*SHI NE SILA!*
😪😪😪Na Princess Amrah
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
(2018)_Wannan shafin sadaukarwa ce ga k'awata *Ummie Amumah* a bisa k'aunar da kike gwada min. Ina jin k'aunarki har cikin raina kuma ana tare._
38~ Zaune su ke shi da Jibo sai firar wata yarinya da ya ma ciki ya ke ma Jibo.
Dariya Jibo ya kece da ita ya ce "Kai mugu ne abokina. Wallahi baka da kirki."
Shima Bash dariyar ya yi ya ce "Wasu matan ne basu da hankali. Su dai kud'i kawai." Ya kunna tv da remote d'in hannunsa.
Ganin ana sanarwa yasa ya miyar da hankalinshi ga sanarwar da a ke. Hoton Khalid ya gani wai ana nemansa ya b'ata tun jiya ba'a ganshi ba, idan da wanda ya ke da masaniyar inda ya ke ya garzaya police station mafi kusa da shi, ko kuma ya nema lambobin waya, sai aka karanto lambobin.
Zumbur suka mik'e a tare, Jibo ya ce "Kar dai kai ne abokina?"
*"Ba ni ba ne* sai dai hakan ya min dad'i sosai." Bash osca ya fad'a yana murmushi.
"Ban yarda da kai ba abokina. Dama fa ka ce zaka d'au masa mataki." Jibo ya fad'a har yanzu bai samu damar zama ba.
Cikin halin ko in kula Bash ya ce "Ehh ni na sa a saceshi d'in." Ya koma ya zauna
Gyad'a kai kawai Jibo ya yi yana tir da Allawadai da hali irin na abokinshi, shi dai bai da halin kirki ko kad'an.
Kashe tv'n ya yi yana mai jin haushin Jibo, ko da ya ke ai dan ya san zai iya aikata hakan shisa ya fad'a, amma a zahirin gaskiya duk ba'kin halinshi ba zai iya sace mutum ba, to ya saceshi ya kaishi ina? Shi 'din da ba wani kud'i ne da shi ba sai 'karfin hali, huzzling d'in da ya ke ma duk ga mata su ke k'arewa.
Wannan ke nan.***
Washe gari da sasaafe Khalid ya fara tunanin ta hanyar da zai bi dan ya sanar da momy zai fita, baya son ya fad'a mata exactly abin da zai fiddasu shi da Ikram, ya fi so sai an gama komai sannan su sani, karma ta nemi hanasu ko dan Goggoji.
Ajiyar zuciya ya sauke had'e da yin d'an murmushi bayan ya tuno kalar k'aryar da zai mata. A daidai shigowar Haidar d'akin suka gaisa ya ce "Kai b'atacce ya? Ka tashi lafiya?"
Murmushi Khalid ya yi ya ce "Lafiya k'alau Yaya, wurin aiki zaka je ne?"
"Ehh." Ya bashi amsa a ta'kaice.
"To Allah ya tsare. Yaya dama akwai abin da na ke son fad'a maka amma ba yanzu ba. Insha Allahu anjima da dare idan ka dawo zan fad'a maka komai."
"To Allah ya kaimu. Ba dai a kan aurenka ba ne ko? Dan bana son wannan maganar."
Wani murmushin Khalid ya yi ya ce "Ko kad'an ba a kanta ba ne yaya. Zan fad'a maka d'in dai insha Allahu."
Fita ya yi daga d'akin Khalid biye da shi suka nufi parlor, Ikram da momy suna zaune suna fira, sallana Khalid ya yi ya gaishe da momy, shima Haidar di'n gaisheta ya yi ya ce "Momy ni zan wuce wurin aiki, amma fa yau sai dare zan dawo dan akwai abubuwa da yawa da zan yi, kin san duk week d'in nan ban samu na je ba."
Fara'a 'kunshe a fuskarta ta ce "To Allah ya taimaka. Amma ba zaka tsaya Ikram ta kawo maka abin kari ba?"
Kallon Ikram ya d'an yi kad'an sannan ya kawar da kanshi ya ce "Zan karya a Office." Kawai ya fitarsa daga d'akin.
Kad'a kai kawai momy ta yi ta ce ma Khalid "Saifullahi ya gajiyarka? Kan ya warke ko?"
D'an dafeshi ya yi a hankali ya ce "Wash! Akwai zafi sosai momy. Ina tunanin ko sai na je asibiti dai? A yi x-ray dan kar a je ya shiga har cikin k'walwata."
Ido momy ta zaro had'e da fad'in "kuma fa haka ne. Ka zo ka shirya mu tafi asibitin."
'Dan satar kallon Ikram ya yi itama ta kalleshi dan tuni ta gano inda ya dosa. Da sauri ta ce "Momy ki bari kawai sai mu tafi tare, dama yau ba zan je makaranta ba."
Momy ta ce "To babu damuwa, sai ku kula sosai, ku d'auki wannan motar ta yayanku wadda ya daina hawa tun da dai tana da tint, bana so wani abu ya faru daku."
Kallon juna suka sake yi hade' da sakin murmushi a tare.
"Bari na tashi to na shirya sai mu tafi. Daga can ma sai ka rakani gidan su miemie na dad'e bamu gaisa ba, ita bata zo ba nima kuma ban je ba." Ikram ta fad'a bayan ta mike.
"Lallai kam ya kamata, ni fa dama na so na tambayeki ita, sai kuma wannan tashin hankali da ya zo garemu. Ki hanzarta to, ku samu Yayanku dan ya ce yana da aiki da yawa."
Saurin had'iyar yawu Khalid ya yi ya ce "A'a momy ai ba sai mun je wurinsa ba tun da dai ya ce aiki ya masa yawa, bari kawai sai mu je private hospital yanda ba zamu b'ata lokaci ba sosai."
Na'am ta yi da maganar tasa, Ikram kam tuni ta haye sama domin ta shirya dan dama ta rigada ta yi wankanta.
Shadda ce ta saka gizna hot pink wadda ta sha aikin embroidery blue, bata wani yi make up ba sai dai mac powder data shafa wacce ta yi kamar ta shafa foundation. Lip gloss kawai ta shafa sanaan ta shafa kwalli a idonta dan bata son yawan magana, girman idonta a duk sanda bata shafa kwalli ba yawaita ya ke wanda sanadiyyar haka ke jawo mata yawan magana ga mutane. D'aurin 'dankwali ta yi mai kyau wanda ya k'ara fito da zahirin kyawunta, kallo d'aya zaka mata ka san cewa lallai ta had'a iri da larabawa.
Blue mayafi ta fiddo da hand bag blue sai takalmi pink, turaren cinema ta shafe jikinta dashi sannan ta d'auko wayarta ta sauko daga bene.
Tun daga nesa Khalid ke kallonta ya kasa d'auke idonshi saboda wani irin kyau ya ga ta masa.
Har ta iso wurinsu bai sani ba sai da ya ji ta ce "To na shirya yaya."
Saurin zabura ya yi ya ce "Ko kyau ma baki yi ba."
Gatsine ta masa had'e da fadi'n "Kyau'n ka ga na maka saisa ka tanka."
Da fara'a momy ta ce "Ke rabu dashi 'yata, kin yi kyau sosai shisa ya maganta. Na tabbatar matar da ya ke tutiyar ya tsayar babu abin da ta kaiki."
D'an shiru ya yi bai ce komai ba kafin ya yi k'arfin halin fadi'n "Ni matar da zan aura ta zarceki komai, kyau, gashi, iya kwalliya, taku..." Bai k'arisa ba momy ta ce "Ka tashi ku tafi sai surutu kamar aku."
Mik'ewar ya yi, Ikram kam tuni ta cika ta yi fam, ke nan ma wacce zai aura ta fita had'uwa, 'Ya Salaam!' Ta fad'a a zuciyarta cike da damuwar wannan al'amarin, kamar da wasa wai Khalid ya fitar da matar aure.****
Misalin 'karfe goma saura kwata na safe suka isa kotun, kai tsaye Office 'din Kareema suka wuce, sun sameta zaune tana had'a takardu, bayan sun yi sallama ta basu izinin shiga suka zauna.
"Yanzu kuwa na ke tunanin kiranku. Saura minti sha biyar a shiga." Ta fad'a bayan ta sake duba agogon hannunta.
Fira suka 'dan tab'a har Kareema ke tambayarsa babu wani labari game da wanda suka saceshi? Ya amsa mata da har yanzu dai shiru ne.
Goma saura minti biyu suka tashi, bayan ta had'a komai suka bar office d'in ta rufe.
Wurin shari'a suka nufa kai tsaye, a lokacin dandazon mutane a wurin har sai da su Ikram suka yi mamaki.
Shiga suka yi suka nemi wurin zama, Kareema kuwa ta zauna inda aka tanada domin zaman lauyoyi.
Ba'a jima ba sai ga su Abbas sun iso, Sameerah ri'ke da Goggoji da ke tafiya da k'yar da k'yar kamar wacce k'wai ya fashewa a ciki.
Kallo Khalid ya bisu da shi, gyad'a kai ya yi ya ce "Munafukan banza da wofi!"
Ajiyar zuciya Ikram ta sauke ta ce "Wancan ne saurayin nawa?" Ta nuna Abbas da yatsa had'e da yin dariya.
Shima Khalid dariyar ya yi ya ce "Ehh shi ne fa, Abbas, ba zan tab'a manta wula'kancin da ya ma Abbanmu ba, har da rik'onshi a ke wai sai ya mari Abbanmu."
"Wayyo, amma da alama fa ya nadama, kai ka ga yanayinshi ka'dai ya isa ya tabbatar da hakan." Ikram ta fad'a.
"To Allah ya kyauta dai." Suka yi shiru daga nan sanadiyyar isowar alk'ali.
Nan fa mai gabatar da k'ara ya tashi ya gabatar, Barr. Kareema ta tashi domin zayyane komai da ya faru had'e da kaf hujjojinta bayan an fiddo da su Goggoji.
Ko ka'dan basu musa ba, cike da nadama Goggoji ke kuka tana fad'in "Ha'ki'ka *mun tafka babban kuskure* a baya, duk abin da yarinyar nan ta fa'da gaskiya ne, mu muka sa aka sace Nafeesa sai dai wallahi bamu sa a mata fyad'e ba.." ta 'kara fashewa da kuka.
D'an shiru ya biyo baya a kotun kafin alk'ali ya umurta da a tafi da Sameera a nemo mutanen da suka sa su sace Feenah, tun da dama ita ce asalin samosu. Tsayar da sharia'ar aka yi na awa biyu kafin a dawo da wancan mutanen. Awa biyu cif kuwa sai gashi an dawo dasu, kotu ta sake zama inda alk'ali ya fara bayani kamar haka;
"A bisa dogon nazari na wannan zama da aka yi, kotu ta zartar da hukunci ga masu laifi, wannan samari da aka kamo wanda suka yi wa Nafeesa fyad'e wanda ya yi sanadiyyar mutuwarta, an yanke masu hukuncin 'daurin rai da rai, Sameerah da zainabu kuma wanda *su ne silar* komai, za'a d'auresu tsawon shekaru biyar a gidan yari, kotu ta yi duba da wannan tsohuwa wadda ko tsayuwar kirki bata iyawa, ta yafe mata tare da bata shawara a kan ta yi gaggawar neman yafiya ga Allah, saboda Allahu Gafururraheem ne. Kooootu!" Ya buga gudu had'e da mik'ewa ya fita, kowa ma fitar ya yi banda Goggoji da ta isa inda Khalid ya ke ta rungumeshi sai rusar kuka ta ke, Abbas kuwa tun bayan da aka yanke hukunci ya ke bin Ikram da kallo, hotonta ya gano a wayarshi ya yi zooming sannan ya sake kallon Ikram da ke ta fara'a cike da jin dad'in yau dai burinta ya cika. Tun bayan da Momy ta bata labarin feenah ta d'auki alwashin sai ta cika masu burinta, ko ba komai sun taimaki rayuwarta, sun yi *silar* wanzuwar farin ciki a rayuwarta, banda Haidar da *shi ne silar* rugujewar farin cikinta.
Duk da damuwar da ke ransa ta hukuncin da aka yanke wa mahaifiyarsa bai hanashi takawa ya isa har inda Ikram ta ke ba.
Ko da ta juyo ta kalleshi saurin kawar da kanta ta yi saboda kunyar data kamata na abin da ta masa, shi kuwa kallo ya bita dashi ya ma rasa ta inda zai fara yi mata magana.*team Ikramhaidar*
*team ikramkhalid*
![](https://img.wattpad.com/cover/145187938-288-k711487.jpg)
YOU ARE READING
SHI NE SILAH!
Romanceshi ne silar rugujewar farin cikin rayuwarta. shine silar shigar ta cikin kunci da bakin ciki. shi ne silar rashin gata hadi da galihu a rayuwarta. shin waye silah? ku biyoni a cikin wannan labarin inda zan warware maku zare da abawa.