*SHI NE SILA!*
😪😪😪Na Princess Amrah
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
(2018)_♥♥♥ A friend is one who …. Sees your first drop of tear … …Catches the second ….. Stops the third … … and turns the fourth into a Smile ♥♥♥ HAPPY MARRIED LIFE MY DEAREST FRIEND *XARAH~B~B*....MAY YOURS BE AMONG THE BEST._
67~ Gudu sosai Ikram ke yi har ta isa reception tana neman fita, da ƙarfi Haidar ya riƙo ta yana faɗin "Ina zaki tafi?"
Bata ce komai ba sai ƙoƙarin fizge hannunta da ta ke amma kuma ta kasa.
Sai da suka isa bakin mota sannan ya umurce ta da ta shiga, bata musa masa ba kuwa ta shiga, shima ya shiga ciki sannan Marwan ya ja motar suka bar asibitin.
Baysn sun yi nisa da asibitin kuma har yanzu bata daina kuka ba Haidar ya ce "Ya isa haka ki daina kukan nan. Bana so a fahimci wani abu daga gare ki. Yanzu ina za'a kaiki?"
Cikin kuka Ikram ta ce "Bana jin zan iya komawa gidansu Miemie bayan duk abin da na mata. Ka kaini wurin momy kawai."
Haidar ya ce "Ya za'a yi a kaiki gidan momy kina wannan kukan? In dai kina so a kaiki can to dole ki yi shiru, idan kika je kina wannan kukan kin san dai halin mutane da tsegun-guma. Wasu ma zagin momy zasu yi a kan laifin da bata ji ba bata gani ba, ana iya cewa auren dole zata miki dan ta ga ba ita ta haife ki ba."
Da sauri Ikram ta ce "Ka daina faɗin haka dan Allah yaa Haidar.." Ta yi shiru daga nan, har kukan ma ta daina.
"Za'a kaiki gidan momy. To amma sauran ƙawayen naki ya za'a yi da su? Kuma kayanki wanda zaki saka ba suna can ba?" Ya tambaye ta cikin rarrashi.
"Duk wannan mai sauƙi ne. Dama yau ɗin zamu koma gida ai, duka har da sauran ƙawayen ma. Kayana kuma zan ce Husnah ta tarkato min komai idan zasu taho."
Wayarshi ya miƙa mata ya ce "Ungo ki kira ki ce ta shaidawa ƴan matan su shirya, nan da ƙarfe goma za'a je a kwaso su. Tun da ɗaurin auren na ƙarfe sha biyu ne."
Karɓa ta yi jiki babu ƙwari ta rubuta lambar wayarta. Wasu lambobi ta ga an yi saving ɗin lambarta ta ita, bata wani tsaya tunanin ko lambobin miye ba ta latsa kiran.
A ɓangaren Husnah kuwa har ta gaji da mitar ɗawayensu, wai amarya da Miemie sun tafi sun barsu. Kira ne ya shigo a wayar Ikram da Husnah ta liƙa jikin chaji. Tana ganin sunan Yaa Haidar ne kamar kar ta ɗauka sai kuma jikinta ya bata ƙila Ikram ce. Ɗauka ta yi ta kara a kunnenta.
"Hello Husnah." Ta juyo muryar Ikram cikin kuka.
Da sauri Husnah ta fita daga cikin mutane sannan ta ce "Ya ake ciki Ikram? Dama ina ta neman yanda zan yi in ji halin da ake ciki. Kun gano inda miemie'n ta ke?" Karaf sai a cikin kunnuwan Mama da ta fito daga ɓangaren Abbansu Miemie zata nufi ɓangarenta.
Tsayawa ta yi cikin mamaki tana kallon yanda Husnah ke yin wayar a munafurce bata so a jita.
Ikram ta ce "An gano ta. Yanzu haka tana Al-Ihsan Hospital bata da lafiya."
"Subhanallahi! Al-Ihsan Hospital? Me same ta?" Husnah ta faɗa a razane wanda har mama sai da ta ji. Gabanta ne ya mummunar faɗuwa jikinta sai rawa ya ke.
"Bata da lafiya ne. Yanzu haka tana can tare da Yaya Kareema. Ta ce wai bata son ganina shiisa likita ya ce kawai in tafi." Ikram ta faɗa tana kuka.
"To ai da sauƙi tun da suna tare da Yaya Kareema ɗin. Allah ya kyauta. Ke kina ina yanzu?"
Da sauri mama ta bar wurin jin cewa Miemie na tare da Kareema, kuma an faɗi sunan asibitin.
"Gani nan zan koma gida. Nan da ƙarfe goma za'a zo a ɗauke ku a kawo gidan momy. Ki haɗo min duka kayana dan Allah."
"To shi ke nan. Insha Allahu zan faɗa masu. Dan Allah Ikram ki kwantar da hankalinki. ki cire duk wata damuwa daga ranki, Allah ya rufa asiri." Ta kashe wayar daga nan.
Ikram na kuka ta miƙawa Haidar wayar. "Ci gaba kika yi da kukan ko?" Ya tambaye ta cikin faɗa.
"Ka bita a hankali Aliyu. Ka san tana cikin yanayin damuwa ne dole ka ganta a haka. Ikram ki daure kin ji?" Marwan ya faɗa a daidai isowarsu unguwarsu.
Kai kawai Ikram ta jinjina ba tare da ta furta komai ba.
"Karɓi wannan." Haidar ya miƙa ma Ikram wani rawani duk ya yi ƙura alamun ya daɗe a cikin motar. "Ki cire wannan gwaggwaron ki ɗaura wannan a kai. Ki saki jikinki idan kin shiga. Duk wadda ta miki wata tambaya ki yi ƙoƙarin kawar da damuwa ki bata amsa."
Bayan ta karɓa ta cire gwaggwaron ta yafa rawanin.
Wayar Haidar ce ta ɗauki ringing yana dubawa ya ga baƙuwar lamba. Tsaki ya yi bai ɗauka ba har ta tsinke sai ga wani kiran ya sake shigowa. Nan ma dai ƙin ɗauka ya yi sai da Marwan ya ce masa "Ango wayarka fa na ringing ka ɗauka ko wani babban dalili ne yasa aka kiraka."
"Ina jin patients ne, cikin weekends ma ba za'a bar mutum ya huta ba." Ya faɗa haɗe da miyar da wayar a silent.
Suna isowa ƙofar gida ta buɗe motar ta fita, ko ɗaukar gwaggwaron nata ma bata yi ba kawai ta fice.
Tana shiga ga mata nan da yawa wasu na wanke wanke, wasu shara, wasu kuma wankin waken ƙosan kalaci su ke, saboda har yanzu takwas bata yi ba.
Ƙirƙiro murmushi ta yi ta gaishe su tana ƙoƙarin wucewa wata mata ta ce "Amaryar ce da kanta ashe. Yo ya aka yi kika ƙumo wannan sammako haka kamar wadda aka koro?"
"Wa fa zai koro ni? Ra'ayin kaina ne kawai." Ta faɗa haɗe da barin wurin, tana matuƙar jin haushin irin wannan magulmatan matan.
Ta ƙofar kitchen ta bi, nan kuma ta ci karo da masu suyar dankali, wasu kuma suna yin fanke. Kayan kalaci dai kala kala.
Nan ma dai gaishe su ta yi bata ko tsaya saurarensu ba ta nufi ɗakinta. Tun tana hawan benen ta fara jin alamun cike ya ke da mutane hakan yasa ta sauka ƙasa ta nufi ɗakin Nana mai aikinsu. Nan ɗin ma dai a cike ya ke da mata. Tsaki ta yi ta nufi side ɗin su Haidar.
Tun a corridor ta haɗu da momy wadda da ka ganta ka san tana cikin hidima.
Rungunar momy Ikram ta yi sai hawaye wanda bata san sanda suka fara fitowa ba.
"Ikram ƴata har an iso? Dama yanzu na ke son kira in ce ku zo da wuri. Tun da muma nan namu taron muke yi. Tun da dai da wuri za'a ɗauki amarya gwara a yi komai cikin lokaci."
Da sauri ta share hawayenta ta ce "Ni kaɗai ce ma na yo gaba ai. Miemie ce bata da lafiya yanzu haka tana asibiti a can ma muka kwana tare da Yaya Kareema." Sai wani hawayen kuma.
Cikin yanayin damuwa momy ta ce "Ayyah! Me same ta?"
Ikram ta ce "Nima kaina ban sani ba. Amma dai ta ji sauƙi sosai ƙila ma da safen nan su bata sallama."
"To masha Allahu. Allah ya ƙara lafiya. Gashi kuma ɗakinki a cike ya ke, nima nawan ya cika sosai shiisa na kawo wasu baƙina a ɗakin Khalid. Amma jeki ɗakina ki buɗe kit zaki ga keys da yawa, ki ɗauko bunch ɗin nasu ki zo ki ringa gwaggwadawa a ɗakin yayanku har ki dace. Sai ku zauna a ciki tun da dai shi kaɗai ne babu mutane, duk ɗakunan gidan ciccike su ke."
Nufar ɗakin momy ta yi duk da mutanen da ke ciki a haka ta daure har ta isa inda wardrobe ɗinta ta ke, bakin gado ta hau sannan ta ɗauko kit ɗin daga bisa wardrobe ta buɗe ta ɗauko makullan.
Bayan ta ɗauka ta koma ɗakin Haidar, nan da hau gwaggwada makullan har Allah yasa ta dace da spare key ɗin ɗakin.
Bayan ta buɗe ta koma ta miyar da sauran sannan ta dawo ta shiga ciki ta ɗan turo ƙofar.
Tsaf ɗakin ya ke kamar ba na namiji ba. Ga ƙamshi da ya ke baɗaɗawa ta ko wane saƙo.
Miƙewa ta yi ta kunna ac sannan ta zauna ta rafka tagumi ta ci gaba da tunani. Bata ankara ba ta ji an turo ɗofar ɗakin, momy ce ta gani ɗauke da food flask a ɗayan hannunta kuma flask ne sai kofi da cokali da kuma plate.
Ajewa ta yi ƙasa sannan ta ce "Na san rabonki da abincin kirki kin jima. Ga kunu nan na san kina so, a food flask ɗin kuma dankali ne da ƙwai, ba'a kai ga soya ɗosan ba yanzu ma aka kai shi niƙa. Ki ci ki ƙoshi autata." Ta sakar mata murmushi.
Saukowa ta yi ƙasa ta zuba kunun a kofi sannan ta buɗe kular ta fara karyawa, duk da muguwar yunwar da ta ke ji samun kanta ta yi da kasa ci. Da ɗyar ta tuttura kaɗan sannan ta ɗaga kofin bata sauke ba har sai da ta shanye kunun tas.
Tana gamawa ta shiga banɗaki, pad ta ke son canzawa amma babu. Tunawa ta yi da tana da ita a ɗakinta hakan yasa ta kwashi kayan kalacinta ta nufi kitchen da su ta ajiye.
Ɗakinta ta wuce daga nan, bayan ta gaisa da kakarta da sauran danginta ne ta shige banɗaki ta ɗauko babbar ledar virony sannan ta jawo wata ƴar loka ta ɗauki baƙar leda guda biyu, ta saka jakar virony ɗin a ciki gudun surutun mutane, sannan ta riƙe gudar ledar a hannunta ta sauka zuwa ɗakin Haidar.
Cikin lokaci kaɗan Ikram ta yi wanka sannan ta ɗaura towel ɗin Haidar wanda ya tsaya mata bisa cinyarta.
Zama ta yi a bakin gado babu jimawa momy ta shigo ta ce "Su Husnah basu iso ba har yanzu?"
"Ehh momy basu iso ba. Na san dai sun kusa tahowa tun da gashi har tara ta wuce."
"To idan sun zo in suna da buƙatar wani abu na kalaci akwai komai a wadace. Sai su ɗibo duk abin da ransu ke so. Ki tashi ki nemi kaya ki saka dan kar a ringa shigowa a same ki a haka."
Ikram ta ce "Momy kayan suna can na baro ai. Husnah zata taho min da su yanzu."
"Ko zata taho miki da su ai ba su kaɗai ne kayan da gare ki ba. Ki je ɗakina ki duba makullin wardrobe, ki fiddo kaya a cikin nakin da kika ajiye a ciki."
"To momy kuma a haka zan fita?" Ta faɗa cikin muryar shagwaɓa.
"Zauna to bara in ɗauko miki. Amma fa da sharaɗin duk wanda na ɗauko miki sai kin sakasu. Dan ni ba wani sanin wanda kike so na yi ba."
Ɗan murmushi ta yi ta ce "Ehh na yarda momy."
Fita ta yi sai gata da wata jar shadda gizna, wadda aka ma ɗinkin doguwar riga mai matuƙar kyau.
Godiya Ikram ta mata sannan ta saka kayan, a lokacin har momy ta fita.***
Tun sanda Mama ta ji wayar da Husnah ke yi ta fasa zuwa ɓangarenta ta koma na Abbansu. Wayarta ta ɗauka ta latsa kiran Kareema amma bata ɗauka ba. Hankali a tashe ta fice ko mota bata tsaya hawa ba ta nufi bakin titi. Keke napep ta tsayar ta hau ta faɗa masa inda zai kaita.
Su Husnah kuma suka hau shiri, a lokacin ko gama haɗa kalaci ba'a yi ba.
Momy na isa asibitin ta nufi reception, mutane ta gani zazzaune wasu suna jiran ganin likita, wasu kuma masu jinya ne suna kallon labarai.
Wata mata ta tambaya ko ta san wata miemie mara lafiya? Amma matar ta ce bata santa ba sai dai ko ta je nurses station ta tambaye su.
A ruɗe ta isa wurin nurses ɗin, bayanin Miemie da Kareema ta masu wata nurse ta ce "Ehh na gane ta. Tana female ward ne."
"Dan Allah ina ne female ward ɗin?" Ta tambaye su a rikice.
Kwatanta mata suka yi ta nufi can ɗin da sauri ta shiga ɗakin.
Hango Miemie ta yi kwance fuskarta ta kumbure tsabar kukan da ta sha. Ga kuma Kareema zaune daga gefenta ta yi tagumi.
"Me ya faru da ƴata? Mesa kuka ɓoye min halin da ƴata ta ke ciki?" Mama ta faɗa haɗe da kama hannun Miemie.
Kallonta miemie ta yi tare da ƙirƙiro kurmushi ta ce "Mama kar ki ga laifinsu ni ce na ce masu kar su sanar miki."
"Wane irin kar su sanar min miemie? Gaki kwance baki da lafiya shi ne zaki ce a ɓoye min?"
Wani murmushi mai cike da takaici ta yi ta ce "Ba fa wani damuwa ba ne Mama. Na ji sauƙi sosai."
Mama ta ce "To Allah ya ƙara lafiya. Kareematu me ya same ta ne?"
Saurin kaɗa mata kai Miemie ta yi hakan yasa ta ce "Jiya ne wurin dinner ta faɗi ta bige kanta, duk ma basu sani ba sai daga baya. To kuma kan ya dame ta da ciwo shiisa tsakar dare kawai na ce wa Ikram ta taso mu kawo ta asibiti. Abin da yasa ba'a sallame ta ba sai an gama binciken kan nata, dan kar a je wani abu ya bugu daga ciki ba'a sani ba."
Cike da gamsuwa mama ta ce "Ni fa na ji Husnah na waya da Ikram. Kawai ji na yi ta ambaci rashin lafiyar miemie, sannan kuma ta ambaci sunanki da asibitin nan. Babu ma wanda ya sani kawai na hawo napep na zo."
"Eyyah! Ai komai da sauƙi mama. Kawai ki koma kin ga babu daɗi ga ƴan mata a gidanki kuma a ce babu kowa a cikinmu. Na ji sauƙi sosai ki tafi kawai, da likita ya zo zai bani sallama."
Mama ta ce "To shi ke nan bara in koma Miemie. Allah ya bada lafiya." Ta tafi.***
Tana isa gida a lokacin su Husnah sun shirya amma basu ganta ba, gashi kuma Haidar ya kira wai nan da minti goma masu ɗaukarsu zasu iso. Kuma suna so su ma Mama sallama kafin su tafi.
Tana shiga da sauri Husnah ta iso gare ta da fara'a ta ce "Mama inata nemanki ai, har abin karyawarki na kai ɗakinki amma ban ganki ba."
Murmushi ta yi ta ce "Ahh babu komai. Na je wani wuri ne. Har kun shirya ma ko?"
Husnah ta ce "Ehh mun shirya. Yanzu za'a zo a kwashe mu a kai gidan momy. Yau taron nata ne." Ta sakar mata murmushi.***
Ba'a wani jima ba sai ga kiran Haidar, ya ce da Husnah su firfito ga motocin sun iso. A lokacin ƙarfe goma da minti biyar ne.
Bankwana suka ma Mama sannan suka firfita, wasa wasa ƴan matan suna da yawa, dan a ƙalla sun kai su ishirin har ma da ɗori.
Shiga motocin suka yi, yayin da Marwan ya kira Khaleesat a kan wai kar ta hau motar kowa ta matso daga gaba tashi na nan. Hakan ne kuwa ya kasance, da ita da Juwairiyya sai Khadija candy suka hau motarshi.
Suna isa gidan momy suka sassauka, Husnah ta masu jagoranci har suka ƙarisa cikn gidan.
Da momy suka ci karo, gaishe ta ƴan matan suka yi da fara'a ta amsa, sannan ta shaidawa Husnah cewa su je ɗakin Haidar Ikram ɗin na can, kuma a can zasu zauna. Idan ma bai ishe su ba sai ta ma wancan ƙawayen nata transfer daga ɗakin Khalid su koma wani ɗakin.
*Team Ikramhaidar*
*Team Ikramkhalid*
YOU ARE READING
SHI NE SILAH!
Romanceshi ne silar rugujewar farin cikin rayuwarta. shine silar shigar ta cikin kunci da bakin ciki. shi ne silar rashin gata hadi da galihu a rayuwarta. shin waye silah? ku biyoni a cikin wannan labarin inda zan warware maku zare da abawa.