66

853 49 0
                                    

*SHI NE SILA!*
           😪😪😪

              Na Princess Amrah
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
                           (2018)


66~  Horn suka yi mai gadi ya leƙo don ganin ko waye a cikin daren nan. Ganin baƙuwar mota yasa ya ƙariso inda su ke yana ɗaga masu hannu.
    Ikram ce ta leƙo yana ganinta ya washale baki ya ce "Hajiya Ikram ce cikin daren nan?"
   Ƙoƙarin kawar da damuwarta ta yi ta ce "Ni ce fa. Miemie ta yo nan kuwa?"
    Mai gadi ya ce "Ehh to, ta zo bada jimawar nan ba ita da wasu mutane. To kuma dai ina jin jikin nata ne babu daɗi, sun dai tafi asibiti har da Maman Khairat ɗin ma."
    Dafe kai Ikram ta yi ta yi salati sannan ta ce "Wace asibitin suka tafi?"
     Shiru ya yi kaɗan kafin ya ce "Gaskiya ban sani ba. Amma dai ki kira Maman Khairat ɗin sai ta faɗa miki inda su ke."
     Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce "Amma dai ba wani babban abu ne ya faru da ita ba ko?"
      "Gaskiya ba zan iya faɗin wannan ba. Abin da na sani dai tallabo ta suka yi suka saka a mota. Amma dai ki daure ki dubo ta gaskiya dan ko sanda suka shigo gidan ita da mutanen da an ga yanayinta an san tana cikin damuwa."
     "To shi ke nan, na gode." Ta koma cikin motar tare da rafka uban tagumi hawaye na sintiri a bisa kumcinta.
     "Ba kuka zaki yi ba Ikram. Dole ki binciki asibitin da su ke. Ko kuma kawai mu bari sai gobe tun da dai yanzu an tabbatar da inda su ke ɗin." Marwan ne ya yi wannan maganar a hankali shi kanshi tausayin Miemie ya ke sosai.
     "Bana jin zan iya kiran Yaya Kareema a waya yanzu." Ikram ta faɗa cikin kuka.
    "Mesa?" Haidar ya jefo mata tambaya.
    "Ban san da wane kunne zata saurari muryata ba a halin yanzu. Na so sai dai mu haɗu da ita kawai in mata bayani. Ban taɓa zaton abin zai kai har haka ba." Ta duƙar da kanta tana kukan nadama.
     "Ina wayar taki?" Haidar ya sake tambayarta.
    "Ban san a ina ta ke ba. Ina jin tana wurin Husnah ko kuma Miemie'n." Ta faɗa a hankali.
      "To yanzu ya ke nan? Ko kina da lambar Husnah a kanki?" Marwan ya tambaye ta.
     "Ina da dai ta Smart tun muna makaranta amma, mun jima kuma bamu yi waya ba ban san ko har yanzu da ita ta ke amfani ba." Ikram ta faɗa.
    Marwan ya bata wayarshi ya ce "Ungo saka a nan. Allah yasa a dace."
     Karɓa ta yi ta rubuta lambar Smart ɗin sannan ta miƙa masa ya latsa kiranta.
     Sai da ya kira har sau uku amma Smart bata ɗauka ba. A na huɗu ne ta ɗauka cikin hayaniya ta ke magana.
    Ɗan janye wayar ya yi sannan ya tambayi Ikram sunan Smart na gaskiya.
    "Hello Halimatu kina jina?" Ya faɗa da ƙarfi yanda zata ji.
    "Ehh ina ji. Ina cikin hayaniya ne, bari idan na fita zan kira." Ta faɗa.
   Saurin dakatar da ita ya yi ya ce "Dan Allah ko kina kusa da Husnah? Ina nufin ƙawar amarya."
    "Na'am, bana ji." Ta faɗa da ƙarfi saboda sautin da ke tashi a wurin.
   Maimaita mata ya yi sau biyu sannan ta ce "Ehh, kar ka kashe barin kai mata." Ta nufi wurin Husnah ta bata wayar.
    Karawa ta yi a kunnenta ta ce "Hello, waye?"
    Miƙawa Ikram wayar ya yi ta ce "Husnah fita daga mutane idan kina jina."
    Kaɗan kaɗan Husnah ta ji maganar amma jikinta ya bata Ikram ce. Da sauri ta fita daga hall ɗin ta yi waje inda kaɗan kaɗan ake jin sautin kiɗa ta ce "Ina jinki Ikram."
    "Wayata na hannunki ko?" Ta tambaye ta.
    "Ehh, gata nan cikin purse ɗita, nima ban kula da ita ba sai daga bayan nan na ji tana ringing na ɗauka. Momy ce ke tamyar ko mun koma gida."
     "Ba wannan ba ni dai Husnah. Ki duba yanzu ki turo min lambar Yaya Kareema. Dan Allah ki hanzarta."
   Husnah ta ce "To, yanzu kuwa insha Allahu." Ta kashe wayar tare da zaro ta Ikram daga purse ɗinta ta dubo lambar, sai dai kuma babu kuɗi a cikin wayar. Tata ta fiddo daga purse ɗin sannan ta saka lambar a ciki ta tura a lambar Marwan da aka kirata.
    Tana shigowa wayar Marwan ya karɓa daga hannun Ikram ya latsa kiran. Bugu biyu Kareema ta ɗauka tare da yin sallamah. Amsawa ya yi sannan ya ce "Dan Allah wace asibiti ce aka kai Miemie?"
     "Al-Ihsan Clinic." Kawai ta faɗa Marwan ya kashe wayar ya ce "Na gane inda su ke." Ya ci gaba da tuƙinshi.
    Babu jimawa suka isa Clinic ɗin, tun da dama ba wani tazara tsakanin gidan Kareema da can ɗin, shiisa ma suka je ta.
    Marwan na gama parking Ikram na fita, da sauri bata jira komai ba ta hanzarta shiga ciki. Abin mamaki sai ga amarya sanye da gwaggwaro da takalma masu tsini amma kuma sai baza sauri ta ke.  Sauƙinta ma dare ne kusan duk babu mutane, sai dai irin masu jinyar wasu wanda aka kwantar.
    Tana shiga reception ta ci karo da Kareema ta zabga uban tagumi hawaye na zirara daga idanuwanta. Ganin haka yasa Ikram ta ƙara rikicewa, Kareema jarumar mace ce wadda samun irinta ke da matuƙar wahala a halin yanzu. Duk da baƙin halin mijinta yana da wuya ka ganta tana kuka.
    Jiki babu ƙwari Ikram ta ƙarisa inda ta ke, tana zaune a kujera Ikram kuma ta duƙa ta ɗora kanta bisa cinyar Kareema haɗe da riƙe mata hannuwa duka biyun. Wani irin kuka ta ke mai tsuma zuciyar mai sauraro.
    A hankali Kareema ta ɗago fuskar Ikram da tuni kwalliyar ta lalace da kuka, bata iya ce mata komai ba haka kuma bata zare hannunta daga cikin na Ikram ɗin ba.
    Su Haidar da daidai isowarsu wurin ke nan Marwan ya ce "Sannu fa."
    Share hawayenta ta yi ta ce "Yauwa sannu." Ta faɗa a hankali.
    "Ya mai jikin?" Ya tambaye ta cikin sanyin murya.
    "To, alhamdulillahi za'a ce." Ta bashi amsa wani hawayen na fito mata.
    Haidar ya ce "Tana ina yanzu?"
    "An shiga da ita emergency. Tun ɗazu ana kanta ban dai san halin da ake ciki ba yanzu. Amma dai sun ce kar wanda ya je har sai sun buƙaci hakan."
    Sai a lokacin Ikram cikin kuka ta ce "Ku yafe min Yaya Kareema. Na san *ni ce silar* komai. Amma wallahi ba da niyya na yi ba. Allah ya sani ina ƙaunar Ikram har cikin zuciyata."
    Cikin rawar murya Kareema ta ce "Ba ta wannan ake ba yanzu Ikram. Farfaɗowar Aminatu ke gabanmu. Daga baya duk an yi wannan. Tana cikin haɗari ne sosai, likitan ma faɗa ya mana wai bamu da hankali ƙaramar yarinya har ta shiga cikin wannan yanayin."
     "Dan Allah Yaya Kareema ina roƙon wata alfarma a wurinki." Ikram ta faɗa a hankali.
    "Ina jinki." Kareema ta furta tana kallon Ikram.
    Cikin raunanniyar murya Ikram ta ce "Dan Allah idan baki riga da kin sanar ma Mama ba kar a faɗa mata. Na tabbatar da hankalinta zai tashi. Idan ma faɗin ne a bari sai gobe, yanzu ki kirata ki ce ni da Miemie a gidanki zamu kwana kawai, tun da can ɗin mutane sun yi yawa."
   Ba tare da Kareema ta ce komai ba kuwa ta latsa kiran Mama a wayarta, babu jimawa ta ɗauka ta ce "Kareematu lafiya dai ko?"
    Saurin ɓoye damuwarta ta yi ta ce "Lafiya ƙalau Mama. Dama ce miki zan yi fa Ikram da Miemie gasu nan sun wuto gidana wai a nan zasu kwana. Saboda nan ɗin an samu ƙarin ƙawayensu da zasu kwana kuma zasu takura."
    Mama ta ce "To babu damuwa. Amma dai ai da ita miemie'n sai ta dawo nan saboda ta kula da ƙawayen nasu ko? Tun da dai hakan suka yi ai shi ke nan. Ga ƙarar motoci nan ma na ji da alama su ne suka fara dawowa."
    "Sai da safe mama." Ta yi saurin faɗi saboda kukan da ta ji yana fito mata.
    Sai misalin ƙarfe ɗayan dare sannan Marwan ya ce ya kamata su je gida da safe sun dawo, saboda dare ya yi sosai yanzu. Haidar ya jinjina kai cike da tausayi suka ma Kareema da Ikram fatan alkhairi sannan suka tafi.
     Kareema ta kama Ikram ta zaunar a bisa kujera kusa da ita. Jin kukan da Ikram ke yi sosai yasa ta yi ƙarfin halin goge nata hawayen ta ce "Ikram ya isa haka dan Allah. Kukan fa babu abin da zai amfana mana. Kawai mu duƙufa roƙon Allah insha Allahu shi zai maganace mana komai."
     Bata iya cewa komai ba sai dai ta rage sautin kukan da ta ke, amma fa har yanzu ba wai ta daina yi ba ne.
     A haka suka zauna har misalin ƙarfe huɗu na asubah babu wani labari game da Miemie, haka su kuma babu wanda ya koda rintsawa ne a cikinsu.
      Sai da aka fara kiran Assalatu a masallacin cikin asibitin sannan suka ga giccin wata nurse sai keta zufa ta ke, da alama ma Kareemar ta ke nema.
    Da sauri Ikram ta sha gabanta ta ce "Sister ya ake ciki game da Aminatu? Wadda aka kawo unconscious ɗin nan da daddare."
    Nurse ɗin ta ce "Ahh wannan patient ɗin ai tun around 11pm Dr. Ya gama da ita. Ta samu high blood pressure (hawan jini) ne, kuma ya hau sosai har yana neman shafar zuciyarta. Da alama ta jima da shi kaɗan kaɗan sai yanzu ne ya tsananta. Duk da halin da ta ke ciki amma tanata furta *Ikram ce sila* har sai da aka mata allurar bacci sannan ta yi shiru. Yarinyar tana da buƙatar wani abu da alama, ku ƙoƙarta taimaka mata tun kafin abin ya tsananta. Saboda in har tana samun irin wannan zai iya zame mata paralysis (mutuwar ɓarin jiki) sannan kuma ya illata mata zuciya. Dan haka sai ku kula da kyau." Tana gama faɗin haka ta kama hanya zata tafi. Da sauri Kareema ta ce "Wane ɗaki aka kaita yanzu?"
     "Tana female ward (dakin nata) amenity ɗinmu ya cika ne. Dama ke na zo nema, zaki depositing kuɗin ɗaki 30k."
    "A ina zan biya?" Ta tambaye ta cikin kuka, saboda tun da ta masu bayanin abin da ya samu Miemie hankalinta ya ƙara tashi.
    "Zaki je pharmacy gashi can daga baya. Idan babu cash zaki iya bada ATM naki a cira." Ta bata amsa.
    Hanyar pharmacy'n suka nufa ita da Ikram, tana badawa kuwa aka cira sannan aka basu rasiɗi suka kai guda ɗaya suma suka riƙe guda ɗayan a hannunsu.
   Female ward ɗin kuwa suka nufa, gadaje ne kusan guda shida amma guda biyu kawai ke akwai patient, daga na farko wanda da ka shiga sai shi, sai kuma wanda ke fuskantarshi wanda miemie ce kwance an maƙala mata oxygen (abin taimakawa mutum ya shaƙi numfashi) sai baccinta ta ke, ga make up a fuskar ga kuma sawun hawaye wanda har ya ɗan kumbura mata kumatu.
   A hankali Ikram ta ƙarisa inda ta ke ta zauna  a farar kujera ta jawo hannun Miemie ta riƙe. Wani irin tausayin Miemie ta ke ji yana ratsa zuciyarta.
    Kareema kuma ta zauna a tabarmar waccan ɗaya mara lafiyar wadda mai jinyarta ta daɗe da yin bacci.
    Daga zaman da Kareema ta yi bata san sanda bacci ya kwashe ta ba. Ikram kuwa ko alamar baccin ma bata ji, ta dake sosai kamar ba ita ba.
   A haka har aka tada iƙama a masallaci, hakan yasa ta matsa inda Kareema ta ke ta ɗan bubbugata a hankali ta tashi.
      Miƙa ta yi sannan ta ce "Lokacin sallah ya yi ko?"
    Ikram ta ce "Ehh, ina jin ma har an fara sallar."
    "Ban san sanda baccin ya ɗauke ni ba wallahi. Ya miemie'n? Ta motsa kuwa?" Kareema ta faɗa tana hamma.
    "Har yanzu bata motsa ba Yaya Kareema." Sai kuka daga nan.
    "Ni fa ba kuka na ce ki yi ba Ikram. Kuma ai ba abin tashin hankali ba ne ba dan bata tashi ba, tun da dai allurar bacci ce aka mata." Ta faɗa bayan ta miƙe tsaye ta iso inda su ke.
    Taɓa jikin Miemie ta yi ta ji alamun har da zazzaɓi a jikinta. "Kamar ma akwai zazzaɓi na ji." Ta furta tana kallon Ikram.
    "Ehh, ina jin na kukan da ta yi ne. Nima nan Dr. Na ke jira ya zo in faɗa masa kaina kamar zai fashe saboda ciwo." Ikram ta bata amsa tana tallabe kan nata.
    "Ikram ai dole ki yi ciwon kai. Na tabbatar da ko rintse baki rintsa ba. Ga kuma kukan da kika sha."
    Ikram dai bata faɗi komai ba sai kallonta da ta miyar ga miemie cike da tausayinta.
     Banɗaki Kareema ta shiga ta ɗauro alwala, tana fitowa waccan ɗayar mai jinyar ma ta tashi.
   Bayan ta gabatar da sallah ne ta ce "Ya kamata fa in faɗawa mama gaskiyar halin da ake ciki."
    Cikin kuka Ikram ta ce mata "Dan Allah kar ki faɗa mata yanzu. Ki bari sai can zuwa anjima."
     "Ban ga amfanin ɓoyon ba Ikram. Ya kamata a ce a faɗawa mama haka nan, ko addu'a ta mata ai an ci riba."
    Kuka ta sake fashewa da shi tare da ƙanƙame Kareema tana roƙonta a kan dan Allah kar ta sanar da Mama abin da ya ke faruwa.
    Ajiyar zuciya ta sauke ta ce "To shi ke nan ya isa haka. Yanzu ya kike so a yi?"
     Shiru Ikram ta yi kafin ta ce "Mu bari har farfaɗowar miemie, insha Allahu babu abin da zai same ta. Kin ga sai mu koma gida lafita lau."
    "Hmm!" Kareema ta yi ajiyar zuciya. "To Allah ya bata lafiya."
     "Ameen ya Allah." Ta faɗa a hankali.
    Ƙarfe bakwai da mintuna sai ga Haidar da Marwan sun zo. Sai da Marwan ya kira Kareema ta faɗa masa ɗakin da su ke sannan suka shigo hannunsu riƙe da kalaci.
    Bayan sun gaggaisa suka miƙawa Ikram ledar Marwan ya ce "Ga kalacinku nan."
    Haidar ya ce "Ya mai jikin?"
    "Da sauƙi. Amma fa Yaa Haidar har yanzu bata tashi ba. Ina jin tsoro...." Ta fashe da kuka.
    "Ya isa haka to. Insha Allahu babu abin da zai same ta. Ke dai kawai ku dage da addu'a." Haidar ya ce da Ikram dan ita kanta tana matuƙar bashi tausayi, duk da ya fi bata laifi a al'amarin.
       Suna nan zaune har ƙarfe takwas ta yi likita ya fito zagaye da nurses biyu biye da shi sun riƙe files guda biyu na Miemie da na ɗayar marar lafiyar.
     Yana zuwa kuwa ya ga Haidar ya sanshi suka gaisa yana faɗin "Dr. Aliyu Haidar dama kasan patient ɗin nan ne?"
   Da murmushi Haidar ya ce "Ehh na santa fa."
     Cikin wani yanayi ya ce "Ban san wace irin damuwa ce ta sakata a wannan halin ba."
    Haidar bai faɗi komai ba sai kallon Ikram da ya yi. Daidai Ikram zata miƙe Miemie ta buɗe idonta ta yi tozali da fuskarta.
     Saurin kawar da kanta ta yi zuwa ɗaya sashen tana faɗin "Ki tafi ki bani wuri in dai ba so kike ki ƙarisani ba. Ikram na tsane ki! Ki ɓace min daga gani...." Kuka sosai ta ke.
     Kamo hannunta Ikram ta yi ta ce "Na san baki tsane ni ba Miemie, kina cikin jin haushina ne kamar yanda nima kaina na ke jin haushin kaina. Dan Allah Miemie ki saurare ni. Wallahi bana nufinki da sharri."
     Ɗago kanta ta yi ta hango Yaya kareema data matso kusa da Ikram cike da damuwa. "Yaya Kareema ki ce ta tafi ta bar wurin nan in dai ba so kuke ku rasani ba. In har ina ganin fuskarta damuwa zata ci gaba da damuwa har in ƙarisa lahira. Hmm!" Ta yi murmushin takaici. "Ko da ya ke ai ba abin mamaki ba ne dan na ƙarisa lahira. Tun da dai na rasa Yaa Haidar, bana jin akwai sauran abin da ya rage a rayuwata." Ta kuma fashewa da kukan takaici.
      Dr. Ne ya matso inda Ikram ta ke ya zauna a kan kujerar data tashi ya ce "Am sorry, Aminatu right? (Ko?) Ki daina saka damuwa a ranki, hawan jini ya hau sosai wanda bai kamata ya hau ga yaribya kamarki ba. Sanann kuma yana neman ya shafi zuciyarki."
      "Dr. Sai me dan zuciyata ta illata? Ina son ka sani cewa zuciyata ta daɗe da illata tun sanda na gane aminiyata ta ci amanata. Me ya yi saura kuma. Ka ce mata ta bar wurin nan dan Allah. Wallahi bana son ganinta." Har yanzu kuma bata kula da Haidar da Marwan da ke tsaye can nesa da su ba.
    Cikin natsuwa likita ya kalli Ikram ya ce "Ki yi haƙuri, yarinyar tana cikin halin da ya kamata ki nisanta da ita, tun da dai a iya fahimtata kamar ke ce damuwarta. Dan haka ki yi haƙuri, idan ta ji sauƙi sai ki dawo."
    Kuka sosai Ikram ke yi ta ce "Shi ke nan Miemie, zan tafi. Allah ya baki lafiya." Da gudu ta fice daga ɗakin.
    Runtse idonta ta yi tana mai tsananin jin raɗaɗi a zuciyarta, har yanzu ganin abin ta ke kamar a mafarki. A haka idonta rintse Haidar da Marwan suka bi bayan Ikram, gudun kar itama wani abu ya same ta.



*Team Ikramhaidar*
*Team Ikramkhalid*

SHI NE SILAH!Donde viven las historias. Descúbrelo ahora