30

1.1K 75 0
                                    

*SHI NE SILA!*
           😪😪😪

              Na Princess Amrah
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
                           (2018)

_Wannan shafin naku ne baki d'aya masoyan *Amrah* na nesa da na kusa, wanda na sani da wanda ban sani ba. Masoyana masu bibiyar labarina *ina alfahari daku* ina maku irin mugun son nan wanda ba kowa na ke ma irinshi ba. Kar ku ji komai kuma ku d'auka a ranku cewa *#anatare#*_

30~  Ita kuwa Ikram sosai ta yi farin ciki da abin da Bash Osca ya mata.
   Har da musayar lambar waya suka yi sannan suka rabu, Bash kuwa ya masifar jin dad'in lambar Ikram da ya samu, ko ba komai ita d'in kyakkyawa ce.
    Kai tsaye hanyar gida ta kama, daidai ta kusa isa gida Khalid ya kirata, tana kallo wayar na ringing amma bata d'auka ba. Har ta tsinke sannan wani kiran ya sake shigowa, sai a sannan ta d'auka ta saka a handsfree tana driving a hankali.
   "Ke sai kin ja wa mutane clasa sannan zaki d'auki kiran?" Ya tambayeta.
    "Lallai ma yaa Khalid d'in nan, duk kiran da na maka baka d'auka ba sai ni ce zaka ce ina ja maka aji?" Ta fad'a cikin tsiwa.
   "Ke wallahi bana gida ne, ina gidan Hajia a kan wata magana ne. Sai yanzu na shiga mota na gani ashe a ciki na barta."
    "Ok, dama a kan wannan maganar ne da muka fara ni da kai, shi ne Barr. Kareema ta ce na kiraka wai zata maka wasu tambayoyi,  amma wai mu had'u cikin weekend. Gani nan ma na kusa gida."
   "Wallahi kuwa nima wata magana muke. Ina ma kan hanyar gidan." Ya fad'a.
   "To shi ke nan sai ka zo." Ta tsinke kiran a daidai isarta k'ofar gida.

****
     Sosai Haidar ke kai da kawowa a cikin d'akinshi, tun bayan dawowarshi gida ya rasa abin da ya ke damunshi, da zarar ya tuno abin da ya gani sai ya yi d'an guntun tsaki had'e da fad'in "Kai ba wannan ne na ke jima haushi ba." Ni kam Amrah murmushi kawai nake ina tuno da my Candy, wai ita a dole sai Haidar...lol.
   
***
    Ko da Ikram ta shigo gida momy na zaune tana kallo, sai Naanah gefenta suna labari. Da sallama ta shiga ta gaishesu momy ta ce "Ikram yau na ga kin dad'e, lafiya dai ko?"
    Da fara'a k'unshe a fuskarta ta ce "Lafiya lau momy, na biya ta gidan su wata k'awata ce."
    "To madalla, sai ki je a yi wanka a zo a ci abinci ko?"
   "To momy." Ta fad'a ha'de da hayewa sama.
   Tana hawa ana kiranta, Bash ta gani rubuce hakan ya sa ta saki murmushi sannan ta d'auka.
    "Kyakkyawa har kin isa gida ne?" Ta jiyo sassanyar muryarsa ya yi magana.
   "Uhm, Kai dai baka gajiya da tsokana. Shigowata gidan ke nan."
    "To kyakkyawa, yanzu abin da ya kamata shi ne a yi wanka, a yi sallah sannan a ba ciki hak'k'insa." Ya sake fa'di.
    "To yanzu kuwa Bash. Na gode." Ta tsinke wayar, bata san me yasa ba ta saki murmushi, ta  matuk'ar jinda'din taimakon da Bash ya mata.
   
***
   "Gaskiya wasu matan dai shashashu ne, wai yanzu daga d'an wannan abun daya faru har ka shawo kan Ikram?" Jibo ya fad'a yana dariya.
    "Ahh to ya son ranka. Kuma wallahi masifar sonta na ke." Bash ya fad'a.
    "Ai na saba jin wannan. Wace budurwa ce baka fad'awa haka?" Jibo ya sake fad'i yana kallon Bash.
    D'an guntun murmushi Bash ya yi ya ce "Ba zaka gane ba ne Jibo, wallahi wannan sonta na ke tsakanina da Allah. Kai ni wallahi idan zata amince min ma aurenta zan yi."
    Ido Jibo ya zaro ya ce "Aurenta? Kai d'in? Inda fa ban sanka ba."
    Kafa'darshi ya dafa ya ce "Wallahi Jibo ina son Ikram har cikin zuciyata daga had'uwa da ita yau. Kai ina ji a jikina ita ce matata wadda na dad'e ina mafarki."
    Kai kawai Jibo ya jinjina yana mamaki sosai da wannan sabon  al'amarin.

****
    Ranar lahadi suka yanke zasu tafi gidan Kareema. Tun da safe Ikram ta cewa momy tana so zata je gidan su miemie yau, saboda sau d'aya kawai ta tab'a zuwa gidan nasu. Momy kuwa ta amince kuma ta ji dad'in hakan sosai.
    "Sai ki fad'awa yayanki Khalid ya kaiki idan kin shirya." Momy'n ta fad'a a lokacin da suke yin kalaci.
    "Ehh na fad'a masa dama, ya ce idan na karya sai mu tafi." Ta fad'a tana cin indomie d'inta.
    "To shi d'in fa ba zai karya ba? Je ki d'akinshi ki kirashi ya karya dan na kula da shi yanzu abinci bai dameshi ba."
   Tashi kuwa ta yi da saurinta ta nufi d'akin domin kiranshi.
   A daidai corridor 'din da ya raba d'akin Khalid da na Haidar ta yi kicib'is da shi har ta kusa kai mashi karo, santsi ne ya jata da 'karfi ta sulale zata fa'di. A jikin mutum ta jita ta fad'a hakan ya bata damar k'ara langab'ewa a jikin nashi saboda har ta sadak'as cewa ta isa k'asa sai ta ji sab'anin haka. Saurin janyeta ya yi daga jikin nashi fuskar nan murtuk da ita.
   "Wai ke sai yaushe zaki yi hankali? Kin girma amma kin kasa sanin kin girma. Mtsw!" Ya ja dogon tsaki.
    Rarraba idanu ta hau yi tana 'dan sosa kanta dan ta san tabbas ita ce bata da gaskiya, sam bata kula shisa ta ke yawan kai masa karo idan yana tafiya.
    "Allah ya baka na mai bara." Ta fad'a had'e da shigewa k'ofar Khalid.
   Jawo hannunga ya yi da k'arfi ya ce "Au...haka ma zaki ce?"
   D'ago kanta ta yi ta kalleshi, sai kuma ta janye idon daga kallonshi da ta yi, saboda matuk'ar ta had'a ido da shi ba zata iya fad'in komai ba, tsabar k'warjini da ya ke mata.
    "To me zan ce maka idan ba haka ba?" Ta murgud'a baki had'e da k'ok'arin janye hannunta da ya rik'e, sai dai kuma ta kasa saboda tam ya rik'e mata hannun.
    Khalid da duk abin da ke faruwa ya na ji a cikin toilet ya fito ya saka kaya bai daina jiyo hayaniyarsu ba. Murmushi ya yi ya ce "Yaya da Ikram dai basa shiri, ban san ranar da zasu shirya ba. K'ila kuma sai ranar da ya ga ta zama sarakuwarsa, wato matata ke nan." Ya fad'a a bakin gadonshi yana dariyar jin dad'in maganar da ya ma kansa.
    Tashi kuma ya yi ya samesu sai tsiwa Ikram ke masa, shi kuwa ya k'i sakin hannun nata ya ce masifa da rashin kunyarta sai su sa ya saketa d'in.
     "Me ya ke faruwa ne yaya?" Khalid ya fa'da a lokacin da ya iso inda su ke.
    "Yaya Khalid babu fa abin da na masa, karo ne muka kusa yi kuma fa na bashi hak'uri amma ji yanda ya rik'eni kamar wacce ta masa sata." Ta k'arisa maganar da satar kallon Haidar d'in tana neman sake murgud'a bakin.
    "Ki  murgud'a 'din mana da, waye ya ce ki fasa?" Ya fad'a ya k'are matse mata hannu.
    "Wannan wasa naku dai ya isa haka yaya, tun d'azu na ke d'an jiyo muryarku sama sama ashe wasan fad'a kuke" ya yi dariya.
    "Da wa zan yi fad'a ba dai da wannan k'wailar ba? Allah ya kyauta min. Ke wallahi wannan wanda ya aureki ya aurarwa kansa marar natsuwa dan sai kin wahalar dashi." Ya fad'a had'e da sakar mata hannu yana binta da wani mugun kallo.
     Bata kuma fa'din komai ba dan tana gudun kar ya sake rik'o hannun nata.
     "Yaya ni fa momy ce ta aikoni wurinka, wai ka zo ka karya mu tafi." Ta fad'a tare da saurin barin wurin tana cewa "Kuma Allah ya isar min mugu kawai."
     Bai jita ba saboda ya riga da ya shiga d'akinsa, dama dawowarshi gidan ke nan a asibiti ya kwana.

SHI NE SILAH!Where stories live. Discover now