34

932 55 0
                                    

*SHI NE SILA!*
           😪😪😪

              Na Princess Amrah
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
                           (2018)

_Wannan shafin kyauta ce ga members na group d'in *KHADIJA CANDY* domin jin dad'insu. Na gode da k'aunar da kuke ma labarin *SHI NE SILA!*. Amrah na shaida maku cewa #anatare…_

34~  Ta jima tana kuka kafin ta tashi ta nufi ban d'aki, alwala ta d'auro sannan ta gabatar da sallar azahar.
    Bayan ta gama ma komawa ta yi ta kwanta ranta dagule, jin alamar tafiya yasata saurin share hawayenta, sai dai kuma kallo d'aya za'a mata a gano tana cikin damuwa.
    Sallama aka yi ta yi saurin amsawa had'e da k'ak'ulo murmushi, Naanah mai aiki ce ta shaida mata an gama abinci ta sauko ta ci, babu musu kuwa ta bi bayanta suka sauka.
    Bata yarda ta had'a ido da momy ba sai nufar dinning da ta yi, momy kuma tana zaune a parlor tana cin abimci.
    "Ikram 'yata bacci kika yi amma? Na jiki shiru tun da kika hau sama."
    Bata juyo ba cikin sautin fara'a ta ce "Bacci ya d'an 'daukeni kam, amma dama na farka har na yi sallah ko da Baabah ta shiga."
    "To madalla. A ci abinci kuma a zo a bani labarin makaranta, yaushe rabon da mu yi fira da ke?" Momy'n ta fad'a tana mirmushi.
    "An jima kam momy, bara na gama to sai na baki labarin School." Ta zuba abinci.
    Kad'an ta ci abincin tsabar damuwa da ta ke addabar birnin zuciyarta, ta samu ta shiga kitchen ta d'an sake wanke fuskarta sannan ta fito, ta samu fuskar ta d'an sake, sai dai za'a iya cewa ko bacci ne ta fara bai isheta ba.
     Fara'a 'kunshe a fuskarta ta ce "Momy na gama to."
    Momy ta ce "Nima na gama, sai a fara."
     "To, an gama koya mana abubuwa ta rubutu, yanzu practical muka fara shima kuma 'din nan da kwana uku insha Allahu zamu gama. Idan muka gama sai a koya mana  yanda a ke nad'in head kala kala, daga wannan matakin kuma sai balarabiyar dana ta'ba baki labarinta ta koya mana different yanda ake rolling veil. After that sai gyaran jiki wanda shi ne k'arshe, shi kuma ba'indiya ce zata koya mana."
    "Ahh madalla. Yanzu ke nan idan na baki fuskata zaki iya canca'da min kwalliyar nan irin ta zamani?" Ta yi dariya.
    Da sauri Ikram ta ce "Me zai hana momy? Ko na d'auko kayakin da gareni a yi?"
    Cikin mamaki momy ta ce "Allah ya kyauta min Ikram, ai ko ke kika ji na ce zan yi make up sai ki hanani. Ki bari dai sai ranar aurenki sai ki min."
     Cikin shagwab'a Ikram ta ce "Wai momy sai ana maganar kirki ki fara ambatar aure."
    Momy murmushi ta yi ta ce "Maganar aure ba maganar kirki ba ce ke nan?"
    Cike da kunya ta ce "Ni dai momy a closing chapter'n nan abeg."
    "To Khalid dai abokin fad'an naki ma aure zai yi har ma ya fitar da mata. Ke kuma kin ga sai ki ci gaba da zama ke kad'ai tun da bakya son auren." Momy ta fad'a.
    "Ba wai bana so ba, amma ai na yi k'aranta da yin aure ko Baabah Naanah?" Ta kalli Naanah da ta iso wurin a daidai lokacin.
    Dariya ta yi ta ce "Lallai Ikram a gaisheki, yo idan a k'auye ne kamarki ai kin aje yara hud'u. Mu kam ki fiddo miji mu sha biki. Kin ga lokaci d'aya sai momy'nku ta aurar da duka yaranta, a barmu a gida daga ni sai ita, mu ci karenmu ba babbaka." Ta sake yin murmushi.
    Baki tunzure Ikram bata kuma fa'din komai ba, a zahirin gaskiya bata jin da'di ta ji an ambaci wai Khalid ya fitar da matar aure.
     "Ai ba ita kad'ai ba ce, shima yayan nasu ya 'ki fitar da matar ban san dalili ba. Shi dama mata basu dameshi ba ba tun yanzu ba, mai rawar kan dai sai Khalid, duk da shima d'in ba wai ya cika kula matan ba ne. Amma fa lokacin da yana BUK wata yarinya ta tab'a kirana tana kuka, wai Khalid ya ce zai aureta kuma yanzu ya fasa saboda kawai ya kirata call waiting. Ni abin ma ya bani dariya na ce ta bari zan masa magana. Ko da na masa magana dariya ma yayi ya ce kawai na fidda kaina daga maganar, wallahi da k'yar na samu yarinyar nan ta k'yaleni, wai ita a dole sai na sashi ya aureta, lokacin ma ko auren bai isa ba."
     Dariya suka saka su duka. Momy ta ce "Idan akwai wani wanda kika san ya fara nemanki ki fad'a min."
    Shiru Ikram ta yi bata ce komai ba, saboda tana kunyar momy sosai.
    Sake maimaita mata momy ta yi "Akwai wanda ya ke nemanki ko babu?"
    Kai ta d'aga a hankali ta ce "Babu.."
    Ajiyar zuciya momy ta sauke kafin ta d'an murmusa ta ce "A matsayin wa kika d'aukeni Ikram?"
    "Matsayin uwar data haifeni." Ikram ta bata amsa.
    "Good, yanzu idan na zab'a miki miji na gari na yi laifi?"
    Sai a lokacin ta d'ago kanta ta kalli Momy, kar dai momy da gaske ta ke auren zata mata.
    "Baki yi laifi ba ko kad'an momy. Ai uwa bata ma 'yarta laifi." Ikram ta fad'a cikn k'arfin hali.
    "To na gode 'kwarai Allah ya miki albarka. Je ki kwanta ki huta dan da alama har yanzu kina jin bacci wanda kika yi bai isheki ba."
    Babu musu kuwa ta tashi ta haye sama, zuciyarta sai sak'e sak'e ta ke mata, wani b'aren zuciyar ya ce mata "Me yasa momy ta ke son aurar da ni, kuma waye zata aura min?' Wani kuma ya ce 'To ai ba laifi ba ne ba tun da bani da wani tsayayye, kuma na san ba zata zab'a min wanda ba na gari ba.' Da wannan tunane tunanen bacci ya yi awon gaba da ita.

SHI NE SILAH!Tahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon