23

1K 73 1
                                    

*SHI NE SILA!*
           😪😪😪

              Na Princess Amrah
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
                           (2018)

23~ Ganin yanayin miemie kamar akwai magana a bakinta ya sa Ikram dafa kafad'arta ta ce "ya dai k'awata, akwai damuwa ne?"
    Murmushi ta k'ak'ulo ta ce "Babu damuwa ko kad'an, kawai dai tambayarki na ke son yi."
    Murmushin ta miyar mata da shi ta ce "Akwai dai damuwar ke nan, to ina saurarenki."
    Wurin zama suka nema, kad'an daga gate d'in hostel daga ciki kusa da Zarah house.
    "Wai Ya Khalid d'in nan, yayanki ne ko?" Ta tambayeta cikin wani yanayi.
    Dam! Gaban Ikram ya fad'i, bata so ta fad'i alak'arta da Khalid ko dan halaccin da momy ta mata, ba dai ta fad'i cewa Ikram ba 'yarta ba ce da kanta. Hakan ya sa ita ma ta ke matuk'ar son ta ga ta b'oye wannan sirrin b'oyen.
    "Kika yi shiru 'kawata, ko da matsala?"
     Cikin inda inda Ikram ta ce "Ehh yayana ne mana Ya Khalid, wani abu ne?"
     Ajiyar zuciya ta sauke tare da fa'din "Na dad'e ina dakon son yayanshi, Dr. Aliyu Haydar, ina raka Yaya Kareema ne wani lokaci kar'bar magani asibiti. Duk da ba wurinsa muke zuwa ba amma na kamu da sonsa. Yanayin halinshi na wulak'anta jama'a ya sa na kasa tinkararsa da maganar duk da kuwa halina da kika sani bana cutar kaina kuma bana zurfin ciki. Lokacin da na fara fad'awa Yaya Kareema halin da na ke ciki ta ce 'a hir d'ina! Kar ma na sakawa kaina soyayyarsa saboda zan b'atawa kaina lokaci ne kawai. Dr. Aliyu Haidar mugun d'an wulakanci ne, babu wanda ya ke ragawa.' Kwatsam wata rana na rakata asibitin na je kusa da Office 'dinshi kamar yanda na saba, in dai zan je asibitin to ina kusa da office d'inshi, saboda ko ba komai idan na ganshi zan ji dad'i. Ya Khalid d'in nan na gani ya fito daga Office d'in Dr. Aliyu sai dariya suke har da tafawa. Dariyar ta matuk'ar yiwa Dr. Kyau duk da kuwa bai saba ba! Wannan karen shi ne farkon ganinsa da na yi yana dariya. Har bakin mota ya rakashi sannan ya taho. Cikin lokaci kad'an kuma ya d'aure fuska kamar ba shi ne ya gama dariyar nan ba. Office d'inshi zai shiga sai ga masinjanshi ya fito. Ya kirasa da yalla'bai sannan suka yi magana wadda ban san abin da suka fad'a ba. Fasa shiga office d'in ya yi sai gani na yi ya koma ya shiga motarsa ya bar harabar wurin.
     Masinjan nashi na kira, bayan na gaisheshi na ce "Baba dan Allah tambayarka zan yi."
    "Yau dai Allah ya yi zaki yi magana ke nan. Ina yawan ganinki a nan, wani lokacin ma da gangan na ke gittowa ta kusa da ke ko zaki ce wani abu saboda na fahimci kina da dalilin da ya sa kike zuwa wurin, amma sam kika 'ki magana. Ina saurarenki. Allah dai ya sa ba fad'awa tarkon soyayyar Dr. Ali kika yi ba. Saboda akwai irinki sun fi hamsin yanzu haka. Kuma banda wulak'anci babu abin da ya ke shiga tsakaninshi da su."
    Yana fa'din haka na ji gabana ya yi mummunar fad'uwa. Samun kaina na yi da kasa fad'in komai sai dafe kaina na yi da ya ke min barazanar fashewa. Cikin lokaci kad'an na ji baki d'aya na canza kamar ba ni ba.
     "Ki fad'i ta cikinki 'yar nan, barin kashi a ciki baya maganin yunwa." Masinjan ya fad'a.
     Daurewa na yi na ce "Ban tab'a ganin dariyarsa ba, kullum tsakaninshi da mutane sai raini da wula'kanci. Amma abin mamaki yau na ganshi yana dariya da wani har da tafa hannu. Shi ne abin ya d'aure min kai. Dan Allah ya yake da wancan? Wata k'ila idan na tinakreshi da maganar zai saurareni." Kuka ya kufce min.
    Cikin rarrashi ya ce "Ki daina kuka, tun wuri ki cirewa kanki son wannan bawan Allah. Wallahi na san ba zai tab'a sonki ba. Ke yarinya ce k'arama, bana so ki sakawa kanki damuwa har wata cutar ta kamaki. Yi hak'uri kin ji ko?"
    Kai kawai na d'aga masa alamar na ji. Na ce "Ya yake da shi Baba?"
  "K'aninshi ne uwa d'aya uba d'aya. Da shi kad'ai ya ke irin waccan dariyar. Babu ruwanshi da kowa, amma na ji an ce wai wani abu ne ya faru da shi yasa ya koma haka, wai daa ba hakan yake ba."
    "To amma Baba mesa baya son mata? Ko mata ne suka masa abin?"
    Bai bani amsa ba sanadiyyar dafani da na ji an yi. Yaya Kareema ce hannunta rik'e da Khairat. Ganin ina kuka ya sata damuwa sosai ta ce "Wai ke Miemie wannan wane irin rayuwa ce? Wane irin hali kike nema ki jefa kanki a ciki? Kina fama da DAFIN SON wanda bai ma san kina yi ba. Ki wuce mu tafi! Kuma wallahi ba zaki sake ko rakoni asibiton bama barin har ki zo gaban office d'inshi ranki yana b'aci." Ta ja min hannu muka tafi. Har muka bar wurin ban daina waigen wurin ba.
    Rabona da zuwa asibitin ke nan, sai yau da Allah ya sake had'ani da Ya Khalid." Tana gama fad'in haka ta share hawayen fuskarta.
    Ikram da tun da Miemie ta fara magana ta sake bakinta mamakinta bai wuce sunan da ta ji an ambaci yayan Khalid ba. Kar dai zargin da ta ke yi ya tabbata. Idan kuwa haka ne tabbas akwai matsala babba!
     Cikin wani yanani mai wuyar fassarawa Ikram ta ce "A duk gidanmu babu wani mai suna Aliyu Haidar. Akwai dai yayanmu likita wanda yanzu haka ma baya k'asar nan yana UK. wata k'ila dai ba Ya Khalid ba ne kika gani, kawai dai kama ce."
     Cikin rashin yarda da maganar Ikram miemie ta ce "Ba gaskiya ba ne Ikram, kawai dai akwai abin da kike b'oye min. Ko dai bakya so yayanki ya so ni ne? Miye matsalata? Ban yi miki bane?"
     Damuwa k'arara a fuskar Ikram ta mik'e tsaye. "Wace irin magana kike haka Miemie? Wane irin bana sonki? Ke ko wani zai fad'a miki haka zaki yarda ne?"
     Ita ma mik'ewar ta yi ta kamata ta zaunar "Calm down k'awata. Dan Allah ki fad'a min abin da ya ke ranki. Na san akwai wani abu."
    Duk yanda Ikram ta so ta b'oye maganar kasawa ta yi. Kaf labarinta ta kwashe ta fad'awa miemie. Ko A bata rage a ciki ba.
     Sosai ta tausayawa Ikram, kuma ta k'ara tabbatar da cewa Dr. Aliyu Haidar *SHI NE SILA* da Ikram ta rasa ummanta.
      "Mesa kika kamu da son mutumin da na fi tsana a rayuwata? Mesa kika kamu da son mutumin da *SHI NE SILAR* mutuwar ummana? Haba mana miemie! Dr. Aliyu Haidar *SHI NE SILAR* rugujewar farin cikina. Dr. Aliyu Haidar *SHI NE SILAR* rashin uwata wacce ta kawoni duniya. Bana k'aunarshi na tsaneshi!" Ta fashe da kuka sosai tare da d'ora fuskarta a kan cinyar miemie tana ci gaba da kuka. Ji ta ke komai ya dawo mata sabo, mutuwar ummanta ta dawo mata dal. Sosai ta ke k'ara tsanar Dr. Aliyu.
     "Kin san an ce zuciya bata da k'ashi Ikram! Ni kaina ban so zuciyata ta kamu da sonshi ba. Na san Dr. Aliyu na san waye shi. Duk yanda na so na yakice soyayyarsa daga zuciyata na kasa. Dan Allah ki taimaka min Ikram. Ki taimaka Dr. Aliyu ya so ni, ko da bai aureni ba!" Ita ma ta fashe da nata kukan.
     Sun jima a haka har aka kira sallar isha'i sannan suka tashi. D'akinsu suka nufa don canja kaya, kallo d'aya za'a masu su duka biyun a gane babu walwala a tattare da su.
     Suna gama canjin kaya suka fara 'kok'arin tafiya masallaci sai ga smart ta shigo cike da farin ciki. "K'awayena ina kuka shiga ina ta nemanku. Babu inda ban zagaya ba amma ban ganku ba."
    Cikin k'arfin hali Ikram ta ce "Aikuwa muna kusa da Zarah house, labarin duniya kawai mu ke."
     Guntuwar harara ta jefesu da ita kafin ta ce "Wallahi baku da kirki! Wai mesa kuke son wareni dan Allah? Ko dai baku d'aukeni kamar yanda na d'aukeku ba?"
     Saurin dod'e mata baki miemie ta yi ta k'irk'iro murmushi ta ce "Haba wane mutum! Wallahi yanda kika d'aukemu haka muma muka d'aukeki. Ai ke kika ce zaki je Rerbee'art house ko? To daga nan mu kuma sai muka zauna. Albishirinki k'awata."
   "Goro." Ta fad'a, tuni ta manta da wani b'acin rai, ita dama smart haka ta ke, b'acin ranta na lokaci guda ne, musamman ma ga k'awayenta abin alfaharinta.
      "Fari ko ja?" Miemie ta sake tambayarta.
     "Fari tas!" Ta fad'a tare da karkad'e kunnuwanta.
    "Dr. Aliyu Haidar da na ke baki labari."
    "Ehh na ji dai k'awata. Ba dai shi ma ya kamu ba..."
     "K'awata wuyata da ke baki iya cin ribar zance ba. Just keep quite yanzu zan baki labari."
     Ikram dai kallonsu kawai ta ke tana murmushi, amma fa ta ciki na ciki. Ji ta ke ma yanzu baki d'aya har su Momy da Yaa Khalid d'in sun fita ranta.
      "Ashe yayan Ikram ne uwa d'aya uba d'aya. Yaa Khalid ke bi mishi, sai ita. Kin ga kuwa ai nesa ta zo kusa ke nan."
       Wata irin shewa smart ta saka da k'arfi, rungumar Ikram ta yi tana fad'in "Shi ke nan kuwa, dama haka Allah ya ke nashi ikon! Yau bak'in cikin k'awata ya kau. Ikram ki taimaka mana dan Allah. An ce wai yana son 'yan uwanshi. Idan har kika saka baki tabbas Dr. Haidar zai k'aunaci miemie sosai."
    Kai kawai Ikram ta gyad'a tare da k'wace jikinta tana fad'in "Ni dai kar ki karyani. Na ji to"
      Ko masallacin ma basu je ba, a nan d'aki suka yi sallar, smart uwar yawo kuwa wani d'akin ta tafi ta barsu sai sak'ar zuci su ke, ko wace da kalar tunaninta.
     Da dare Ikram kasa bacci ta yi. Ji ta ke ta tsani kanta baki d'aya. Ashe tare ta ke da family'n wanda *SHI NE SILAR* mutuwar farin cikin rayuwarta. Wanda ta fi tsana a rayuwarta. 'In har na ci gaba da rayuwa a gidan su Momy to tabbas ban wa kaina adalci ba. Kuma ban yi wa ummana adalci ba. Duk irin soyayyar da ta gwada min a rayuwarta? Har ta mutu da soyayyata amma ina rayuwa a gidan su *MAKASHINTA?* Ya zama dole na gudu daga garesu. Na nisancesu wata k'ila hakan ne zai zame min mafita. Matuk'ar na ci gaba da rayuwa a gidan su momy to ba zan tab'a barin bakin ciki ba. Saboda ko ba dad'e ko ba jima Dr. Haidar zai dawo, barin ma ance wata tara zai yi. Idan ya dawo kuwa zan ringa kallonshi, kallonshin da zan yi kuma zai ringa tuno min da shi ya kashe min uwa, ko bai kasheta kai tsaye ba dai *SHI NE SILAR* mutuwarta! Ya zama dole a gareni na san abin yi, yau d'in nan ma ba sai gobe ba.'
       Zumbur ta tashi zaune. D'an guntun hasken da a ke bar masu kunne ta duba, kowa bacci ya ke, a hankali ta fara k'ok'arin saukowa daga up, miemie ce down kuma bata da nauyin bacci ko kad'an.
      Bayan ta samu ta diro ta lalibo fitila a kan locker d'inta, a hankali ta fara sand'o tana tattakawa har ta bar kusa da gadonsu.
       "Ina zaki tafi cikin daren nan?" Ta jiyo muryar miemie ta fad'i haka cikin muryar bacci.
      Baki d'aya tama rasa abin da zata fad'a, miemie na neman b'ata mata plan, bayan kuma bata so kowa ya sani.
     "Fitsari zan yi." Ta fad'a ba dan ranta ya so ba.
     "Shi ne kuma ba zaki tasheni na rakaki ba? Kin fa san halin mutane, idan baki tsoraci aljani ba ai mutum ma abin tsoro ne! Mu je na rakaki." Ta sauko daga kan gadon.
     Dafe kai kawai Ikram ta yi suka nifi ban d'akin. Babu nisa nan da nan suka isa, ta shiga ciki, bata jin fitsarin jawoshi kawai ta yi, ta fito suka koma d'aki.
****

      Washe gari ta kama Monday, haka Ikram ta yini babu walwalar kirki, miemie ma kanta bata da walwalar sosai, smart ta fahimci hakan amma sai ta k'yalesu, ta ce a ranta 'Idan ta yi tsami ma ji.'
     Da yamma bayan sun taso daga evening prep suka kama hanyar dawowa hostel, kallon ginin sosai Ikram ke yi, tana tunanin hanyar guduwa, saboda ta riga ta sama ranta cewa ba zata sake kwana a makarantar nan ba. Dole ta san abin yi.
     Bayan sallar isha'i suka koma, abinci suka ci sannan suka nufi school area kuma don yin night prep. K'arfe takwas a ke farawa a gama k'arfe goma na dare.
      Malaminsu bai zo ba hakan ya sa aka kawo masu prefects wanda zasu tsaresu su yi karatu kuma kar su bari kowa ta yi bacci.
     Sosai Ikram ta ji dad'in haka. Baccin k'arya ta k'irk'ira  ta rufe fuskarta da littafinta.
     Saukar bulala ta ji a fuskarta hakan ya sa ta zabura da 'karfi tare da yin mitsi mitsi da ido kamar gaske baccin ta ke.
      "Fita waje ki yi tafiya, daga class d'in nan zuwa SS3, ki ce wai Social prefect ta zo in jini. Saura kuma ki je ki yi zamanki."
     Wani irin dad'i ta ji a ranta. Purse d'inta ta lalubo ta mak'ale a wandonta sannan ta fita tana tafiya a hankali dan a ce baccin ta ke yi.
     "Ki saki jiki ki yi tafiya. Minti biyu na baki kuma ki dawo." Prefect d'in ta fad'a.
     Fita kuwa ta yi, kai tsaye ta nufi hanyar da katangar makarantar ta ke. Ta yi tafiya mai nisa kafin ta isa. Kallon katangar ta yi sosai, tana da tsawo sannan kuma zagaye ta ke da security wire. Ajiyar zuciya ta sauke tare da dafa katangar tana k'ok'arin hayewa.
    "Hey! Who is there?" Ta ji an fad'a da k'arfi...

Vote me on wattpad: Princess Amrah

SHI NE SILAH!Where stories live. Discover now