*SHI NE SILA!*
😪😪😪Na Princess Amrah
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
(2018)_Ina kuke kawayen albarka RAZ (Rerbee'art sk and Zarah bb), Queen miemie, Ashnur, Stylish amarya, Haneefah Usman, Biebie Isa. Wannan shafin mallakinku ne domin farin ciki da annashuwarku. Ikram na gaisheku lodi lodi._
27~ Fahimtar ce wa da shi momy ta ke ya sa ya taka burki tare da tsayar da motar.
Fitowa Khalid ya yi daga tashi motar ya isa inda Haidar ya ke, ta gefenshi ya je ya ce "Big bro wai momy ta ce ka tafi da su Ikram zata raka k'awarta gida."
Fuska babu annuri ya ce "Taka motar fa?"
"Yaya tawa ta lalace ne, in ba haka ba ka ta'ba ji an ce ka kai Ikram wani wuri?"
Tsaki Haidar ya yi a karo na biyu bai ce komai ba, sai dai tsananin takaici da ya ke ji na umurnin da momy ta bashi.
"Baka ce komai ba yaya, yamma ke yi fa." Khalid ya fad'a yana kallon 'dan uwan nashi mai wuyar sha'ani.
"Allah idan baka kirasu ba zan tafiyata." Ya fad'a a k'ufule.
Da sauri Khalid ya bar wurin tare da komawa inda su Ikram su ke.
"Ku yi sauri kar ya tafiyarsa, kun san hali." Khalid ya fad'a yana murmushi.
Momy ta ce "Manya ke nan, wannan yaya naku akwai miskili." Ta yi murmushi.
Baki Ikram ta tunzuro ta ce "Momy ni dai ba sai na rakasu ba tun da dai Ya Haidar ne kuma na san ba dawowa dani zai yi ba."
"Khalid ka bata kud'in hannunka, ki hau adaidaita ki dawo mana, ya za'ayi Miemie ta tafi ita kad'ai bayan kuma na ce za'a ma Khairat siyayya?"
Ba da son ran Ikram ba ta karb'i ku'di hannun Khalid. Kafin su isa inda motar Haidar ta ke sai da ya masu horn ya fi biyar.
Ko da suka isa tsaye suka yi dan basu san wanda zai zauna gaba ba. Ganin tsayuwar ta yi yawa ya sa Ikram bud'e gaban motar ta zaunar da Khairat ita kuma suka zauna gaba ita da miemie.
Wani irin sanyin dad'i miemie ke ji har cikin zuciyarta. Satar kallonshi kawai ta ke ta side mirror dan dama ita ta zauna daga bayanshi.
Cikin k'arfin hali kamar ba zata yi magana ba ta ce "Zamu biya shop a sai ma Khairat sweets." Bai ce mata ko uffan ba.
Ganin haka ya sa ta sake yi mashi magana ta fad'a masa unguwar su miemie dan bata so ta sake yi mishi wata maganar.
Babban abin da ya basu mamaki shi ne ganin yanda Haidar ke wasa da Khairat kamar ba shi ba. Shi dama haka ya ke, yana son 'kananan yara sosai kuma yana jan su wasa. Dama in dai ba shi da Khalid ko momy ba to baya yi wa kowa dariya sai idan ya had'u da k'ananan yara.
"What is your name?" Ya tambayi Khairat yana mata murmushi.
"Ummul-khair M. Lawal." Ta bashi amsa tare da miyar masa da murmushin, duk da ita ma Khairat ba wani son mutane ne da ita ba.
"Inyee, 'yan mata. Do you want chocolates?" Ya sake tambayarta.
"No." Ta bashi amsa.
"Why?" Haidar ya tambayeta cikin mamaki, saboda ya san yanda k'ananan yara su ke da son chocolates.
"Mamina ta ce I shouldn't collect anything from the stranger."
"Am not a stranger to you. Gidanmu fa kika je Ummul-khair. Ko kina nufin tun da kika je baki ci komai ba?"
Juyawa ta yi ta kalli miemie a bayan mota wadda ke ta dariya ita kad'ai ba tare da ta san tana yi ba.
Shiru ya yi daga nan bai kuma fad:in komai ba har suka isa bakin wata shop.
Parking ya gyara yana k'ok'arin fita Ikram ta mik'a masa kud'i. "Ga kud'in ya Haidar..." bata rufe baki ba ya bud'e motar kawai ya fita ba tare da ya ce mata komai ba.
"Wannan mutumi akwai wuyar sha'ani. Mtsw." Ta buga tsaki.
"Ai kin san kowa da irin halinsa. Shi nashi halin ke nan kar ki ga laifinsa." Miemie ta fad'a har yanzu bata daina murmushi ba.
"Bak'in hali ne kuwa wannan. Allah ni ba zan tab'a iya zama da wancan mutumin ba. Duk wacce ta aureshi kuwa tana cikin matsala, dan sai ya d'aura mata hawan jini."
"Ni wallahi in dai zai aureni ko hawan ruwa ne ma ya d'aura min ba wani abu zan ji ba." Ta fad'a ko a jikinta.
Suna cikin wannan firar ne Haidar ya shigo hannunshi rik'e da wata k'atuwar leda da ya yi wa Khairat shopping.
Shiru suka yi su duka biyun kaman wanda ruwa ya cinye.
Ko da ya shigo motar tadata kawai ya yi ya kama hanyar da Ikram ta kwatanta masa.
Sun yi 'yar tafiya mai tsawo ne ya mik'awa Khairat ledar da ya yo shopping d'in ya ce "Ungo baby Ummul-khair, am not a stranger to you. Ki karb'a ko kuma mu b'ata." Ya ha'de fuska wanda dama aikinshi ke nan, yana da wuya ka ga Haidar ya yi dariya sai da babban dalili.
A d'an tsorace ta kar'bi ledar tana d'an satar kallon miemie. "Thank you Uncle." Ta fad'a tare da rungume ledar tam a jikinta. Dama Ummul-khair ba dai son kayan zak'i ba.
A daidai k'ofar gidan ya paka, bai ce komai ba dama kuma basu yi tsamman zai ce d'in ba.
K'ofar gefenta ta fara k'ok'arin bud'ewa amma ta jita a rufe, tana son yi masa magana amma ta kasa. Da k'yar ta iya fad'in "Yaa Haidar k'ofar a rufe ta ke." Guntun tsaki ya yi had'e da bud'e k'ofar ta zagaya domin bud'ewa Khairat.
Ita ma Ikram bud'e tata ta yi ta fita tana jiran Khairat ta fito su yi bankwana da miemie ta hau adaidaita sahu ta koma gida.
Sun yi tsaye tana jiran a daidaita ta ji horn, ko da ta waiga Haidar ta gani shi bai motsa da motar ba, girman kai kuma ya hanashi yi mata magana.
Banza dashi ta yi bayan ta d'auke kallonta daga gareshi tana taunar chewing gum d'inta.
"Yar rainin hankali. Ji yanda ta ke wani cin chewing gum kamar tsohuwar kilaki." Ya fad'a cike da jin haushinta.
"Ikram kamar fa da ke Yaa Haidar ya ke." Miemie ta fad'a bayan ta d'an saci kallonshi.
"Na sani ai, ke rabu da uban 'yan girman kai, zai ji da shi dan ni dai ba kulashi zan yi ba." Ta fad'a a tsiwace.
Wani horn d'in ya sake yi a karo na biyu amma ko waiwayenshi bata yi ba.
A k'ufule ya tada motar kamar mai shirin tashi sama, yana zuwa daidai inda su ke ya taka burki.
Wani mugun kallo ya watso mata tare da fad'in "Ke bakya ganewa ne?"
Banza ta yi dashi tana dube duben gefenta.
Wani haushi ne ya sake kamashi, da k'yar ya sake fa'din "Ke wai wace irin sakarya ce? Ba da ke na ke ba?"
Sai a wannan karon ta ce "To kaima dai Yaa Haidar dan Allah, 'ke' fa ka ce, ni kuma na ga babu 'ke' a nan, shisa na ke d'an dube dube ko 'ke' d'in ta zo ban sani ba." Ta tab'e bakinta cike da tsana da raini.
Ji ya yi kamar ya faffalla mata mari, sai dai kuma shi bai tab'a ra'ayin duka ba.
Guntun tsaki ya yi wanda iyakarshi a la'b'banshi kawai ya ce "Ina zaki je?"
"Zan koma gida ne." Ta bashi amsa tare da tsayar da adaidaita sahun da ke k'ok'arin gittawa ta bisa titin k'ofar gidan su Khairat.
"Ki shiga ciki ki jirani, ba zan dad'e ba idan an yi magrib in d'aukeki." Ya fad'a, bai ko jira abin da zata fa'di ba ya tayar da motarshi ya k'ara gaba.
Cike da mamaki ta bi bayan motar da kallo, wai yau ita ce Ya Haidar ya ke wa maganar kirki, wannan bai tab'a shiga tsakaninsu ba. Ko sanda ya ke fad'a mata rasuwar ummanta ba wani da mutunci ya fad'a ba.
"Mu shiga ciki to, tun da dai ya ce zai dawo d'aukarki." Miemie ta fad'a tare da nufar mai adaidaita sahun domin ta bashi hak'uri.
"Ni kam da kin barni na tafiyata miemie, ko dan in bak'antawa wannan uban 'yan girman kan." Ikram ta fad'a.
"A'a ba za'ayi haka ba. Mu je ki jirashi, kin ga magrib ma ta kusa sai ki yi sallarki kawai kafin ya zo d'aukarki."
Nufar hanyar gidan suka yi su biyu, Khairat kam dama tuni ta shige gida tun isowarsu k'ofar gidan.
Sosai Yaya Kareema ta yi farin ciki da ganin Ikram, bayan sun gaisa ne suka nufi yin salla.
Gama sallar suka koma parlor inda Kareema ke zaune tana duba wasu takardu.
"Yaya Kareema aiki a ke ke nan?" Ikram ta tambayeta bayan ta zauna kusa da ita tana d'an dudduba takardun.
"Wallahi kuwa Ikram, kin san yanayin aikin namu. Yanzu haka wani case na ke mai tsananin d'aure kai. Wata yarinya ce ta kawo k'arar matar ubanta a kan tana takurata, to ita matar uban sai ta ke nunar da wai yarinyar ma tare ta ke da baban nata, ta ta'ba kamasu kwance suna aikata alfasha."
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Yaya Kareema ashe irin wannan abubuwan suna faruwa da gaske." Ikram ta fad'a cike da mamaki.
"Suna faruwa sosai ma kuwa Ikram, sai idan kina zuwa kotu zaki tabbatar da hakan. Amma yanzu wannan fa ba wai tabbatarwa aka yi da hakan ba, muna kan bincike ne wai, kin san ko k'azafi matar uban zata iya yi wa yarinyar tun da dai ta tsaneta dama."
"Haka ne kam. Tou Allah ya kyauta...yauwa, ni kam Yaya Kareema wai kuna yawan had'uwa da irin cases 'din nan na fya'de kuwa?" Ta tambayeta bayan ta ajiye takardun ta miyar da hankalinta ga Kareema.
D'ago kanta ta yi ta ce "Ana samu kuwa sosai ma Ikram. Ai yanzu kusan ma abin da ya fi komai yawa ke nan. Har k'ananan yara yima fyad'e a ke. Kwanaki ma mun yi wani case na wata yarinya, wai uwarta ta rabu da baban yarinyar lokacin tana da cikin yarinyar bata haifeta ba, bayan ta haihu ne ta auri wani mutumi kuma ya ce ya yarda zai rik'e yarinyar har iya rayuwarshi. Wallahi Ikram watan yarinyar nan bakwai mijin uwar tata ya mata fyad'e, fita ta yi ta bar gidan ta bar yarinyar da mijin nata, har da diaper a jikin yarinyar amma babu imani bawan Allah'n nan ya cire ya aikata b'arna da ita. Saurin barin gidan mutumin ya yi, yana fita sai ga yayan yarinyar wanda suke uwa d'aya uba d'aya ya zo, ganin yarinyar male male cikin jini ya tayar mashi da hankali. A rikice ya d'auketa yana kuka sosai, suna cikin wannan halin ne uwar ta dawo. Ta shiga tsananin tashin hankali, ta ce kuma yayan yarinyar shi ya mata fyad'e, babu kalar rantsuwar da bai mata ba a kan a haka ya tayar da ita amma ta k'i yarda. Tana kuka sosai suka nufi asibiti. An dudduba yarinyar sosai har aka kwantar dasu, a lokacin ni kuma aka kawo min case d'in, baban yaron ne ya shigar a kan cewa an yi wa yaronshi k'azafin fyad'e. Sai da muka yi zama kotu sau uku kafin gaskiya ta bayyana, ashe wani mak'wafcinsu ya zo gittawa ya d'an ringa jiyo kukan yarinyar, koda ya lek'o ya samu mutumin yana aikata d'anyen aiki. Sauri ya yi ya bar gidan, tsabar tashin hankalin da ya shiga ko abinci bai iya ci ba a gida. Washe gari shi kuma aka aiko masa da sak'on mutuwar mahaifinshi shi ne ya tafi. To ta hanyar dai wannan mutumi ne aka gane gaskiya. Har yanzu mijin matar yana d'aure ba'a yanke masa hukunci ba har sai yarinyar ta yi shekara goma sha takwas an sake auna lafiyarta sannan a san kalar hukuncin da za'a yanke masa, idan kuma kafin nan ya mutu to shi kenan." (Wannan labarin da na kawo na fyad'en da gaske ne.)
Ko da Kareema ta gama ba Ikram wannan labarin sosai jikinta ya yi sanyi sai hawayen tausayi ta ke.
"Ki daina kuka Ikram, in dai kotu ne dama ai baki gama ji ba. Wani abin wallahi sai kin rasa ta hanyar da zaki b'ullo masa, amma idan kin ri'ki gaskiyarki zaki ga komai ya zo da sauk'i. Allah dai ya kyauta kawai."
"Amin yaya Kareema, labarin nan sai ya tuno min na Feenah k'anwar su Ya Khalid, ita mutuwa ma ta yi kuma har yanzu ba'a gano wanda suka mata aika aikan ba, asali dai da niyyar kidnapping ne suka nemi kud'i har miliyan tamanin, bayan an kai masu kud'in suka jefota a cikin wani yanayi, take yarinyar ta rasu. Tana 'yar shekara sha bakwai ne abin ya faru."
"Allah sarki! To kuma basu d'auki wani mataki ba?" Kareema ta tambayeta.
Ikram bata kai ga bata amsa ba sai ga mai gadi ya shigo ya ce "Wai wani mutumi mai mota ya ce Ikram ta zo."
Tashi Ikram ta yi ta ce "To bari na tafi Yaa Kareema, ma k'arisa maganar ko ba yanzu ba. Yaa Haidar ne masifaffe na san da zarar na b:ata lokaci zan sha masifa."
Yafa mayafinta ta yi ta tafi, Miemie da ke ma Khairat karatu sai bankwana kawai suka yi Ikram ta ce ta yafe mata ba sai ta rakata ba.
Fita ta yi ta sameshi ko kashe mota bai yi ba yana zaman jiran fitowarta.
Zuciyarta cike da sa'ke sak'e ta bud'e bayan mota zata shiga. Duk da baya son ta miyar da shi driver girman kai bai barshi ya ce mata ta dawo gaba ba kawai ya tayar da motar suka nufi hanyar gida._Godiya ga d'umbin masoyana na nesa da na kusa. Hak'ika baki ba zai furta yanda kuke a birnin zuciyata ba, sai dai ina son ku sani cewa har kullum k'aunarku na cikin zuciyata. Ku ajiye a ranku cewa Amrah na masifar kaunarku a duk inda kuke._
YOU ARE READING
SHI NE SILAH!
Romanceshi ne silar rugujewar farin cikin rayuwarta. shine silar shigar ta cikin kunci da bakin ciki. shi ne silar rashin gata hadi da galihu a rayuwarta. shin waye silah? ku biyoni a cikin wannan labarin inda zan warware maku zare da abawa.