*SHI NE SILA!*
😪😪😪Na Princess Amrah
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
(2018)*A yi hak'uri na rashin ji na kwana biyu, hakan ya faru ne bisa wasu dalilai manya, amma insha Allahu zaku ringa jina akai akai, ba wai kullum ba kamar yanda na ke yi a baya. Na gode k'warai ga wanda suka nuna damuwarsu a kaina, wanda suka kirani a waya, wanda suka bini ta private chart da kuma wanda basu samu damar yi min magana ba nagode k'warai da k'aunarku a gareni, Amrah na sonku lodi lodi. Allah ya bar zumunci amin.*
19~ Sai da Ikram ta yi kuka sosai sanda su Momy zasu tafi. Ganin bata da yanda zata yi yasa ta hak'ura ta daina kukan har suka dawo daga rakiyarsu.
A daidai isowarsu Hajia Hinde ta kira wata metron, "Ga bak'uwa nan, a kaita block na SS2 Amrah house ke nan, a shaida masu cewa bak'uwa ce, gobe zata fara zuwa classes, sai a had'ata da captain ta block d'in, a samo kamar d'alibai hud'u ko biyar su kwashe mata kayanta. Amma fa a kula sosai Salame, kin san halin d'alibai."
Fara'a k'unshe a fuskar Salame ta ce "To insha Allahu yanda kika ce a yi haka za'a yi ranki ya dad'e." Ta kalli Ikram "Mu tafi 'yan mata, ya sunanki?"
"Sunana Ikram" Ta bata amsa.
Gaba ta yi Ikram ta mara mata baya goye da jakar makarantarta.
Hostel suka nufa kai tsaye, akwai tazara daga Staff q. Zuwa hostel d'in, hakan yasa suka d'an jima kafin su isa. Sosai Ikram ke bin makarantar da kallo, gini ne irin na zamani kamar ba ginin makaranta ba, ya tsaru iya tsaruwa, an kashe kud'i sosai a ginin.
Isarsu hostel Ikram ta sake bin ginin da kallo. A gaban hostel d'in an rubuta *NAGARTA HOSTEL.* Daga ciki kuma gini ne guda shida ko wane ginin bene ne hawa uku. Na farkon an rubuta JSS1 *(Zarah House),* na kusa da shi kuma JSS2 *(Rerbee'art House),* mai bi mishi kuma JSS3 *(Ashnur House),* su ne suke jere na JS. D'ayan side d'in kuma aka rubuta SS1 *(Queen miemie)* a na farkon, na biyu kuma SS2 *(Amrah House),* na k'arshen kuma SS3 *(Hauwa Nayaya).*
Tsayawa da kallon ta yi kafin Salame ta ce "Mu tafi mana Ikram, sai magana na ke miki ko baki ji bane?"
Bata ce komai ba ta ci gaba da binta har suka isa bakin Amrah house, shiga suka yi, second floor suka nufa inda metron d'in d'akin ta ke. Bayan sun gaisa Salame ta ce "Ga bak'uwa nan Indo, PC ce ta ce a kawota, kuma a had'ani da d'alibai su d'auko mata kaya. Wane d'aki ne bai cika ba?"
Murmushi Indo ta yi ta ce "Ai dama Salame na san ba'a ganinki d'akin nan sai da dalili. Ku nufi 3rd floor, room 45 shi ne bai cika ba, ina ji mutum biyu ne ko uku a ciki."
Sake hawa wani benen suka yi, daidai gaban room d'in da aka fad'a masu suka isa, a bud'e ya ke hakan ya basu damar shigewa ciki. 'Yan mata ne su biyar, biyu suna bacci ko wace a kan gadonta, ukun kuma a kan gado d'aya su ke suna ta fira suna shewa.
Sallamar da Salame ta yi ya sa su yin shiru tare da amsa sallamar suna kallon su Ikram.
"Ku nawa ne asalin 'yan d'akin nan?" Ta tambayesu, saboda rashin gaisheta da suka yi sam bai dameta ba, dan ta san halin d'aliban makarantar ba wani isasshen tarbiyya ne da su ba.
"Mu uku ne, wa innan bak'i ne na yi." Wata daga cikinsu ta bata amsa.
"Ok, ke nan akwai gado biyu wanda babu mai shi ko?"
"Ehh." Ta fad'a tana yatsina.
"To ga bak'uwa nan, sunanta Ikram Mahmoud. Yau aka kawota, PC ce ta ce a kawota nan, kuma ku kula, bata son jin wani k'orafi a kanku."
Wadda ke d'ayan gadon mai bacci dan tun shigowar su Ikram ta farka, da sauri ta sauko daga kan gadon ta rungumi Ikram tana fad'in "Oyoyo oyoyo, sannu da zuwa k'awata, sannu Ikram, sunanki mai dad'i."
Kallonta Ikram ta tsaya yi, ita dai ta san bata ko tab'a ganinta ba, amma tana mata magana kamar ta santa, ko da yake, dama haka wasu mutanen su ke, suna da son mutane sosai. "Sannu fa, nagode, nice to muti you." Ta fad'a dan ta tab'a ji Khalid ya fad'awa wani haka, a tunaninta ko hakan da ta fad'i shima haka ya ce.
Da k'arfi 'yan matan nan guda uku suka d'auki shewa suna dariya sosai, d'aya na nuna d'aya suna fad'in "wai nace to muti you. Shams kin iya turanci." Suka sake fashewa da wata dariyar.
D'aure fuska wadda ta tashi baccin ta yi, "Sholie miye haka? Baki da kirki wallahi. Mtsw." Ta yi tsaki tare da cewa Ikram "Ki yi hak'uri k'awata, haka su ke dama."
Murmushi Ikram ta yi ta ce "Babu komai." A ranta kuwa tunanin yanda zata zauna da wa innan 'yan rainin wayon mutanen ta ke.
Cikin rashin jin dad'in abin da ya faru Salame ta ce "Bari na tafi Ikram, za'a kawo miki kayanki yanzu. Sai kin kula da kyau kin kuma kai zuciyarki nesa." Ta fita daga d'akin.
Shewa wannan 'yan matan suka kuma d'auka a karo na biyu kafin suka koma bakin gado suka ci gaba da firarsu daga inda suka tsaya.
D'aya mai kirkin ta ce wa Ikram "Kin ga gadaje guda biyu su ne empty, ga wani can nesa ga kuma wancan na kusa da nawa, sai ki zab'a wanda kike so."
D'ayan ta kalla ta ga kusa ya ke da na Sholie, hakan yasa ta ce "Bara na zab'i na kusa da naki d'in." Ta mata murmushi.
"To ba damuwa, mu je a karb'o bed sheet d'in wurin Baabah Indo." Ta kama hanyar fita Ikram ta mara mata baya.
Bayan sun karb'o a second floor suka dawo ciki, a lokacin har d'ayar ta tashi daga bacci tana k'ok'arin dama madara.
"Miemie kin tashi ke nan."
"Wallahi kuwa na tashi Smart. Ya wannan fa? Ko bak'uwa muka yi?" Ta fad'a tare da kallon Ikram.
"Wallahi kuwa bak'uwa muka yi, yau aka kawota sunanta Ikram. Ikram wannan ma a nan d'akin ta ke, Halimatu sunanta amma smart muke kiranta da shi."
Murmushi Ikram ta mata tare da mik'a mata hannu suka gaisa. Itama smart hannun ta mik'o mata cike da fara'a ta ce "Sannunki da zuwa Ikram, sunanki mai dad'i."
A daidai nan Salame ta shigo da kayakin Ikram, seti guda na akwati da kuma wasu jikkunan kuma. Ajiyesu wanda suka d'auko kayan suka yi sannan suka fita, Salame ta ce "Sai su taimaka miki ki jera kayanki a wardrobe, akwatinan kuma ki d'orasu sama idan kin fitar da kayan. Ga makullin wardrobe d'in na karb'o miki." Ta mik'a mata. "Na ce a bani bedsheet wai kin karb'a."
"Ehh, Miemie ta rakani mun karb'o." Ta bata amsa.
"To yayi kyau, dan Allah Miemie ki mata bayani sosai a kan makarantar da yanda zata zauna da mutane, saboda bata tab'a yin makrantar kwana ba"
"Insha Allahu kuwa Baabah Salame yanzu zan mata bayanin komai."
"Abu yayi kyau. Bara na tafi ni, Ikram sai na sake zagayowa."
"Nagode k'warai, Allah ya saka miki da alkhairi."
"Amin." Salame ta fad'a had'e da barin d'akin.
Kayakin suka hau jerawa a cikin wardrobe, da taimakon miemie da smart nan da nan suka kammala komai, sholie da k'awayenta kuwa tuni suka bar d'akin cike da takaicin Ikram, haka kawai suka ji bata cikin tsarinsu, dan da alama bak'auya ce, tambayar da suke yi wa junansu shine wai ma ya akayi Ikram ta zo wannan makrantar wadda yaran masu kud'i kawai ke cikinta? Rashin samun amsar yasasu shiru da maganar tare da ci gaba da uzurin gabansu.
Bayan sun gama had'a kaya duka aka fara ringing evening prep, gajiyar had'a kaya da suka yi yasa su k'in zuwa prep d'in, ko da captain d'insu ta zo bayanin abin da ya faru suka mata, kasantuwar ta san da zuwan Ikram Salame ta mata bayani yasa bata tirsasasu sai sun tafi ba.
Wanka Ikram ta yi sannan ta fito d'aure da towel, yalwataccen gashin kanta ne ya bazu a bisa bayanta. Baki smart ta rik'e cike da mamaki ta ce "Na shiga uku! Ikram duk gashinki ne wannan?"
Ikram bata bata amsa ba sai murmushi da ta mata.
"Tun da na ke a rayuwata ban tab'a ganin irin wannan gashin a zahiri ba sai dai ko a kallo. Tubarakallah masha Allah, Allahumma arzuk'ni." Miemie ta fad'a tana murmushi.
Ita dai Ikram fara'a kawai ta ke masu, bayan ta zauna tana shafa mai ne Smart ta ce "Ikram zan baki shawarwari a kan yanda zaki yi rayuwa a makarantar nan. Kin ga dai yanda makarantar ta ke ba sai na fad'a miki ba. Saboda haka sai kin zabure, makaranta ce wadda kowa take da 'yancin kanta, dan haka kema sai kin zama mai 'yancin kanki sannan zaki k'waci kanki daga rainin d'alibai." Shiru ta yi sannan ta ci gaba da "Yanda kika ga muna yi dole kema haka zaki yi, idan ba haka ba kuma wallahi sai kin raina kanki, sai kin ji kin tsani makarantar, amma da zarar kika nuna kema wayayyiya ce, to sai ki zama 'yar lele a idon kowa, barin yanda kike da kyau da gashi, babu wanda zai rainaki ta nan. Kin ganni nan?" Ta nuna kanta, "Wallahi wani lokacin har bana so a yi hutu tsabar son makrantar, sai dai kawai na san kewar gida dole ce." Ta yi shiru daga nan.
Miemie ta d'ora da "Yanda kika ma Sholie d'azu wallahi in har kika ci gaba da haka to ba zaki tabca jin dad'in zaman d'akin nan ba, duk da kike ganin mu mun d'aukeki da daraja. Saboda Sholie da kike gani ta gagari kowa sai mu ne bata gagara ba, hatta da teachers shakkunta suke, prefects kuwa wasu sai yanda ta yi dasu, saboda babanta shi ne mataimakin gwamnan jihar nan (Kebbi), saisa ta ke taka kowa yanda ta ga dama, k'awaye kuwa kullum cikin canzasu ta ke, kuma duk na banza babu na kirki. Dan haka ki zabure kema, muma kuma zamu taimaka miki da yardar Allah."
Godiya Ikram ta masu, tare da d'aukar aniyar ba zata tab'a bari Sholie ta rainata ba, saboda itama fa ba kanwar lasa ba ce, kawai dai ta yi sanyi ne tun rasuwar Ummanta.
Washe gari kiran farko aka fara busa usur, hakan ya sa Ikram zumbur ta tashi tare da kunna wutar da ke sama da gadonta, a lokacin Smart ma ta farka tana k'ok'arin saukowa daga kan gado. Tashin miemie suka yi suka k'yale sholie, sanin ko sun tasheta ba tashi yin sallah zata yi ba dan dama ba damunta ta yi ba.
Kai tsaye alwala suka gabatar sannan suka nufi masallaci, Ikram dai ganin abin ta ke kamar da wasa, rayuwar boarding school wadda bata tab'a sakawa ranta yi ba.
Bayan sun baro masallaci suka hau shirin tafiya school area, da taimakon su smart Ikram ta shirya, sosai uniforam d'in suka karb'i jikinta, ita kanta ta san ta yi kyau. Powder da lip stick kawai ta saka kamar yanda su smart suka fad'a mata ana yi, zira hijabinta ta yi suna k'ok'arin fita sholie ta tashi.
"Wai miemie har time ya yi ashe?" Ta tambayi miemie.
"Yo to ke zai tsaya jira? See this mumu." Smart ta fad'a.
"Ni fa ba ke na tambaya ba daallah malama, baku da kirki da baku tasheni ba." Basu kuma kulata ba sai fita da suka yi, Ikram kam ko kallo sholie bata isheta ba, saboda ta d'auki hud'ubar su smart sosai.
K'arfe bakwai da rabi suka isa school area, class suka zarce kai tsaye, irin kujerun nan ne na zaman mutum d'aya, form master d'insu suka ma bayanin Ikram, da kanshi ya d'auko mata kujera ya kawo kusa da miemie dan dama miemie ita ce gaba, to yanzu sai ta dawo ta biyu Ikram kuma ta dawo ta farko. Sai second period sannan sholie ta iso.
Zaune Ikram ta ke ba wai wani gane karatun ta ke sosai ba, saboda da turanci ake koyawar ita kuma ba wani gane turancin ta ke ba, tana dai d'an tsintar jefi jefi.
****
B'angaren momy kuwa sosai ta ke kewar Ikram, ji ta ke kamar ta shekara rabonta da ita, ta tsananin shiga ranta tamkar jininta haka ta ke jinta.
Tana zaune ne wata tsohuwa ta shigo gidan, shekarunta zasu kai kimanin tamanin a duniya. Ganinta da momy ta yi yasa ta saurin mik'ewa tsaye tana fad'in "Sannu da zuwa Goggoji."
Fuskar matar da aka kira da Giggoji babu annuri ta ce "Yauwa. Na zo ne na ji ya maganarmu ta kwana? Kud'in sun fito ko kuwa? Yarana suna buk'atarsu."
"Ki zauna ko ruwa ki sha Goggoji, sai na miki bayanin komai." Momy ta fad'a da murmushin k'arfin hali.
"Ba zan zauna ba, ki fad'a min yanda ake ciki ni sauri na ke." Ta fad'a cikin fad'a.
"Ki yi hak'uri, har yanzu babu wata magana mai k'wari, kamar yanda na fad'a miki insha Allahu da zarar wata mgana mai k'wari ta fito zan kira Samira ta fad'a miki."
Tsoki matar ta yi cike da takaici ta ce "Duk yanda ka yi da jaki sai ya ci kara, duk laifinsa ne ai da ya kwaso mana ke a zuri'armu, matar da cikakken asali ma bata da shi." Ta bar gidan ba tare da ta sake furta komai ba.
A hanyar fitarta ta ci karo da Khalid, fuska d'aure babu ko alamar annuri ya d'auke kanshi. Jawo hannunshi tsohuwar ta yi da d'an murmushi ta ce "Jikana ina ka shiga ne ka daina ziyartana kwana biyu."
Babu annuri ya ce "A kan me zan zo bayan kina nuna mana sanuwar ware? K'arara kike nunar da kin fi son jikokinki na 'ya'ya mata alhali kuma ba wani abu muka miki ba, saisa muka barki da su ai." Ya k'arisa shigowa d'akin ba tare da damuwar maganar da ya miyar mata ba.
Kallon mamaki ta bishi da shi, tabbas ta san ba k'arya Khalid ya fad'a ba, ta fi nuna soyayyarta ga sauran jikokinta fiye da jikokin d'anta d'aya tal namiji. Fita ta yi kawai ta nufi inda driver'nta ya ajiye mota.
Momy kuwa fad'a ta hau yi wa Khalid a kan bak'ar maganar da ya fad'awa kakarsa, ko alamar nadama babu a fuskarshi ya ce "Ai momy gwara ana nunar mata da hakan, saboda makaho bai san kana ganinshi ba sai ka tab'ashi, idan muka ci gaba da zama da ita babu sauyi abin ci gaba zai ringa yi." Shiru kawai momy ta yi, gaskiya ne maganar Khalid, ita ma ta so ace tana miyarwa surukar tata magana, amma kasantuwar wanda ya had'asu d'in babushi a yanzu yasa ta ke respecting d'inta, ko ba komai ta yi zaman amana da mutunci da danta.
YOU ARE READING
SHI NE SILAH!
Romanceshi ne silar rugujewar farin cikin rayuwarta. shine silar shigar ta cikin kunci da bakin ciki. shi ne silar rashin gata hadi da galihu a rayuwarta. shin waye silah? ku biyoni a cikin wannan labarin inda zan warware maku zare da abawa.