32

1K 58 0
                                    

*SHI NE SILA!*
           😪😪😪

              Na Princess Amrah
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
                           (2018)

32~  Dariya sosai Khalid ya yi bayan ya tsinke wayar, kiran Ikram ya yi a waya ya shaida mata abin da ya faru, ita ma ta bashi labari nan suka sha dariya sannan suka yi sai da safe kowa ya kwanta.
     Washe gari da sassafe Ikram ta bud'e data, sa'kon Abbas ta fara gani ya rubuta mata "Hy Nadiya. Abbas ne."
    D'an guntun murmushi ta yi sannan ta miyar masa da "Ok." Kawai.
    A lokacin baya online saboda ta duba last seen d'inshi tun jiya suna gama waya ya turo mata. Sauka ta yi sannan ta fita parlor ta gaishe da momy.
    Kiran Abbas ne ya shigo a wayarta hakan ya sa ta d'an saci kallon momy ko tana kallonta, ganin hankalinta baya ma wurin ya sa ta d'auka a hankali ta yi magana. "Hello Abbas." Wani sassanyar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce "Ya kike Nadiya?"
    "Lafiya." Ta fad'a a tak'aice.
    "Jiya na kwana da tunaninki, har da mafarkinki sai da na yi yanzu na hau charting..." tun bai gama fad'i ba ta ce "Ok mu ha'de yanzu." Ta tsinke kiran.
    Data ta bu'de sannan ta shiga watsapp, nan fa suka hau charting da Abbas sosai, ita kuwa sai wayo ta ke masa yanda zata k'ara shiga zuciyarsa.
   Daga 'karshe ya turo mata hotonshi sannan ya ce itama ta turi masa nata.
   "Inyee, lallai kana da kyau sosai Abbas, ka cijeni, wannan wanka haka." Ta yi dariya sosai saboda yanayin hoton irin na 'kauyancin nan ne, har da d'ora fuskarshi a kan hannayenshi, ga wata tsayuwa da ya yi shi a dole ajawo.
   Har sai da momy ta ce mata "Dariyar me kike haka Ikram? Da alama dai duniyar ta miki da'di."
    Da k'yar ta samu ta tsayar da dariyar sannan ta ce "Wallahi kuwa momy.."
    Katseta momy ta yi ta ce "To a yi dariya da kyau 'yan matana."
     Sake rubuta mashi ta yi "Sai dai kuma ni bani da kyau, dan Allah idan ka ga hoton ka goge dan kar ya ringa baka tsoro cikin dare."
    "Ni dai na ji Nadiya, ki turo min please."
     Wani hotonta wanda ta yi masifar kyau ta tura mishi, ranar da aka fara yi masu practical na make up da fuskarta aka fara kuma an d'auketa hoto, sosai sifarta ta larabawa ta bayyana. Ta saka glasses irin babban nan amma kuma fari ne ana ganin k'wayar ido, ta sha d'aurin d'an kwali kamar wata amarya, ga jan lalle a hannunta dan dama da wuya a rabata da lalle.
    Bayan ta tabbatar da hoton ya je ta kashe data d'inta tare da hawa up stairs dan ta san dole sai ya kirata.
    Tun bata k'arisa shiga d'akin nata ba kuwa kiranshi ya shigo, d'auka ta yi ta ce "Hello Abbas, ka ganni ban maka ba ko?"
    "Haba mana Nadiya, wallahi ki ringa godewa Allah. Yanzu duk wannan baiwar kyawun halittar da Allah ya miki baki gode ba? Bari ki ji wani abu, ni tunda na ke a rayuwata ban ta'ba ganin kyakkyawa kamarki ba. Ke ko a kallo ma kyawawa irinki k'alilan ne. Kareena Kapour uwar 'yan kyau ma kin zarceta.." yana neman ci gaba da magana ne Ikram ta katseshi da cewa "Abbas wannan zuzutawar ta isa haka. Ai sai kasa kaina ya fashe."
    "Ba maganar zuzutawa sai gaskiya. Wlahi Nadiya ke mai kyau ce, ina masifar sonki. Dan Allah kema kina sona?"
    "Ina sonka mana Abbas, ai tun da naga hotonka nima na ji ka sace min zuciya. Ina matuk'ar k'aunarka. Amma kafin komai dai ina neman wata alfarma a wurinka."
     Da sauri ya ce "Zan miki wannan alfarmar kuwa komai tsananinta."
     Ta ce "Ina so mu yi soyayya mai cike da aminci da kyautatawa. Duk wani abu da na ke so ka yi min shi da gaggawa. Ka amince?"
     "Na miki alkawarin zan yi komai kike so Nadiya." Ya fad'a.
     "Na ji dad'i sosai kuwa. Kamar yanda na fad'a maka cewa soyayya na ke so mu yi da kai cikin sirri bana son kowa ya sani, amma da zarar na gama makaranta sai ka turo a yi maganar aurenmu ko?"
    Sakin baki ya yi cike da farin ciki, jinshi shiru ya sata fad'in "Ya dai, ko hakan bai maka dad'i ba ne?"
    "Ya min da'di mana Nadiya. Tsabar k'aunarki ce kawai ta sani yin shiru."
    Wayar soyayya suka ci gaba da yi har sai da ta fara jiyo motsin taku alamar ana nufo d'akinta, da sauri ta masa bankwana tare da tsinke wayar ta fita. Daidai zata fita sai ga Naanah. Murmushi ta mata ta ce "Hajia ta ce na kiraki ki karya."
   "Dama kuma ina k'ok'arin saukowa ke nan. Mu je to." Ta yi gaba.

SHI NE SILAH!Where stories live. Discover now