13

1.1K 73 4
                                    

*SHI NE SILA!*
           😪😪😪

     Na Princess Amrah
              (NWA)
               2018

   _wannan shafin sadaukarwa ne gareki my dear Ashnur Pyaar, You mean alot to me, Allah ya bar min ke ya raya miki zuri'a baki daya._

13~ Tafiya kuwa ta yi, babu tantama ta isa har Office d'inshi, wani mutumi ta gani tsaye a bakin k'ofar alamun shi ke gadin wurin,
    "Sannu Mallam, dan Allah nan ne Office d'in Dr. Aliyu Haidar?" Ta tambayi mutumin.
    "Ehh nan ne, lafiya?"
   "Ba lafiya ba, ni dai ina son ganinsa please idan yana nan."
    "Ba zaki samu ganinsa ba yarinya, saboda bai fad'a min akwai wacce zata zo nemansa ba, dama kuma in har bai fad'a ba to dokarsa ce wannan, babu wanda zai shigar masa office ko da kuwa ma'aikatan wurin nan ne sai dai su bayar da sak'o na fad'a masa, idan ya bada izinin su shiga sannan na barsu su shiga d'in."
    Kuka Ikram ta fasa tana masa magiya, "dan Allah ka taimaka min, wallahi mahaifiyata ce, bata da lafiya bana so na rasata."
    "Ki yi hak'uri ki tafi, wannan umurni ne daga yallab'ai ba daga ni ba." Ya fad'a.
    "Ka taimaka min, Manzon Allah (SAW) Ya ce; duk wanda ya ji k'an wani shi ma Allah zai ji k'ansa." Jin haka yasa mutumin d'an jinkirtawa kafin ya ce "duk abin da zan wa mutum da zarar ya ambaci sunan manzo sai na ji baki d'aya jikina ya mutu, saboda haka zan barki ki shiga, amma da sharad'i, ki ce masa lokacin da kika zo baki samu kowa ba, tunda kin ga yanzu lokacin sallah ne, barin tafi masalla..." bai k'arisa fad'i ba ya ji k'arar bud'e k'ofa.
    Shiru ya yi cike da tsoro da fargaba jikinsa sai rawa ya ke kar a ce Dr. Aliyi ya ji maganar da ya ke. Cikin sa'a kuwa ashe bai ji ba, bai ko kula da Ikram da ke tsaye ba ya ce "Musa a gyara min Office d'in nan na ga ya d'an fara yin datti, ka kula kar ka hargitsa min kaya, ka san bana son na ajiye abu na tarar da shi ba a wurin ba."
    Kallo Ikram ta bishi da shi. Rataye ya ke da bak'ar suite sai fara a jikinsa da bak'in wando, idonsa sanye da dark glasses wanda ko k'wayar idonsa baya bayyanawa, matashi ne kyakkyawa very giant wanda duka shekarunsa ba zasu wuce talatin ba.
    "Musa wannan fa, wa ta ke jira?" Ya tambayi Musa masinja bayan ya kula da Ikram da ta zuba masa ido tana kallo.
     "Yallab'ai nima ban sani ba, ta dai ce min wai tana son ganinka shi ne na ce baka san da zuwanta ba ba zan barta ta shiga ba."
     "Ok." Ya fad'a had'e da k'ok'arin tafiya.
    Dakatar da shi Ikram ta yi ta hanyar fad'in "Dr. Dan Allah ka tsaya ka saurareni..."
    Tsaki ya yi ya ci gaba da tafiyarsa, saboda ya tabbatar da cewa 'yar neman alfarma ce, ya saba da irinsu kuma dama.
    Sauri ta yi ta tari gabansa ta ce "ka saurareni Dr."
    Kai ya gyad'a sannan ya ci gaba da tafiyarsa.
    "Dr. Aliyu Haidar." Ta fad'a da k'arfi. Har cikin zuciyarsa ya ji kiran da Ikram ta masa, hakan ya sa ya tsaya cak ba tare da ya waiwayo ba.
    Gabansa ta kuma sha tare da duk'awa har k'asa tana kuka ta ce "ka rufa min asiri kamar yanda Allah ya rufa maka, ka taimaka min Dr. Allah kad'ai ya san ladar da zaka samu, ka ji k'an mahaifiyata ka mata aikin nan yau, nurse ta ce wai appendix yana daf da fashe mata, kuma kace idan har ya fashe zai iya gurb'ata mata da kayan cikinta, dan Allah ka tausaya mana Dr. Wallahi ina son Ummana, ita kad'ai gareni, bani da kowa da ita na dogara." Ta kama hab'ar wandonsa tana kuma fad'in "da Allah na had'aka Dr. Bani da ku'din da zan iya biyanka, Allah ne kawai zai baka lada, taimakon rai ne zaka yi."
     Cikin sanyin murya Dr. Aliyu ya ce "ki sakar min wando tun kafin na wulak'antaki, an fad'a miki an tab'a samun irinki wadda zata min haka ne? Ko a haka aka tashi kin zama babbar mai sa'a."
    Sakinshi ta yi amma bata fasa yi masa magiya ba.
    Da k'arfi ya daka mata tsawa, "na fiki sanin halin da ta ke ciki saboda ni na dubata kuma na mata scanning, sannan kuma na fiki sanin illar appendix ya kumbure, dan haka ki k'yaleni, ina da abin yi na ce sai gobe zan mata aiki." Ya fice abin sa bai kuma fad'in komai ba daga nan.
      Har ya bar wurin Ikram bata daina kuka ba, bata kuma tashi daga tsugunin da ta yi ba.
     Musa Masinja ne ya iso inda ta ke ya ce "ki tashi ki tafi yarinya, wannan kukan da kike ba shi zaisa ko kad'an yallab'ai ya tausaya miki ba, idan ya yanke magana ta yanku ke nan babu tashi, tunda dai ya ce sai gobe ki je ki mata addu'a, insha Allahu zata samu lafiya."
    Tashi kuwa ta yi babu musu ta tafi, a cikin zuciyarta tana tir da hali irin na Dr. Aliyu, zuciya k'ek'asasshiya wadda babu ko kad'an d'in tausayi a cikinta. "Na tsaneka Dr. Aliyu bana sonka, me ake da mutane marasa imani irinka?" Ta fada a bayyane.
   Tana tafiya har ta buge wata mata bata sani ba, ko da ta ankara hak'uri ta bata sannan ta isa d'akin da aka kwantar da Ummanta, ga kayansu zube an aje kusa da gadon.
      Drip ne d'aure a hannunta, baccinta kawai ta ke shara kamar ba ita ce mara lafiya ba.
      Bata san sanda ta saki murmushi ba, ganin Ummanta ta samu bacci ya bata tabbacin ta samu sauki.
     Toilet ta nema ta d'auro alwala sannan ta zo ta gabatar da duk sallolin da a ke binta.
    Bayan ta gama ne kuma yunwa ta fara tambayarta, tashi ta yi ta nufi wurin zaman nurses, tambayarsu ta yi inda zata samu abincin siyarwa amma wata nurse ta ce mata "gaskiya yanzu dai kam babu inda zaki samu a nan ciki sai dai idan waje zaki fita, kuma fita babu wanda zai rakaki zai iya zama matsala. Gwara kawai ki hak'ura idan dai ba yunwar ta addabeki sosai ba."
     "Kin ga wani abinci nan sauran na Jalilah, babu dai yawa." Wata dayar nurse ta mikawa Ikram.
     Jiki na rawa ta karb'a tana godiya sannan ta koma wurin gadon Ummah.
       Bayan ta ci abincin ne ta kishingid'a k'asa bacci mai nauyi ya d'auketa saboda ta gaji sosai.
     Can tsakiyar dare ciwon Umma ya tashi, sosai cikinta ya ke ciwo, magana ma gagararta ta yi, gashi kuma Ikram k'asa ta ke kwance.
      Cikin sa'a sai ga nurse ta zo ta duba ko drip ya k'are ta canza wani, salati ta d'auka da ta ga Umma rik'e da ciki sai hawaye ta ke.
     A razane ta bubbuga Ikram firgigit kuwa ta tashi,
    "Ina amfanin irin wannan jinyar? Majinyaci da aka sani da kula da mai ciwo?"
      "Innalillahi, wallahi ban sani ba bacci ya da'ukeni, Umma jikin ne?"
     Kai Ummah ta d'aga mata a hankali ruwan hawaye na zirara daga idonta.
       Nan da nan Nurse din ta kira abokiyar aikinta, nan fa suka ci gaba da kula da lafiyar Umma, sannan suka mata allurar bacci, babu jimawa kuwa wani baccin ya d'auketa.
     D'ayar nurse d'in ce ta ce "ai dama in dai allurar baccin nan ta saketa ta tashi to tabbas da ciwon cikin zata tashi, sai idan an rabata da mugun abin nan ko zata samu sassauci."
     D'ayar ta ce "wallahi Dr. Aliyu bai da mutunci ko kad'an, ashe ma wai shi da kanshi ya dubata amma wai ya k'i ya mata aikin a lokacin saboda wani uzurinshi wanda bai kai ya kawo ba. Allah dai ya shiryeshi ya sa ya gane gaskiya." Suka tafi.
      Ikram ta koma bisa kujera ta zauna, banda kallon Ummanta babu abin da ta ke yi, cike da tausayi hawaye na zuba daga idonta. Tun daga wannan lokacin bacci ya yi k'aura daga idonta, ko rintse bata sake yi ba har sai da asuba ta yi aka fara kiraye kirayen sallah.
   Umma kam baccinta kawai ta ke yi, bata kuma farkawa ba har sai da gari ya waye ta tashi.
    "Sannu Umma kin tashi? Ki samu ki yi sallah ko na jiya baki yi ba, idan ba zaki iya ba sai ki yi daga kwance."
    "To Ikram, samo min dutse na yi taimama daga kwancen sai na yi sallolin."
    Tashi Ikram ta yi ta samo mata dutsen, taimamar ta yi sannan ta gabatar da duk sallolin da a ke binta.
     Bayan ta gama ta samu har Ikram ta samo masu abin kalaci, tea da bread ne sai soyayyen kwai ta siyo,
     Ita ta ringa ba Umma a baki duk da fadin ta ke ta koshi amma Ikram ta tilasta mata akan sai ta ci. Bayan ta gama bata ita ma ta ci nata.
     K'arfe goma na safe aka kawo wa Umma riga da hula ta saka wai za'a shiga theatre da ita, duk da lafiya ce za'a nema mata amma bai hana Ikram fasa kuka ba.
     Bayan ta saka rigar aka tafi theatre room da ita, Ikram na biye dasu har bakin k'ofar d'akin. Ciki aka shiga da Umma ita kuma Ikram ta tsaya tana ta faman kuka har da shessheka.
   Tana cikin haka ne Dr. Aliyu ya zo shima sanye da rigar theatre da mask ya rufe bakinshi da shi, biye da shi kuma wani nurse ne namiji rik'e da kayan aiki shima da irin shigar da Dr. Aliyu ya yi.
     Kallon Ikram ya yi ya gyad'a kai, a ranshi yana tunani jiya jiyan nan ta ke rok'onshi ya taimaka ya ma ummanta aiki, yau kuma gashi zai mata amma kuka ta ke masa.
     Ita kuwa a ranta wani irin k'ara tsanarshi ta ke yi, tun da ta ke a rayuwarta shi ne mutum na uku da ta ma irin wannan tsanar, daga mahaifinta Halle, sai Goggo Indo sannan shi.
     Zaune ta yi ta buga tagumi, a wannan lokacin har da kukan ma ta daina sai kukan zuci da ta ke yi.
   Shiru shiru ba'a fito aiki ba har kusan 5 hours, ko da yake dai dama aiki in dai har da na kidney stone akan d'an jima ana yinsa.
     A cikin theatre room kuwa likitoci hud'u da nurses hud'u ne a kan Umma suna mata aiki, Dr. Aliyu ne shugabansu, bayan  ya yankata ya fara bubbud'o daidai inda appendix d'in ya ke, nan ya ci karo da appendix ya yi kaca kaca a cikin hanjinta, tun daga k'asan hanjin har sama sama ya b'aci da shi. Shi kanshi Dr. Aliyu d'in hankalinshi ya tashi, barin sauran abokanan aikinsa da suka gama rud'ewa da ganin haka.
     Da k'yar ya samu ya tattaroshi, ya fitar sannan ya koma ga aikin kidney. Ba kad'an din lokaci aka d'auka ana aikin ba. Tun goma da rabi aka fara amma sai bayan azahar aka gama kusan k'arfe uku na rana. A lokacin Ikram ta ci kukanta ita kad'ai babu mai tayata.
     Ta duk'a ta had'a kai da guiwa ne ta ji k'arar gado, da sauri ta d'ago kanta nan ta ga Ummanta kwance idonta biyu saboda irin aikin nan wanda ake yi a farke ne aka mata. Murmushi Umman tata ta mata a hankali, cike da jin dadi ita ma Ikram ta miyar mata da murmushin sannan ta bi bayan mai turin gadon. Ta jima bata yi farin ciki kamar wannan ba har aka isa dakin da ita aka kwantar kan gadon sannan suka fito, nurses din ne suka daura mata drip sannan suka fice. Ikram tsananin farin ciki ta kasa zaune ta kasa tsaye, sai jara godewa Allah ta ke yi.
@wattpad: PrincessAmrah

SHI NE SILAH!Where stories live. Discover now