shi ne sila page 2

1.7K 127 2
                                    

*SHI NE SILA!*
       😪😪😪

Na Princess Amrah
        ®NWA
            2018

2~Ikram bata farka ba sai da sallan azahar Ummanta ta tashe ta. Da kyar ta iya bude idonta saboda kumburin da suka yi tsabar kukan da ta sha. Sunan Allah ta ambata hade da yin mika ta tashi zaune.
    "Ki tashi ki yi sallah har biyu ta wuce ki fara haramar zuwa tahfiz tun da dai kin ji saukin zazzabin." Ummanta ta fada.
     Ajiyar zuciya Ikram ta sauke kafin ta ce "Ummah kaina yana min ciwo sosai, ga shi kuma da kyar na ke iya bude idona, ban sani ba ko ciwo ya ke min."
     Cikin tausayi umma ta ce "kukan da kika yi ne Ikram, ki yi sallah sai ki koma ki kwanta, na san kafin ki tashi kan ya daina ciwo, idon ma kuma zai saki."
     Mikewa tsaye ta yi tana kokarin fita kuma ta juyo ta ce "Umma kin samo min abinci? Yunwa na ke ji sosai wallahi."
    Da fara'a kunshe a fuskarta ta ce "ni na isa in k'i samar wa 'yar Umma abinci bayan kuma na san tun jiya da rana rabonki da ki ci wani abu? Ki yi sallah zan kawo miki ki ci ki koshi kin ji?"
    "Allah sarki Ummana, ina matuk'ar kaunarki. Allah ya bar min ke." Ta fada cike da soyayyar mahaifiyarta. Fita ta yi daga dakin ta nufi ban daki domin dauro alwalar sallar azahar.
    Umma kuwa zancen zuci ta hau yi "to ni yanzu da na ma Ikram karyar na sama mata abinci alhalin kuma ban samo mata ba ya zanyi? Dole na samu mafita kafin ta gama sallah." Ta tashi ta fita sai tufka da warwara ta ke.
    (Allah sarki! Wani abu sai uwa, kamar yanda iyayenmu su ke kokarin faranta mana Ya Allah ka bamu ikon kamanta kyautata masu.)
     Wata dabara ce ta fado mata, ta shiga dakin Goggo Indo ta sameta zaune ta yi bakuwa suna fira. Bayan ta gaishe da bakuwar ne ta ce "Goggo na gama girkin tun dazu."
    "To ai na sani tun da har ma na ci nawa."
     Shiru ya biyo baya kafin ta yi karfin halin ce wa "baki fitar min da nawa ba to."
    Cike da kosawa da maganar Goggo ta ce "sai ki tashi mu je na zuba miki ai, kuma ban ce ki ba wannan mai sifar magunan abincina ba."
   Umma ta ce "dama ba zan bata ba ai Goggo."
    Fita ta yi Goggo ta mara mata baya, kai tsaye madafa suka je ta zuba mata abinci dan kadan a wani kwano sannan ta ce "saura kuma dan kin ga na yi bakuwa ki ba Ikram abinci na."
   Ba ta ce mata komai ba ta nufi dakinta a daidai gama sallar Ikram.
     Da murmushi kunshe a fuskarta ta shiga dakin ta ajiye abincin a gaban Ikram, "Ikram 'yata ga abincinki nan, a ci a koshi kuma ban ce a rage ko kadan ba."
    Murmushi Ikram din ma ta yi ta ce "Umma ke nan, wannan ai daidai cikina ne, kar ki damu ba zan rage ko guntu ba." Ta fara kokarin cin abincin.
     Da sauri da sauri ta ke ci saboda yunwa ta ke ji sosai, Umma kuwa ta tsura mata ido cike da tausayin 'yarta. Ga wata irin yunwa da ta ke ji, amma ta gwammaci ta hana kanta dan ta ciyar da 'yarta. Bata san lokacin da hawaye ya fara kwaranya daga idonta ba, bayan ta ankara ne ta yi gaggawar shareshi dan bata son tana tayarwa Ikram da hankali.
      Sai da ta cinye abincin tas sannan ta yi hamdala ga Allah, ga Ummanta ta juya ta ce "na gode kwarai Ummah, Allah ya saka miki da alkhairi, kamar yanda na ci abincin nan na ji dadi ke ma Allah ya kawo miki farin ciki a rayuwarki, Allah ya gusar miki da duk wata damuwa da ta ke addabarki."
    "Ameen, 'yata 'yar albarka. Allah ya baki miji na gari ya gwada min ranar aurenki."
    Kunya ta ji sosai hakan ya sa ta sunkuyar da kanta kasa tana kokarin daukar kwanon abincin domin ta fitar da shi.
   Gudun kar Goggo Indo ta gane ce wa Ikram ce ta ci abincin ya sa Umma saurin karbar kwanon ta fita da shi. Ikram kuwa gyara dakin ta yi sannan ta sake hayewa katifa ta kwanta.
     Da dare Ikram ta dauko Qur'aninta tana tilawa, kasantuwar ta yi kwana biyu bata je islamiya ba ta san an wuceta da yawa. A hankali ta ke jiyo nishin Ummah sama-sama alhalin kuma ta san tun dazu ta yi bacci. Aje Qur'anin ta yi da gaggawa ta juyo bakin katifar, ganin Umma rike da ciki sai cizon labba ta ke ya sata fadin "ummah lafiya? Me ya sameki?"
     Da kyar ta iya fadin "babu abin da ya sameni Ikram, ci gaba da karatunki." Ta kirkiro murmushi.
    "Kamar ya babu abin da ya sameki Ummah? Cikinki fa kika rike, dan Allah ki fada min gaskiya."
     "Ikram ba wani abu ba ne, cikina ne ya ke min ciwo amma ba sosai ba, ci gaba da karatunki insha Allahu na san zai daina ba da dadewa ba."
    Ba wai dan Ikram ta yarda da maganar Ummanta ta koma kan sallaya ta ci gaba da karatunta.
    Bayan kamar minti sha biyar ta kuma jin nishin Ummah, wannan karen ma har da alamar kuka amma ba da karfi ba.
    "Sadakallahul azeem." Ta fada tare da rufe Qur'anin.
     "Umma wallahi baki da lafiya, dan Allah ki fada min, me sameki?" Ta fada a razane ganin Ummanta na kuka hawaye sai ambaliya suke daga idonta.
     "Cikina ciwo ya ke Ikram, kirjina kamar zai tsage, ban taba irin wannan ciwon ba, ji na ke kamar zan mutu."
   "Ya salaam! Ummah dan Allah ki daina kukan, bana son ganin hawayenki, sannu, insha Allahu za ki samu lafiya."
     Kai kawai ta dagawa Ikram saboda ita kadai ta san abin da ta ke ji.
     "Umma na san ko na fadawa Goggo Indo ba lallai ba ne ta zo, ga shi kuma Mallam bai dawo ba sai jibi zai dawo wai, barin je chemist din Rabe idan bai rufe ba ya zo ya dubaki." Ta fice da sauri ko mayafi bata dauka ba.
      A rashin sa'a ta je chemist din, ya rufe har ya shiga gidanshi saboda sanyi da ake yi. Tsaye ta yi ta ma rasa yanda zata yi. Fasahar shiga gidanshi ce ta fado mata hakan ya sa ta burma cikin gidan, ko sallama ba ta yi ba sai dai ta shiga tsakiyar gidan.
     "Dan Allah Mallam Rabe na nan?" Ta fada cikin shesshekar gudu.
     "Lafiya, wa ke nemansa?" Matarsa ta fada da buta rike a hannunta.
     "Mahaifiyata ce ba lafiya shi ne na ce ko zai taimaka mu je tare ya dubata."
    "Wacece ne wai?" Matar ta tambayeta.
     "Ikram ce, Ikram ta wurin Umma Rumana." Ta bata amsa cike da kagara Mallam Rabe ya fito.
     "Ikram? Au! Wato har gida  ki ke biyo min miji ko? To ba ki isa ba! Dama sarai na samu labarinki daga wurin mutane da yawa, na ji yanda kike wa mata kwacen mazajensu, 'yan mata kuma kike kwace masu samarinsu. Gaske dai Rabe ya ke min maganarki, dama ban yarda da shi ba dan yanda na ji ya nace akan wai yana tausayinki ke da uwarki. Idan kin yi wa wasu kin ci riba ni kam asara zaki yi. Ki fice min daga gida ko kuma in babballaki."
     Kuka Ikram ta fasa da karfi tana fadin "dan Allah ki yi hakuri, wallahi ba kwacenshi zan miki ba, ummana na kwance rai hannun Allah tana fama da ciwon ciki."
     Tana gama fadin haka Rabe ya fito daga daki. "Lafiya dai na ke jin maganganu Larai? Ke da waye a cikin daren nan?"
     Kamar tana jiranshi ta ce "ni da munafukar nan ne ko kuma in ce shegiya mara asali. Asirinku ya tonu daga kai har ita, ka fada mata ta fice min daga gida tun ban fitar da ita ba."
      Hankali tashe ya ce "Ikram me ya faru kika zo a cikin daren nan?"
     "Mallam Ummana ce bata da lafiya, ina tunanin ko asumarta ce ta tashi, amma kuma na ga har da rikon cikinta ta ke ta ce wai yana mata ciwo, shi ne na zo ka taimaka ka bini dan ka ganta da kanka ko da wani magani da za'a bata."
     "Allah sarki! Mu je to" ya fada cike da tausayi.
     "Ku je ina? Ai wallahi ba ka isa ba! Babu inda zaka je in dai ina raye."
     Babu yanda bai yi da ita ba amma ta hana, sai ma rantsewa da tayi akan in har ya fita to ta gama aurenshi.
      Babu yanda ya iya ya ce wa Ikram "ki dauketa ki kaita asibiti su bata taimakon gaggawa, ki yi hakuri kinji? Allah ya sa rashin zuwan nawa ya fi zama alkhairi."
      Ko ameen bata ce ba a tsiwace ta ce wa matar Mallam Rabe "kin samu yanda ki ke so, kuma ki sani, wallahi in har ummana ta mutu ke ma sai kin bita." Ta share hawayenta ta fita abinta.

SHI NE SILAH!Où les histoires vivent. Découvrez maintenant