*SHI NE SILA!*
😪😪😪Na Princess Amrah
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
(2018)35~ Janshi suka yi suka tura a cikin wata mota bak'a mai tint wadda da alama ta d'aya daga cikinsu ce. Motar Khalid 'din kuma wannan d'ayan ya tuk'a ya bi bayan wacce aka saka Khalid a ciki.
Sosai suke tafiya har sai da suka fita daga garin Sokoto suka kama hanyar da zata isar da mutum har Shagari. Sun yi sa'a kuma basu had'u da check point ko d'aya ba.
A daidai bakin wani babban gidan gona suka isa, bayan sun paka motocin ne suka fitar da Khalid da har yanzu jininshi bai daina fita ba, bai kuma dawo a hayyacinsa ba.
Wani mutumi ne da matarsa sai 'ya'ya biyu wanda duk k'ananan yara ne ke zaune bakin wani madaidaicin d'aki.
Ganin matasa suka yi rik'e da wani wanda baya cikin hayyacinsa. A lokacin duk sun ciccire mask d'in fuskokinsu.
Matar ce ta 'dan murmusa bayan ta ga fuskar wanda ta sani a cikinsu. "Umari ashe ku ne, lafiya dai ko?"
Murmushi Umarin ya miyar mata dashi tare da fad'in "Wannan bawan Allah'n mahaukaci ne, ya tari motarmu bamu ankara ba muka kad'esa. Muna gudun kar sai mun kaishi asibiti ya farfad'o ya nemi tara mana mutane tun da dai hankali bai wadaceshi ba. Shi ne na ce bara na kawoshi nan sai mu 'daureshi, idan ya farfa'do na san zai ta maku sabbatu kar ku sakeshi kar kuma ku tsaya saurarenshi dan zaku b'atawa kanku lokaci ne kawai. Gobe zamu dawo sai mu san abin yi."
Cike da tausayi mijin ya ce "Allah sarki! Su fa dama marasa lafiyar nan akwaisu da tarar motoci kuma ko a jikinsu. Wayyo aikuwa gashi nan jini sai fita ya ke daga kanshi. Amma dan Allah kar ku d'aureshi, ku sakashi a wancan d'akin da babu kowa sai a rufeshi, gani na ke kaman zai cutu idan aka d'aureshi."
Jinjina kai matar ta yi alamar ta aminta da maganar mijin nata.
Wanda aka kira da Umari ya ce "To babu damuwa. Isiya a kaishi can ciki."
Cikin wani d'aki suka shiga da shi, dattin d'akin kanshi abin a duba ne, ga k'ayoyi da abubuwan cutarwa sosai amma a haka suka jefar da Khalid da har yanzu bai farfa'do ba.
Murmushi Isiya ya yi ya ce "Umurni ne daga oganmu, azaba kuwa baka fara shanta ba yanzu zaka fara." Suka fice daga d'akin tare da dosar inda su Umari su ke.
Bankwana suka ma mutanen tare da tafiya suka nufi motocinsu, ta Khalid kuwa cikin gidan gonar suka shiga da ita tare da shaidawa mutanen cewa zasu bar d'aya motarsu a nan saboda ta d'an samu matsala sai sun zo da bakanike.****
Tun da Haidar ya ke a rayuwarsa bai tab'a shiga tashin hankali kamar lokacin da aka sace Feenah da abin da ya sameta ba, sai gashi yanzu yana neman sake shiga wani tashin hankalin saboda tilasta masan da Momy ta yi na cewa lallai sai ya fitar da matar aure. Shi kuwa matan ma basa gabanshi, shi irin abin nan ma wanda maza ke yi idan sun ga mace su d'an kalleta shi baya yi, tsaki ma ya ke idan ya kula da mace ta cika kallonshi da yawa.
Office ya ke zaune amma ya ma kasa aikata komai, har da takarda aka aiko masa wai ana gayyatarshi wani meeting da za'a yi a General Hospital Sokoto, k'arfe goma na safe za'a fara amma har kusan sha d'aya bai iya tashi ya tafi ba.
Wayarshi ce ta d'auki ringing da sauri ya diba mai kiran, koda ya fahimci cewa daga wurin meeting d'in ne ake nemansa sai ma ya kashe wayar tashi duka, saboda ya san ko ya je ba wani abin kirki zai aikata ba, dan halin da ya ke ciki baya jin zai ko iya saurarensu.
Ganin zaman ya yi gashi ba komai ya ke aikatawa ba ya sa ya tashi da niyyar ya nufi gida. "Kar kuma na je ta sake min maganar mace fa." Ya yi d'an guntun tsaki had'e da komawa ya zauna.****
Driving ta ke mai cike da natsuwa a bisa titin Mr. Bigs, wak'arta 'yar kullum ta ke ji ta wait for me tana d'an bi a hankali kamar kullum. Jin wayarta na ringing yasa ta rage k'ara tare da duba mai kiran. Ganin Momy ce yasata murmusawa a hankali ta d'auka tare da yin sallama. Amsawa momy ta yi ta ce "Ikram kin taho ne?"
"Ehh ina ma hanya momy." Ta bata amsa.
"Ok dama aikanki zan yi. Kin san fa tun jiya rabonmu da Khalid kuma ba'a samun wayarshi idan an kira. D'azu da safe da kike tambayata na ce miki may be ko ya dawo da dare ne ya yi fitar sassafe. To bayan tafiyarki na tambayi mai gadi shi ne ya shaida min bai ji zuwan Khalid da dare ba gaskiya, haka kuma bai jishi da safen ba, fitar yayanku kawai ya ji. Hankalina ya d'an fara tashi musamman yanda ba'a samun wayarsa idan an kira. Yayan naku ma na kira tashi d'azu bai d'auka ba. Yanzu kuma dana kira a kashe. Shi ne na ke so ki je min FMC ki sameshi a Office 'dinshi, idan baki san Office 'din ba sai kiyi tambaya kowa kusan ya sanshi. Ki binciko min ko lafiya? Sannan kuma ko yana da masaniyar inda Khalid ya tafi tun jiya bai dawo ba."
Ita kanta Ikram d'in hankalinta ya tashi. Ido bud'e ta ce "To ina Yaa Khalid ya shiga?"
"Nima kaina ban sani ba Ikram. Ki hanzarta zuwa asibitin dan Allah." Momy ta fad'a hankalinta a tashe.
Bayan ta kashe wayar ta fara tunanin yanda zata iya tinkarar wurin aikin babban mak'iyin nata. Sai dai kuma ai lafiyar Khalid ta ke son bincika, babu yanda ta iya dole ta canza hanya zuwa FMC.
Ba wani sanin asibitin ta yi ba, sai da ta tambaya ma sannan aka gwada mata hanyar da zata isar da ita asibitin.
Misalin k'arfe d'aya na rana ta mata can, dama ta san Office 'din tun da ba zata ta'ba mantashi ba ko dan *silar* mutuwar mahaifiyarta da ya yi.
Tsaki ta yi bayan ta paka motar tata ta kashe sannan ta fito, hannunta rik'e da hand bag da makullin mota ta isa bakin office d'in.
Kamar ko yaushe Musa Masinja na zaune a bisa kujerarsa yana saurarar radio.
Sallama Ikram ta masa ya amsa sannan ya ce "Lafiya 'yan mata?"
"Lafiya 'kalau." Ta bashi amsa.
Zare glasses ta yi daga idonta sannan ta ce "Ina son ganin Dr. Aliyu Haidar ne."
Da mamaki ya kalleta ya ce "Ya san da zuwan naki ne?"
"Bai sani ba." Ta fad'a cikin halin ko in kula.
"To ki kirashi a waya ki shaida masa, idan ya bada izinin ki shiga sai ki shiga."
Ita bata ma da lambarshi sai yanzu ta tuna, kuma ma ko tana da ita ai momy ta ce ta kirashi a kashe. "Lambarshi bata shiga. Amma ka ce masa wai Ikram ce, Momy ta aikota wurinshi."
Shiga kuwa ya yi ya masa sallama sai dai bai amsa ba ya yi zurfi a duniyar tunani.
"Yallab'ai ka yi ba'kuwa ne. Ta ce a ce maka wai Ikram ce, momy ta bata sa'ko wurinka. Ta kira lambarka bata shiga."
Sai ma yanzu ya tuna da ya ga missed call d'in momy kafin a kirashi maganar meeting. Guntun tsakin da ya saba ya yi kafin ya ce "Ka ce ta shigo." Ya jawo laptop ya fara rubutu game da meeting d'in da bai samu ya je ba.
Shigowa Ikram ta yi bayan Masinja ya fad'a mata sak'on Haidar.
Babu sallama ta tako ta zauna a kujerar da ke fuskantar tashi. Shi bai d'ago kai ya kalleta ba haka itama bata ce masa komai ba sai chewing gum d'inta da ta ke tauna.
Sai da ya gama typing 'dinshi ya tura masu ta Email sannan ya d'ago fuskarshi da babu annuri a cikinta ya ce "Ke ba'a koya miki sallama ba ne?"
Bata daina cin chewing gum d'in ba ta ce "Sani na yi ko na maka ba amsawa zaka yi ba. Dan ba yanzu aka fara ba."
Bai kalleta ba ya ce "Kuma ki cire chewing gum 'din nan daga bakinki ko na tsittsinka miki mari." Dan dama Haidar ya bala'in tsanar ya ga mace tana cin chewing gum.
"Tab'di! Mari fa ka ce." Ta fad'a tana jinjina kai.
"Ehh mari fa, ko ba zan iya ba?" Ya fad'a har yanzu bai kalleta ba.
"Ni dai ba wannan ya kawoni ba. Momy ce ta aikoni, wai tun jiya Yaa Khalid bai dawo gida ba, kuma tanata kiran lambarsa bata shiga. Kai kuma ta kira baka d'auka ba sai ma ka kashe wayarka a k'arshe. Wai lafiya?"
"Ba'a ganshi ba? To shi yaro ne dan bai dawo gida ba sai an binciki inda ya shiga?" Ya fad'a cikin mamaki.
"To ni dai sak'o ne ta bani kuma na isar. Dan haka sai anjima." Ta mik'e tana ci gaba da taunar chewing gum d'inta.
K'was k'was k'was ta ke taku da takalminta high heel.
"Ke!" Haidar ya fad'a bayan ya mike tsaye.
Tsayawa ta yi cak ba tare da ta waiwayo ba.
"Jira mu tafi tare dama na gama." Ya fad'a bayan ya saka suite d'inshi yana neman d'aukar laptop.
"Nima na zo da motar ai. Kuma point of correction, Ikram sunana ba ke ba." Ta fice daga Office d'in.
Har ta fita ta turo masa k'ofar bai daina binta da kallo ba. Lallai yarinyar nan wuyanta ya isa yanka. Ita har ta isa ta raina masa wayo? Tun da ya ke bai tab'a tsayawa mace tana masa irin yanda Ikram ta ke masa ba. Dole ma ya tasar mata tsaye.***
Ko da ta koma gida ta samu momy ta kasa zaune ta kasa tsaye, ita kanta Baabah Naanah ta yi tagumi tama kasa aikata komai, da mamaki ace Khalid tun jiya baya gida, mutumin da ba cika yawo ya yi ba, kuma ma duk inda zai je sai ya sanar da Momy, kuma ko k'arfe nawa zai kai a waje idan ya dawo sai ya sanar ma momy dawowarshi.
Ganin halin da su ke ciki yasa ta isa inda momy ta ke tsaye, kamata ta yi ta zaunar ta ce "Dan Allah momy ki kwantar da hankalinki. Insha Allahu babu abin da ya faru da Yaya Khalid, zai dawo bada jimawar nan ba."
Kalaman Ikram ya sa momy fitar da hawaye, saurin share mata su Ikram ta yi ta ce "Bana son ganin hawayenki suna fita momy. Ko so kike ki jawa kanki wata cutar?"
Kai kawai ta gyad'a ta ce "Ikram tun da nake da Khalid bai ta'ba fita irin haka ba. Ko da bai sanar dani fitarshi ba to zai kirani a waya ya shaida min. Amma fa tun jiya bai dawo ba. Kuma ba'a samun lambarshi." Ta sake fashewa da wani kukan a daidai shigowar Haidar.
Ganin halin da mutanen uku su ke ciki yasa jikinshi yin sanyi. Taku biyar ya iso dashi gaban Momy da Ikram. Kama hannun momy ya yi yana fad'in "Ba fa wani abu ya sameshi ba na sani. Khalid ai ba yaro bane barin ace ko b'acewa ya yi. Ki daina kuka please." Haidar yana takaicin ya ga mahaifiyarsa tana kuka, sosai hankalinshi ya ke tashi da hakan.
"Dole ne a gareni na yi kuka. Ina Saifullahi ya shiga? Ina ka shiga ka barni Khalid?" Kuka ya ci k'arfinta.
Tuni Ikram ma ta fashe da nata kukan, wannan wane irin tashin hankali ne su ke cikinshi?
Haidar ma da bai yi kukan ba idanuwanshi suka kad'a suka yi jajur! Ganin hakan ba zai zama mafita ba yasa ya ce "Bari na tashi na je Station ko da wani taimako da zasu mana. Daga nan zan je MTN office su bincika mana layinshi, da wa ya yi wayar k'arshe? Kuma a daidai ina ya yita? Wata 'kila zamu samu wani information a kan inda ya ke."
Mik'ewa Momy ta yi ta ce "Mu tafi tare, ba zan iya zama ba tare da na san inda Khalid 'dina ya ke ba."
Fita suka yi har da Ikram da ko mayafinta bata cire ba dama, Baabah Naanah kawai suka bari itama a cikin tata damuwar.***
A hankali ya ke bud'e idonshi sanadiyyar wani irin saaraa da yaji kanshi yana yi.
Sai da ya bud'e idon duka sannan ya fara tariyo abubuwan da suka faru kafin ya fara wannan dogon bacci mai k'unshe da mafarkai kala kala.
Bayan ya gama tunanin ne ya bud'e tas idanuwan ya fara kallon d'akin da ya ke, wata irin k'ura ce ya gani a inda ya ke kwance ga hannunshi duk jini saboda k'ayoyin da suka caccakeshi.
Saurin tashi zaune ya yi yana k'ara bin d'akin da kallo yana tunanin 'me ya kawoni nan? Me na zo yi?'
Salati ya d'auka had'e da neman inda k'ofa ta ke domin ya fita. Jin 'kofar a rufe yasashi bubbugata da k'arfi yana fad'in "Wa ya kawoni nan? Ku zo ku fitar dani, ku bud'e min k'ofa na tafi gidanmu."
A hankali matar gidan ta ke jiyo murya daga d'akin da aka b'oye bak'o kamar yanda suke kiransa da shi. Da hanzari ta isa inda k'ofar ta ke tana fad'in "hannu hard'o, ashe ka tashi."
Jin muryar da bai sani ba yasashi d'an dakatawa ba tare da ya fad'i komai ba. Can kuma ya ce "Ki bud'eni na koma gidanmu."
D'an jaa da baya ta yi tunawa da ance masu shi d'in mahaukaci ne. "Aradu ba zan bud'eka ba ka bubbugeni hard'o. Ance min kai 'din mahaukaci ne."
'Mahaukaci?' Ya nanata a ranshi, bai san sanda hawaye ya fara fito masa ba, wanda rabonshi da zubar da hawaye tun mutuwar k'anwarsa Feenah. Komawa ya yi ya zauna ba tare da ya sake furta komai ba.Team Ikramhaidar
Team Ikraminnocentkhalid
ESTÁS LEYENDO
SHI NE SILAH!
Romanceshi ne silar rugujewar farin cikin rayuwarta. shine silar shigar ta cikin kunci da bakin ciki. shi ne silar rashin gata hadi da galihu a rayuwarta. shin waye silah? ku biyoni a cikin wannan labarin inda zan warware maku zare da abawa.