*SHI NE SILA!*
😪😪😪Na Princess Amrah
(NWA)
2018_Wannan shafin naku ne *Aunt Hauwa Nayaya da Ummu Abrar,* ina k'aunarku a ko da yaushe._
16~ Washe gari da sassafe sai ga Khalid ya iso, d'ayan hannunshi rik'e da kwando sai d'ayan hannun kuma flask d'in ruwan zafi ne.
Sallama ya yi sannan ya duk'a har k'asa ya gaishe da Momy, "lafiya k'alau Khalid, ya kwanan gidan?"
"Alhamdulillahi, ya mai jikin?" Ya tambayeta.
"Ahh mai jiki da sauk'i ta warware, wata k'ila yau sai sallama."
"Ai ko baki fad'a ba Momy, kai da ganin wannan mara lafiyar ka san ta warke sarai. Tashi ayi gwaji Ikram."
"Zaka fara ko? To wallahi daidai na ke da kai yau, saboda wani irin sabon k'arfi na ke ji da kowa zan iya karawa."
"Yarinya k'aryarki ta sha k'arya ba dai ni ba. Ai yau zamu koma gida dole sai an yi gwaji."
"Uban surutu fa ya iso, k'yaleshi yarinyata bari na zuba miki abin kalaci." Momy ta fad'a tare da sauka daga bakin gadon ta fara k'ok'arin zuba abin karyawa nata da na Ikram.
Tea ta fara had'awa Ikram sannan ta zuba mata soyayyen dankali da k'wai da plantain sai sauce d'in hanta. Mik'a mata ta yi ta karb'a sannan ta ce "Momy sai dai kuma bana shan madara, tea'n ma duka bai dameni ba bari dai na ci dankalin kawai."
"A'a Ikram, bari dai ko ruwan lipton na had'a miki ki sha, ai ya kamata ki gasa hanjinki ko?"
"Haka ne Momy, kad'an zan sha to."
"'Yar albarka kad'an d'in zan zuba miki." Ta yi murmushi tare da sake zuba mata wani.
Khalid ya ce "Ah to ni bani wanda kika had'a mata d'in na sha, dama ban karya ba."
"Ka ji d'an rainin wayo, Khalid baka da dama, yanzu kana nufin baka karya ba ka fito? ko kuwa dai dole sai ka ci namu kalacin?"
"Wayyo Momy kin ga fa ni ne sabon autanki tun da Feenah ta rasu, autanni kuma lelensu a ke amma ke sai korata kike yi."
"Waye autan kai? Gardin wa? Allah kyauta min, ni Ikram ce autata, kuma ita kad'ai zata min shagwab'a na d'auka."
Baki ya ringa turowa yana kukan k'arya, "shi ke nan Ikram ta min over_taking, babu komai na hak'ura, amma wallahi ba zan yarda ba sai an biya kud'in cin hanci da rashawa, ehe."
Dariya Ikram ta yi tare da fad'in "Allah dai ya shiryeka Yaya Khalid."
"Ke, me kika fad'a? Yaya Khalid, wayyo har na tuno Feenatuwata, Allah ya miki rahama ya bi miki hak'k'inki." Sai kuma ya d'an canza fuska.
Ihu Ikram ta d'auka tana fad'in "ashe dai ba ni kad'ai ba ce wadda ba jaruma ba, kaima gaka namiji daga tuno mutuwa fuskarka ta canza kamar zaka yi kuka."
K'ok'arin sauya fuskarshi ya yi da dariya ya ce "waye ya fad'a miki? Yarinya babu abin da ya ke sakani kuka, Feenatuwar zan wa kuka? Kasheta fa akayi, wadda ta yi mutuwar shahada ai asarar hawaye ne yi mata kuka, saboda kowa ya san makomarta."
"Haka ne, kaima kuma ka yi magana, insha Allahu sai asirinsu ya tonu." Ikram ta fad'a, saboda tun da Momy ta bata labarin Feenah ta ke tausaya mata.
"To Momy ita ma Feenah haka ta sha fama da halin Yaya Khalid?"
"Ikram ke nan, mai hali fa baya barin halinsa, haka halin Khalid ya ke tun yana yaro kuma ya tashi da shi, ko kafin mahaifinsu ya rasu haka ya ke, sai ya kirashi ya zauna tare da shi dan kawai yaita bashi dariya."
"Uhm, to sannunka, Feenah ta tafi wata Feenah ta dawo." Ikram ta fad'a cike da jin dad'i.
"Zancenki hak'k'un, ita ma kuma kin ga tana SS2 ta rasu, da tana raye SS3 ta ke ke nan yanzu, ke d'in ma kuma SS3 d'in ki ke." Momy ta fad'a tare da ajiye plate d'in dankali saboda har ta gama ci.
Nurse ce ta taho hannunta rik'e da tray d'in magunguna, bayan ta gaishe da Momy ta mata ya mai jiki ta juya ga Ikram, "Ikram kin ji sauk'i ko?"
"Alhamdulillahi, Sister jiki ya warware."
"Bari ma kawai na baki sallama to tun da dai kin warke, sai ki kula sosai, ki cire duk wata damuwa a ranki, magani kuma ki sha cikin lokaci." Ta bata magungunan da zata sha yanzu sannan ta ce "Bari na kawo miki sallamar da sauran magungunan da zaki ci gaba da sha." Ta tafi.
"Kai wannan Sister'n ta yi kama da wata lecturer d'inmu sanda ina BUK, wata arniya 'Bakutu muke kiranta, Allah sifarsu d'aya kawai waccan ta fi wannan k'iba ne, k'ibar 'Bakutu ta kai ta Momy Allah a cire batun wasa."
"Ya Salaam! Yaya Khalid wane irin mutum ne wai kai? Idan kana tsokanar min Momy sai mun ringa sab'awa da kai, ka tsaya can a 'Bakutunka ba sai ka tab'o min uwa ba."
"Da gaske fa na ke, kai Allah sarki har na tuno B'akutu, wallahi idan tana mana lecture ta juya tana note muita d'aukarta hoto ta baya, idan muka rasa abin yi wa dariya kuma sai mu dubo hoton mu ringa dariya, ya zama photo of the day." Ya k'yalk'yale da dariya.
"Mtsw, Allah dai ya shirya." Momy ta fad'a.
Sister'n ce ta dawo Ikram na kallonta wata dariya ta zo mata saboda tuno labarin B'akutu da ta yi. K'ok'arin danne dariyar ta yi ta hanyar dod'e hancinta da bakinta.
Momy ta mik'awa takardar tare da ledar magunguna ta ce "Gashi, sai a kula da shan magani, ta ringa shan shi k'a'ida, ta kuma yi k'ok'arin cirewa kanta duk wata damuwa dan gudun wata matsalar."
"To insha Allahu za'a kula Sister, mun gode Allah ya saka da alkhairi."
"Ameen, Ikram Allah ya bada hak'uri ya ji k'anta da rahama, sai a ringa ziyartarmu ko?"
Dariya ta yi ta ce "insha Allahu kuwa Sister."
"Da yake yayansu ma a nan ya ke aiki, baya nan ne ya tafi UK ai da sun ringa zagayoku."
"Allah ya dawo da shi to." Ta fad'a tare da barin wurin.
"Dariya Kahlid ya saki ya ce "kai, wallahi har da dariyarsu tana shige, ko dai 'yan uwa ne wai? Ai kuma ita waccan Inyamura ce, wannan kuma bahausa ce."
"Kai dai ke kid'anka ka ke rawarka." In ji Momy. "Ni tashi ka fara fita da kaya mu kama hanyar gida."
Tashi kuwa ya yi ya fara fita da kayakin, babu jimawa ya dawo ya kwashe sauran, ya yi gaba Momy da Ikram suka bi bayanshi.
Tafiya mai nisa ce ta sadasu da unguwar su Momy, gaban wani rantsattsen gida Khalid ya yi horn, shiru ba'a bud'e ba sai a karo na biyu wani tsoho ya taho da saurinshi yana d'agawa Khalid hannu alamar ban hak'uri. Shima Khalid hannun ya d'aga masa tare da shiga cikin gidan.
Tun da suka shiga ciki Ikram ta hangame kanta sai faman kallon gidan ta ke, gida ne babba mai kyau da tsari, ko a mafarki bata tab'a tunanin zata ko matso kusa da irinshi ba barin ta shigeshi. Amma sai gashi wai yanzu ta zo da niyyar zama cikinsa na har abada.
"Ikram sauko ko?" Momy ta fad'a tana mata murmushi.
"Idan baki fita ba yarinya zan yi 'yan dubu dubu da motar nan." Khalid ya fad'a.
"Miye kuma 'yan dubu dubu?" Ikram ta tambayeshi.
"Wani abu ne ake yi da mota, idan na yishi kina ciki sai kin yi zawayi tsabar rikicewa." Khalid ya bata amsa yana tintsira dariya.
"Ta Allah ba taka ba mugu kawai." Ta yi saurin ficewa.
"Lallai yarinyar nan wuyanki ya isa yanka, ni kike cewa mugu?"
"Ehh d'in na je na ce mugu, mugu kawai." Ta yi saurin barin wurin.
Bata san inda zata dosa ba hakan yasa ta dakata har sai da Momy ta cimmata.
A jere suka nufi babban sashen gidan wanda ya ke da 'yar tazara daga inda ake ajiye motoci.
Wata k'ofar glass ce suka ci karo da ita, nan ma dai kallo Ikram tasa tana tunanin ta ina zasu shiga? Wani malatsi ta ga Momy ta danna a hankali k'ofar ta bud'e da kanta. Shiga suka yi tare cike da mamaki, lallai abin kallo baya k'arewa, dukiya tana inda ta ke.
Ko da suka shiga wani babban falo ne suka ci karo da shi, jere ya ke da tsadaddin kujeru kusan seti uku kala kala, iya tsaruwa ya tsaru.
Wata irin k'atuwar tv ce a falon, sai wasu manyan frames masu zanen fulawowi girke gefe da gefen tv, daga gaban tv d'in kuma tum tum ne da babban capet sai throw pillows an jera su. Sosai d'akin ya had'u, nan ma dai kallo kawai Ikram ke binshi da shi.
Naana mai aiki ce ta fito daga wani d'aki tana masu sannu da zuwa.
"Yauwa Naana, a kai Ikram d'akin Feenah, ta samu ta yi wanka, ki gwada mata kayakin nan na Feenah wanda na ci gadonsu, ta saka kafin ta k'ara murmurewa Khalid ya kaita ta siyo wasu."
"To Hajiya, amma d'akin Feenah wane ciki kike nufi? Na saman ko na k'asan?" Naana ta tambayi Momy.
Ga Ikram Momy ta juya ta ce "Ikram kan bene kike so ko k'asa?" A daidai shigowar Khalid.
"Aikuwa yarinya ba zan ringa kaiki wurin mai kamu ba, saboda dai idan kika zab'i bene kullum sai kin yi ciwon k'afa, kuma na san ni Momy zata ce na kaiki a miki kamu."
Baki ta tunzuro ta ce "Ehh na ji d'in, kuma benen zan tafi dole a kaini kamu idan ina ciwon k'afa."
Murmushi Momy ta yi "ku kam wa'innan 'yan drama ne, inda kike so can zaki tafi 'yata, ko kuma ki ringa canji, duk inda kika yi ra'ayi ki je, idan kika yi ra'ayin k'asa sai ki dawo k'asa, ranar da kika gaji kuma sai ki koma sama, haka Feenah ma ta ke yi kafin ta rasu."
"To Momy, yanzu bari na tafi na sama d'in."
"Ok to, Naana ki kaita na sama, dama dai na san a gyare ya ke kullum kina gyaranshi, yau mamadin mai shi ta zo." Ta yi murmushi. "A gwada mata yanda zata yi amfani da komai har Toilet."
"To Hajiya, yanzu kuwa insha Allahu." Ta yi gaba Ikram ta mara mata baya.
Benen kanshi wata had'uwar ce, saboda wasu irin k'arafa da aka yi amfani da su kamar ba a k'asar nan ba. D'akin farko suka shiga, Naana ta hau yi mata bayanin komai har toilet suka shiga ta gwaggwada mata yanda zata yi amfani da abubuwa, irin su shower, flushing, da sauransu. Kai kawai Ikram ta jinjina, saboda ta san ko tana gane wasu abubuwan ba yanzu ba, dan ita sam hankalinta ma baya wurin.
Bayan ta yi wanka ne ta saka wasu riga da zani na atamfa da Naana ta fiddo mata na Feenah, java ce bak'a mai manyan flowers jajaye. D'as ta cika kayan kuma suka mata kyau sosai, abinku da jar fata, kamar dama dan ita aka yi kayan.
Powder da ke kan mirror kawai ta shafa sannan ta yi d'aurin kallabinta irin nasu na k'auye ta fito.
Tun da ta ke saukowa daga kan bene Momy ke kallonta, k'ara ganin kyawun Ikram kawai ta ke. Zaune su ke ita da Khalid suna fira, bayan ita ma tayo nata wankan.
Zama ta yi k'asa tana hararar Khalid da ke guntse dariya yana kallonta.
"Kin yi kyau sosai 'yata." Momy ta fad'a.
Kunya Ikram ta ji ta rufe fuskarta. "Hau kan kujera ki tashi daga k'asan nan."
Babu musu kuwa ta koma kan kujerar.
Khalid ya ce "Yanzu dai dan Allah joke a side, magana zamu yi ta kirki, tell me little about Yourself, I mean Your schooling and everything."
Shiru ta yi dan bata san inda ya dosa ba, ta dai ji ya ambaci School kuma ta san makaranta ke nan, saboda dama karatun nasu na k'auye ba wani mai kyau bane, ita wai tana ma d'aya daga cikin masu k'ok'arin makarantar ke nan.
Shiru ta yi bata bashi amsa ba sai shi ya ce "kin ga ni sunana Khalid, ni ne d'a na biyu a gidan nan, ina da yaya d'aya mai suna Haidar, sai kuma k'anwata d'aya wadda ta rasu na san Momy ta baki labarinta. Na gama BUK yanzu haka ina service a INEC ne, dan dama political science na karanta. Ke kuma fa?"
"Ni kuma SS3 na ke yanzu haka, muna daf da fara zana jarabawar kammalawa muka baro garin. Ina son yin zurfi sosai a ilimin boko. B'angaren na addini kuma na yi sauka tun ina 'yar shekara goma sha biyar."
"Allah sarki! Kusan komai nata daidai ya ke da Feenah ko Momy?" Ya juya ya kalli Momy.
"Wallahi kuwa, nima haka na fad'a mata." Momy ta fad'a murmushi k'unshe a fuskarta.
Fira suka ci gaba da yi sosai Khalid ya tambayeta "Amma wane b'angare kike son yin karatu a kai?"
"Ehh to, na fi son zama likita, amma kuma na ji malaminmu yana fad'in wai akwai wahalar samu da kuma karatu, to ni bana jin karatun, tun da duk abin da mutum ya saka kansa to zai iya, samun dai ne wahala."
"Kwantar da hankalinki, in dai can kike so na miki alk'awarin da kaina zan samo miki admission, ke dai ki ci gaba da addu'a, amma ya kamata ki koma makaranta ko da daga SS2 ne, saboda ki k'ara sanin abubuwa da kyau."
"Babu damuwa Yaya, Allah dai ya saka maku da alkhairi." Har rana ta yi sannan suka nufi yin sallar azahar.
@wattpad: PrincessAmrah

YOU ARE READING
SHI NE SILAH!
Romanceshi ne silar rugujewar farin cikin rayuwarta. shine silar shigar ta cikin kunci da bakin ciki. shi ne silar rashin gata hadi da galihu a rayuwarta. shin waye silah? ku biyoni a cikin wannan labarin inda zan warware maku zare da abawa.