45

1K 56 0
                                    

*SHI NE SILA!*
           😪😪😪

              Na Princess Amrah
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
                           (2018)

*_HBD YAYA HAYAT! INA TAYAKA MURNAR ZAGAYOWAR RANAR HAIHUWARKA. ALLAH YA 'KARO MAKA SHEKARU MASU ALBARKA YA K'ARA D'AUKAKA DA BASEERAH. WANNAN SHAFIN SADAUKARWA CE GARE KA DOMIN JIN DAD'INKA. Amrah na tayaka murna sosai da sosai._*


45~  Yana isa Office a ranar ya fita ward round, sai da ya fara zuwa female ward ya duba wanda ya ma aiki sannan ya wuce male ward biye da shi wata nurse ce da ke rik'e da file d'in ko wane patient.
     Male ward suka nufa, a hankali ya ke duba mutane har ya isa bakin gadon Halle. Mallam Maharazu na zaune yana masa fifita Haidar ya isa. "Ya mai jikin?" Ya tambaye shi had'e zama.
    "To! Mai jiki da sau'ki za'a ce, amma dai jiya bai yi baccin kirki ba, sai ciwon ciki da ya addabe shi. Yanzu haka bacci ya yi amma ciwon cikin ya farkar da shi."  Maharazu ya fad'a cike da tausayi.
     Kar'bar file d'insa ya yi ya ce "Ku bamu wuri." Yanayin da ya yi maganar nurse d'in ta gane har da ita ya ke nufin ta tafi. Tafiyar kuwa suka yi aka barshi daga shi sai Halle da ya yi zuru zuru ciwo sai addabarsa ya ke.
     "Sannu fa." Haidar ya ce da shi.
    "Yauwa." Halle ya fad'a a hankali.
      "Ko ka san ciwon da ya ke damunka?" Haidar ya fad'a cikin sanyin murya.
    "A'a ban sani ba likita sai ka fad'a."
    Ajiye file 'din ya yi a kan tebur sannan ya fara masa bayani "Amma kai d'an homo ne ko? Ina nufin d'an luwad'i. Kar ka min k'arya saboda na tabbatar da hakan kafin komai. Idan baka sani ba ka sani! Luwad'in da kake yi shi ne ciwonka. Ya sakar maka muguwar cuta wadda ba zaka ta'ba warkewa da ita ba sai ko wani iko daga Allah, wata k'ila ma idan baka bi a hankali ba ita ce ajalinka."
    Ido bud'e Halle ke bin Haidar da kallo, bai musa masa ba sai dai tsabar mamakin da ya ke ta ya aka yi Haidar ya san hakan?
    "Kana mamaki ko? Shekarata bakwai ina karatun likitanci, sannan kuma na koma na yi wata bakwai d'in a 'bangaren nervous system. Ka ga kuwa ai wannan ba abin mamaki ba ne ba dan na sani."
    Har yanzu Halle bai dai kallon Haidar ba. Ya ci gaba da fa'din "Ka jima kana aikata luwad'i, wata k'ila ka yi shekara ashirin da biyar kana yi. Ba zan ce lallai a cikin shekara ashirin da biyar d'in ko kuma fin haka ko yaushe kana yi ba, sai dai kuma zata iya yiuwa ka yi ne sai ka daina, daga baya kuma ka ci gaba."
    Murmushin takaici Haidar ya yi ya ce "Ga ka mutum har mutum, dattijo har dattijo, sai dai kuma kash! Duburarka ta lalace, ba zaka sake morarta cikin da'di ba. Ba dubura kad'ai bama, abin fitsarinka kanta tana da rauni wanda bana jin zaka iya sake saduwa da mace a halin yanzu. Ciwon cikin da kake fama dashi kuwa ruwan maniyyi ne ya ke shiga ba ta inda ya dace ba. Cikin duburarka a ke zubashi, hakan yasa ya kai inda bai dace ba har ya fara illata maka wasu daga cikin kayan cikinka. Ba zaka ta'ba daina fama da wannan ciwon cikin ba har sai sanda aka maka aiki aka fitar da maniyyin da ke ciki. Wannan aikin kuma dole sai ta duburarka za'a yishi, babbar matsalar kuma duburar ta riga da ta rub'e, babu yanda za'a yi a maka aiki a wurin. Sannan kuma a cikinta akwai wata babbar tsutsa wadda ta hayayyafa, ita ce ta cinye maka baki d'aya duburar har ta rub'e haka."
     Sosai gaban Halle ke fad'uwa, iya kad'uwa ya ka'du, lallai biri ya yi kama da mutum, ashe shisa ko yaushe ya ke yawan jin kamar ana cizonsa, duk sanda zai ji wannan cizon kuma in har bai je ga namiji ba ba zai tab'a samun natsuwa ba.
    Haidar ya ci gaba da bayani "Yanda abin ya ke shi ne, a duk lokacin da namiji ya ke saduwa da d'an uwanshi namiji ta duburarsa, ruwan maniyyin da ke shiga wani zai shiga cikin ciki ne, wani kuwa zai tsaya baki baki wanda ya ke zama tsutsotsi, a k'arshe wannan su ne zasu koma guda d'aya babba, a duk lokacin da aka bata maniyyi sai ta shanye shi tana k'ara girma sosai. Duk sanda ta ke jin yunwa ba'a bata ba shi ne sai ta ringa tsikararka ko ta cije ka wanda dole sai ka nemi namiji a lokacin ya zuba mata wanaan ruwan maniyyin. Wannan dalilin ne ya sa duk wanda ya fara homo ya ke zama addicted da shi, baya tab'a dainawa har sai sanda ya samu maganin da zai kashe masa wannan tsutsar. A halin yanzu kai kam naka abin ya yi worst, kominka ya fara lalacewa, amma a haka ba zaka hak'ura ka mik'a lamurranka ga Allah ba? Na tabbatar da idan yanzu abokin yin naka ya zo ya nemi ku yi ba zaka musa masa ba saboda ka zama addicted da abin. Mesa? Mesa ka zab'arwa kanka wannan rayuwar? Haba mallam! Shekarunka nawa a halin yanzu? Ya isa ace ka koma ga Allah yanzu, a k'alla ba zaka kasa ma shekaru arba'in da biyar ba. Kana da tabbacin zaka maimaita shekarunka na baya?"
     Kuka sosai Halle ke yi, tabbas duk abin da Haidar ya fad'a masa gaskiya ne, to amma kuma me? Bai san yanda zai yi ba.
      Haidar bai kuma fad'in komai ba sai rubutu da ya yi a kan takardar da ke cikin file d'inshi. Bayan ya gama ya d'ago kanshi ya ce "Ga maganin da za'a sai maka nan. Ka dage da shanshi sosai kar ka yi wasa." Ya mik'e had'e da nufar d'ayan gadon, ko da nurse ta hango shi da sauri ta k'ariso ta mi'ka masa file d'in d'ayan gadon da ya je d'in.
     Kuka mai sauti Halle ke yi a daidai isowar Maharazu, ya dafe kanshi damuwa fal a zuciyarsa. Hak'uri Maharazu ya rainga bashi dan shi ya yi zaton ko azabar ciwo ce ta sakashi kukan, wanda sam ba hakan ba ne, duk da yana jin ciwon amma bai kai zafin maganganun da Haidar ya fad'a masa ba. Ke nan babushi babu yin aure, babushi babu ganin jininshi da sunan d'a ko y'arsa. Duk da ya ke shi 'din ba mai ra'ayin yin aure ba ne, amma Allah ya d'aura masa son yara, har sha'awa ya ke ya ga uba da 'ya'yansa, amma shi babu wannan, iyayen dama babusu, babu dangi babu kowa. Kuka sosai ya sake cin k'arfinsa sai kad'a kai ya ke.

SHI NE SILAH!Donde viven las historias. Descúbrelo ahora