14

1.1K 84 9
                                    

*SHI NE SILA!*
           😪😪😪

     Na Princess Amrah
              (NWA)
               2018

_Na yi mistake na page number, last page ya kamata ya zama 13 sai na saka 12, ku yi hakuri wannan shi ne 14. Ina fatan kun fahimceni._

14~ Ta zo fita ke nan ta jiyo wasu nurses suna magana, "wai na ji ashe har ma appendix d'in ya fashe mata ko?"
    D'ayar ta ce "ehh haka fa, kuma tun da na ke ban tab'a jin appendix ya fashema wani kuma ya rayu ba. Amma kin ga ita an gama successfully, lallai Allah ya taimaketa."
    "Nima dai haka, da k'yar wai Dr. Ya tattaroshi ya fitar duk ya had'e da sauran hanjinta, ke ni fa in dai ba gani na yi ta tashi ba fa akwai matsala, saboda tana iya yiwuwa sun rigada sun gurb'ata."
   D'ayar ta bud'e baki zata yi magana ke nan suka kula da Ikram da ta yi tsaye tana sauraren duk abin da su ke fad'i. Saurin canza maganar suka yi da fad'in "kin ga an yi aikin baiwar Allah'r can lafiya lau wallahi, Allah dai ya k'ara bata lafita."
    Kai kawai Ikram ta kad'a tare da barin wurin, a ranta tana fad'in "ta Allah ba tasu ba, kuma insha Allahu Ummanta ta warke ke nan, ta rabu da cutar ciwon ciki har abada, sai dai kuma ta ulcer, ita d'in ma kuma zama da yunwa ne ke tasar mata da ita.
    Bayan ta gama abin da zata yi ta dawo wurin Ummanta, ta jima zaune kafin Ummanta ta farka, allura ta saketa hakan yasa ta ringa jin azaba sosai kamar d'inkin da aka mata zai bud'e.
    A rikice Ikram ta ringa k'walawa nurse kira, jin haka ya sa nurse d'in saurin isowa tana fad'in "ta farka ne?"
    "Ehh ta farka sister, cikinta ya ke mata ciwo." Ikram ta bata amsa.
    "Ok, kar ki damu wannan is normal, dama dole ta yishi idan allura ta saketa, bari na sake yi mata wata."
    Ta fara k'ok'arin d'ura ruwan allurar a cikin drip, tana gamawa ba jimawa kuwa wani baccin ya d'auketa.
     Sai da dare sannan aka ce Ikram ta fara bata ruwan zafi, samun ruwan zafin kanshi aiki ya zame mata, sai daga baya fasahar zuwa wurin mai shayi ta fad'o mata, biyan kud'i ta yi aka bata kofi guda sai sugar kad'an, da hanzari ta iso.
    Sai da ya d'an huce sannan ta ringa bata a hankali, dama kuma yunwa ta ci k'arfinta, hakan ya sa ta ji dad'in ruwan zafin sosai da sosai.
    Haka suka ci gaba da zama ana kula da Umma sosai kamar ba asibitin gwamnati ba, dama kuma FMC sun gaji haka, akwai kula sosai.
    Bayan Umma ta cika kwana uku a asibiti ta warware sosai kamar ba ita ba, kamar bata tab'a yin wani ciwo ba, magani kuma tana shanshi cikin tsari da kulawa, ita kanta Ikram yanzu ta samu sassauci a zuciyarta, kallo guda za'a mata a gano tsantsar farin cikin da ta ke cikinshi.
   Kwatsam Ikram na bata abinci wani irin amai ya zo mata, nan fa ta ringa amai sosai har sai da ta harar da komai da ke cikinta, da k'yar ta ke yink'urin aman saboda d'inkin da aka mata.
    Cikin tashin hankali Ikram ta tashi da sauri ta kira nurses, nan fa suka hau bata taimako, amma ina, abin ya ci k'arfinsu, har da wani irin abu ta ke hararwa kamar kayan cikinta.
   A rikice wata nurse ta cewa d'ayar "ki kira Dr. Aliyu Haidar da sauri, shi ya mata aikin gwara ya sani dan ya san abin da zai bata."
    Wayarta ta d'auko kuwa ta latsa kiran Dr. Aliyu, sai da ta kira sau biyar amma bai d'aga ba, "dama na san ba d'auka zai yi ba ai, barin tafi Office d'in kawai, Allah dai yasa yana nan, kin sanshi akwai commitments." Ta fita da sauri Ikram biye da ita.
    Bayan sun isa Office d'in suka tayar da Musa masinja tsaye, ganinsu yasa ya ce "Sister lafiya?"
    "Ba lafiya ba Baba Musa, patient garemu da ke unconcious dole sai Dr. Aliyu ya taimaka mana saboda shi ya mata aikin."
    "Subhanallahi! Kuma gashi bak'o gareshi, amma bari na fad'a masa wata k'ila a dace, kin san halin mutumin nawa."
     Ya shiga ciki. Ya sameshi sai fira ya ke da wani har da dariya da tafa hannu, a ranshi ya ce "oh, ashe Dr. Aliyu Haidar yana dariya." A zahiri kuma ya ce "yallab'ai akwai damuwa."
    "Me ke tafe da kai Musa?" Ya tambayeshu.
    "ka ji yaya Ali wai Musa, babu ko rab'a Baba a sunan?" Ya yi dariya. Shima Dr. Aliyu dariyar yayi kafin ya miyar da kallonshi ga Musa yana jiran amsarsa.
    "Yallab'ai wata Sister ce ta zo, wai akwai patient da ke unconcious, tare take da wata yarinya kuma na gane yarinyar, ita ce wacce ta zo jiyan nan tana rok'onka kama Ummanta aiki."
     Cikin halin ko in kula ya ce "dama na san definitely sai hakan ta faru. Ina zuwa Khalid." Ya mik'e tsaye. Rigarshi ya zira sannan ya d'auki duk abin da ya san zai buk'ata ya fito, gaba ya yi Sister da Ikram suka mara masa baya.
     Ko da suka isa wurin Umma ciwon ya ci tura, amai ya tsaya amma kuma dafe ta ke da cikinta, idonta ya yi jajur kamar zai zazzalo waje tsabar azaba.
    Nan ya hau duddubata,  numfashinta ya fara aunawa ya ga ba daidai ya ke tafiya ba, yana yi yana tsayawa. Da sauri ya zaro wata allura ya mata wadda zata tsayar da ciwon cikin, amma sai tsananta ma da ciwon ya k'ara yi.
     Cikin kuka Ikram ta rik'e hannun Ummanta ta kasa furta komai sai kallonta da ta ke, itama Umman tata kallonta ta ke kafin a hankali ta bud'e baki ta ce "tafiya zan yi Ikram, bana jin zan ci gaba da rayuwa a duniyar nan, ki kula da kanki ki kula da rayuwarki, kar ki damu da wurin da zaki ci gaba da rayuwa, Allah yana tare da ke kuma shi ne gatanki. Tawa ta k'are saura kuma ke, Allah ya miki albarka ya baki miji na gari wanda zai ji k'anki, wanda zai kula da ke, wanda zai baki soyayyar uwa, uba da kuma dangi."
    Sosai Ikram ke kuka kamar ranta zai fita, ta kasa furta komai ta kuma kasa sakin hannun Ummanta. Tun daga nan Umman bata sake furta komai ba sai numfashinta da ke fita sama sama.
    Wani abu Dr. Yasa yana dannar k'irjinta da shi sosai amma ina, ana cikin haka babban likita ya zo, Azara'ilu ke nan mai d'aukar rai, mai warkar da ko wace cuta lokaci d'aya.
     Ajiyar zuciya ta sauke da k'arfi a lokacin da ranta ya gama fita.
     "Appendix idan ya fashe a ciki yana da wuya mutum ya haye, Ummanki Allah ya d'auki rayuwarta ki bita da addu'a." Yana gama fad'in haka ya yi gaba.
    "K'arya kake Dr. Ummana ba zata tab'a tafiya ta barni ba, saboda ita ce gatana bani da kowa sai Allah, na san ba zata tab'a barina cikin rashin galihu ba."
     "Ta riga da ta tafi, wannan surutan naki ba zasu dawo da ita ba." Ya fad'a.
     Rik'e kwalar rigarsa ta yi ta ce "idan har ta mutu to *kai ne sila* kai ka kasheta wallahi kai ne." Ta sakeshi tare da zubewa k'asa.
     Bisa wani benci ta buga kanta hakan yasa kan yaita jini sosai.
    "Sister ku bata taimakon gaugawa, ni zan tafi, k'arfe sha biyu na rana jirginmu zai tashi." Ya yi gaba.
   A daidai fitarsa wannan wanda su ke tare da shi a Office ya shigo.
    "Yaya Haidar inata jiranka na ji shiru kuma Umma ta zo tana Office d'inka tana jiranka." Matashin mai suna Khalid ya fad'a.
     "Wallahi na tsaya dubata ne, ta rasu ma dai daga k'arshe."
    "Innaa lillahi wa innaa ilaihi rajiun! Ta rasu?"
     "Wallahi kuwa, bari na yi sauri na je, kar na makara, ka kaini Airport."
    Yana maganar sam hankalin Khalid baya wurinsa yana kan Ikram da ke kwance cikin jini male male ga nurses tsaye sun kasa tab'uka komai, su kansu tausayin  Ikram su ke yi.
     "Yaya waccan fa da ta ke kwance jini sai malala ya ke daga kanta?" Ya tambayi Dr. Aliyu.
    "D'iyar wadda ta rasun ce, suma ta yi da na fad'a mata mahaifiyarta ta rasu." Ya bashi amsa.
    Wani salatin Khalid ya sake yi kafin ya ce "wayyo Allah! Shi ne kuma Yaya ba zaka tsaya ka kula da ita ba?"
   "Ka cika surutu da yawa Khalid, ka fa san k'arfe sha biyu zan tashi, yanzu duba ka gani k'arfe nawa?"
    "To yaya ka tafi ni dai bari na kira Umma na fad'a mata ta zo wurin yarinyar nan, tun da dai ka ga babu wani babba a tare da ita, ga kuma gawa, dole a bata kulawa saboda ta farka ta fad'i inda za'a kira danginsu a kai gawar kar ta fara wari."
     Gyad'a kai kawai Dr. Ya yi, ya rasa wane irin hali ne d'an uwanshi gareshi, yana da tausayi sosai, kuma ya samo wannan halin ne daga wurin mahaifiyarsu.
     Gaba ya yi sannan Khalid ya bi bayansa, Sisters kuma suka fara k'ok'arin kula da Ikram.
     Koda suka je Office d'in Dr. Aliyu mamanshi na zaune tana jiransa. Ganin halin da Khalid ya ke ciki ta tabbatar da ba lafiya ba, "Saifullahi lafiya na ganka haka?" Ta tambayeshi.
     "Momy wata yarinya ce..." ya bata labarin komai.
     Sosai ta tausaya mata, hakan yasa ta kiran Direbanta ta bashi makullin mota ta ce ya kai Dr. Aliyu Airport, ita kuma idan ta gama abin da ta ke zata tafi a motar Khalid tun da dama Dr. Aliyu a nan ya ke barin motarsa.
    Tafiya suka yi Khalid na gwada mata hanya har suka isa, a kusa da gadon da gawar Ummanta ta ke aka kwantar da ita, nurses sun kasa zaune sun kasa tsaye, jini ake buk'ata urgently saboda ta zubar da jini sosai.
      Ko da Khalid suka iso ciki sun tayar da an d'aurawa Ikram drip, a rud'e ya ce "bata farfad'o ba har yanzu?"
    "Bata farfad'o ba, jini ma ake buk'ata urgently, gashi kuma bamu san wani nasu ba barin a bayar, ko kuma su bayar da kud'i a siya." Wata nurse ta bashi amsa.
      "Waiyo baiwar Allah! To dama basu kawo wani sun ce nasu bane?" Mahaifiyar Khalid ta tambaya.
      "Basu kawo kowa ba kam, though dai muma karb'ar duty'n muka yi bada dad'ewar nan ba, ko daga kalamun matar kafin ta rasu ta nunar kamar basu da kowa, amma dai ban sani ba gaskiya."
     "To ko za'a diba nawa a saka mata? Wane iri ne da ita?" Khalid ya fad'a.
      "Blood 'O' negative ne, mai wuyan samu ma."
     Da sauri ya ce "aikuwa nima irinshi gareni, ko tantama babu ma kuwa irinshi ne da ni."
     "Shi kenan fad'uwa ta zo daidai da zama, yanzu mu je laboratory a yi duk abin da ya dace." Ta tafi, Khalid ma ya bita cike da tausayin Ikram.
        Gawar Ummanta kuwa ganin lokaci na neman k'urewa ya sa aka fitar da ita, mutane da dama suka sallaceta aka kaita k'abarinta, wato gidanta na gaskiya.
     Bayan an sakawa Ikram jinin ma bata farfad'o ba, jin shiru ya sa maman Khalid ta ce "Khalid ka tafi gida, ka fad'awa Nana ta girka abinci mai kyau, wanda mara lafiya zata buk'ata, sannan a kawo duk wani abu da ya dace kar ta tashi da yunwa."
       Khalid bai ce komai ba ya tafi, kamar Ikram na jira ya tafi ta farka, a hankali ta fara bud'e idonta da ya gama kumburewa tsabar kukan da ta sha.
     Cikin hanzari Momy'n Khalid ta ce "laah kin farka? Sannu kin ji? Sannu. Sister!" ta k'wala kira da k'arfi.
     Kallo Ikram ta bita da shi, saboda duk abin da ya faru gani ta ke tamkar a mafarki, kamar zata bud'e ido ta ganta a gaban Ummanta tana mata murmushi.
      Isowar Nurses wurin ya yi daidai da fasa kukan da Ikram ta yi, *"SHI NE SILA!* Wallahi shi ya kashe Ummana, ya cuceni ya ci amanata kuma ba zan tab'a yafe masa ba, na tsaneshi bana k'aunarsa kuma sai Allah ya saka min..." Ta fara k'ok'arin tsige jinin da ake k'ara mata.
       "Me kike k'ok'arin yi ne Ikram? Kar ki cire jinin mana, wannan jinin da ake k'ara miki shi ne rayuwarki, kin san da yanda aka sameshi?  ko kina so ki rasa rayuwar taki ne?"
      "Ina so in rasa rayuwata Sister, mi ye amfanin rayuwata bayan kuma babu Ummana a cikinta? Miye amfaninta Sister?" Ta ringa gyad'a kanta wasu sabbin hawayen suna fita.
    Cikin natsuwa da dattako Momy'n Kahlid ta iso bakin gadon Ikram, zama ta yi a hankali ta fuskanceta sannan ta ce "Ikram" cikin sanyin murya.
    Bata amsa ba sai kallonta da ta mayar gareta tana ci gaba da kukanta.
      "Na san ke musulma ce, kin kuma san cewa imani da k'addara mai kyau da mara kyau yana d'aya daga cikin rukunnan imani, sannan kuma kin san cewa Allah mad'aukakin sarki ya ce; duk kan mai rai mamaci ne. Ko da ciwo ko ba ciwo idan lokacin mutum ya yi dole sai ya tafi. Kukan me ki ke wa mahaifiyarki bayan kuma babu abin da zai yi mata? haba mana Ikram, addu'a ita ya kamata ki yi mata kin ji? Insha Allahu ni zan zame miki uwa, zan zame miki madadinta a rayuwarki."
    Ikram bata san lokacin da ta rungume Momy'n Khalid ba, lokaci guda ta ji ta aminta da ita. Ita ma Momy rungumarta ta yi tana tayata kukan wanda bata san dalilin yinshi ba. Suna a haka ne Khalid ya zo hannunshi rike da kaya, biye da shi kuma wata mata ce wacce ba zata wuce sa'ar Momy ba, ta riko kwando mai dauke da food flasks da plates a cikinsa.

_Ikram da Ummanta sun baku tausayi ko? To kar kuyi kuka please, idan zaku yi kuma ku yi kad'an, dama Maman Abdurrahman ta ce wai na cika saka mutane kuka a novel, kar ku damu, bayan wuya sai dadi in ji hausawa. Ni ma dai na tausayawa rayuwar Ikram, amma kuma bature ya ce *nothing is permanent but change* dan haka komai mai wucewa ne Ikram, wasu zasu ce bani da hankali dama ana yiwa novel kuka ne? To ana yi sosai ma kuwa, dan ko ni na yi wa rayuwar Ummimah kuka a cikin littafin *WATA SHARI'AH* Nagode kwarai masoyana._

@wattpad: PrincessAmrah

SHI NE SILAH!Where stories live. Discover now