*SHI NE SILA!*
😪😪😪Na Princess Amrah
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
(2018)_Ina kike Hafsy Ƴar mutan Gusau? Yau shafin kyauta ne gare ki domin farin ciki da jin daɗinki. Soyayyar da kike wa *SHI NE SILAH!* har ta wuce misali. Su Ikkey na gaishe ki kyauta ba da ko sisi ba._
71~ A falo suka tsaya bayan sun ajiye ledojin da su ke riƙe da su. Husnah da Ashnur ne suka riƙo Ikram da ke rufe da ƙatuwar hijabi kalar ruwan madara ta saka fuskarta a wuyan hijabin.
Sauran ƙawayen wanda aƙalla zasu kai goma sha biyu suka biyo su. Ciki har da Miemie da ke ta sakin murmushi.
A kan doguwar kujera Khalid ya ke zaune, hakan yasa suka zaunar da itama Ikram ɗin a kujerar kusa da shi.
Salim ne ya ce "Wani ya mana addu'a."
Abokin Khalid mai suna Sultan ne ya gabatar da addu'ar sannan suka shafe.
Nasihohi sosai Salim ya ma ango, bayan ya gama Miemie ma ta yi ma amarya iya tata huɗubar wadda ta sani, daga baya Khadija candy ta ɗora da tata.
Bayan sun gama kuma sai aka hau barkwanci. Salim na faɗin "Daga nan kuma sai gidan wa?"
Cike da kunya Miemie ta duƙar da kanta ta ce "Ni dai yaya ce ba ƙanwa ba." Duka aka saka dariya.
Ƙarfe sha ɗaya saura kwata suka miƙe, ɗakin Ikram suka miyar da ita tare da ƙara mata wasu huɗubobin masu kyau sannan suka ƙara gaba Ikram na ƙara yi masu godiya. Cikin wasa Husnah ta ce "Sai mun zo cin kaza gobe." Harararta Ikram ta yi ta ce "Ƴar rainin hankali. Babu dai abin da zai faru kin fi kowa sani."
Husnah ta ce "Ko bai faru yau ko gobe ba dai dole sai ya faru." Ta fice da sauri dan a lokacin sauran duk sun fita.
Har bakin gate Khalid ya rakasu, abokan angon suka tafi da ƙawayen amaryar dan dama su duka ukun kowa da motarshi ya zo. Miemie kuma dama ta kira Haidar yana waje yana jiranta ta same shi a motar Marwan suna tafi.
Bayan ya rufe gidan ya koma ciki. Tun daga falo ya cire babbar rigarsa wadda ya sanyo a gidan su Salim, sannan ya shiga ɗakinta da sallama ƙunshe a bakinshi.
Zaune ta ke ta rufe fuskarta. Sai dai kuma yanzu ta cire wancan hijabin ta yafa wani gyale mai shara-shara da duwatsu manya jere a jikinshi.
Amsa sallamar ta yi ba tare da ta ɗago kanta ba. Murmushi ya yi ya ce "Amarya bakya laifi. Amma fa in dai baki buɗe mayafin nan ba zaki iya yin laifin."
Shiru ta masa sai dai murmushi da ta ke wanda ita kaɗai ta san tana yinshi tun da kanta a duƙe ya ke.
"Ki tashi mu gabatar da sallar godiya ga Allah da ya cika mana burinmu a lokacin da bamu taɓa tsammani ba daga ni har ke ɗin." Ya faɗa cike da soyayya.
Sai a lokacin ta ɗago kanta a hankali idanuwanta suka sauka bisa kyakkyawar fuskarsa mai cike da ƙwarjini da kamala.
"Irin wannan kallo haka ai sai kisa na sume." Ya ringa dafa zuciyarshi.
"Ahh to bara na daina kar na sumar da miji..." Ta dafe bakinta bata ƙarisa maganar ba.
Zama ya yi kusa da ita a bakin gadon ya ce "Me hanaki ƙarisa maganar ko kunya kike ji?"
Saurin ɗaga mishi kai ta yi tana murmushi.
"Kunyar wa kike ji? Ba dai tawa ba ko?" Ya faɗa a hankali.
Nan ma kai ta kuma ɗaga mishi tana murmushi.
"Hmm! Zaki barta." Kawai ya faɗa haɗe da miƙewa. "Tashi mu yi sallah ga abinci nan ki ci. Dan na san rabonki da abincin kirki kin jima."
Cikin kunya ta ce "Ka je ka yi kawai."
Da mamaki ya ce "Ke kuma fa? Ko sai na fito zaki shiga?"
Kai ta ɗaga tare da saurin sunkuyar da kanta.
Shiga banɗakin ya yi babu jimawa ya ɗauro alwalar ya fito yana goge ruwan fuskarshi ya ce "To malama Ikram na fito a je a yi."
Duk rashin kunyar da ta ke ma Khalid sai ta neme su ta rasa. Wata irin kunyarshi ce ta mamaye ilahirin zuciyarta. Ta ma rasa ta hanyar da zata faɗa masa bata yi.
Da ƙyar ta iya daurewa ta ce "Ina hutun sallah."
Sai a lokacin ya gano dalilin da yasa ta ke ɗan nonnoƙewa.
Tashi sallar ya yi ba tare da ya ce mata komai ba har ya gama.
Rigarshi ya cire ya zama daga shi sai singlet da wandon shaddar yana faɗin "Ashe abin da ya faru ke nan amarya. Wannan baƙo kuwa bai iya zuwa ba." Yana murmushi.
Murmushin ta yi itama ta ce "kai da baka da lafiya?"
"Ke ni fa na warke tun isowata ƙasar nan ɗazu. Garas na ke babu abin da ba zan iya ba, musamman..." Ya yi shiru daga nan.
Falo ya nufa ya ɗauko ledojin ɗazu. Buɗewa ya yi, ta farkon kaji ne guda biyu gashin injin. Ta biyun kuma lemuka ne kala-kala. Ta ƙarshen ita ce wadda ta fi girma, kayan tea ne tun daga madara, milo, ovaltine da kwalin sugar cube ɗin nan.
Kitchen ya nufa ya kai kayan tea ɗin sannan ya ɗauko plate guda ɗaya da cups biyu ya dawo.
"Sannu Yaya Khalid. Sai hidima ka ke." Ta faɗa a hankali.
"Ba dole na yi hidima da matata ba?" Ya faɗa haɗe da kanne mata ido ɗaya.
"Allah ka daina ni kunyarka na ke ji." Ta faɗa cikin muryar shagwaɓa.
"Ba kunyata kike ji ba? Na miki al-ƙawarin zan fitar miki da ita." Ya bata amsa yana fito da kajin daga leda yana ɗorawa a plate.
Bayan ya ajiye a gabanta bisa gadon ya zubo lemon freshyo a cofi ɗaya, sannan ya zuba sprite a cofi ɗaya. Mai Sprite ɗin ya miƙa mata ya ce "Na sanki da son sprite. Aje shi daga can dan kar zakwaɗi yasa na zubar miki. Ki ci kazara sannan ki sha tun da mai gas ne ba'a shanshi ba'a ci komai ba."
Ikram ta ce "Ni fa Yaa Khalid na ƙoshi."
"A'a kar mu yi haka da ke. Ki ci tun kafin ni in baki da kaina."
Hannu tasa ta ɗauko gaɓa ɗaya ta kazar amma ta kai minti biyar a hannunta ta kasa kaiwa bakinta. Ganin haka yasa ya karɓa ya ci gaba da bata a hankali tana ci saboda dama yunwa ta ke ji. Tun kunun safe da momy ta kai mata rabonta da cin komai.
Ta ɗan ci ba laifi kafin ta ce ta ƙoshi. "Ki ɗan ƙara kaɗan wifey." Ya faɗa alamar magiya.
"Allah kuwa na ƙoshi yanzu dai." Ta bashi amsa.
"To na yarda. Ɗauki lemon ki sha."
Bata musa mishi ba kuwa ta ɗauka ta kai bakinta. Sai da ta shanye tas sannan ta ajiye kofin tana faɗin "Na gode."
Kallonta ya yi ya ce "You are always welcome wifey. Sai ki tashi mu koma wancan ɗakin dan da alama shi ne nawa ko?"
Bayan ta kalli inda ya gwada nata da hannu ta ce "Shima nawa ne. Naka na can side ɗin da falo ya ke."
Da mamaki ya ce "Ahh lallai mu ƴan gayu ne. To tashi mu tafi can ɗin."
Babu musu ta yi gaba ya bi bayanta saboda ita ce ta san ɗakin.
Suna isa nan ma bedrooms biyu ne, na daga hannun daman suka shiga wanda gado ne ƙirar royar, light brown ce kalarshi. An shimfiɗa wani dakakken zanin gado mai matuƙar kyau kalar light blue kamar yanda ko ina ya ke a gidan.
"Da wannan kayan zaki kwana?" Ta ji muryar Khalid ya tambaye ta.
Kai kawai ta ɗaga haɗe da hayewa bakin gadon ta makure a zuciyarta sai mamaki ta ke; wai a ce yau ita ce zata kwanta daga ita sai namiji a ɗaki ɗaya, a matsayin mata da miji. Idonta ta runtse tana mai ƙara godiya ga Allah daya aurar da ita ga wanda ta ke so kuma ya ke sonta.
Sai da ya cire wandon shaddar sannan ya kashe wutar ɗakin ya haye bisa gadon yana faɗin "ki saki jikinki ki kwanta, babu abin da zai faru kin ji? Nima wasa na ke miki ko lafiyarki lau ni jikina har yanzu babu daɗi sosai."
Jin hakan ya sa ta ɗan saki jikinta ta kwanta.
Asuba ta gari Ikramkhalid.
YOU ARE READING
SHI NE SILAH!
Romanceshi ne silar rugujewar farin cikin rayuwarta. shine silar shigar ta cikin kunci da bakin ciki. shi ne silar rashin gata hadi da galihu a rayuwarta. shin waye silah? ku biyoni a cikin wannan labarin inda zan warware maku zare da abawa.