takwas wanda itama zata yi kwalliyar biki da shi.
Haka dai suka ringa siyayya kai ka ce kuɗin ba masu ƙarewa ba ne. Ko da ya ke, ai ba abin mamaki ba ne, momy'n kanta mai kuɗi ce, ga uwa uba Haidar wanda banda na gadonshi ma, albashinshi kawai ya ishe shi rayuwa, kuma da wuya ya fitar da su, da zarar ta ji alert sai dai kawai ya yi transferring na kuɗin su koma Saving account ɗinshi.
Sai yamma liƙis sannan suka yi shatar taxi guda biyu, saboda guda ɗaya ba zata kwashe masu kayansu da su kansu ba.
Sunan Hotel ɗin suka faɗa aka kaisu, ma'aikatan hotel ɗin suka ringa kwasar kayan suna kai su ɗakin su momy.
Bayan sun yi sallah suka ci abinci momy ta ringa fiffitar da kayan suna ƙara kallo.
"Yanzu sai kuma gobe idan Allah ya kaimu sai mu tafi wata kasuwar, waccan zamu samu atamfofi masu kyau. Jibi kuma akwai wadda zamu je a siyo akwatuna."
Ikram dai shiru ta yi, a ranta tana mamakin hali irin na mony, sam bata da ƙyashi, abin da duk zata iya yiwa kanta ko kuma ɗanta, to bata jin haushi dan ta yi ma wani.
"Shima angon ya kamata a masa tasa siyayyar, a haɗa mashi lefe shima." Momy ta faɗa bayan ta ɗago wani royal blue lace, wanda aka ma zane da golden colour.
"Kai Ikkey wannan lace ɗin ya yi kyau sosai, kuma gashi baki ɗaukowa kanki irinshi ba "
Murmushi kawai Ikram ta yi bata ce komai ba.
Momy ta ce "To ko nawa ɗin kawai zaki ɗauka?"
Dafe baki Ikram ta yi da kunya ta ce "Ki rufan asiri momy. Wallahi na gode."
Momy ta ce "To ni kam gaskiya ya burge ni. Ai da yake ba yanzu zamu tafi ba. Sai mu koma shagon ko da bayan an gama siyayya duka ne a siyoshi, bari zan kira mai shagon in kwatanta masashi ya ajiye miki. Gaskiya ya burge ni sosai."
Murmushi kawai ta yi ba tare da ta ce komai ba.***
Haka su momy suka ringa siyayya babu ko gajiya, kwanansu goma suka shiga wata kasuwar wadda materials ne kawai ake siyarwa a ciki. Nan momy ta ce wa Ikram ta zaɓarwa ƴan mata wanda zasu saka ranar bridal shower ɗin, daga nan kuma akwai shagon da zata kaita inda ake siyar da kayakin amare.
Baki ɗaya idon Ikram ya rufe, tsabar kyan materials ɗin shagon yasa tama rasa wanda zata zaɓa.
Da ƙyar ta zaɓo wani pink and yellow mai masifaffen kyau, wanda ta san zai iya yi wa kowa kyau baƙi ko fari.
Head ɗinsu ta tambaya a inda za'a samu, mutumin ya kwatanta masu wani shago ya ce ko wane irin head su ke nema zasu samu a can.
Can ɗin kuwa suka nufa, yellow head ta sa aka fitar da guda hamsin, sannan aka fitar dana baki ɗaya ƴan *RAZ NOVELLA.*
Daga nan kuma suka nufi shagon da momy ta ce za'a samu kayan amare, nan ta ci karo da materials da net masu kyau irin wanda ta ke ganin ƴan matan masu kuɗi suna sakawa ga bikinsu.
Guda huɗu ta zaɓa duk da bata san events ɗin da za'a yi ba.
Tun daga head, sarƙa, abin hannu, mayafi da komai da amarya zata buƙata sai da suka siya a wannan shagon.
Ranar sai dare suka koma gida, saboda sun gama siyayyar ba zasu sake fita ba, sauran kwana huɗun da ya rage masu zasu huta ne kawai.*Bayan kwana huɗu*
_(Ba zan taɓa manta page 55 ba, saboda ni kaina sanda na ke rubutashi I was enjoying, na ji daɗinshi sosai, haka kawai ban san dalili ba. I hope kuma ya maku daɗi.)_
*team Ikramhaidar*
*team Ikramkhalid*

VOUS LISEZ
SHI NE SILAH!
Roman d'amourshi ne silar rugujewar farin cikin rayuwarta. shine silar shigar ta cikin kunci da bakin ciki. shi ne silar rashin gata hadi da galihu a rayuwarta. shin waye silah? ku biyoni a cikin wannan labarin inda zan warware maku zare da abawa.